Showing 423001 words to 426000 words out of 450388 words

Chapter 142 - Gudun Aure Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

4062

blood group ma komai ya daidaita yadda ake so. Tsakanin shi da ita sai na rasa wanene ya fi farinciki kasancewar yanzu na taka tudu biyu sai girman da yake ba ni ya kara tsananta duk da maigidan ya gaya masa yayata ce amma risina mini yake yi kuma ba shi yarda mu had'a ido. Ni dai da muka dawo daga asibitin a mota na bar su shi da ita suna zantawa.
Ina shiga ciki na riski Hauwa tare da Mairo a falo suna hira yaran dama sun tafi skull tun safe.
Na zauna kan kujera cikin hijabi don ban iya cire shi ba ganinta a falon a zaune sai nake tambayar zuciyata dalilin zuwanta.
Muka gaisa sosai da sakakkiyar fuska abin har ya so ya ba ni mamaki amma dai na share ban nuna mata na ji dadin zuwanta ba haka zalika kuma ban nuna mata na ji haushin ganinta ba ta ce mini sallama ta shigo ta yi mini farkon wataran maulid wanda saura kwanaki uku kacal mu shiga za ta tafi umara kasa mai tsarki. Na taya murna sosai da fatan alheri mu kad'an ta'ba hirar yara kad'an kafin ta tashi da zumar tafiya ni ma na mi'ke har bakin kofa na taka mata ta fita tukkuna na dawo falon na ce da Mairo ta shiga kicin ta cewa Baba Tabawa su dafa zogalen nan da Masa'udu ya kawo mana tsaraba daga garinsu domin kafin maigidan ya fita ya ce a yi masa kwadonsa idan ya dawo da yamma zai ci.
Ta tashi da azama kuwa ta nufi kicin goye da Hassan a bayanta. Usaini kuma ina da tabbacin yana bayan Taburni tunda kusan tare suke rainon su biyu wasu lukutan Hadiza da Baba Tabawa na sanya musu hannu.
Hadiza ta shigo cikin annashuwa sai na fashe da dariya ina kallonta cikin zolaya na ce." Masoya masu kafasiti Hadiza na fahimci Sukairaju ya saye zuciyarki kina sonsa ba."
Ta zauna tana kallona da murmushinta har yanzu ta ce." Sosai kam, kin san lokacin kuruciya sakarci muka dinga yi na zo na za'bi mugun mutumin nan Alhaji Halilu Umma da Baba Sule suka rud'e saboda watsi da kudin da yake mini, lokacin wallahi ban san menene so ba Amina ni ma kudi da jin dad'in kawai nake hange ashe mugu ne azzalimi na ci wahala a hannunsa ba kad'an ba."
Na gyada kaina a tsanake na ce." Kaddara ce ai Allah ya zano shi a matsayin mijin da za ki aura amma shawara anan shine kada ki yarda ki nuna masa tsananin son da kike yi masa maza suna da wani abu a duk lokacin da suka gane mace na mutuwar sonsu to sukan kwatanta rashin adalci a kanta. Amma ba duka ne suke da wannan halin ba. Ban ce kada ki nuna masa k'auna ba amma daidai misali."
Ya gyad'a kanta a hankali tana fad'in." In sha Allahu zan lura amma fa ni kaina yanzu ne nake jin ina soyayya Amina."
Na yi shiru ban ce komai ba sai ta cigaba da cewa yanzu muka gaisa da Hauwa a farfajiya ta tare ni da fara'a sosai abin har ya ba ni mamaki."
Na ce." Ta sauko ai tana neman shiri ta zo yi mini sallama ne wai za ta tafi umara cikin satin nan."
Ta ce." Allah Ya kar'bi ibada ya sa ta je lafiya ta kuma dawo lafiya."
Na amsa da Amin ta d'an yi jim kafin ta cigaba da cewa." Wai tambayata take yi yaushe zan je gidanta mu gaisa sai na ce mata zan zo in sha Allahu. Shine ta wuce tana cewa wai tana saurarena kafin ta tafi umara."
Na ce." Wata gaisuwar kuma za ku yi bayan wadda kuka yi a yau Hadiza?"
Ta ta'be bakinta tana fad'in." To ni ma haka na gani sabon salon makirci ne ai babu inda zan je kuma ni ban yarda da wannan faram-faram din na ta ba, hausawa suka ce ruwan da ya dake ka shine ruwa.
Ban ce komai sai murmushi na saman lebe Hauwa kenan neman mutane take yi yanzu ga shi kuma ba ta iya mu'amula ba. Nusaiba ta sha gaya mini wai tana kiranta a waya ita har tana mamakin a ina ta samun lambarta yarinyar da ta yi wa zagin tsamar nama da cin zarafi shine yanzu take janta a jiki saboda tana kishin yadda yaran ke dabdala a gidana domin ko zuwan Salim hutu nan wurina yake d'aukar abinci kamar yadda d'an uwansa ke zuwa ya d'auki na rana da daddare Adam kwana ne kawai ba ma yi a tare a gidan. A can gidansu yake kwana tun bayan abinda ya faru da Nabila to yanzu kuma sun juya Legos din shi da Salim din domin cigaba da gudanar da abinda zai kawo musu cigaba a rayuwarsu. Lamarin yana yi mata zafi ba tun yau ba na lura da cewa ta tsani duk wanda zai ra'be ni shima sai ta dasa masa k'iyayya. To yanzu kuma taga hakan bai yi ba ta fito da wani salon. Lambar waya ai ba za ta yi mata wahala ba ko a wurin mijinta za ta iya samu.
Kafin ya shigo gidan ya kira ni a waya yana fad'in zogalan nan da Masa'udu ya kawo dama buhu guda ne d'anye sai uwar doya da albasa ya ce a dibarwa Hauwa na ce to ina mamaki shin shine ya gaya mata ko kuwa a takaice dai na ce." Zogalan kad'ai ka gaya mata an kawo ko da sauran abubuwan?''
Na ji shi yana fad'in.'" Shi tace tana buk'ata idan ma aka ajiye shi zai bushe ko ya lalace ku d'ibar mata tunda tace tana buk'ata."
Na ce." Ba wani lalacewa da zai yi ai kana son miyar zogale sai mu busar da shi."
Ya ce." A d'ibar mata dai na ce." Sai na tare shi da sauri ina fad'in." Ai shine na ce iya zogalan kawai ka gaya mata an kawo ko da sauran tsarabar."
Ya ce." A a ni ban gaya mata ba Giwa mun yi waya ne yanzu take gaya mini ta shigo yi miki sallama bayan ta fita suka gaisa da Masa'udu tasan ya yi tafiya zuwa garinsu shine ya gaya mata abinda ya kawo muku."
Na ce." To tunda hakkinta za ta fitar mata ai kamata ya yi ta buk'aci sauran kuma saboda neman magana ni me yasa ba zata gaya mini ba."
Cikin k'osawa ya furta." Ba ni son 'karamar magana ta zama babba Amina kwana biyu abubuwa sun yi sanyi dalili na fahimci kowacce a tsakaninku kada ki girmama lamarin don ta sanar da ni ba wani abu ba ne, ni kuma ai gashi na gaya miki."
Na ce." Munafurci ne kawai idan da yarda babu wani nufi a zuciyarta ai ni ya kamata ta gayawa tana buk'ata tunda tana da lambar wayata."
Ya datse kiran ba tare da ya ba ni amsa ba.
Kicin din na shiga na ce su raba tsarabar nan kashi biyu daidai a bawa Hauwa.
Hadiza dake gyara alayyahu ta ce." A a ai nan kuke da yawa Amina na yi zaman gidan iyali na gani kin san dai Alhaji Halilu matansa biyu ni ce ta uku ko, to duk abinda ya kawo nawa ne kad'an tunda ba ni da yara. Me zai sanya za a yi haka kuma?"
Ina dariya na ce." To Masa'udu garin kaud'insa ya gaya mata ya kawo tsarabar zogale da albasa tare da doya shine tana zuwa gida ta kira maigidan wai tana son zogale.
Taburni ta ce ." Ban da abin Hajiya Hauwa ai ke da ita duk daya ne sai ta gaya miki tana buk'ata ta shigo ta dibi yadda ranta yake so."
Murmushi kawai na yi ban sake tankawa ba Ina jin su suna ta magana. Hadiza na fad'in." Idan an raba an bata biyu ba a yi miki adalci ba."
Anan ne na ce to wannan tsaraba dai ta Masa'udu na neman ta janyo cecekuce ayi dai yadda na ce din idan ma kyautar da su za ta yi shikkenan a bata zogale ne dama yake yi mana wahala don ta doya da albasa wannan ai ba matsalarmu ba ce ko ku raba daidai a had'a mata cikin buhu sai ta aiko ta d'auka."
Na juya na fita daga kicin ina jin maganganunsa akan lamarin.
Yana kuwa shigowa da abinda ya fara kenan na ce an raba kashi biyu ta aiko ta d'auka ko kai ka d'auka ka kai mata.
Yadda na fadi maganar a harzuke shine abinda ya sanya shi tsirawa fuskata ido yadda ya nuna kamar abin ba na tashin hankali ba ne gashi ina ko'karin girmama shi. Ni abinda ya ba ni haushi yadda ta kasa tambayata sai shi zata tambayata tunda ai Masa'udu direbansa kuma shi ya kawo kayan babu buk'atar ta tambayeni wanda yake zaune dominsa shi za ta tambayata ni ban isa ba. Yanayin yadda ya damu da lallai sai an bata tamkar wadda ta bawa umarni.
Haka dai ya dinga kaucewa neman fitinata domin so na yi ya tanka na fad'i abinda yake raina sai ya'ki biye mini ya kira ta a gabana yana fad'in ta turo Ladidi ko yaron dake bawa shokokin gidanta ruwa ya d'aukar mata.
Ya kashe wayarsa. Ya dinga jana da hira a lokacin da nake zaune a gefansa yana aiki a computer na ki biye masa ni ma. Sai ya ja bakinsa ya yi shiru tsayin minti ashirin da biyar ya gama abinda zai yi ya rufe Loptop din Yana kallona ya ce." In banda dole sai an janyo mini tsiya a gidana ya za a yi rigima akan zogale Amina wai don Allah menene yake damunku ne?"
Na dube shi ina fad'in." Halin tsiya ai yana wajanta Allah Ya yi maka mai kyau duniya da lahira ni ai ban ce komai ba, ka ce a dibar mata zogale an yi yadda ka ce din to kuma sai ya zama lefi."
Ya gyad'a kansa still idonsa a tsaye a kaina ya furta." Shine na ce ai kuna nema ku ba ni kunya saboda rashin tsinkaye da tunani ita tana can tana surutai na banza bisa wani zargin da bashi da toshe ke kuma gaki ba ki da fahimta wato cewar da na yi a dibar mata zogalen da Masa'udu ya kawo sai ya zama a lefi a wurinki Amina har ki dinga ko'karin zagi na."
Da sauri na ce." Yaushe na zage ka don Allah?"
Ya nuna kirjinsa da yatsa yana fad'in." Kin san dai ba zan yi miki k'arya ba ko, ai ni ba kurma ba ne na ji lokacin."
Kasa'ke kawai na yi ina kallonsa da mamakin yaushe ya koyi 'karya mai lasisi irin haka. Nasan dai gwani ne shi wurin juya magana idan yana so ya kare kansa ko ya kashe wata rigima yanzu nan zai sar'kafe ya cukurkud'a magana ya kuma dage shine da gaskiya yanzu ma abinda ya shirya yi kenan uana so ya d'aure ni da jijiyar jikina ban zage shi ba amma gashi yana fad'in na zage shi ai ba mahaukaciya ba ce ni.
Ya cigaba da sakin maganganu." Duka kun raina ni wallahi saboda na yi sanyi ina bin kan kowacce da abinda take so babu wadda nake tsoro na yi miki ta bafulatani aradu na d'aga 'kafa ne kawai don ganin yarana suna girma nan da shekaru takwas twins dina sun zama cikakkun 'yan mata 'yan 16years lokacin ko ina raye ko ba na raye Allah ne ka'dai masani."
Ya sassauta maganar cikin alhini tare da 'kura mini ido.
"Hum kawai na ce kafin ajiyar zuciya ta biyo baya na furta." Allah Ya kyauta dai Ina ganin dai ko tsufa muka yi gaskiya da wahala matarka ta canza domin ko kai kasan yadda nake hakuri bisa dabi'unta yanzu don girman Allah menene don ta kira ni ta ce tana son zogale kai ba ka yi tunanin cewa akwai wani abu a zuciyarta ba har yanzu."
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Yadda ba zata canza ba haka zalika kema ba za ki janza ba giwa. Na san halin kowacce a cikinku. tunda Ubangiji na ya jarrabeni daku a matsayin abokanan rayuwa dole na yi hakuri mussaman kuma da kuke ha'kuri da ni."
"To yanzu dai idan na fahimta ka goyu da bayan abinda ta yi kenan tunda na ga kamar kana kare ta."
"Ban goyu da bayanta ba Amina na nuna mata cewa tana da ikon shiga kicin dinki ko kuma ta tambayeki ba ni son kumbiya-kumbiya fa wasu lukutan daga cikin dabi'unki na burge ni domin ba ki da rufi kuma ba ki da munafurci na gane shine dalilin da ya sanya idan an yi miki hakan yake yi miki zafi."
Na janye idona daga kansa ba tare da na ce komai ba. Ya saki ajiyar zuciya yana fad'in." Kafin na shigo Sukairaju ya yi mini bayani har results din duka ya nuna mini. Na yi murna na kuma yi addu'a kwarai abinda za a yi yanzu da kaina zan tashi zuwa Kano wajan Baba domin nemo auran hakan ya yi ko?"
Na d'an saki fuskata ganin yadda ya karrama ubana har yana kiransa da Baba na ce hakan ya yi sosai Allah Ya tabbatar da alheri."
Ya amsa da Amin yana fad'in." Idan kuna da idon sanin can garin nasu Sukairaju hakkinku ne domin fad'ad'a bincike a kansa da zuriarsu domin sake gazgata abinda muke hasashe da wanda na sani a kansa."
"Gaskiya ba mu da kowa a garin wallahi, amma komai na Allah ne kuma tunda ka ba da tabbacin akansa da zuriarsu ai ba sai an sake wani binciken ba alheri dai muke ta addu'a akan Allah Ya wanzar musu damu gabad'aya.''
Ya ce." To hakan ya yi in sha Allahu rabbi cikin satin nan zan shirya zuwa Kano kuma babu buk'atar d'aukar dogon lokaci tunda dukkaninsu babu yaro a ciki."

***
To idan Ubangiji na ikonsa babu wani mahaluki da duk iko da shahararsa a duniya da ya isa ya dakatar buwayar Allah domin kuwa rahamominsa suna da yawa. Ni dai ban taba tunanin wai akwai dangantaka ta aure tsakanin Hadiza da Sukairaju ba sai yanzu da Allah ya bankad'a abinda yake rubuce a kudirarsa. Kamar yadda nake wannan tunani da mamakin itama nasan haka take cikin wannan tunanin na kasantuwar auransu da Ubangiji Allah yake shirin tabbatarwa.
Bayan zuwansa wajan Babanmu an samu nutsuwa sosai da fahimtar juna tare da amincewa daga kowane bangare domin kuwa ba su riga ma sun tsayar da maganar d'aurin auran ba sai da kawunan Sukairajun suka zo su biyu daga Zamfara aka yi zaman dasu tare da bada sheda da tabbacin cewa sun kar'ba bisa amana. A take a lokacin ya biya sadakin Hadiza bisa jagorancin kar'bar auran da ya biyo ta hannunsa. Hadiza ta yi goshi dubu dari biyar sadaki suka tsayar da ranar d'aurin aure ranar takutaha ranar da aka haifi manzon Allah s.a.w domin samun falala da dacewa.
A ranan da daddare Ummansu ta kira ni a waya godiya kamar za ta yi kuka har sai da na ji wani iri a raina na dinga tausarta domin dai kukan da ta dinga dannewa sai da ta yi shi a cikin waya da kyar muka to sallama. Na kira anti Yagana a gaban Hadizan na sanar mata da yadda aka yi itama murna kamar ta zuba ruwa a k'asa tasha. Hadiza na gefe sai murmushi take yi domin tunda na gaya mata mun yi waya da maigidan ga yadda ake ciki ta rasa yadda za ta yi da ranta saboda farinciki.
Kwanansa hud'u a kano ya dawo da daddare tare suka je da angon dama. Na tarbe shi sosai tare da yi masa bangajiya da godiya a daran kuwa ya samu tar'ba mai kyau mai tafe da sabon salo wanda bai san shi ba.
Muka shirya tafiya kano kafin zuwan ranar ni da ita da yaran duka tunda an yi musu hutun boko da islamiyya mun shirya walima domin nuna farincikinmu ga Allah anti Yagana ma tana can tana shiri domin ta ce kaf yaranta da su zata zo.
Saura kwana biyu mu tafi Hamusu ya kira ni yana gaya mini Sukairaju ya sanya shi had'a lefe akwati shida tambayata yake yi aure zai yi?"
Hadizan tana zaune a gefena a lokacin da muke yin wayar na gaya masa aure zai yi kuma Hadizar gidanmu ya kuwa shiga farinciki sosai yana ta fad'in ta samu lefe domin milayan shida ya tura ya ce a had'a lefe na kece raini kuma a shagonmu." Lamarin ya yi mini dadi sosai na juya ina kallonta tana murmushi bayan mun yi sallama da shi na dube ta kafin ma na yi magana ta furta." Kudin ya ce zai ba ni sai kawai na ce ya yi magana da Hamusu ya kuma tura masa shi zai had'a komai."
Da murmushi a tare da ni na furta." Na taya ki murna Hadizan gidanmu ta yi goshi kin zama bazawara mai kafasiti yanzu abinda ya rage muna dira kano a yi gyaran jiki sannan na kai ki gidan GARKUWAR MATA ta had'a mini ke da kyau!
Ta kuwa fashe da dariya sai ka ce wata shashasha. Na shiga taya ta sai muka zama kamar sakarkaru rayuwa kenan bayan wucewar kalubale mabambamta da 'kin jinin juna tare da 'kyama ashe akwai ranar da Hadiza za ta k'aunaci cigabana duk son kud'inta sai ta ce a a gwara a yi sayayya a wurina saboda na cigaba. Lallai bahaushe ya yi gaskiya da yake fadin ranar naka sai naka.............
'?
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*172*
Duk abinda ya kamaci Hadiza na gyaran jiki ni na d'auki nauyi don har tana cewa za ta gayawa angon ya bata kudin gyaran jikin na ce a a kada lalacewar ta yi yawa yadda ya fitar da kudi masu kauri domin yi mata lefe irin na budurwa mai jini a jika bai kamata a ce ya bada wasu kudin ba. Sosai na yaba masa dangane da abinda ya yi mata duk a kokarinsa na ganin ya dakusar mata da damuwa kuma da alama yadda Allah Ya jarrabeta da sonsa haka shima yake k'aunarta domin matar so ai ake yi wannan hidimar a matsayin dai Sukairaju tsayayyan namiji mai suffa da mazantaka ina da tabbacin ba zai rasa 'yan

Chapters

Related Ebooks
03, August 2026
Aisha kabir iliyasu

Please book for gudun aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login