Showing 219001 words to 222000 words out of 450388 words

Chapter 74 - Gudun Aure Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

4230

na gode sosai sai da safe." Sai ta kashe wayar. A sanyaye na ajiye tawa a saman cinyata jikina duk ya mutu Hajja kuka take yi da gaske dalilin da ya sanya ma kenan ta katse wayar da sauri. Sai kawai ni ma na ji ruwan hawaye ya ciko idanuwana wani kutittiran abu ya tsaya mini a wuya. Lallai matar nan ta wuce ta nemi alfarma a wurina na tsaya yin jayayya da gaddama ba zata cutar mini da yara ba. Wannan maganar zuciyata ke ta nanata mini. ........
'?
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=?N?*

*TALLAH*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya


Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 n

*93*
"Maganar
Hauwa ai bata shafe ki ba Amina don haka babu ruwanki wannan tsakanina da ita ne kawai tunda ta ce ba ta ji to sai mu zuba ni da ita shege ka fasa."
Ya fad'a yayin da yake sake janyo ni jikinsa. Na janye a hankali na ce."Ya zaka ce babu ruwana bayan kai ma kasan a saboda ni da abinda ya shafe ni kuka samu sa'ba ni har da rabuwa ai gaskiya ba zan iya yin shiru ba domin abinda ka yi bai dace ba. Kamar yadda take ha'kuri da kai ya kamata ace kaima ka yi hakuri da halayenta ai zaman auran kenan."

"To yanzu ya ki ke so ayi?"
Ya fadi hakan cikin 'kosawa da maganar domin gabad'aya yanayinsa ya nuna ba itace a gabansa ba.
Na ce." Ka mayar da ita tunda ciki ne da ita sanin kanka ne a musulunci babu kyau sakin mace da ciki, kuma idan Hajja ta ji hakan ranta ba zai yi mata dad'i ba gaskiya."
"Ai ita Hauwa ba ta duba haka ba Amina, kuma cikinku wallahi kada wadda ta kuskura ta gayawa Mahaifiyata akan hakan rai zai 'baci."
"Ai kai zaka gyara matsalar gidanka kafin ta fita waje idan ba ka so Hajja ta ji abinda ka yi sai ka yi gaggawar gyara kwabar da ka yi."
Ya 'bata rai yana fad'in." Kina so ki ba ni umarni kenan?"
"Ba umarni ba ne ban isa ba, shawara ce nake ba."
"To ba zan d'auka ba har sai kun je ke da ita kun bawa Maryam da 'yar uwarta ha'kuri akan abinda ku ka yi musu. Na rashin kyautawa."
Ido na zuba masa ina kallonsa da mugun takaici.
Na gyada kaina tare da janye idona daga kansa ban ce komai ba..
Sai ya cigaba da ce wa." Wannan shine kawai, ki ja ta tunda tare kuke kulle-kullenku sai ku je ku ba su ha'kuri domin mun yi magana da Nabila ce wa gobe za ta koma jos, to kafin ta tafi din sai ku gyara kuskuranku, ni kuma sai na mayar da ita dakinta."
Na juyo fuskata a d'aure " Wannan kuma shine ba zai yiwu ba, idan hakurin da ka ba su bai isa ba, shikkenan don Allah ka cikashewa Hauwa sauran igiyoyinta da suka rage, idan hakan ma bai yi maka ba sai ka had'a har da ni gabad'aya."
Ya ce." To kada ki sake yi mini magana akan abinda ya shafi tsakanina da Hauwa, ba ke ki ke auranta ba, ni ne babu ruwanki wannan shine maganarmu dake ta k'arshe akanta."
Na dinga kallonsa zuciyata na sake suyuwa da kutun takaici da b'akinciki. Wannan wani abu ne da zai yi masifar wahala a ce Hauwa ta je ta bawa Momi da Nabila ha'kuri saboda iya zaman da na yi da ita na gane cewa macace mai mugun girman kai da kifad'i, ga taurin kan tsiya, bai shirya kwantar da rikicin ba, domin da ya shirya mutuwar matsalar ba zai 'bullu da wannan abinda ya san lallai da wahala ya yiwu.

Jin an kira shi a waya ya sanya na tashi na fita daga d'akin ba tare da na sake cewa komai ba, matsalarsu ce can ta family iyakacina shawara, kuma ni ban tura Hauwa cewa ta yi abinda take yi ba, akan kanta take yi saboda wata manufa tata da kuma masifar kishi, duk wanda zai zarge ni da hannu akai ya d'auki hakkina. Ba zan sake cewa masa komai ba.

Bai kwana a gidan ba a ranar sai washe gari wajen daya da rabi ya shigo cikin kayan shan iska da cazbaha a hannunsa ga dukkanin alamu daga massalaci ya fito mabiyin sunnah ne sosai da zazzafar akida da rashin son bidi'a da yawa. Bai fad'a ba amma tuntuni na gane ce wa mugun dan izala ne tunda yawanci abokanshi larabawan nan na madina duka 'yan ahalissuna ne.
Muna falo duka a zaune ya shigo ya d'an tsaya ana gaisawa ya amshi ta kowa a d'an sake. Ina kallon Hauwa bayan sun gaisa ta tashi a sanyaye ta shige daki. Sai na ji wani iri a raina, na yi shiru tare da yin k'asa da kaina ina jin suna ta labari da Baba Tabawa kamar yadda suka saba. Ya jima a tsaye a wurin suna magana ban tofa tawa ba. Kafin ya haura samansa.
Baba Tabawa ta juyo tana kallona da wani yanayi na alhini da damuwa ta ce." Irin wannan matsalar nake ta guje muku faruwarta Amina, rayuwar nan gabad'ayanta 'yar ha'kuri ce, shi namiji yana fa da wani irin iko da damar da Allah bai bawa mace ba, yakan iya yin komai ya kwana lafiya amma ita mace za ta yi abin ya zame mata matsala gagarima, ita wadda kuke ta ha'kilon akanta tana can hankalinta kwance mijinta ya kar'bar mata rigimar tunda ai kun had'e mata kai, ai ta fi ku wayo ta kuma fi ku shekaru da gogewa ta yaya ko tana da laifi zai gani bayan koyaushe cikin nuna alherinta take. Ki duba ki gani cikinku babu wanda ya fi kusanci dashi sama da Hauwa amma yau an wayi gari tana wasan 'buya da shi. Shi kuma ko a jikinsa bai damu ba, ya kamata a ce ku nemi sulhu ita Hauwa ta kar'bi kuskuranta tunda a bayyane yake ta yi ba daidai ba."
Murmushi na yi irin na rashin sukuni na ce." To Baba Tabawa ya za a yi ne, mun jima muna magana dashi jiya da daddare abinda ya tsiro dashi ne nake ganin da wahala ace ya yiwu nasan Hauwa sai dai a rabu akan ta je ta ba su ha'kuri abinda ya ce kenan muddin tana so su daidaita ta je ta bawa Momi ha'kuri da k'anwarta Nabila akan zagi da 'kaharun da ta yi wa iyayensu, ni kuma nasan halin taurin kanta da mugun kifad'i."
Ta gyada kanta cikin damuwa tana ce wa." To ke dai ki yi takatsantsan sosai, amma a shawarce ina ganin ta bi umarinsa kawai domin zahiri mijinku ba irin wanda ake tursasawa ba ne ko kuma mace ta juya shi.
Na ce." Mu dai ba za mu juya shi ba. Amma ai matarsa da yake tare mata fad'a juya shi take yi kamar waina a tanda idan ba haka ba menene dalilin da zai sanya ya saki matarsa a kanta uwar babban dansa namiji kuma yar uwarsa. Baba Tabawa ki dubi lamarin nan fa da kyau!"

Baba Tabawa ba ta kai ga magana ba kiransa ya shigo wayata da take ajiye a gefana. Ina d'agawa ya ce." Ki zo yanzu." Bai bari na ce komai ba ya datse kiran. Na yun'kura na tashi da wayar a hannuna ina fad'in.'' Baba bari na sauko sai mu cigaba da tattauna maganar da muke yi."
Ta ce." Shikkenan a sauko lafiya."
Ina hawa saman gabana ya fadi ganinshi zaune daga shi sai karamin wando na ciki ya cire kayan dake jikinsa. Kallo daya na yi masa na d'auke idona domin lokaci guda na fahimci menene a cikin kwayar idanuwansa. Gabana bai daina bugawa ba har na isa inda yake zaune. Na zaune zuciyata cike da zullumi da damuwa. Ya ce." Za mu sake gaisawa ko?" Kallonsa na yi cikin nauyin baki na ce." Ai mun gaisa da ka shigo.
Ya kamo hannuna yana duba yatsun kafin ya rintse da nasa ya hade yatsunmu wuri d'aya a hankali ya ce." Wata kalar gaisuwa na zo miki ta mussaman kamar yadda kike ta mussaman a wurina."
Shiru na yi tare da yin k'asa da kaina. Wai dadin baki zai yi mini da kalamai saboda yana so ya kwanta da ni???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?, tun jiya na gama gane inda ya dosa.
Na fara jin cikina yana murd'ewa domin ban san ta yadda zan sanar dashi cewa cikin nan fa ya sake ficewa ba.
"Kuna da abinci ko, domin ina so na cika cikina kafin na wani lamari mai girma ya faru a tsakaninmu."
A hankali na ce." Da abinci Baba Tabawa ta yi sai dai ba irin wanda kake so ba ne jallop din taliya ne da kifi.''
Ya d'an sake rintse hannuna dake cikin nasa a karo na biyu yana shafa mini tsakiyar hannu
ya ce." Gaskiya kam ba irin nawa ba ne, amma in dai da zafi a ba ni zan iya ci a haka."
Na ce." Da zafi mana tunda a kula yake." Hannuna nake ko'karin cirewa daga cikin nasa ya rike yana fad'in." Wai ke ba kya yin irin 'kunshin nan ja da 'baki zai yi mini kyau domin kina da kyawun fata ina so a dinga yi mini."
Shiru na yi. Ba tun yau ba na fahimci yana son lalle sosai, ni ce dai ban mayar da hankali ba, amma na lura matarsa Momi tana yawan yi. Amma henna ake yi mata a kafafu da yatsun hannuwanta. Ya ce" Akwai wata yarinya dake yi wa Maryam zan sanyata ta turo muku ita sai ta yi muku."
A takaice na ce." Sai ta zo. Ya bi bakina da kallo yana lumshe Ido. Wani irin yanayi na ji a jikina amma nan da nan na shiga taitayina domin na fi kowa sanin cewa matsala ce kwance-kwance. Cikin 'yar damuwa na ce." Na kawo maka abinci ne?"
Ya girgiza kansa alamun a'a. Na ce." Saboda me?"
"Ke kadai za ki iya gamsar da ni yunwar cikina."
Na yi shiru dai. Ina jinsa ya matso sosai tare da janyo ni jikinsa yasa hannu a dokin wuyana yana tatta'ba wajan da ya zama guru-guru kafin yasa baki ya sumbata. Shi kuma wuyana yana bashi sha'awa ko sunna muke yi ya dinga sumbatar wurin kenan har dasu sanya harshe.

Ya dora hannuwansa biyu duka a saman kirjina. Ajiyar zuciyarsa na ji a saitin kunnena. Ganin ya fara ki'dimewa sai na dan ja baya tare da jan hanci domin na ma kasa cewa komai sai zare ido nake yi.
Ya sake matsowa yana fad'in." Menene haka, yaushe rabon ma da na nemi wani abu Hajiya ko ba ki yi kewata ba ne.......
'?
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=?N?*

*TALLAH!*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya


Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 ne kachal=?L?
*94*
Na ce." Ba haka ba ne, kawai dai ina so na gaya maka ne cewar ba ni da tsarki."
Sai ya yi sakato yana kallona har ya so ya ba ni dariya domin wata kala ya zama kamar wani sakarai. Na yi kasa da kaina na ji yana cewa." Ina ce 24 ga kowane wata na bature kike yin al'ada ko ba haka ba ne, yau nawa ga wata?"
Ya fad'i maganar yana tsatstsare ni da ido. Ban dube shi ba na ce." Yau shida ga watan aprilu."
"To mai ya kawo jini kuma?"
Shiru na yi domin kuwa zahiri ba na so na yi masa k'arya amma da sai na ce ai lokaci ya kan canza sa'i, da lokaci mussaman idan shekaru suka tura.
Tambayarsa ya sake maimaitawa idonsa a kaina. Cike da shahada da kundubala na ce." Dama ina so na gaya maka ban san yadda za ka kar'bi lamarin ba, amma ni Allah ne shaidata, shine kuma zai tsaya mini a ko'ina, wallahi shekaran jiya cikin da nake d'auke da shi ya fita. Amma na alak'anta faruwar hakan da wannan rikicin da muke ciki, alhamdulillahi babu wata matsala domin Hauwa ta sanya Masa'udu ya sayo mini magungu?a masu kyau sun taimaka mini k'warai wurin wanko mini mahaifata."
Lokaci k'ankani yanayinsa ya daidaita babu wani rausaye-rausaye da lumshe-lumshen Ido irin na fitina, zahirinsa ne ya bayyana ya 'kura mini idonsa da wani irin yanayi na mussaman tattare da shi.
Kasa jimirin kallonsa na yi sai kawai na yi 'kasa da nawa idon cikin zuciyata ina fad'in 'Duk abinda za ka yi, ka yi wanda ya fi shi a baya kaddara ce.
'Dakin ya d'auki shiru na tsayin mintina bai tanka mini ba amma a jikina na ji cewar har yanzu bai cire kwayoyin idanuwansa daga kaina ba.
Cike da ko'karin ture rauni da kasalar dake ko'karin dabaibayi ni na dago idona. Karaf idonsa ya shiga cikin nawa, gabana ya fadi ganin cikowar k'walla a dukkanin kwarmin idonsa don sauran kad'an ma ta fara tsiyaya.
Gwiwa ta sage cikina ya sake murdawa. Cikin gaggawar na sake yin k'asa da kaina ban yadda na sake kallonsa ba domin ji na yi gabad'aya na sare lamarin har ya kai a ce za a zubar da kwalla. Na san a yanzu abinda ya fi buri da buk'ata bai wuce ganin gidansa cike da yara ba. To ni ba budurwa ya aure ni ba, balle ya ce, sannan kuma shekaruna sun yi nisa dukda dai ban wuce haihuwar ba, bayan haka kuma ni dashi muna da matsala wadda ya taketa da k'afafunsa na kuma yi hakuri na bi shi a yadda yake so. Ba ni da niyyar sake zubar masa da ciki tunda alkawari na d'auka tun lokacin sulhunmu da Baban Saude. Idan zan samu ciki ya kasance duk yaron da zan haifa yana da matsala zan jure dalili alkawari da rantsuwar da na yi wa Baban Saude Allah ne mai yin yadda ya so.
Kuma wallahi ni kaina na ji b'akincikin fitar cikin to don babu yadda zan yi ne kawai ya sanya ni ha'kuri ne tare da barwa Allah ikonsa. Ba ni jin ko da wasa duk irin rikicin da za mu yi dashi zan sake yun'kurin zubar masa da ciki da gagan domin tun farkon fari na gane hakan lamari ne mai mutukar hadari daka iya janyo babba matsalar da za a yi wahalar shanyo kanta dalili na ci wuya 'barin da na yi sakamakon shan kwayar zubar da ciki shiyasa gabad'aya lamarin ya fice mini daga rai na ajiye a zuciyata cewa zan haihu idan Allah ya kaddara mini koda yaran za su kasance masu rauni ta kowace siga.

Gyaran muryarsa ya dawo da ni daga dogon tunanin da na tafi. Dubansa na yi sai na ga babu kwallar gogeta ya yi ko mayar da ita ya yi Allah ne masani.
"Ta shi ki ba ni wuri kawai Amina, Allah Ubangiji ya yi mini sakayya." Wannan maganar ya furta mini babu sukuni a tare da shi.
Ban ce masa komai ba kuwa na tashi na kama hanyar fita daga d'akin kamar yadda ya buk'ata. Allah ai al'musauwiru kuma da zuciyar bayi yake aiki.
Jikina gabad'aya duk a sanyaye ban san kuma mai ya taka ba tunda zahiri yanayin da ya shiga ya nuna mini cewa ya ji zafin abin.
Bayan kwanaki biyu gidan na mu ya kasance kamar kufai. To babu motsin yara shiru. Hauwa kuma ta tsiri zaman d'aki sai na yi, na yi da ita ta fito falo ta'ki. Sai yamma muke zama ni da Baba Tabawa mu d'an yi hira. Shi kuma maigidan tun shekaran jiyan da ya fita bai sake leko mu ba.
Baba Tabawa tana kicin domin d'ora sanwar dare na fito falon da waya a kunnena.
Bikin Yusura ne ya tashi kuma abinda ya kawo tsaiko a wancan lokacin balagorun da saurayin ya yi libiya domin neman kudi dalilin da ya sanya iyaye suke ce a bari ya dawo sai a d'aura auran tunda duk gidana. Mun gama magana da ita akan kada na ga ta sayi ko cokali domin tun da aka kawo kudin nake jadadda mata. Wancan karon ma na sanyata ta yi amfani da maganin sanyi hakan ba zai 'ki ba tunda ai 'ya macace, ita kuma duk inda take 'yar gyara da kula ce. Kuma koyaushe ba'a rabata da maganin sanyi domin shine tushen gyara aure da lalatashi. Garkuwar mata itace mai magungu?an Islamic din da na aminta da ita, dukda ita Hauwan ce ta had'a ni da ita, amma dalilin yawan sayan kayanta da nake yi ya sanya muka

Chapters

Related Ebooks
03, August 2026
Aisha kabir iliyasu

Please book for gudun aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login