Showing 6001 words to 9000 words out of 450388 words

Chapter 3 - Gudun Aure Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

4018

biyar baya kuma neman kudin nake yi, ba a san abinda gobe zata haifar ba. D'akin da nake bashi da yalwa ga zafin tsiya, Ina ganin zan komai gidan da shagona yake sai na samu 'yar tayin zama. hankalina zai fi kwanciyar da hakan. Ina kallon duk abinda yake faruwa ba, bayan haka zan samu saukin zurga zurga tunda ba ni da abin hawa.
Wannan shawarar ita na gayawa Babanmu. Ya jima yana dawurwura kafin ya amince. Na ce zan tafi da Usaini. Sannan zan nemi alfarma Sahura ta ba ni Yusura.
Da kawu Sule ya ji sai ya hau fada yana cewa na yi arziki zan guji gida na tafi uwa duniya na yi zaman kaina. Allah ya ce Annabi ya ce, dole idan zan tafi na d'auki daya daga cikin yaransa mata.
Na ce hakan ba matsala ba ne Fiddau ta shirya kayanta sai mu tare gabad'aya.
Itama Sahura bata musanta mini ba, ta ba ni Yusura har tana cewa babanta ya ce ya bar mini har auranta. Na yi dariya sosai ina fad'in Allah Ya ba ni ikon sauke nauyi.

Cikin ikon Allah komawata kuntau sai ta fashe mini. Domin na nemi sa'a a wurin Allah, na kuma mika masa al'amura ya kuma dubi zuciyata.
Harkoki suka bud'e mini neman kudin nake yi haikan. Bayan manyan dinkun nan da nake yi ana fitar mini dasu. Har zannuwa Ina sayarwa. Na sanya aka yi mini singbord mai d'auke da tambarin shagona A&A fashion designer wato (Amina Aminu kenan) a jikin bannar din hotona ne cikin ado da kwalliya irin na mutanan nijar da sinigal sun yi masifar kyau. Wani irin jiki ne da ni mai d'aukar ado babu wanda zai ce na ta'ba aure balle yara biyu.
Singbord daya aka sanya shi a farkon titi. Na biyu Kuma aka sanya shi a kusa da shagon.
Hakan sai ya k'ara haskaka lamarin. Cikin unguwar da sauran dake makotaka da ita suka fara kawo mana aiki.

Ba na kwatanta yin hakan akan Fiddau da Yusura dalili iyayensu Amana suka ba ni. Kuma 'yan mata ne, akwai mutanan da ba su da fahimta. Hankalina bai kwanta ba sai da na tabbatar sun cigaba da karatunsu, boko da islamiyya duk makarantun kudi ne har Yusi. Sune dai suke yi mini hidimar gida idan sun dawo, Usaini kuma yana tare da yaran shagona.
Ni kuma aikina tallata kasuwancina a kafafan sadarwa. TikTok fece book Instagram Whasap da sauransu. Sutturuna suka yawaita dalilin fashion din da nake nunawa a duniya bagraoud muke samu a cikin gidana mai kyau a yi mini hotona masu kyau cikin dinkuna kala kala na watsa a Media tare da lambobin wayarmu da location dinmu.
Hakan ya kar'bu mutuka gaya dalilin kyawun suffata. Duk kayan da na sanya sai sun zauna mini.
Kafin wani lokaci na tara followers na ban mamaki. Sai ya zamana 'yan film suka mayar da shago da gidana sansaninsu.

Jin haka hankalin Babanmu ya tashi ainun! Takanas ya zo da sassafe ya rufe ni da fad'a irin wanda bai ta'ba yi mini irinsa ba.

"Amina kada ki ga na zuba miki Ido ki nemi ki zubar mini da mutunci a duniya. Ina samun labarin duk irin abinda kike aikatawa. Wato watsa hotonanki da kike yi media hakan bai wadatar ba har sai kin had'a guiwa da 'yan film me kike so ki zama a duniya, Ashe shine dalilin da ya sanya ki ka nemi da ki kebance ke kad'ai domin ki yi abinda ki ke so ko? To ki kiyayeni wallahi, zan sa'ba miki muddin baki daidaita hankalinki ba, ni ba zan yarda ki juya ni ba don kina ri'ke da gidana hakan ba zai sanya na zuba miki Ido ki zubar mini da mutunci ba."

Duk yadda na so Babanmu ya fahimce ni ya ki sauranta. Ransa a b'ace ya tafi domin ko abinci ma bai zauna ya ci ba.
Na kira anti Yagana na gaya mata duk yadda ake ciki. Ni dai 'yan film din nan ba ni nake gayyatosu ba, zuwa suke yi su kawo aikinsu. Ta ba ni shawarwari masu yawa da kuma addu'oi. Wannan fad'an da Babanmu ya zo ya yi mini akwai sanya hannun mak'iya sune suka tunzura shi, amma dai ta jadadda mini cewa na kiyaye sosai na kuma yi takatsantsan.

Ban fasa tallata kasuwancina ba, amma na kiyaye mu'amulata da 'yan film d'in tunda hakan zai janyo mini matsala.
Allah buwayi gagara misali. Wato duk lokacin da Ubangiji yace kasance akan bawa babu mahalu'kin da ya isa ya dakatar. Zuwa yanzu na bud'e shaguna uku biyu ana hada hadar dinkuna dayan kuma cike yake da zunnuwa mayafai da takalma. Hamusu shi yake ri'ke da shagon zannuwan yayin da Usaini yake tsaye akan biyu.
Na yi k'arfi sosai Allah ya yi mini abinda dole na gode masa. Gidan da nake ciki maigidan ya siyar mini dashi miliyan shida da dubu dari biyu. Abinda nake dashi a yanzu sun haura miliyan ashirin bayan jarin da nake juyawa. Wannan dalilin ya sanya na yanke shawarar biya mana umara ni da Babanmu domin ina so na je d'akin Allah na yi godiya a gare shi.
Ranar dana gayawa Babanmu na biya masa umara da Azimi zamu tafi sai ya fashe da kuka. Yana fad'in." Amina ashe ina da rabon zuwa makka. Ashe a jikinki zan huta Amina, kin ri'ke mini gida, kina kula da ni, kin hana ni shan wahala. Yau kuma kin yi mini albishir din zuwa d'akin Allah. Amina ina ro'kon Allah ya yi mini albarka. Ya bunkusa kasuwancinki ya yara mini zuriararki. Burina a duniya ki yi aure Amina domin Ubangiji ya gama yi miki komai na Jin dad'in duniya."
Na ce." Baba ka daina kuka, duk abinda na zama a duniyar nan kune sila. Aure kuma lokaci ne idan ya zo dole ne zan yi ko ina so ko ba na so, ka yi tayi mini addu'a dai."
Har na baro gidanmu Babanmu bai daina ya sanya mini albarka ba. Matan gidan kuwa kowacce ta watsar da makamanta, idan na je kamar zuma kowa yana so ya jingina da ni.

****
Uku ga Azimi muka tashi zuwa kasa mai tsarki. Fiddau da Yusura kowacce ta tafi gidansu. Domin zamansu su kadai a gidan bai dace ba, dalilin da ya sanya kenan na ce su je gida idan na dawo sai suma su dawo, dama an yi hutun makaranta..

Tunda muka isa kasa mai tsarki koyaushe ni da Babanmu muna harami, dan shi wasu lukutan ma anan yake kwana ni ce nake komawa masaukinmu. Sai dai da safe idan na je na same shi.
Godiyata ga Allah bata yankawa kafin na fara rokar wani abu sai na yi godiya bisa ni'imar da ya yi mini. Sannan na shigar da bukatata. Miji nagari shine burina a yanzu wanda zai ri'ke ni tsakani da Allah ya kuma ri'ke yarana. Ban wuce aure ba kamar yadda kowa yake gaya mini, to idan Allah ya kaddara mini dole sai na 'kara wani auran a duniya ina rokansa ya azurta ni da nagari wanda mutuwa ce zata raba.
Wannan addu'ar ita nake ta nanatawa hannuwana dafe da ka'aba hawaye na kwaranyo mini.

Kunnuwana suka jiyo mini sautin kukan dattiijuwa tana fad'in." Allah wannan yaron bawanka ne, kafi ni sanin abinda yake lullube a cikin sha'aninsa. Ka yi masa komai a duniya Allah ina ro'konka ka bashi ikon duba matar da zai raya sunna da ita. Allah idan bashi da lafiya ta wannan fannin Ubangiji ka bashi lafiya. Ya rabbi Allah idan asiri akayi masa matansa suke mutuwa Allah ka kawo karshen lamarin nan. Ya Ubangiji Allah Ina da buri a duniyar nan kafin ka d'auki raina naga yaran wannan yaro. Allah Ka kawo karshen wannan lamar........Bata k'arasa ba wata mata dokekekiya ta bangajeta duk a kokarinta na zuro hannunta ta dora a kan ka'aba. Abinka da jikin tsufa babu kwari a take ta zube a kasan wurin. Da saurin gaske na bi ta na kamata ta tashi da kyar tana numfashi. Wata mace mai kama da ita ta kutso wurin ta ri'ke gefan kafad'arta tana fad'in." Hajiya sai da na ce miki kada ki shiga jikinki babu kwari, kuma wasu mutanan ba hankaline da su ba. Allah yana jinki a duk inda za ki yi addu'a."
Na ce." Wallahi wata mara hankali ce ta bangajeta, kuma ba ta san ma ta yi ba."
Muka fito sarari da ita kekenta yana can gefe muka zaunar da ita a akai sai numfashi take yi da alama ma bata da cikakkiyar lafiya.

"Sannu fa mun gode sosai ."
Murmushi kawai na yi. Na juya da niyyar barin wurin sai na tsinkayi maganata a karo na biyu bayan godiyar da ta yi mini.
"Kamar na san fuskarki, kina yin film ko?"
Girgiza kaina na yi. "A'a ba na yin film Hajiya."
"Amma dai kamar Ina ganin hotonanki na yawo a kafafan sadarwa mussaman Instagram da TikTok fece book da sauransu."

Babu wata damuwa na ce." E, ni ce, Hajiya Amma ba na film Ina gudanar da harkokin kasuwanci na ne a sahar."
Ta girgiza kanta da murmushi a fuskarta ta furta." To Allah Ya taimaka ya bada sa'a, idan kina neman wata gudumawa sai ki neme ni zan baki lambar wayata. Sunana Hajiya Saratu Ibrahimu 'Danbatta."
Gabana ya fad'i. Tsira mata Ido na yi na 'yan sakkoni, ashe kallon tsoro na yi mata da farko sai yanzu na hangi kamarsu daya da Alhaji Tajo.
Jikina ya mutu sosai. Ashe dattijuwar mahaifiyarsa ce. ita kuma wannan din diyarta ce.....
'?
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=?N?*

*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay


*BOOK2
*4*
"Ko za ki ba ni lambar wayarta ki ne."
Maganata ce ta dawo da ni hankalina. A didirirce na ce." To bari na baki." Ban kawo komai a raina ba na fara fad'a mata lambata ta yi serving tana fad'in." Ke yar wane gari ce? Mu dai 'yan Kano ne."
"Na ce." Ni ma 'yar Kano ce, an haife ni a cikin unguwar kabuga."
Maganar Hajjan tasu ta d'auki hankalinmu ni da ita gabad'aya ina take fad'in 'Yar nan shin kina da aure ne?"
Tambayar da ta yi mini kenan. Gabad'aya sai muka zuba mata Idanuwanmu.
"Murmushi Hajiya Saratun ta yi kafin ta ce Hajja kenan, har na fahimci abinda yake kasan zuciyarki."
Shiru muka yi gabad'aya ni dai haka kawai sai na ji gabana na bugawa.

Hajiya Saratun ta Nisa cikin wani yanayi kafin ta cigaba da cewa "Kin yi wa mutumin sha'awarta ko? ke duk maccen da ki ka gani sai ki ce kin yi wa Tajo sha'awa, shi kuwa wannan ina ga haka zai koma ga Allah bai yi aure ba."
Da saurin gaske ta furta." Bakinki ya sari danyan kashi Saratu, wai mai yasa ke ba ki iya magana ba ne, kada ki manta fa muna cikin kasa mai tsarki gaban ka'aba, amma kina nema ki jefi d'an-uwanki da baki irin haka."
Cikin dariya ta ce." Allah Ya baki ha'kuri Hajjata."
Sai ta kalle ni.
"Amina kina da aure ne? Hajja tana tambayarki.
Lokaci guda bakina ya fara rawa, dan wani bala'in kwarjini suka yi mini......."A a yanzu dai bani dashi amma ina shirye shiryen y......"Ai ba a daura ba ko?"
Hajja ce ta katse ni."
Na ce." E ba a daura ba Hajiya amma an kusa."

Sai ta riko hannuna katamau! " Don Allah ki auri Tajo kin ji 'yar nan, na yaba da hankalinki, kuma duk na ji irin addu'oin da ki ke yi akan neman miji nagari, ki sanya a ranki adduarki ta kar'bu shiyasa Allah ya hadamu anan, don Allah don Annabi ki taimakeni ki auri yaron nan kin ji ko."
Gwiwa ta dinga rawa kafafuna sukayi mugun sanyi jin yadda matar take ta hadani da girman Allah har jikinta na rawa. Muryarta na wani irin karkarwa wai sai na amince tukkuna zata sakar mini hannu.
Hawaye suka kwace mini da rawar murya na ce." Hajiya ni ba budurwa ba ce bazawara ce, aurena biyu, ina da yara biyu, sannan ba a auran na taso a gaba ba, neman kudi nake yi duk domin iyaye da yarana, don Allah ki yi hakuri ku bar maganar nan."

Sai kawai itama ta fashe da kuka. Tana ce wa." Ai taimako na ce ki yi, duk abinda kike buk'ata na rayuwa kin samu a wurin Tajo, ni na haifi abina wallahi bashi da matsala, lafiyarsa lau, kaddara ce kawai take d'awainiya dashi, amma in sha Allahu daka kanki komai ya zo karshe "

"Hajja wace irin rigima ce wannan, dan Allah ki sakar mata hannu, kada hankulan mutane ya dawo kanmu, dole sai an bi komai a hankali, idan Allah ya kaddara sai ki ga an yi amma ba wai yanzu a tursasata amincewa ba."

Gabad'aya muka dubeta a lokacin da take maganar ni ina can tunanin abubuwa masu yawa. Mahaifiyarsa tana nan tana shaidarsa mutumin kirki ne, bata san manemin mata ba ne.
"Saratu haka kawai na ji yarinyar nan ta kwanta mini a raina, na tabbata addu'ar da na yi ce Allah ya kar'ba a take, ko kina so na mutu banga abinda Tajo zai haifa ba."
A sanyaye ta ce." Ina so mana Hajja, amma kamata ya yi a bi komai a hankali."

Duk maganar da suke yi hannuna yana cikin nata ta ri'ke kamatau! da kyar na furta." To shikkenan Hajiya zan yi shawara in sha Allahu, duk abinda muka tattauna da mahaifina sai na sanar daku."
Ta sassauta rikon da tayiwa hannuna Kin tabbata."
Kaina na d'aga mata tare da furta"In sha Allahu rabbi, na yi hakan ne domin ta cika ni ba wai don na amince da bukatartata ba.

Maganar da Hajiya Saratu take yi a waya itace ta d'auke mana hankali gabad'aya.
"Cikin dariya take fad'in." Ga mu nan a tare ai ta samu wata yarinya wai dole sai ta aureka tana nan ta ri'ke ta tamau don rigima, to kai Tajo ai ka yi mata kuma."
Da yake hands free ne muna jin muryarsa yana fad'in." Matar aure kuma a ina?"
Ta ce. Anan muka had'u da ita, ni ma kuma na yaba gaskiya na yi maka sha'awarta."
" Ku ajiye maganar nan Saratu, kada ku kawo 'yar mutane ta rasa rayuwarta, na ha'kura da auren nan fa, ba ni ma sha'awarsa gabad'aya."
Abinda ya fad'a ya daga hankalin mahaifiyartasa ta kar'bi wayar ta fara yi masa fada akan me zai sa ya furta haka.
Ha'kuri ya dinga bata har ta sassauta. Yana fad'in." Ina sa ran yau da daddare zan shigo garin sai na ga matar na amince, indai hakane burinki Hajja."
Ta juyo tana kallona." Kin ji shi ya amince ko, kema kin amince ko Amina?"
Shiru na yi ban iya furta komai ba, kawai Ina mamakin karfin hali, da rikici irin na tsufa. Haka kawai daka ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaki. Ni abinda ya fi d'aga mini hankali ma yadda duk matan da ya aura suke mutuwa. Ta ya za a yi Ina ji Ina gani na kashe kaina, akan wane dalili, tabbas dana san taimakon da na yi mata haka zai janyo da na yi gaggawar barin wurin ban tsaya mayar da magana da su ba.
Babanmu na hango Yana zuwa wurin da muke tsaye.
Yana karasowa na ce." Hajja ga Babana nan tare muke da shi." Da sauri ta saki fuskarta. Na ce." Baba wannan mahaifiyar Alhaji Tajo ce wannan dan kasuwar, ita kuma wannan 'yar'uwarsa ce."
Cike da girmawawa ya gaisheta ya d'ora da fad'in." Mun gode sosai da karamancin da akayi mana, Allah Ya saka da alheri, ai yaro ma tuni muka tura shi makaranta yana nan ya shiryu yana ta yi wa al'kur'ani hidima."
Ita dai murmushi take yi don bata gano akan abinda yake magana ba.
Hajiya Saratu ta ce." Kada

Chapters

Related Ebooks
03, August 2026
Aisha kabir iliyasu

Please book for gudun aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login