Showing 435001 words to 438000 words out of 450388 words

Chapter 146 - Gudun Aure Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

4271

ni ma cikin nema na gan ki muka yi aure kina neman ki, bata yarda ba ta kai kara wurin Hajja wai kamar ni Hauwa ke yawon kaini k'ara saboda ba ta da mutunci tana ganin na fifitaki ina kashe miki kudi ita na bata tsohon kamfani sai dai a canza mata da abinda na yi miki shin a cikinku ko akwai wadda ta sanya ni d'aukar dukiyata na baku, alheri ne kawaii na yi muku ganin tare duka aka nemi dukiyar daku tana ganin abinda na yi miki ya fi wanda na yi mata akan hakan kuwa lallai ranta zai b'aci don ban ga dalilin da zai sanya ta tsananta k'yashi a kan ki ba, kema Allah ne ya yi miki daidai gwargwado kuma kin nema ni hannu kawai nasa miki kuma sai daga karshe ko ba haka ba ne?"
Na gyad'a kaina ina fad'in." Hakane amma akan hakan ka ke cewa za ka saketa ai ba hujja ba ce wannan kuma abinda ta nema ka fi karfinsa don ta tsananta kishi da k'yashi a kaina babu lefi ko ka manta kishi ne a tsakaninmu kowa fa da irin zuciyarsa, wallahi ban ji komai ba amma don girman Allah in dai zan baka shawara ka d'auka to ka yi mata yadda take so tunda kana da iko ka daidaita tsakaninmu itama ka bude mata plazar sai ka kar'bi kamfanin ka kawai tunda dama wahalarsa yawa gareta."
Ya girgiza kansa." Idan na yi mata plaza sauran shops din na kwari market kuma wa zai yi mata? tana cewa ai duk ni na yi miki"
Yar dariya na yi kad'an na ce sai ka yi mata menene a ciki ai Allah Ya hore maka?"
Ya girgiza kansa a nutse ya furta." Babu wanda zai karya mini rantsuwa Giwa ai na ce ta bar shi a hannuna zan a cigaba da aiki da shi a madadinta kuma abinda take han'koro za ta samu rashin yarda ne kawai da ci da zucci. Ba zan yi wata plaza ba yanzu wannan shine karshen magana."
"To kasan halinta da rashin yarda da kuma taurin kai kenan idan kai da kake matsayin jagora baka yi yun'kurin ganin ka nemo mafita ba lamarin zai lalace ai."
"Ai na nemi mafita tuntuni aiwatarwa zan yi kawai ko kin ga na yi miki kama da namijin da mace za ta juya ne Amina. Wasu lukatan Kawai ina biye muku ne domin ba na son hayaniya wa za ta gayawa taurin kai ne ni da ita shege ka fasa."
D'akin ya d'auki shiru bayan ajiye maganarsa na sauke numfashi Ina dubansa na ce." Yanzu kasan yadda za a yi tunda abin ya zo da haka me yasa ba za ka kara mata kudi akan kamfanin ba."
Harara ya wurgo mini kafin ya ja tsaki yana fadin. "Ba zan k'ara mata ko kwabo ba wallahi."
Rantsuwar da ya yi a karon farko sai jikina ya mutu ba wai bashi dashi ba ne bayarwa ne kawai ba zai yi ba Amma ni ina ganin idan har ya k'ara mata kudi akan kamfanin da take ganin darajarsa ba ta kai plazata ba zuciyarta zata yi sanyi ga shi kuma ya rantse da gaggawa.
Na ce." To ni zan k'ara mata amma a madadinka."
Ya dinga shillo mini harara kafin ya yun'kura ya tashi bai ce komai ba ya shige toilet yana tsaki. Ni kuma a ganina ai ba abin jin haushi ba ne don zan bata kud'i ba ni son ya saketa ko kad'an wallahi domin abin ba zai yi mata kyau ba daraja dai da alfarmar tana a hannunsa ta yi hakuri ta barwa Allah ikonsa kamar yadda ya fadi yanzu Ubangiji ne ya yi mini wallahi ban ta'ba tunanin zan kai matakin da nake a yanzu ba.
Kwanaki biyu muna ta abu daya gabad'aya ma ya'ki ya saurare ni da shawarar da na kawo sai hanya hanya yake yi yana ta shirye-shiryen tafiya Legos abinsa ni kima ina ta damuwa ga ciwo ciwon da na fara cin karo da su na kasala da zazza'bi taruwar yawu a baki da yawan bacci ciki ne da ni na tabbatar domin ban ga al'adata ba rashin sukuni da abubuwan da suka kutso ya sanya bai lura da canje-canjen da na sake samu ba.
Cikin wannan yanayin muka bude shagunanmu da bisimillah abin sai godiya da sake godiya wurin Ubangiji mun samu alheri kwarai da gaske domin yanayin yadda aka s'aukaka farashi a karon farko ya sake janyo mana suna a duniya da costumer's mabambamta. Daga cikin manema labarai ('yan jarida) har da ni Binta Umar Abbale na tafi da biro da takardata domin d'auko rahoto na samu abin rubutu a kai
Na shiga cikin mutane ina ta ra'be-ra'be duk na ki'dime hankalina ya kasu kashi -kashi shin rahoton zan d'auko ko kuwa kallon zan yi kaya na alfarma kamar za su bud'e ido jama'a kuwa ga su nan hamsha'kai suna ta parking din motocinsu
Allah sarki ashe ta hango ni a labe ina le'ken shagon supplements dinta da ya tumbatsa da ya kaya ni shine ya yi bala'in d'auke mini hankali na saki baki galala ina ta hango manyan supplements din da suke tumbatsar da mace da tayar mata da komad'ar jiki cikin zuciyata ina ta fad'in dama ina da kud'i zahiri da na sayi wanda zai dawo ni shamshakiyya kalar 'yan gayu irinta duk da yake supplements din kala kala ne amma dai ga dukkanin alamu duk abinda yake cikin wannan shamsh'akin shagon nata sahihi ne babu cutarwa. 08089965176 domin neman karin bayani Aikuwa ganina sai ta yafitoni da hannu da wannan fara'arta tata ta ce da ni na za'bi abinda nake so. Na dinga washe bakina don saura kad'an na daka tsallen murna na ajiye 'yar zabirata a can wani waje inda wani mutum yake zaune da Loptop a gabansa amma ban iya ajiye biro da doguwar pepper din da take hannuna ba.
kai tsaye shagon na kutsa ina zagaye shi bakina ya ki rufuwa.
Wani kwando nai zurfi na ciko da supplements ina ayyanawa a raina Allah Ya sa kada ta ce sun yi yawa na mayar ni kaina nasan na so zuciya amma cikin ikon Allah ta kar'ba ta dudduba tana murmushi ta ce a zuba mini a leda.
Na yi ta godiya na kar'ba ina duba jikin ledar wadda ta kasance ta mussaman mai d'auke da logo da bayanai bambamta a jiki.
Daf da zan fita kawai na hangi wasu mata masu kumari sun k'oshi 'kwarai daka gani sun ci sun tayar da kai
suna ko'karin kutsa kansu shangon zannuwa. Kowacce rataye da jaka sai na bi bayansu ina ji suna fad'in dole kam ai Amina ta mu ce dole mu yi patronizing d'inta duk dai ta kafu ta tsaya da k'afafunta amma yadda ta yi kwasha-kwasa da kayanta irin haka ba kowane d'an kasuwa ne zai iya yin abinda ta yi ba. La'bewa na yi inda ba za su gan ni ba don da kunya ace ta sake ganina tunda ta sallame ni bayan sun shiga sai na le'ka kaina abinda ya ba ni mamaki bai wuce ganin yadda suke gaisawa cikin raha da wasa da dariya ba ashe k'awayenta ne Nahajarama Maryam Saminu Sulaiman Maman Fu'ad da Mama Hauwa zaria na yi zuru ina ta lek'ensu suna ta hira ta sanya an basu wurin zama har da lemo bayan sun gama hutawa suka tashi suka fara dudduba shops din suna sanya albarka da fatan alheri. Can na hangi wasu iyayena suma sun shigo plazar cikin annashuwa ban yi mamaki ba domin dai duk cikinsu babu mutuniyar banza mata ne nagartattun da suka mayar da d'an wani nasu Hajia Usainakaita Mommy fossima Nijar hajia Halima wada kura hajia karimatu Haladu Nasiru da hajia Halima Dalha shehu. Na kuwa ji dadin ganin yadda ta karrama mini iyaye suma kuma sun yi mata halin karamci da dattako turaman atamfofi suka saya masu yawan gaske wanda nake da tabbacin cewa ba d'aurawa za su yi a jikinsu ba rabar da su za su yi ga iyayan marayu.
Ina nan tsaye da ledar kayana na hangi k'awayen nan nata sun fito kowacce da ledoji a hannunta niki-niki ita kuma ta biyo bayansu da raha da barkwanci na yi saurin b'oye kaina ta raka su har bakin motarsu suna yin sallama hannuwansu ri'ke da juna kamar kada su rabu.
Na sake gyara biro da takardar dake hannu ina kallonsu da wani irin murmushi wanda ni kaina na kasa gane ko na menene lallai Amina ta cancanci k'auna da soyayya domin kyawawan halayenta..

****
To cikin sa'a aka kammala bikin bude shops wanda aka d'auki tsayin sati guda ana kai kawo da hidima da jama'a cikin k'warewa da jajurcewa ta kowane fanni anyi katari kuwa domin kuwa an cimma nasara akan abinda ake nema.

Duk nisha'din da cigaban da na samu ban samu nutsuwa yadda ya kamata ba domin kuwa har yanzu maigidan ba a nutse yake ba yana dai ta yin al'amuransa ne a matsayinsa na namiji mai juria amma ni da nake tare da shi na kuma san halinsa na san a cikin damuwa yake kawai yana danneta ne. Kuma na gaya masa a wannan tsukin da shi kansa ya kasa control din matsalarsa yana da kyau ya tsananta da addu'a domin neman zabin Allah amma zahiri shirinsa da yanayin yadda yake kasancewa cikin damuwa ya fara damuna ina ganin dole na sanya hannuna a wannan rikicin duk kuwa da alwashin da na ci a baya a kan fita daga sabgarta don ganin ya fita daga cikin damuwar da yake cikinta a yanzu.

Yadda Allah Ya yi mini babu wayo kuma babu dabarata dalili kuwa in banda ni da yaran shops dina a yanzu babu wanda yasan adadin alherin da na samu a cikin kwanakin nan kacal shi kansa bai sani ba kuma ina so na gaya masa na samu riba da yawa a cikinta zan cire wani abu na bawa Hauwa tunda shi ya riga ya rantse ba kuma na so na karya masa rantaywarsa.

Ranar dana gaya masa zan cire 10m shima ya cire 10m mu had'a mata 20m kawai ya ji ne amma uffan bai ce mini ba har garin Allah Ya waye bai sake tayar da maganar ba ni ma ban tasheta ba sai bayan kwana biyu na sake yi masa magana. Aikuwa ya fara fad'a sosai kamar dama kiris yake jira yana fad'in kamfani ya yi niyyar bata tunda ta ce bata so kanta ta yi wa kwabonsa ba zai k'ara mata ba. Tunda nayi niyya na bata kud'ina ne amma shi ba a isa ba.
Sai na kyale shi kawai bayan kwana biyu na kira Hajja a waya muka gaisa sosai na sha addu'a da fatan alheri domin Hamusu ya kai mata turaman atamfofin da na ce a dinka mata anan ta dinga godiya da addu'a har sai da na ji hawaye ya ciko idona ba zan yi maraicin uwa ba tunda Hajja tana raye bata yi mini k'yashi da ba'kinciki irin na wasu iyayen mijin ko wannan alherin ya isa ni ma na ture komai. Duk da bani da hurumi akan lamarin amma Allah ya ga nufi ne sam ba ni yi wa Hauwa sha'awar abinda take yi wa kanta hasashe yadda ya d'auki wannan zafin wallahi kiris ya rage a yi ta kare. Duk shawarar da na yanke na gaya mata domin kuwa ko anti Yagana ban gayawa ba duk da nasan bata da ganin k'yashi amma za ta iya hana ni tace babu ruwana.
Wannan maganar tawa ta yi wa Hajja bazata ainun ta rasa abinda zata ce sai da na ji shurun ta yi yawa tukkuna na sake magana sannan na ji sautinta tana ta godiya tana sanya albarka tana fad'in tunda shi ya rantse ba zai k'ara mata komai ba to itama ta sanya 5m sai a had'a mata 15m na ce hakan ya yi amma da sunan duka ita ta bata kada sunana ya fito ciki. Ta ce hakan ba hujja ba ce dole a gaya mata jin ta fad'i haka sai na gane cewar ba ta fahimci azancina ba. Na jima kuwa ina yi mata bayani idan har Hauwa ta tabbatar da cewa ni ce ma na bata kudi ba shi ba ko ita Hajjan to babu shakka wutar ba zata mutu ba ruruwa ma zata sake yi tunda duk rikicin a kaina ne. Tsayin lokacin da na d'auka ina yi mata bayani ya sanya ta gane hujjata sai ta amince da hakan tana ta sanya mini albarka da addu'a akan Allah Ya ninka mini abinda na bayar ya kuma albarkaci kasuwancina.........
'?
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK.*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*175*
Bayan kwanaki biyu da kanta Hajjan ta kira ni a waya tana yi mini bayanin cewa an daidaita komai yanzu haka ma suna tare da Hauwa a gidanta da kuma mahaifiyarta kamar yadda muka yi da ita bata nuna musu da sanya hannuna ba kawai dai ta kira su ne akan su zo a tattauna domin samun maslaha kudi kuma ta kar'ba a madadin shi ya bayar domin itama ba ta nuna musu da sanya hannunta a ciki ba. Hakan ya kwantar da tarzomar da take yun'kurin tashi da uwar da 'yarta ta duka bakinsu d'aya dama tuntuni Inna Uwani ta daina b'oye -boye yanzu fili take fitowa ta nuna tana bayan d'iyarta tunda ta sha fadi cewa itace gorar gida ko ma baya. Ita Hauwa tun kafin su amsa kiran Hajjan yan-uwanta da k'awaye abokanan arziki suna ta yi mata fad'a da nuna mata daburun zama da miji da kishiya anti Zeey wato Zainab Khabir Ishak tana d'aya daga cikin wad'anda suka dinga nusashshe da ita cewar wannan abinda take yi bashi ne zai ri'ke ta a gidan aure ba domin yanzu kai ya waye an daina irin wannan kishin irin na jahilan mata da yake macace mai tsage gaskiya duk d'acinta ba ta yi shakkarta ba ta gaya mata kuskure da lefinta ta gaya mata cewa lallai ne fa sai ta gyara halinta zata cigaba da jin dad'in zama da mijinta tunda har ya iya k'ara mata miliyan goma sha biyar bayan kamfanin da ya mallaka mata to lallai hakan ya nuna yana son cigaba da zama da ita. Ita kuwa Mum Sajeeda takaicin abinda Hauwan take yi gabad'aya ya 'kumeta ta rasa ma abinda za ta ce saboda yadda take jin haushinta tana fad'in kamar wadda ba ta yi boko ba tana aikata ayyuka irin na gidadawa mata k'awar Sadiya ta wurin aikinsu nan ma ta ji labarin abinda yake faruwa har gida ta je ta samu Hauwan ta yi mata wankin babban bargo acan wajan aiki suna kiranta da anti Hally macace mara son wargi sannan tana da zafi-zafi mafiakasarin masu sunan suna da fad'a da kuma fad'in gaskiya komai d'acinta. Haka dai suka yi mata rubdugu a can bauchin Maman Ummul-kairi ta zauna da ita a tsanake ita cikin nutsuwa ta dinga jan hankalinta tana sake jadadda mata cewar ita kishiya ba a cin ta da ya'ki irin na bayyane tunda har ta fahimci abokiyar zamanta ta fita soyuwa a zuciyar mijinsu sai ta nemi hanyar ganin ta samu zaman lafiya da ita Asmau Muhammad jabbi ta sanya bakinta tana cewa kuma ta ji an ce kishiyartata bata da mugunta sannan macace mai karamci da halin girma mussaman idan an duba da irin abubuwan da ta gudanar a cikin kwanakin da suka gabata wurin sassauto da farashin kayanta. Ita kuwa Eama kallon sakarai take yi mata domin tun tana bata haushi yanzu dariya take bata tana kiranta da sokuwar mace
Aishatu waziri kuwa fadi take yi ki gurgu'de auren ki dawo ki zauna a gida wallahi akwai wadda na yi masa sha'awarta kuma a cikin mu take duk yadda zan yi sai na yi kokarin ganin ya nemi auranta tunda ke baki da wayo kin gama bayyanawa miji da kishiya munanan halayenki.

***
To ni dai Hajja bata gaya mini ranar da za ta dawo ba amma hankalina ya kwanta sosai jin cewar komai ya daidaita har ta kar'bi kudi to na tabbatar da cewar kuwa ba zata kara yin wasu kwanakin masu tsayi ba za ta dawo dakinta
Yanayin yadda yake tafiyar da al'amarunsa ban tsammaci ya san abinda yake faruwa ba gaskiya domin kuwa da ya sani tabbas sai ya yi mini maganar amma gashi yau har kwana biyu da yin waya da Hajja ban ji ya ce komai ba.
Sai da daddare tukkuna bayan ya gama cin abinci ya dube ni a nutse yana fad'in." Kin dawo da Hauwa ashe."
shiru na yi ban ce komai ba sai aunar maganar da ya yi nake yi.
Ya tsira mini ido kafin ya cigaba da cewa." Tunda kin dawo da ita sai ki gaya mata zamanki take yi babu yawuna ba kuma ruwana da ita."
Jikina ya yi sanyi ganin ta hanyar da ya 'bullo kuma hakan bai yi masa ba kenan haushi ya ji.
Na daure na furta." Ba ni da na dawo da ita ba Hajja ce."
Ya d'an harare ni yana fad'in." Duk abinda ki ka aikata mahaifiyata ta sanar da ni. Ita dai kin yi mata gwaninta kuma ta yi miki addu'a amma ni sam ba ki burge ni ba."
Na yi shiru ina kallonsa kafin ya cigaba da cewa." Tunda kudin cizonki suke yi mai zai sanya ba ki sayi fili kin yi k'aramin massalaci ba hadiya ga mahaifiyarki ko ki yi rijiyoyi na ruwa ko kuwa ki kai gidan marayu sam baki burge ni ba wallahi idan ma don ni ki ka yi bai ban sha'awa ba.
Shiru na yi na kasa tanka masa saboda jin haushin gwaliyar da yake yi mini. Ganin ban ce komai ba sai ya cigaba da sakin maganganu na gaji da sauri na daga masa hannu ina fadin." Ni don Allah na yi ai ba don na burgeka ba tunda Hajja ta yi farinciki kuma hakan ya yi mata daidai alhamdulillahi maganar ta mutu haka don Allah."
Ya tashi zaune sosai yana kallona kafin ya ce." Magana ba zata mutu ba tunda ba ni na ce Hauwa ta dawo ba na

Chapters

Related Ebooks
03, August 2026
Aisha kabir iliyasu

Please book for gudun aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login