Showing 390001 words to 393000 words out of 450388 words

Chapter 131 - Gudun Aure Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

4025

ri'ke shi nasa mata a jikinta ya tare da hannunsa. Ta saki dariya tana ta'ba kumatunsa ya d'an bud'e ido d'aya sai kuma ya rufe tasa dariya tana cewa." Baba ka ga ya bud'e idonsa nan d'insa ya yi ja ko ciwo ya ji." Ta nuna kumatunsa da wani tabo a wurin wanda ya yi jaa sosai ya bambamta da fatarsa. Da wannan alamar Allah Ya bambamta mana su Amma kamanninsu daya shi Usainin ne mai wannan tabon.
Ya ce." Ba ciwo ya ji ba haka Allah ya yi masa baiwa."
Ta ce." Mama kin bar mini shi ko?" Na d'aga kaina. Yarinyar bakinta ya'ki rufuwa tasa yatsanta a cikin hannunsa ya kuwa d'amke ta dinga k'yalkyala dariya tana duban 'yan uwan "kin gani ko ya rike ni, Usaina kin ga ya rike mini hannu."
Su dai dariya kawai suke yi mata. Khalil ya shigo bakinsa har kunne da yake sun riga shi dawowa shi yana cikin yaran da za su yi saukar al'kur'ani sun bambamta musu lokacin tashi mahukunta makarantar.
A nutse na ce." Shigo sosai mana." Ya shigo yana ta washe baki ya ce." Masa'udu ne ya gaya mini Mama ta haihu kuma guda biyu Irina."
Uban ya kama yi masa dariya. Ya matsa kusa da shi yana ta duba fuskar yaran ya kar'bi na hannun Usaina yana cewa." Wannan shine a babban mama." Na ce." Shine na hannun Minal kuma Usaini." Abinda ya yi gabad'aya sai da ya ba mu mamaki har uban ya rungume shi a kirjinsa ya rintse idonsa kimanin minti biyu ya bud'e cike da kwalla ya dinga fad'in." Allah Ya raya ku, Allah Ya sa mu yi zumunci domin Allah mu so junanmu domin Allah, Ubangiji Allah Ya yi wa Babanmu tsayin rai."
Na yi saurin sunkuyar da kaina kasa jin k'walla ta cika mini ido. Yaron nan yana da kaifin basira da tunani. Yasan shekarun girma sun cimma Babansu gasu k'ananu shine yake wannan addu'ar yana so su girma tare dashi
Shi kansa jikinsa sai da ya mutu. Amma da yake namiji ne bai nuna rauninsa ba yaron ma yana addu'a amsa masa yake yi. Sai da ya gama tukkuna ya ce." Za mu je umara bayan mun yi bikin suna ni da kai ko Babana." Ya gyad'a kansa cikin dauriya da ko'karin hana 'kwallar idonsa zuba." Ya furta." Akwai wurin da zan nuna maka jikin d'akin Allah sai ka tsaya sosai ka roke Allah Ubangiji Ya raya ni cikinku na ga girmanku ko?"
Shiru ya yi bai ce komai ba 'kwallar dai da yake ko'karin hana ta zuba ita ta fara d'igowa saman towel din jaririn da yake hannunsa.
Ya ce." Menene haka kuma Baban masu gida, a gaban 'kananka za su yi maka dariya."
Ya d'an share hawayen ya fakaice ya dube ni yana cewa." Mama."
Na amsa Ina kallonsa da wani irin yanayi gabad'aya duk ya dakusar mana da walwalarmu."
Ya cigaba da cewa." Mama ta ji kin haihu ko na je na gaya mata?"
Na ce." A a bata ji ba dama jira nake ku dawo daga makaranta."
Ya tashi tsaye da yaron a hannunsa Usaina na mik'a hannu ya bata ya k'i ya mi'ko mini uana fad'in." Zan je yanzu na gaya mata."
Na kar'be shi a hankali na ce." To hakan ya yi."
Fita ya yi daga d'akin da d'an sauri.
Muka dubi juna ni da shi bai ce komai ba haka zalika ni ma haka. Na dube su a nutse na ce. "Ku je ku cire kayan makaranta a yi alwalar magriba sannan a samu nutsuwa a ci abinci."
Suka tashi a tare har ita Minal din da take saman cinyarsa ya kar'bi yaron dama kusan rabi a hannunsa yake ta dira kasa tana kallona ." Mama za ki goya mini shi idan an jima ko?"
Na gyad'a kaina alamar E ta juya da niyyar fita tana d'an tsalle.
Shiru na wani lokaci kafin na ji sautin numfashinsa." Ko yanzu Ubangiji Allah Ya d'auki raina Amina kin gama biyana hakika alherin da yake tattare da tarayyata dake ba zan k'idaya shi babu abu mafi girma da arziki face wannan. Allah Ya saka da alheri, ba zan boye miki ba na jima ban tsinci kaina cikin yanayi na farinciki kamar wannan rana ba. Sai dai jikina ya yi sanyi ainun da lamarin yaron nan Khalil ko lokacina ya kusa ne zan tafi na bar ku."
Hararsa na yi ina fad'in." Kai ma abinda za ka yi kenan wace irin magana ce wannan don Allah."
Ya dubi fuskar yaron da yake hannunsa a tsanake ya ce." Sai dai shekarun girma suka cimmani Ubangiji Allah Ya azurta ni da 'yan baiwa gasu nan kin san dai ba zan maimaita shekarun da na yi a baya ba ko Annabi Muhammadu s a w ya ce sittuna au saba'una. Yanzu hamsin da takwas nake."
Shiru na yi ban ce masa komai saboda takaici mutuwa dole ce amma a ganina bai kamata a kawota a yanzu da muke cikin annashuwa ba.


Wannan littafin na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Wayarsa aka kira ya canza harshe larabci yake yi sosai. Na tsinci wasu daga cikin abinda yake fad'a wasu kuma ban fahimta ba yana dai ta fad'in sunan Sukairaju a maganarsa ya gama ya dube ni yana fadin." Ba'ki na yi daga madina akan wani lamari ina barar addu'a."
Na ce." A cikinta nake kullum Allah Ya yi riko da hannayenka, ni ma na gode sosai Allah Ya saka da alheri."
Ya tsare ni da ido yana fad'in." Me na yi na godiya Amina?"
A takaice na ce." Abubuwa da yawa. " Ya yi shiru bai ce komai yana dai ta kallona ina kici-kicin gyara rigata ya taimaka mini Hasan din ne yake mamulan baki da neman abinci ya d'ora mini shi saman cinyata na tallafe shi sosai nasa masa nonon a baki. Ya kuwa kama yana sha yaran yanzu duka da wayonsu ake haifarsu amma dai duk da haka na d'an taimaka masa wajan ganin ya rike a bakinsa.
Ya ce." Idan Allah Ya kaimu za mu je asibiti tare kamar yadda na fadi da farko domin a duba mini su."
Na ce." Allah Ya kaimu." Ya duba agogon dake d'aure a hannunsa magriba ta yi ya shiga toilet dina ya dauro alwala ya fita zuwa massalaci.
Duka su biyun na shayar. Baba Tabawa ta shigo tana fad'in.'' ko akwai abinda nake buk'ata wanda zan ci. Na ce ta dama mini kunun gyada kawai na fara dumama cikina an jima idan na yanke shawara akan abinda zan ci zan gaya mata.
Ta dubi yaran suna kwance a gado bacci suke yi ta furta." Ko za a goya su ne Hajiya?"
Na yi dariya tare da fad'in." Sultan din fa?"
Itama tana dariya ta ce." Ai ya girma shi ya zama saurayi."
Na ce." Mu bari zuwa gobe tukkuna Babansu zai dawo."
Ta gyadq kai tare da juyawa da sauri ta fita.

Cikin kwanaki biyu da haihuwa dangina da nasa babu wanda bai ji ba. A kuma yau da suke da kwanaki uku a duniya Hajja da yayarsa Hajiya Saratu suka sauka a garin da abin arzikinsu akwati biyu cike da kayan yara kowanne da tasa
Anti Yagana kuma ta ce mini itama dai tana tafe da muka yi waya da ita. Baban Saude kuwa kwana d'aya da haihuwar ya zo bakinsa kamar zai yage ganina kalau yaran ma haka domin ni da shi baban nasu mun sake samun nutsuwa da kwanciyar hankali a lokacin da aka tabbatar mana da ingancin lafiyarsu sai farinkinmu ya sake hauhawa. Kwana ya yi da safe bayan ya karya kummalo ya yi mana sallama ya wuce wajan sana'arsa har yana yi mini alkawarin zuwan iyalinsa tunda mun ce da taron suna ko dai ba su zo gabad'aya ba Anti Saude da Mamansu za su zo idan mun tsayar da ranar da za mu yi bikin sunan ya ce na gaya masa.
Na yi ta murna kuwa ina yi masa godiya kafin ya tafi.
Shud'ewar wannan kwanakin babu Hauwa babu dalilinta. Khalil ya gaya mata ranar dana haihu haka zalika ma mijinta ya gaya mata da bakinsa ya gaya mini ta sani. A yadda na fahimta yana tunanin ta zo tunda ba yini yake yi a gida ba tunda ya yi ba'kin nan bai zauna ba sai da daddare yake shigowa kuma kwana daya da haihuwar ta kar'bi girki. Yau da su Hajja su ka zo ya dawo gidana.
Zuwa yanzu ni ma na fito falo cikinsu amma ta ko'ina jikina a rufe yake kafafuna ma koyaushe suna cikin safa. Tunda na haihu Allah ya hore mini lafiya ba ni jin ciwon irin na gigita bayan haihuwa kuma babu abinda ba na gudanarwa na abinda ya shafe ni. Wannan kad'ai ya isa na godewa Ubangiji.
Rashin zuwan Hauwa ya ta'ba mini rai ainun na kuma yi mamaki ba kad'an ba.
Masu aiki na hidima da yara ta kowace siga kowa k'auna da kulawa yake nuna mini me zan ce da Ubangiji. Salim baya garin yana Legos amma Nusaiba zuwanta biyu Adam ma tunda na haihu yake shigowa haka zalika ma Nabila ta shigo mini kwana daya da haihuwa ta yi mini barka sosai ta fita...
Kwanansu Hajja biyu ranar biyar kenan suka fahimci akwai matsala daga bangaran Hauwa dalili da ni da maigidan da masu yi masa hidima daga waje har zuwa cikin gidan kowa cikin annashuwa yake yi. Hakan ya ta'ba ran Hajja sosai ina d'aki ta same ni, ganin yanayinta ya sanya na nutsu ta zauna a gefena tana duba fuskar Usaini ta ce." Wannan tabon kamar sake rinuwa yake yi a fuskarsa Amina."
Na ce." Ni ma na lura da hakan, amma dai Dr Iliyas ya ce babu matsala in sha Allahu."
Ta sauke ajiyar zuciya a hankali kafin ta dube ni ta ce.'' Menene a tsakaninku da Hauwa, Amina kada ki b'oye mini komai wannan lamarin naku ya fara damuna ya kamata a ce kun girma tunda duka babu yaro a cikinku."
A hankali na furta." Babu komai sai alheri Hajja ranar da zan haihu ma mun yi wa da ita a sanina dai babu wata hatsaniya da ta ratsa tsakaninmu."
Ta yi shiru na d'an wani lokaci kafin ta ce." Ki gaya mini gaskiya ta shigo gidan nan tunda ki ka haihu?"
Na girgiza kaina ina fad'in." Ba ta shigo ba."
Ta furta." Ki ce kuma babu komai Amina haihuwa irin wannan akwai dai wani abu da kuke b'oye mini?'
Na ce." Hajja babu komai wallahi ni dai a nawa b'angaran ban san nata b'angaran ba."
Ta ce." Ke ai na yarda dake Amina kuma na gazgataki domin da da akwai matsala za ki gaya mini, Hauwa ba ta jin maganar kowa, ta raina ni ta raina uwarta kuma ba ta jin shawara."
Na yi shiru ban ce komai ba.
Ta girgiza kanta da damuwa a tare da ita ta tashi ta fita. Sai ta d'an ba ni tausayi domin na gane duk fafutukar da take yi akan gidan d'anta ya gyaru da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa Hauwa ta bari hassada ta yi mata illah a rayuwarta.
Da daddare muka yi waya da anti Yagana cewa suna tafe ita da Ya Falmata ta dawo sati biyu da suka wuce. Na yi musu addu'ar isowa lafiya.
A daran dai da ya dawo wajan goma da wani abin ban jima da yin sallama da su Hajja ba na shiga d'aki domin gasa jikina na kwanta na fito daga toilet na same shi rungume da Hassan yana kafadarsa ya tashi daga bacci yaran suna da tsotso mussaman da daddare Usainin na goye a bayan Taburni yana bacci.
Na sanya kayan bacci a gurguje na kar'be shi domin kuka yake yi sosai na zauna nasa masa nono ya kama. D'akin ya d'auki shiru na wani lokacin kafin ya ce." Gobe ba'kin nan da na yi za su tafi amma jin labarin k'aruwar dana samu suka ce za su zo yi miki barka wasu labarawan Madina ne sharifai ne jinin Annabi Muhammadu S.a.w suka ce wai na tambaye ki za ki ba su yaran?"
Na dube shi cikin rashin gane inda maganarsa ta dosa na basu yara kamar Yaya?"
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Sun ji irin jikokin Annabi Muhammadu S.a.W ki ke haifa kin san akwai su da kara da karamci da tsantsar ha'din kai
sun ta ya ni murna sosai da abin alheri suka ce a baki."
Dariya na yi na ce." Aikuwa na gode sosai amma dai su yi hakuri ba zan ba su ba."
Yana dariyar shima ya furta." Kai tsaye abinda na gaya musu kenan, sun ce wai ke y'ar baiwa ce ta mussaman kina haihuwar yara masu daraja da albarka."
Murmushi kawai na yi
Ya nisa kafin ya cigaba da cewa akwai kud'i da na bawa Nabila za ta had'o musu kaya akwati hud'u Hasan biyu Usaini biyu idan kin duba abinda bai yi ba ko ake buk'ata sai ki yi magana ko?"
Na dube shi sosai ina fadin." Akan me za ka bata kudi kace ta had'o mini kaya, me yasa ba ka yi shawara da ni ba ko ni ban san abinda ya dace da su ba?"
Ya ce." Hajiya sassauta mana ita ta nema ba ni naga dacewar bata kudi ta sayowa yarana kaya ba business d'in ta ne da take yi kenan da aje waje a sayo sai a saya a wajenta ko?''
Shiru na yi ban ce komai ba. Ba zan yarda da wannan shishshigi ba duk abinda yake tsakaninsu ba ni buk'atar ji, jiki magayi ne duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwan kan doka. Ba ha'ka mai ya kawo rami, idan ta yi wari sai mu ji ai!
Ya cigaba da cewa." 'Kiyasin kud'in nan da mutanan nan suka ba ki a matsayin alheri na haihuwar yaran nan sun haura miliyan saba'in. Ni kuma na ba ki tukwucin 'karamin kamfanina na soap (sarrafa sabulun wanka) wanda yake mariri."
Da wani irin mamaki na dago ina kallonsa miliyan saba'in!
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Kad'an kenan daga irin alherinsu ba wani abu ba ne, kin cancanci fiye da haka Allah Ya yi miki albarka."
Na ce." Me yasa za ka ba ni kamfani guda?''
Kai tsaye ya furta." Saboda ina shirye-shiryen bud'e wani zuwan da suka yi kenan!''
Na girgiza kaina a hankali na ce." A a ba zan kar'ba ba gaskiya ka haihu fa, nan gaba da ni da kai ba mu san iya adadin yaran da za ka sake haifa ba duk neman da za ka yi a yanzu saboda su za ka yi don haka ka bar shi na gode sosai da kulawa da addu'a abinda ka yi wa yarana wad'anda ba kai ka
haife su ba wallahi ya ishe ni."
Ya furta." Wanne yara ne ban haifa?'' Ya tsira mini ido da jin haushin maganata.
Na cire idona daga cikin nasa a hankali na kwantar da yaron ina fad'in." Ni dai ba ni neman fitina don Allah idan alheri ka yi niyyar yi mini ka yi daidai gwargwado wannan ya yi yawa.''
Ya ce." Abinda na yi niyyar bayarwa kenan Amina."
Na yi shiru ban ce komai ba amma zuciyata cike take da mamaki bayan zunzurutun kudi har miliyan saba'in da kamfani guda abin kamar ya yi yawa fa.
Koda su anti Yagana suka zo na gaya musu Ya Falmata ta dinga fad'in bake ki ka ro'ka ba baki ya yi akan me za ki ce masa ba kya so. Kowace haihuwa da alherinta tunda har ya iya mallaka miki kamfani to dukiyarsa takai ta kawo wata'kila shima bai san adadinta ba, idan kin lura bayarwa yake yi tana sake ru'banya. Allah Ya kawo wasu abokan nasa su sake baki arzikinki ya ninka na da mu abinda muke so kenan.
Ita dai anti Yagana shiru ta yi da alama yadda abin ya girgiza ni haka ya girgizata. Ta kasa cewa komai sai kallo.
Zuwansu anti Yagana ya 'karawa gidan walwala domin dama can akwai jituwa tsakanin Hajja da ita gefe guda kuma ga Ya Falmata sarkin barkwanci da bada dariya ta zauna tana ta ba su labarin matan da suke zaman shahada a makka da yadda suke shan tiriri da wahala guje-guje itama abinda ya koro ta kenan.
A daran ranar duka muna falon an gama cin abinci sai ga Hauwa ta yi sallama ta shigo Khalil na biye da ita a baya.......
'?
*GARKUWAR BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*161*
Ni tausayi ma ta ba ni ganin gabad'ayanta kamar a ki'dime take da wannan yanayin na rashin gaskiya da kame-kame duk a k'okarinta na kare a kanta suka gaisa da Hajja tana ta nanata musu cewa ba ta da lafiya a kwance take har yanzu jikinta babu dadi har da 'yar 'kwallarta wai an gaya mata kwanansu biyu da zuwa amma ba su je gidanta ba.
Hajja dai shiru ta yi mata kawai ta zuba mata ido Hajiya Saratu ce ta tanka mata itama ba wata magana mai tsayi da muhimmaci ba. Yadda dai ta girba 'karya tare da d'orawa kanta ciwo duk mai hankali yasan da cewa k'arya ce tsagwaronta babu wani mashahurin ciwo a tattare da ita balle ya hana ta zuwa duba jininin d'an uwanta. Ko ba ta zo domin ni ba tunda kishiyarta ce ta zo domin mijinta kuma d'an uwanta balle ma ni ban ga abinda na yi mata mai muni ba da zata sanyawa ranta k'iyayyata mai zafi. Haka kowa ya bi ta da abinda take fad'i ana ta yi mata sannu da jiki
tana rantsewa da Allah wai bata da lafiya itama. Ni kuwa na tabbatar da cewa k'arya take yi tunda halinta ne d'orawa kai ciwo haka take yi ko kunya ba ta ji. Da haka muka gaisa da ita suka gaisa da su anti Yagana babu wanda ya nuna mata wani abu a fuska Ya Falmata ma sai tsokanarta take wai ko itama ta ci wake ne. Ganin haka ya sanya ta saki jikinta saboda yadda aka goya mata baya cewar bata da lafiya har su Hajjan gabad'aya. Khalil ya dinga jin dadi yaron ya d'auki yaran d'aya bayan d'aya ya kai mata tana duba su tana dariya wadda nasan ba ta jin dadi ba ce fadi take kamarsu daya da Babansu yadda ake ta fad'a haka take cewa har tana kallona mun fi

Chapters

Related Ebooks
03, August 2026
Aisha kabir iliyasu

Please book for gudun aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login