Showing 327001 words to 330000 words out of 450388 words

Chapter 110 - Gudun Aure Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

4066

ya tsaya mini a raina. Anti Yagana na kira muka gaisa jin maganata da kasala ya sanya ta fara jero mini tambayoyi na ce."lafiyata lau amma ina zargin ciki ne da ni.'
Ta ce." Ba ki na zargi ba kin tabbatar kuma kin gayawa mai shi ko?"
Yar dariya na yi domin nasan dalilin da ya sanyata ta fad'i haka tunda artabun da aka sha a baya na ce.'' Na tabbatar gaskiya shi din ne smma yanayi bai barni na sanar masa ba amma zan gaya masa yau idan ya dawo ya je bunkure wajan Malam D'aha."
Babu tsammanin kawai na ji ta rufe ni da fad'a. Sai da na bari ta gama na ce." Lokacin da na samu cikin nan fa yana kwance anti Yagana bai ma san a inda yake ba yanzu ne ya dan fara dawowa hayyacinsa babu abinda zai faru in sha Allahu."
Ta sauke ajiyar zuciya kad'an tana fad'in.'' Duk da haka dai Amina tunda kin san halin mijinki da zargi mussaman idan kin samu ciki kamata ya yi ace yanzu ya sani tunda ai ya jima da dawowa nutsuwa ba ki da wata hujja anan."
Na ce." Ki yi hakuri zan gaya masa in sha Allahu anti Yagana ni akwai dalilin da ya sanya ma na kira ki yanzu."
Ta ce." Menene kuma?''
Hanci na dan ja a sanyaye na furta." Hauwa ce take jingina rasuwar Hajiya Maryam da ni." Duk na kwashe sa'insar da muka yi da ita na gaya mata .
Ta ja tsaki tana fad'in." Ta dawo ashe?''
Na ce.''kwarai ta dawo amma ta ki yadda mu zauna lafiya fitinar yau daban ta gobe ma daban tana daga mini hankali wallahi domin ni yanzu anti Yagana babu abinda na fi buk'ata face zaman lafiya duniyar nan tsoro take ba ni."
Ta furta." Kin ga Amina idan za ki kwantar da hankalinki ki kwantar ina abin yake me yasa Hauwa zata razanaki har ki dinga jin fargaba a kanta. Ban yarda ki zalinceta ta kowace siga ba amma ki daina raga mata balle ta hangi lagonki ta raina ki tunda ita Yar iska ce mara mutunci to sai kema ki sanya rigar rashin mutuncin ku buga aga wanda zai ci riba ina dalilin wannan masifar."
Na ce." Anti Yagana ai na riga na yi wa Hajja alkawari ba na so na biye mata wata matsalar ta faru wadda Hajja za ta ji haka kawai dattijiwar take ba ni tausayi wallahi a ganina idan nima na biyewa Hauwa kin ga mun zama sakarkaru gabad'aya kuma maigidan ba zai samu nutsuwa ba.''
Ta ce." Ai ba cewa na yi ki biye mata ba Amina ki fita daga harkarta ki daina raga mata ko ki nuna mata kina son zaman lafiya da ita. Kuma ki yi duk yadda za ki yi wajan ganin kin sake samun gurbi a zuciyar mijinki abinda nake nufi kenan."
Na ce." Ni ma shawarar dana yanke kenan wallahi."
Ta furta." Dada kuwa ba ta da lafiya sosai Amina har sai da ta kwanta a asibiti kwananta biyu jiya aka sallamota."
Da damuwa mai yawa na furta." Mai yake damunta ne?"
Ta ce." Lalura ce kawai irin ta girma da shekarun yau ta ce kafafunta na ciwo gobe ta ce bayanta ya 'kage abinda dai ya tsananta a ciwon har ta kwanta a asibiti ciwon wuya da ta yi eanda ta kai ta kawo ma ba ta iya motsa wuyan ya 'kage amma yanzu alhamdulillahi da sauki."
Cike da tausayinta na ce.'" Allah Ya sawwa'ke idan ya dawo zan gaya masa wata'kila mu zo dubata. Anti Yagana ina labarin Ya falmata ne ko a Whasap na jima ban gan ta ba kuma mun jima ba mu yi waya ba.
Ta ce." Ai Ya falmata tana saudia neman kud'i Baban Saude ya shige mata gaba wajan mahukunta sai da Alhaji Bana ya sake ta."
Na ce.'' To kin ga wannan shine adalci ai ko banza ana samun jajurtatun iyaye a family kamar irinsu Baban Saude da yawa mazan da suke zalintar matayensu za su shiga hankalinsu.
Abinda ya faru shine kowa ya san da cewar Ya falmata macace mai zafin nema domin ni kaina itace madubina kuma sai da na takata tukkuna na tashi. Harkokinta sun bukasa sosai a lokacin da muka had'a karfi da k'arfe domin gina gobenmu muka tashi a tare. Tun bayan da na yi auran nan sai kasuwancin da muka yi da ita ya raunana dalili duka ta nuna mini hanyoyin yadda zan dogara da kaina da kuma yadda kayana za su cigaba da zaga 'kasashen waje irinsu sinigal nijar mali kamaru da chadi har ma da saudiya dama kusan sune suke sayan kayanmu a lokacin da muke fafutar ganin mun tashi manyan matan abuja ma suna saye amma duka ta hanyarta tunda ni ce mai aikin dinkawa na yi mata odarsu zuwa maiduguri ta rarraba a sassasa daban-daban.
Ta cigaba da kujiba-kujibarta ni ma na cigaba da yin tawa har Allah ya sanya ta bude katafaran shago ta zuba iyayen kekunan d'inki manyan kai da k'ananu ya yara suna aiki. Shekara daya ta sake bude wani a takaice dai sai da shagunanta na d'inki suka kai biyar kuma shago bai wai karami ba wanda yake iya cin sama da keken d'inki goma sha biyu.
Mijinta Alhaji Bana shine silar karyata domin had'a ba ki ya yi wasu daga cikin yaranta suka dinga kwashe mata kaya cikin dare suna fita da su a baggo. Idan suka sayar su raba kudin kashi uku shi ya d'auki kashi biyu yaran su d'auki kashi daya. Wataran rigima ta shiga tsakanin yaran nata da suke aikata mata haka har da makami abinda ya assasa musu zuwa gaban hukuma kenan daga nan sai suka fara tonawa junansu asiri dama kuma gefe guda ta sanya Malamai ana ta yi mata ro'kon Allah itama ta tsananta da addu'a. Suka fadi mijinta ne me sanya su da ya ji duka da matsa ya tabbatar da sanya hannunsa wanda da da farko ya fara gardama da jayayya yana fad'in yaushe zai kai matarsa k'asa uwar yaransu har biyu. Daga lokacin ne ta yi tsalle ta dire ta ce sai ya saketa har suka shiga kotu alkali ya yanke musu hukunci daidai da abinda suka aikata ya kuma tilastashi sakinta tunda gaskiya ba namijin da kowace mace za ta yi sha'awar zama da shi ba ne.
Anti Yagana ta cigaba da cewa." Ai tana fita idda ta lallaba Dada ta tafi makka wata shida fa yanzu tun bikin Fadila
Na ce." Allah sarki Ya falmata zuciyarta a tsaye take irin ta Baban Saude ba ta son zama koyaushe tunaninta ya za a yi ta juya biyar ta koma goma. Amma ni da ta yi shawara da ni zan ce mata ta yi zamanta anan ta cigaba da sana'arta kamar zai fi alheri."
Ta ce." To ta dai ce shekara uku kacal za ta yi ta dawo sai dai mu yi mata fatan alheri kawai."
Na ce." Ubangiji Allah Ya taimake mu bakidaya anti Yagana ke kuma me ki ke sayarwa?" Na tambayeta cikin sigar tsokana."
Ta ce." Babu komai hankalinta a kwance har sai da na yi dariya na furta.'' Babansu Fadila ne ya tsaya miki anti Yagana shiyasa kike wanke goma ki tsoma biyar ba ki da matsala."
Ta ja tsaki tana fad'in." Amina ai sai mutum ma ya rasa wace sana'ar zai yi wallahi maza daga waje duk sun k'wace mana abin yi."

Na kudi ne littafin don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Na ce." Anti Yagana ba ni so ki kasance daya daga cikin matan nan da barmani coge take yi wa wa'ka (Sakarai baki da wayo) na yi dariya ina fad'in." Ki yi nazarin abinda za ki sayar na baki jari don Allah."
A tak'aice ta furta."Aikuwa na gode sosai ai ba ki ga yadda Fadila take cinikin ruwan sanyi ba cikin nan da take d'auke da shi ya hanata fara zuwa koyan d'inki don har mijin nata ya sayo mata form na makarantar."
Na ce." Ai ni ya burge ni sosai da ya ke so ta yi Sana'a dalili kuwa rayuwa juyawa take yi ga kuma yadda duniyar ta zama komai ya yi tsada tunda karamin ma'aikaci ne za su taimake ki kan su anan gaba"
Ta ce." K'warai kuwa hakane ni ma in sha Allahu zan yi nazarin abinda zan sayar idan na yanke shawara zan sanar da ke."
Da jin dad'i sosai na furta.'' Yawwa anti Yaganata ko ke fa" Dariya ta yi kawai muka yi sallama cike da barkwanci da k'aunar juna irin ta jini.
Wayar mu da anti Yagana ta kara mini karsashi da kuzari na tashi na je na dauro alwalar la'asar ganin uku da rabi har da minti biyar jim kad'an bayan idar da sallata Dr Sailuba ta kira ni ta iso tana falo na ce mata ta shigo d'aki ta same ni mun saba sosai da ita tuntuni.
Ta shigo kamar yadda na buk'ata ta zauna can kujerar dake gefe a d'akin. Na tashi na same ta muka gaisa cikin kulawa na ji dad'i kuwa da ta zo da abin gwajin bf ta yi mini jinina normal bayan ta gama kai tsaye ta tambaye ni ina da ciki na ce mata eh. Cikin raina ina tunanin fa ranar da Hajiya Maryam ta rasu na same shi tunda mun yi kwanciyar aure a daran ranar idan kuwa hasashena daidai ne bai fi kwana arba'in ba tunda itama gobe za ta cika arba'in da rasuwa.
Bayan magriba ta aiko mana da magungu?ana kamar yadda ta fad'a mini kafin ta tafi muka sake yin waya tana yi mini bayanin yadda zan yi amfani da nawa maganin da kuma bayanin na Sultan tunda shi ma ta duba shi kafin ta tafi zazza'bin hak'ori ne yake damunsa magungu?a ta had'a masa masu kyau tana fad'in daga zarar an bashi maganin zazzabin zai sauka don haka muka yin sallama a wayar na tashi na fita da ledar maganin nasa hannuna. Suna kicin ba su fito ba tunda na duba d'akin babu kowa har ita Nusaiban na same a kacame suna ta aikin kwa'ba fulawa har da Mairo dama yaran gabad'aya ganin Nusaiba ya sanyasu zuwa wajenta tunda akwai sabo kuma yadda take hira da yaran ya tabbatar mini da cewa ko a can baya da suke tare da mahaifiyarta bata tsangwame su ba hakan ya nuna sun yi sabo domin da babu kulawa da ja a jiki nasan babu yadda za a yi su je wajenta za su guje ta ne da kallon rashin sani kamar yadda suke yi wa Hauwa.
Da yake kicin ne mai girma mai d'auke da na'urorin sarrafe-sarrafe hakan bai sanya sun takura ba.
Baba Tabawa da Taburni suna ta aikin towon dare kamar yadda na umarta. Mairo da Nusaiba suna kwa'be-kwaben fulawa.
Na saki fuskata sosai Ina kallonsu suna cikin nishadi lallai d'an adam rahama ne a ko'ina sai na rasa ma gaisuwar wanda zan amsa manyan na yi haka zalika ma yaran na yi na bi duka na amsa ina fad'in." Nusaiba wannan funkason zai yi dad'i har miyau na ya tsinke."
Ta kuwa sanya dariya tana fad'in." Kai anti."
Na dubi Baba Tabawa ina fad'in. " Ga maganin Sultan Dr Sailuba ta aiko da shi a bashi abincinsa sai ba shi yanzu."
Rufe bakina ke wuya Hauwa ta shigo kicin din ta fara bin ko'ina da kallo babu wanda ya yi yun'kurin gaisheta Baba Tabawa ta zo zata kar'bi maganin tana fad'in." Jikin nasa da zafi har yanzu." Ta juya da sauri tana fad'in ko dai bari na fara dama masa kamun nasa. Da yake kamu ake yi masa na nikakkiyar gyad'a ya fi son sa akan duk sauran abubuwan da ake bashi kuma shine yake kara masa kuzari da lafiya babu kuma rama a tare da shi.
Na ji maganarta a cushe tana fad'in." Ba shi da lafiya ne?''
Ba tare da na dube ta ba na ce." Eh.'' A takaice na mi'kawa Baba Tabawa ledar magungan kafin ta kar'ba sai ta yi gaggawar warce ledar daga hannuna. Duka muka bi ta da kallo da mamaki.
Ta fito da magungu?an tana duba su. Na zura mata ido da tsananin takaicinta kamar na mangareta haka nake ji a raina wai ita likita amma mara tunani da kangado .
Ta gama duba magungu?an tsaf ta miko mini na kar'ba ina girgiza kaina duk abinda zan yi a yanzu wallahi ba don ita nake yi ba. Baba Tabawa ta kar'bi maganin daga hannuna. Hauwan ta dube ta tana fad'in." Ba ni shi na duba shi."
Sai ta dan dube ni a tsorace wata'kila tana fargabar ta bata shi ya bude ido ya ga fuskarta tunda ta gaya mini ya ta'ba shid'ewa a kwanakin baya.
Na daga mata kai alamar ta kwanto shi daga bayanta ta bata shi kamar yadda ta buk'ata.
Na ji tsakinta tana fad'in." Sai kin nemi izininta za ki ba ni d'ana na gani Baba Tabawa ko kin manta ni ce na haife shi ne ikon Allah sai kallo ni Hauwa"
Babu wanda ya tanka mata Baba Tabawa ta kwanto yaron daga baya wanda ya yi daidai da lokacin da ya bude ido ya fara kusurkusur sai kuma ya sa kuka. Nasa hannuna a wuyansa da zafi.
Itama ta mika hannunta domin kar'barsa kukansa ya tsananta kuwa ta rike shi yana fizga irin ta yara yana mika hannu domin komawa wajan Baba Tabawa. Kukan da yake yi ya tsorata ni sosai ita kuma ta'ki ba bawa Baban shi gashi dai ta fahimci so yake ya koma hannunta. 'Dif!! kamar an yi ruwa an d'auke ya yi shiru jikinsa ya shika lakaf! Idanunsa suka kakkafe. Suma ya yi.... Ta gigice ainun da sai ta fashe da kuka tana kallonmu na yi gaggawar kar'bar shi daga hannunta muka yi tiri-tiri a kicin din har muna bangazar juna ni da ita Baba Tabawa kuwa tuni ta fara hawaye tana fad'in.'' Suma ya yi.
Kafin mu yi wani yun'kurin Taburni ta nufi friji ruwa mai sanyi gaske ta d'auko ta gumtsa a bakinta ta fesa masa da karfin a gaske a fuskarsa ya saki nishi! Numfashinsa ya fara hawa da sauka. Ya motsa kafafunsa. Muka fita daga kicin din a gaggauce ni da su gabad'aya rasa inda zan nufa na yi da yaron a hannuna d'akinsu Baba Tabawa na nufa hankalina a tashe yaron nan ya mutu ko ya samu wata matsalar mun shiga uku a gidan nan gabad'aya..... Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!....
'?
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124... BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*137*
"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! wannan kalmar ita na dinga nanatawa a cikin raina ina zaune gefan gadon da Baba Tabawa take kwanciya da yaron hannuna. Duka sun yi cirko-cirko a kaina yayin da ita Hauwan take bakin kofar d'akin a tsaye ta gagara shigowa amma kallo daya za ka yi mata ka tabbatar da cewa a cikin tashin hankali take.
Numfashinsa yana ta hawa da sauka kafin a hankali ya bud'e idonsa yana juya kansa ya ga Baba Tabawa sai ya fara mik'a mata hannu alamar ta d'auke shi. Wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke cikin raina ina tasbihi da godiyar Allah.
Ta kar'be shi a gaggauce ta sanya shi a kafadarta tana dan jijjigashi sai lokacin hankalin kowa ya kwanta ganin yadda yanayin yaron ya daidaita na juya babu Hauwa babu dalilinta dama kuma ba ta iya shigowa ba a bakin kofar d'akin ta tsaya.
Minal ta je tana jan zanin baba Tabawa tana fad'in." Mutawa ya yi Sultan din shikkenan ya mutu ko?"
Da sauri na janyota ina girgiza mata kaina alamar a a gabad'aya yaran duk sun yi tsuru-tsuru ganin yadda muka ki'dime don shi Khalil har da yin kuka kuma bai biyo mu d'akin ba.
Na ce Baba Tabawa ta zauna dashi a d'akin ta bashi abincinsa gabad'aya muka fita. Smma ko da na koma dakina kasa zama na yi minti goma a tsakani na sake fitowa Hauwa na samu a tsaye a jikin kujera ita kad'ai don duk sun koma kicin din domin cigaba da ayyukan da suke yi. Muka dubi juna na wuce ta ban ce komai ba na ji ta kira sunana cikin damuwa na juya amma ban amsa ba ta zo ta tsaya daf da ni tana fad'in" Don Allah Amina kada ki gayawa maigidan ina neman wannan alfarma a wajenki."
Na zura mata ido cikin nazartar maganarta ashe mara kunyar 'karya ce. Na ce." To akan me zan gaya masa Hauwa da dai Allah Ya d'auki rayuwarsa ne wannan zama dole ya san dalili yanzu kam tunda Allah Ya sa ya dawo hayyacinsa sai ayi ko'karin kiyaye gaba."
Ta gyad'a kanta tana fad'in na gode. Ban saurareta ba na shige dakinsu Baba Tabawa tana ta kici-kicin bashi kamun data dama masa yana cinyarta a zaune yana kamo hannunta. Na sake sauke ajiyar zuciya ta jin dadi ganinsa kalau har ma yana d'an wasansa. Na zauna har sai da ta gama bashi ta gyara masa jikinsa da bakinsa tukkuna na bude maganin na fara nuna mata yadda za ta bashi koda ta kammala sai ta sanya shi a kafad'a ya yi gyatsa sannan ta d'auki towel dinsa ta goya shi. Yana ta gwalantu irin na yara.
Fitowata daga d'akin ya yi daidai da lokacin shigowarsa. Dama ya ce da wahala ya kwana. Na yi kokari sosai wajan daidaita yanayina na yi masa barka da zuwa ya amsa da kulawa yana fad'in.'' A kawo mini abinci Amina." Ya kama hanya zai hau samansa da wata leda viva a hannunsa. Yaran gabad'aya suka fito daga kicin har da Mairo jin maganarsu ya sanya ya dakata ya tsaya aikuwa suka nufe shi da sauri ya rirri'kesu yana dariya suna ta jero masa sannu da zuwa.
Ina kallo ya dubi Khalil cikin nazari ya riko hannunsa yana fad'in." Kai matsalata da kai zurfin ciki da miskilanci ko akwai abinda yake damunka?"
Ya yi shiru yana sunkuyar da kansa. Karaf muka ji Minal na ce." Sultan ne ya mutu ko Hassana, shikkenan ya mutu, shikkenan ya mutu." Ta dinga fad'a tana tafa hannunta.
Na ji kamar an rad'e mini guiwata da tar'barya. Nusaiba ta fito daga kicin din ganinmu a tsaye ya sanya ta d'an daidaita yanayinta ta dan risina tana

Chapters

Related Ebooks
03, August 2026
Aisha kabir iliyasu

Please book for gudun aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login