Showing 291001 words to 294000 words out of 450388 words

Chapter 98 - Gudun Aure Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

4321

aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


**Gudun aure paid book complete 2k akan telegram. Normal Gruop wsp 1k via 0542382124... Binta Umar gtbank.*
*07084653262*
*122*
Da farko har ya zauna kusa da ita kamar yadda ta buk'ata sai kuma ya tashi zumbur ya fara d'urawa Rukky ashariya yana fad'in ta daina kallonsa. Anti Yabi ta dinga jan hannunsa tana zaunar dashi yana fizgewa tare da ko'karin zuwa inda Rukky take domin dama can sakuwarsa ce kuma abokiyar fadansa.
Da azama ta d'auki wayarta ta fice daga d'akin cikin tashin hankali don ganin kamar itama yana so ya yi mata lahani.
Yabi ta fara fadin." Babu komai na kudi a d'akin nan Bashir tun daran jiya mun binceke komai sai sutturunta kai kuma namiji ne me za ka yi da kayan mata. 'Yar ta Nusaiba ce ta kwashe duk abinda muke hankoro ta boye sai waccan munafukar Nabila itama tana daya daga cikin wad'anda suka san sirrinta amma saboda ba'kar mugunta ta'ki ba mu goyon baya. Da tun farko ta amince mana da duk haka ba ta faru ba ni kaina a cikin wannan nazarin nake ace an watse ba mu tashi da komai ba."
Nabila na kuka take fad'in." Anti Yabi ba kya ganin abinda ya yi mini lefi ma ki ke ba ni, kina ganin yadda ya yanka min kumatu amma duka baku da damuwa."
Saliha tace." Ke ma kin so haka ta faru Nabila tuntuni muke miki magana kina nuna ke ba ki san komai ba bayan na tabbatar da cewar mukkulin dirowar can yana hannunki mugunta ce ta sanya ki boyewa tunda gashi kina fad'in za ki zauna a gidan. Ina yaran suke da za ki ce zaki kula dasu duk sun zama samari. Su wad'anan 'kananun dole ubansu ya mayarwa da iyayensu Nusaiba kuma ba zama za ta yi ba itama gidanta zata koma, kina so mu tafi sai ki yi wad'aka da dukiya ko to ai duk cikinmu babu yaro mun fahimci me ki ke nufi ."
Yabi ta ce." Tunda abin ya fara zama haka Nabila ki fito da key din dirowar nan nasan anti Maryam a cike take ajiye sirrikanta wata'kila zamu samu gwalagwalanta a ciki da takardun shagunanta da ta mallaka sai mu d'auki wani abu daga ciki mu kasafta a tsakaninmu.."
Cike da damuwa da jin rad'adi ta furta." Ban san inda key din nan yake ba anti Yabi ko ku yarda ko kada ku yarda wallahi ni ma ban d'auka ba. Wayoyinta da ATM dinta suna hannun Nusaiba to key din ma yana wurinta ku je ku binkiceta.
Ya tashi yana rangaji da d'ura ashariya ya fita falon ya ritsa Ruky a zaune domin d'akinsu Mairo ma a rufe yake zage-zagen da yake yi ne ya tashe kaf har da yaran abinda ba su saba ji ba sai kuka. Adam da Salim suka tashi a firgice yayin da Bashir ya dinga bugun kofar d'akin da Nusaiba take kwance da yaranta. Itama a gigice ta tashi tana bud'e kofar ya yi ciki da ita ya ritsata. Salim da Adam suka bi shi d'akin. Itama Rukky ta koma d'aki a guje tana gaya musu gabad'aya suka fito a gigice
Lokacin har ya sa mata wu'ka a wuya wai ta bashi kud'i da mukkulin dirowa an ce komai yana hannunta.
Salim ya yi tsalle ya buga masa duka a bayansa tunda yana tsakiyar Nusaiban ya raba kafufunsa a kanta ya saita ta da wuka.
Gidan ya cika da koke-koke a guje-guje. Mairo da gudu ta ja yaran suka koma d'akin suka rufe. Salim ya d'agata ta shi da gaske ya gilla mata wukar a wuya har ya yi sheda ta matsa gefe tare da ri'ke ma'kogwaronta da ya fara d'an fitar da jini kad'an. D gaske yankar rago ya yi shirin yi mata. Jama'a 'kwaya bala'i ce.
Yaranta ihu kawai suke yi. Nabila ce kad'ai ta iya zuwa wurin da take amma su anti Yabi suna can sun rirri'ke Salim da ya shemar da Bashir din a kasa yana dukan hancinsa.
Da yake ba sosai yake kashe wayoyinsa idan zai kwanta ba. Cikin bacci muka ji kiran waya gabad'aya kusan a tare muka tashi zaune ni dashi ya d'auka da sauri yana sanyawa a kunnansa muka ji muryar Adam cikin rud'u da tsananin tashin hankali yana fad'in." Baba ka zo babu lafiya ka zo yanzu Bashir ne zai kashe anti Nusaiba."
Da wani irin hanzari ya sauka daga gadon na taso na biyo shi ya ce na koma. Har ga Allah na tsorata duk da gidansa cike da tsaro ina jin tsoro ya fita jin ana maganar kisa.
Na koma na zauna cikin tsananin tashin hankali da damuwa wace irin masifa ce wannan kuma.
Lokacin da ya shige gidan Bashir din ya samu nasarar ta shi yana ta kai wa Salim suka da wu'kar da take hannunsa 'karama ce amma kisa da illa take yi nan take. Ihu da koke ya cika gidan ita Nabila ga yanka a kumatu ga iskokai.
Da hanzari ya nufe shi duk da ya hangi abinda yake hannunsa. Amma da ya gama fahimtar bashi da wani kuzarin kirki irin na maza dalilin shaye-shayen da yake ya dakusar da garkuwar jikinsa sai ya nemi ma'karfafansa ya kai masa duka a k'irji kafin ya falla masa mari ya murd'e hannunsa da kyau ya k'wace wu'kar ya mi'kawa Salim ita ya kar'ba duk ya yi wujiga-wujiga ai yayi namijin kokari ma wai aka ce ranar naka sai naka tabbas da da tsautsayi yau Nusaiba zata ba'kunci lahira itama.
Ya ce da Adam maza ya fita ya kira masa Sukairaju da 'Dahuru sune majiya k'arfi sosai fadi yake kisan kai za ka yi mana a gida Bashir dama dan ta'adda ne."
Ya yi shiru yana ciccije baki. Ya dubi Nusaiba dake zaune a gefe yaranta biyu a kusa da ita tana share hawaye sai ya girgiza kansa cike da tsananin damuwa ya kalli Anti Yabi yana jin kamar itama ya falla mata mari, tuntuni ya fahimci bata da hankali gabad'ayansu babu na za'be itama Maryam din da yake shedarta ashe ba'kar macijiya ce.
Tun a d'akin Sukairaju da 'Dahuru suka fara tafkar Bashir ya hana su ya ce dai su caje jikinsa tsaf idan da wani makamin su fito dashi haka kuwa aka yi irin wannan wu'kar uku ce a soke a jikinsa sai daurikan wiwi da ganye ya ce su fita da shi.
Ya juya yana kallon Saliha ita din ya tambaya menene abinda ya faru. Ta fara kame-kame.
Nusaiba tana kuka ta ce." Ba haka ba ne wallahi baba tunda Momi ta rasu suke yi mata bincike d'aki wai tunda sun ji an ce ba su da gadonta. Sun 'ki tafiya ne tunda sun shirya halaka ni, anti Yabi duk abinda Momi ta yi muku da irin abinda za ku saka mata dashi kenan yau kwana uku da rasuwarta kuna rigima har da zubar da jini akan dukiyarta. Ba mu da iyaye wallahi domin ba zamu ta'ba nuna ku a matsayin iyayenmu ba."
Suka yi shiru anti Yabi ta yi kasa da kanta tana fad'in." Ba haka ba ne Nusaiba wallahi kada ki zarge mu domin rashin Maryam na kowane. Ba mu da yadda za mu yi da Bashir tunda ya zo yake daga mana hankali wai a raba gado a bashi rabonsa, amma mu ai mun fi buk'atar Maryam akan abinda ta tafi ta bari na dukiya."
Babu wanda ya ce mata komai, ya sake duban Nusaiba a karo na uku yana fadin." Ya aka yi har ya shigo ya yi miki Illa abinda nake so na ji kenan.
Tana kuka ta ce." Wai sai na bashi wayoyin Momi da atm din da kuma mukullin dirowar da take ajiye muhimman abubuwanta."
Ya gyad'a kansa cike da tsananin al'ajabi da mamaki, shi kaddararsa kenan abokinsa ya rasu ya bar shi da rikicin iyalinsa in ba haka ba shi a tarihin rayuwarsa da family dinsu wani abu na tashin hankali makamancin wannan bai ta'ba faruwa ba.
Ya kama hanyar fita yana fad'in." Zo mu je d'akin ki nuna mini dirowar.
Ta tashi da sauri tare da sanya yaranta a gaba ta bi bayansa su kuma suna tsaye cikin jin kunya Ruky ce kawai take tsugune gaban Nabila tana yi mata tofi.
Madaidaiciyar dirowa ce ta mussaman domin ba irin ta gado ba ce wannan maybe daban ta sanya aka yi mata.
Ya d'an ta'ba ya ji yanayin katakon yana da nauyi. Sukairaju ya kira a waya ya ce ya dawo. Ya fito falon Salim da Adam suna tsaye suna magana ya a kira Mairo. Adam ya dinga bubbuga kofar dakinsu tana fad'in." Wanene a cikin tsoro."
Sai da ta yi muryar Adam din tukkuna ta bude ta fito Taburni ta biyo bayanta duk sun gigice kuma a tsorace suke. Ya ce su had'o kan yaran kaf su biyo bayansa. Haka akayi kuwa yaran duk suka fito ganin Babansu ya sanya suka ruga wajansa suna kuka tunda a gabansu abin ya faru lokacin da Bashir din ke ko'karin kai wa Nusaiba duka ga fuskar Nabila da ta'bon yanka da jini."
Duk da Bashir din baya gidan Nusaiba kasa zama ta yi a gidan dalili ta tsorata ainun da 'yan uwan momin nasu. Salim da Adam ne kawai suka koma dakinsu ita kuma ta bi bayansa da yaranta tana kuka cikin tashin hankali ga wuyanta yana d'an yi mata zugi kad'an dole sai ta je asibiti.

littafin gudun aure na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Haka muka k?rasa kwana cikin alhini da damuwa mai tsananin gaske.
Da safe da wuri Salim ya shigo ya biyo ni har d'aki ya gaishe ni amma bai yarda mun had'a ido ba ya ce mini asibiti za su je yanzu da Nusaiba na biyo shi falon sai na same su tare da maigidan a tsaye suna magana itama ta gaishe ni cikin jin nauyi na amsa tare da tambayarta jikin ta ce da sau'ki.
Sai bayan da suka fita ne tukkuna ya juyo yana kallona tare da cewa." Ina yaran suke?"
Na ce." Suna tare da Mairo a can d'akin Baba Tabawa."
Ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce." Sun dawo gidansu daga yau." Cike da godiyar Allah na furta." Allah Ya taya mu riko ya kuma albarkace su."
Sama ya nufa yana amsawa. Ban bi bayansa ba sai da na kintsa jikina tukkuna na hau na same shi shima ya yi wanka yana dan duba wayarsa. Na ce." A kawo maka abin kari ko?"
Ya ce." Bari zuwa an jima kad'an, abin nan da ya faru ya daga mini hankali Amina, wai me wasu suka mayar da zumunci ne, mutane idonsu ya rufe akan abinda duniya. Yar uwar nan ta su sanin da na yi mata lokacin da take raye ta wahalta musu kwarai da gaske domin ko kafin rasuwar iyayensu itace jigon kula da su Alhaji Amadu na yin nasa ko'karin. Ina daya daga cikin mutanan da suka dinga bashi Sha'awar bata goyon baya tare da ha'baka kasuwancinta tunda iyayenta ba su da k'arfi kuma itace babba. Ta yi musu zumunci k'warai ta kuma dinga ko'karin halakar da kanta duk akan su rayu yanzu ta fad'i ta mutu suna rigima akan abinda ta bari, abinda ya fi ba ni tsoro Bashir da yake ko'karin halaka yarinyar nan Nusaiba akan abinda bashi da hakki."
Ajiyar zuciya na sauke tare da fad'in." Gaskiya da tsoratarwa a cikin wannan lamarin. Jiya da daddare na ji ita Nusaiban tana cewa shi Bashir din ya gudu an neme shi an rasa amma yana jin rasuwar ya dawo wai a bashi hakkinsa."
Dariya ya yi irin ta takaici kafin ya ce." Ba shi da hankali ai da alama shaye-shayen da yake ya fara ta'ba masa kwakwalwa wannan barin irinsu ai babbar masifa ce, yana can hannun hukuma ai dama nemansa suke yi d'an iska."
Na kalle shi jin ya yi zagi tabbacin abin ya yi masa ciwo sosai na furta." Allah Ya rufa asiri yasa mu fi karfin zukatanmu."
A tak'aice ya amsa da "Amin."
Idona ya sauka kan bakuwar dirowar da na ga Sukairaju ya shigo da ita a tun jiya da daddaran. Ganin inda nake kallo ya sanya ya ce." Sun ce wai muhimman abubuwanta na ciki an rasa mukkulin kuma dalilin da ya sanya na ce a d'auko mini ita gabad'aya idan na samu nutsuwa zan sanya a bud'e a gaban yaran domin su tabbatar da abinda yake ciki na game da dukiyar uwarsu."
Na ce." Hakan ya yi, Allah Ya kawo musu sau'ki ya kuma takaita."
Ya sake amsawa da Amin Yana fad'in." Kafin na shigo yanzu ai na sake shiga gidan tare da ba su umarni kan cewa duk su had'a kayansu su tafi basu da amfani sam gida kuma ba na Maryam ba ne ballantana su yi magana na Alhaji Amadu ne da y'a'yansa, ba su da gurin zama a cikinsa."
murmushi kawai na yi irin na takaici ina mamakin karfin halin wasu mutanan, a ce akan kudi mutum sai ya sarayar da mutumcinsa. Duk kawaici irin na mutumin nan sun 'kure shi yana korarsu Allah na gode maka daka sanyawa iyayena wadatar zucci shima Baba Sule Allah ya taimake ni ya daina ya kama kan sa ganin yana tara surukai.

Da yamma can kira ya shigo wayata da sabuwar number. Da mamaki na daga tare da sallama. Nusaiba na ji tan fad'in." Anti Amina Ina yini."
Na amsa da kulawa ina sauraranta tana fad'in." Na kar'bi lambarki ne a wurin Adam dama zan gaya miki cewa Salim ya wuce da ni gidana bayan mun dawo daga asibiti ana I gobe addu'ar bakwai zan zo sai na kwana idan an yi addu'a sai na tafi."
Cikin nutsuwa da kulawa na ce." To shikkenan hakan ya yi, Allah Ya huta gajiya ya kuma kiyaye faruwar hakan anan gaba. Ita kuma Mominku Allah Ya yi mata rahama."
Ta amsa da "Amin cikin sanyin jiki muka yi sallama.
Koda na gayawa maigidan yadda muka yi da ita yace ai ta sanar da shi.
A daran ranar Mairo da Taburni suka had'o kan kayansu da na yaran gabad'aya kayansu na sanyawa da kayan wasansu irin wanda Momin take saya musu Minal ta dinga bin Mairo tana kuka wai sai ta tashi sun koma gida a daran. Ta'ki jin rarrashi Hassana da Husaina dama babu fuska domin ba su ganta ba a wajena suna zaune dai suna kallonta duk sun yi shiru kamar a tsorace suke da ni. Sun 'ki sakin jikinsu rigima take yi sosai lallai sai Mairo ta tashi sun tafi na kamo ta ina fad'in." Za ki je wurin Baba?"
Ta d'aga kanta. Na dubi Mairo tare da fad'in." Ta ja su d'akinsu da na ware musu a falon su ci abinci. Baba Tabawa ta samu mataimakiya Taburni tare suka shiga kicin a yammacin ranar.
Na ce su yi sallah isha'i tukkuna kafin su ci abincin."
Ta amsa da "To." Wanda ya yi daidai da lokacin da ya sauko ya dubi Khalil yana fad'in." Yi maza ka dauro alwala mu je massalaci."
Ya tashi da sauri.
Ya dube Minal din dake saman cinyata tana kuka. Hannu ya mik'a mata ta sauko daga jikina ta nufe shi ya sunkuya ya d'auketa ya sanyata a k'ugunsa irin d'aukar dai ake yi yaran da ba su wuce shekara biyu zuwa uku ba.
Ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya ya dube ni yana fad'in." Me aka yi mata ne?"
Na tashi tsaye ina fad'in." Wai sai Mairo ta tashi sun tafi gida."
Ya yi murmushi yana cewa." Amina rigima ai a gidan kike."
Na ce." Gidan Momi fa take nufi."
Ya dire ta a kasa ganin Khalil din ya fito ya ce." Momi ai tana can gidanta na gaskiya Amina, ita kuma Minal nan ne gidansu."
Ya kama hanyar fita Khalil ya bi shi a baya da sauri.
Kaina na girgiza kawai na shige d'akina domin gabatar da tawa ibadar.


***
To ranar sadakar bakwai din kamar yadda ya fad'a abinda ya faru kenan bai ma zauna balle a zo a taya shi zaman. Addu'a kawai ya sanya aka yi mata a massalatai. Nusaiba anan wurina ta kwana duk da Nabila tana can gidansu ita bata tafi tana tare da su Salim don bala'i har da kukanta tana fad'in ba zata iya tafiya ta bar su su kadai ba, kuma mamansu kafin ta rasu ta ce ko bayan ranta ta tsaya ta kula mata da yaranta. Haka suka ha'kura suka kyaleta shima Yallabai din da ya ji cewar ba ta tafi ba sai da abin ya bashi haushi sosai ya k:yaleta ne kawai domin ya ga iya gudun ruwanta. Duk da Nusaiba ta san tana gidan hakan bai sanya ta shiga ba nan su Salim din suka same ta. Ta shiga cikinsu Mairo suka yi aikin funkaso da fanke manyan kuloli aka fita da su domin sadaka.
Tun bayan azahar ya shirya ya fita. Muka kasance da Nusaiba da yaranta har bayan la'asar kafin ta yi shirin tafiya gidanta.

Yana shigowa estate din Sukairaju da 'Dahuru suka yi ram da shi Malam Isiyaku ne Malamin Hajiya Maryam da ya zo kar'bar kudinsa kamar yadda aka al'kawaranta masa.
A mota suka zura shi tare da zuge gilashin motar sai ya fara zare ido na k'aduwa da tashin hankali. Sukairaju ya ce." Maigidanmu ne ya ce mu kai masa kai can gidan hutawarsa za ku tattauna wasu batutuwa ko ba kaine malam Isiyaku ba."
Ya gyad'a kansa da saurin baki ya furta." E, ni ne, Malam Isiyaku."
D'ahuru da yake driving ya ce." To kada ka damu lafiya za ka fito in sha Allahu."
Ya yi shiru yana zazzare Ido. To ai shi ba haka ake yi da shi ba me yasa za a yi masa kamun kazar kuku magana aka yi akan mai hakki ya fito ya fadi hakkinsa a ganinsa hakan da aka yi masa tozarci ne tunda shi ba 'barawo ba ne.

Gabansa suka dire Malam Isiyaku da tunda suka isa guesthouse din suka sanya shi a tsakiya babu wata hanya da zai samu ya fece..
Suka fita cike da bin umarni.
Ya dube shi a nutse Yana fad'in." Nutsu sosai ka kwantar da hankalinka. Na buk'aci ke'bewa da kai anan ne saboda muhimmanan batutuwan da zamu

Chapters

Related Ebooks
03, August 2026
Aisha kabir iliyasu

Please book for gudun aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login