Showing 18001 words to 21000 words out of 450388 words

Chapter 7 - Gudun Aure Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

4097

ji gabana na bugawa. Na ri'ke hannun Yusi da yake ta yun'kurin bud'e motar ya fita. Direban da kansa ya zagayo ya bude mana muka fito. Ya d'auko madaidaiciyar akwatina yana kuma ko'karin kar'bar jakata na hana shi. Da sauri yayi gaba da akwatin. Ni kuma cikin nutsuwa na fara takawa ban yi mamakin yadda jama'ar dake wurin ke risina mini ba. Da yawa sun san ni a hoto da sauran kafafan sadarwa.
Koda na isa wurin da yake sai na dan risina a nutse na furta." Barka da yamma." Ya amsa da "Barka dai." A takaice hankalinsa yana kan wani mutum da yake ta yi masa bayani auran da zai yi wa yaransa kuma bai yi musu kayan gado ba.
Da hanzari na shige don yanayin da ya nuna a fuskarsa kamar bai so na tsaya a wurin ba har na gaishe shi. Jin tsoron abinda zai biyo baya ya sanya na bar wurin da saurin gaske.
Na same su su uku a zaune Hajja da Hajiya Saratu sai wata mai kama da hajjan sak da alama 'yar'uwarta ce.
Hajja ta dinga dariya ganin ni da Yusi fadi take." Amaryar Tajo ta iso fatan alheri a gare ki Amina. Allah Ya albarkaci auranku."
Sosai na yi kokarin sakin fuskata duk domin faranta zuciyar dattijuwar na zube a gabanta da fara'ata na ce." Hajja ina yini ya kufan jiki?"
Ta amsa tana me janyo Yusi cinyarta tana cewa." Kai anan za a bar mini kai ko?"
Yana dariya ya fara gaisheta.
Na juya a tsanake na fara gaishe dattijuwar da take kusa da ita. Babu yabo babu fallasa ta amsa mini Hajiya Saratu ita tun kafin ma na kai ga gaishatan ta gaishe ni duk kuwa da cewa itace gaba da ogan. Hakan ya kara sagar mini da guiwa domin duk inda ake neman karamci da kawaici mutanan sun kai, babu girman kai da d'agawa a cikin sha'aninsu.

"Ayyo! Wannan itace dama, ai ina hasashenta duk da cewa Hauwa ta nuna mini hotonta, na ce ai ba social media nake yi balle na ganeta sai yanzu kuma dana ganta a zahiri na ganeta ina yawan ganin hotonta akan titina ikon Allah."

Dattijuwar dake kusa da Hajja ce ke wannan maganar tana 'kebe baki.
Sunkuyar da kaina na yi sai na ji Hajjan tana fad'in." Ai 'yar kasuwa ce sosai kuma ta sanu akan harkokinta, ai ni irin wad'andan matan burgeni suke yi muddin zasu rike mutuncinsu."

Sai kawai ta ce." Hum Hajja kenan, fate fate ake tonawa kawai Allah ya rufa asiri."
Falon ya d'auki shiru lokacin zuciyata ta dinga tsalle kiris nake jira matar ta sake wata magana na kare kaina domin na fahimci wani irin kallo take yi mini na marasa tarbiya.

Ya shigo cikin hanzari Yana fad'in." Wanka kawai zan yi mu tafi na bar uzurirrikana da yawa a can." Sai kuma ya tsaya yana cewa." A a Inna Uwani yaushe ki ka zo?"
"Kwanana biyu a garin nan. Na ji labarin ka yi aure shine na zo yin Allah sanya alheri, ashe wannan itace amaryar?"
Yana 'yar dariya ya ce." Itace inna Uwa, ina Hauwa ba tare kuka zo ba."
Ta kawar da kanta tana cewa" To me Hawwa zata zo ta yi maka Tajo, humm Allah ya Kyauta."

Murmushi ya yi kawai a gaggauce ya shige yana cewa'' Bari na yi wanka na fito.

Ta kasa daurewa sai ta fara fad'in." Duk tsiya dai gwara ta gida, kuma budurwa nutsatsiyar bafulatana. Ai kowane maganarci yana so ya samarwa zuri'arsa uwa ta gari. Babu wayewa ga auran 'yan social media wad'anda suka kwashe kayansu daga gaban ma'aiki."

Hajiya Saratu ta ce." Inna Uwani wace irin magana ce wannan kuma? Babu dadi cin zarafi ga mutumin da bai yi maka komai ba. Wannan auran hukuncin Allah ne. Kuma tun farko mun so ki bashi Hauwa tun kafin ma ya yi aure na biyu ki ka ce ba zaki bashi ba, saboda Salima ta mutu itama kada ta mutu. Har dake fa masu fad'in yana da aljana to me zai sanya kuma bayan Allah ya aurar dashi ga za'binsa ki damu. Yau kusan sati daya da d'aurin auran nan alheri muke ta gani. Don Allah kada ki kawo mana rud'ani."
Sai ta rushe da kuka tana cewa." Saratu fitsara za ki yi mini akan na fad'i gaskiya har kina cewa har da ni a masu yi wa Tajo zagon kasa ko kin manta uwarsa ce ta saki nono taba ni."

Hajja tace "Saratu kyaleta kada na sake jin kin ce komai. Ke kuma Uwani ki tayar mini da ciwona kin ji ko?"
Shiru tayi tana sha'kar hanci tare da sanya gefan d'ankwalinta tana goge hawaye, tana girgiza kanta tana ta kallona. Ni kuma ta kasan idona nake hangenta.
Kusan daskarewa na yi a wurin ganin yadda muraran matar ta nuna zazzafar kiyayyarta a kaina.

Ya fito tsaf cikin manyan kaya. Wurin ya cika da kamshinsa. Ganin inna Uwani na share fuska sai ya ce." Me ya faru ne na ga fuskokinku duk a b'ace.
Hajiya Saratu ta furta." Maganar Hauwa ta taso da ita. Inna Uwani ta so dama ranta ya baci ne kawai."
Ya zuba mata Ido a tsanake ya furta." To idan wannan ce matsalar ki share hawayenki. Bari mu ga abinda Allah zai hukunta anan gaba idan da rabo sai ayi yadda ki ke so."

"To ai haka ya kama a gaya mini. Ni ban k'yamaci matarka ba Tajo, amma dai ka dawo gida ka yi auran alkunya da fita kunyar jama'a." Ba tare da ya ce mata komai ba ya kalle ni." To zamu tafi yanzu." Ya dubi Hajja da gabad'aya ranta yake a b'ace kan abinda 'yar uwarta ta yi. Ya ce." Za mu tafi Hajja a yi mana addu'a."
'?
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE [6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram akwai normal What'sapp group #700 ga wad'anda karatu a talgrm yake yi musu wahala hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=?N?*

*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay


*6*
Lamarin da ya janyo hayaniya da kace-na-ce, mussaman a social media kowa na fad'in albarkacin bakinsa. Wasu na ganin Alhaji Tajo alfarma ya yi mini ya aure ni. Wad'anda kuma suka san tarihinsa na baya suna ganin kawai kwanana ne ya k'are tunda har kud'insa suka rude ni na aure shi bayan nasan matsalarsa.
Ni dai tunda aka d'aura auran nake ta zubar da hawaye gabad'aya na rasa a da wane ma'auni zan auna lamarin. Wace irin k'addara ce wannan mai sammatsi. Ina zaune a wani d'aki da yake cikin gidansa domin tun jiya da muka zo ni da Baba Hajjan tace mu zauna kawai kayanmu ma dake can masaukinmu sai turawa akayi aka d'aukosu. Ina jin messages (sakkoni) na ta shigowa wayata ban duba ba dalili na riga na san ba ni da nutsuwar da zan bada amsa abinda dai na yanke a zuciyata shine duk wanda ya tambayi ya akayi hakan ta faru zan ce masa ban sani ba. Shigowar Hajiya Saratu d'akin da kaya a hannunta ya sanya da sauri na goge hawayen kumatuna.
Sai ta girgiza kanta ta karaso wurin da nake tana fad'in." Ki yi hakuri don Allah ki daina wannan kukan Amina. Wallahi tallahi kin ji rantsuwar Muslimi ba zamu cutar dake ba. Duk abinda hajiyarmu ta kaunace shi ya zame mana dole mu 'kaunace shi. Kuma albishirin da zan yi miki shine kin yi miji, ba don Tajo d'an'uwana ne ba nake gaya miki haka, mutum ne da rabin mutum. Zai baki kulawa sosai, kuma zaki samu jin dadin rayuwa dake da yaranki. Ki kwantar da hankalinki, kuma jita-jita na mutane ya daina damunki ki barwa Allah lamarinsa tunda ke kanki idan ki ka yi wa lamarin nan duba na tsanaki za ki san shirin Allah ne."

Murmushi kawai na iya bakina ya yi nauyin da ba zan iya ce mata ba na son d'an'uwanta ba. Gashi kuma ina jin nauyinta domin tana da irin sunan Mamana. Kawai sai na sunkuyar da kaina kasa. Ta ajiye mini kayan da ta shigo dashi tana fad'in." Ki shirya yanzu nan ya kira ni a waya na gaya miki za su shigo tare da abokanansa za a yi hoton tarihi."
Tana gama maganarta ta juya ta fita daga d'akin a gaggauce.
Ledojin na bude dogayen riguna ne manya irin na larabawa da hijabai masu kyawun gaske. Da band'aki a cikin d'akin na shiga na yi wanka na fito na zura d'aya daga cikin dogayen rigunan a jikina. Na d'auki karamin hijabi iya kafad'a nasa. Turare na d'auka akan madubi na fesa a jikina na nemi wuri na zauna zuciya gabad'aya a cunkushe.

Sa'kkonin da aka turo mini ta inbox na fara dubawa. Wanda na yi wa duban tsanaki na Anti Yagana da Sahura. Tambayata suke yi shin labarin da suka ji yana yawo a gari da gaske ne. Kuma ya akayi hakan ta faru.
Na basu amsa da gaske ne. Amma ni ma ban san yadda aka yi ba, kawai su taya ni da addu'a. Idan kuma kwanana ya kare suka kula mini da yarana."
Nasa hannu na goge hawayen da ya shiga zarya a kumatuna wanda ya yi daidai da lokacin da aka turo kofar d'akin a bazata na daga kaina muka yi Ido hudu. Ya mayar da kofar ya rufe ruf. Ya nufo wurin da nake cikin shigar larabawa harda alkyabba irin tasu.
Gabana ya dinga bugawa da k'arfi da k'arfi. Zuciyata tana harbawa kamar zata faso kirjina ta fito.
Daf da ni ya tsaya masifaffen kamshin turaransa ya fara surnanowa hancina.
"Amaryar Tajo." Maganar ta daki kunnena. Hanci na ja ban dago kaina ba balle na kalle shi.

Wannan littafin dai na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini muddin ba ki biyani hakkina ba, mu kula sosai hakki komai kankantarsa sunan hakki.

"Na gode sosai, da wannan sadaukarwar taki, kin daraja mahaifiyata. Kin kar'bi ro'konta, wannan dalilin ya sanya na baki gurbi mai girma a zuciyata. Ba ni da ra'ayin aure a yanzu saboda tarin matsalolina. Amma ba ni da k'wanjin yin turjiya ga umarnin mahaifiyata. Kada ki damu yaranki ki zo tare dasu, ai d'a duka na kowa ne, Allah Ya raya su, ke kuma Allah Ya ba ki hakuri da juriyar zama da ni."

"Ba zan iya zama da mazina ci ba. Ba zaka same ni ba har abada. Aure an d'aura dai amma zai zama na kwangila. Zan zauna a gidanka zan cigaba da hurd'odina na yi hakan ne saboda mahaifiyarka, amma ni ba ni da burun auran irinka, abinda yake cikin zuciyata na fito na gaya maka. Kana da damar auro wata, amma ni kam ba zan iya had'a jiki dakai ba."
Ido cikin Ido na gaya masa haka domin tun yanzu gwara ya san manufata. Haka kawai nake masa kallon mai cutuka a jiki. Domin duk mutumin da yake zina ba zaka raba shi da matsaltsalu ba.

Ya jima yana kallona kafin ya nisa. Ya daga kafadarsa yana fad'in." Ai aure ba abin wasa ba ne, ni ba munafiki ba ne, kuma ba zan fara a kan wannan karamin dalilin ba. Ni ya kamata na kyamace ki saboda mazan da ki ka yi tarayya dasu a baya. Amma har kina da bakin fad'a mini magana. Ki zauna a shirye duk lokacin da na tashi kar'bar sadakina zan turo miki likita ta auna ki. Domin ni har yanzu saurayi ne babu wata mace da na sani."

Wani irin kallo na yi masa a watse na ce." Sai dai a auna mu a tare don wallahi ba zan yarda ka shafa mini 'kanjamau ba."
Sai ya fashe da dariya irin wadda ban ta'ba ganin ya yi ba. Ya nuna kirjinsa da hannu yana cewa." Ni ne mai kanjamau!"
Murgud'a bakina na yi na kawar da kaina gefe.

Ya nisa kafin ya ce." Okey to shikkenan yanzu dai ki tashi muje abokaina suna falo wai sai an yi mana hoton tarihi Ina ce Hajiya Saratu ta gaya miki ko?"

Shiru na yi ban bashi amsa ba, kuma ban tashi ba.
"Kin ji ni ko?" Ya fad'a can kasan makoshinsa. Ban motsa ba.
"Amina."
Ya furta sunana a hankali tare da dora hannunsa a kafada. Na goce tare da mikewa tsaye ina gyara karamin hijabin din wuyana. Kawai na tsince shi yana satar kallon kirjina. Da sauri na dan gicciya gabana na faduwa. Ya miko mini hannunsa.
"Sa hannunki a cikin nawa, ai ko ba ma son juna ba za mu nunawa duniya ba ko?" Yafad'a yana matsowa jikina. Na matsa da saurin gaske. Sai ya gyara fuskarsa babu fara'a. Ya furta." Ba na son sakarcin banza, ko kin shirya ba ni kunya ne a cikin mutane? Duk abinda za ki nuna a yanzu kamar kina gayawa duniya yadda akayi auran nan ne, kin san matsayina a ko'ina, kiris jama'a suke jira su samu abin magana. Yadda nake daure zuciyata kema ki daure zuciyarki a yi lamarin nan cikin girma da mutunci ko nawa kike so zan baki."
Hawaye suka zubo mini Ina kuka na ce." Ni bana buk'atar ko kwabo. kuma don Allah ka ce musu ba ni da lafiya su tafi yadda nake jin ciwo a raina ba zan iya nunawa duniya auran so muka yi ba."

"To na ji, yanzu dai ki yi mini wannan alfarmar kin ji ko, a cikin mutanan da suke falon nan akwai manyan 'kasar nan. Kuma kin san balaraben mutum da kara da karramawa, na amince duk yadda ki ka tsara zaman za a tafi a haka, ni ma ai na san tunda na yi rashin Samira a duniya ai babu wata mace da zata maye mini gurbinta. Amma dai ni dake muna cikin damuwa. Ki b'oye kamar yadda nake b'oyewa.

Nasa hannu ina goge fuskata. Sai ya shiga taya ni, Yana cewa."Mutane da fahimta suke Amina, kin ga kukan da kike ta yi ya janyo idanunki sun kumbura sun yi jawur, ummm, ki yi hakuri haka kin ji ko, ki barwa Allah kamar yadda ni ma na bar masa."
Cikin rararshi yake magana yana ta gyaggayara mini fuskata da tafin hannunsa da yake yake kamshi
Na d'auke hannun da sauri bai ce komai ba ya riko hannuna muka fara tafiya a jere daf da za mu fita ya tsaya yana kallona, ni kuwa sai kawar da kai nake yi. Kawai ba zata na ji saukar hannunsa a tudun kirjina da sunan Yana gyara mini zaman karamin hijabin wuyana.
Da sauri cikin zafin nama na buge hannun. Dan ban san ma na yi hakan ba saboda gigicewar da na yi. Na matsa gefe tare da buga kafata. Murya na rawa na ce." Wai menene hakane?"
Ya dube ni cikin nutsuwa ya furta." Menene kuwa, kawai don na gyara miki hijabi shine za ki bige mini hannu."
Zumbura baki na yi." Ba na so ni gaskiya."
"To, na ji ba zan sake ba, mu je, amma ki saki fuskarki."
Ban ce masa komai ba. Amma na saisaita fuskar tawa. Ya kama hannuna muka fita haka.

Har kasa na zube na gaishesu sun kai su shida kuma kamar yadda ya fad'a manya ne don yawancinsu da masu tsaronsu .
Hajja kam sai murmushi take yi ta yi ado sosai cikin wani leshi bulu da farin mayafi. Babanmu ma cikin sababbin kaya.
Hotona akayi sosai duk Ina kusa da shi, wani ya d'an rungomo ni jikinsa wani kuma ya rike hannuna. Shi ma yana ta walwala ni kuwa sai ya'ke na ke yi na rasa abinda yake yi mini dadi a cikin raina.

Gabad'aya da sadakina da kyautukkunan da na samu Hajiya Saratu ta had'a a kwati ta bawa Babanmu shi kuma ya shigo har d'akin da nake ya kawo mini yana kara yi mini bayani sadakina dubu dari biyu ne duk da kudin garin aka biya. Sannan kuma yana kara gaya mini daga zarar

Chapters

Related Ebooks
03, August 2026
Aisha kabir iliyasu

Please book for gudun aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login