Showing 234001 words to 237000 words out of 450388 words

Chapter 79 - Gudun Aure Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

4022

kuma za ki koma dakinki Hauwa kin ji ko?"
Tana kuka ta ce." A, a Baban Saude ni kam na ha'kura gaskiya wallahi zuciyata ba za ta iya d'auka ba."
Baban Saude ya yi shiru yana kallonta da mamaki kafin ya ce."Zuciyarki ba za ta iya d'aukar me ba?"
Kafin ta furta wani abu ya rigata ta hanyar fad'in." Ka ji abinda na ke gaya maka ko, gabad'ayansu fa Maryam ta tsone musu idan ba haka ba menene na fad'in wannan maganar, zuciyarta ba za ta iya d'aukar ganin Ina tare da Maryam ba, idan har ina son zama da ita amsar kawai na saki Maryam sai zuciyarta ta d'auka."

Yana ajiye maganarsa na ce. "Baban Saude gabad'aya maganar ba haka take ba zahirin gaskiya bai gaya maka wasu abubuwan da suke faruwa ba. Wanda ya zama lallai ace an zauna a kansu. Wallahi ba mu ware Hajiya Maryam ba illa iyaka shi da ya fifita a kanmu, gashi nan a zaune idan har na yi masa sharri to ni Amina ina ro'kon Allah Ya d'auki raina a yanzu wallahi tallahi zalitarmu yake yi." Na kai karshen maganar muryarta na rawa.
Ya nisa kafin ya ce." Ai dama shari'a ta aure ba za a ce mutum d'aya ne yake da laifi dole ta kowanne b'angare a samu abin fad'a, kuma dama ni ba ni da niyyar rufe wannan mas'alar ba tare dana tambayi kowaccenku ba,
ni babban abinda ya ba ni haushi daku shine yadda kuka had'ewa abokiyar zamanku kai kuka ware ta sannan da ki ka san cikin ya zube mai yasa ba ki gaya masa ba har sai da aka ja lokaci dole ya d'ora alamar tambaya a kanku."
Hauwa tana kuka ta ce." Dukan mu fa yake yi akan ita Hajiya Maryam din a gaban mai'aikinmu Baba Tabawa ko ita sheda ce ya dinga marina ya tunkud'e ni da karfi na fadi har sai da na yi targad'e a hannuna duk da hakan bai ishe shi ya sake ni."
Ta dinga kuka da iyakacin karfinta! Baban Saude jikinsa ya yi sanyi ya dinga maimaita kalmar duka yana kallonsa shi kuma jikinsa duk ya mutu don da alama bai tsammaci faruwar hakan ba.
Baban Saude ya dube ni yana fad'in." Kenan kema sheda ce Amina?"
Na gyada kaina tare da fad'in." I, wallahi ni na shiga tsakaninsu ma." Na fad'a a dan tsorace dalili ina jin tsoron allura ta tono garma ya gaya masa na ta'ba toshe masa hanci da fillo.
Ya ce."To akan me, Allah ya taimakeka dama akwai duka mai illatarwa a cikin shara'din aure kuma mace mai d'auke da yaron ciki, anya akwai imani a nan?"
Fuskarsa ta had'e sosai yana kallonsa da mamaki.
Sai ya kasa daga kansa ya dube shi cikin kame-kame ya ce." Baban Saude yaran nan ba su da kirki ko kad'an ni kuma ban yi mata dukan da zai illatata ba."
Cikin 'yar 'kure baban Saude ya ce." To wane iri ka yi mata?"
Ya furta." Marinta na yi?"
Ya ce." To ai mari karshen tozarci kenan a mari mutum a fuska yanzu tsakani da Allah ko tunkiya ka daure a gidanka ka mare ta, ina lefin ma gabar da kake yi da su duk da itama a shari'a haramun ce, anya kuwa ranka shi dad'e ka shirya sulhunta gidanka kuwa?"
Shiru ya yi bai ce masa komai ba.
Sai ya juyo kaina yana fad'in." Sai me kuma?"
Na ce." Magana ce akan yaranmu da ya kwashe ya kai wa matar tasa, to wannan ma yana daya daga cikin abinda yake mana ciwo koyaushe idan mun yi magana sai ya nuna kamar ya fi mu iko a kansu yana kiranmu da marasa tarbiya komai muka yi ba mu iya ba."
Ya dinga jijjiga kansa kafin ya sake dubansa a karo na kusan hud'u kansa yana kasa bai dago ba tsabar kunya ta hana shi musantawa yadda na lura yana tsoron ya tanka mu sake 'baro wata wata maganar da za ta zama abar tattaunawa tare da nuna masa kuskuransa.
Baban Saude ya ce." Idan kuwa hakane ka takewa yaran nan hakkinsu Alhaji Tajo kasan tsananin so da k'auna da sha'kuwar dake tsakanin uwa da d'anta kuwa? me yasa ka d'auki ga'barar raba sha'kuwa iyaye da 'ya'yansu. Mai yasa ka fifita Maryam a kan su? Idan har gaskiya ne abinda suka fad'a tabbas akwai zama tsakani na dakai na mussaman ko ba mu yi yanzu ba za mu anan gaba wannan ba daidai ba ne bari na gaya maka, ai ka haihu to muddin kana so 'ya'yanka mata su rayu cikin mutunci da kulawa a gidan mazajensu to kada ka zalinci 'ya'yan wasu tare da biyewa son zuciya. Maganar nan fa gaskiya ce da ake cewa duk abinda ka yi sai an yi maka." Ya nisa kafin ya cigaba da cewa."
Ban yadda ba gaskiya dole nasan a cikinsu akwai wadda ta fi kyautata maka kamar yadda ka gaya mini yanzu kana jin dadin zama da Maryam. Amma baka da dalili mai karfi ko a shari'a da za ka kwashe musu yaransu ka bawa wata bayan duk suna raye da ransu da lafiyarsu ba su mutu ba. Ina lefin ma su dinga zuwa suna gaisheta suna dawowa gaban iyayensu."
Ya yi shiru dai bai ce komai ba. Yana ta d'an lallatsa computer amma na tabbata babu abinda yake fuskanta. Jikinsa kuma ya yi sanyi ainun.

Ganin haka ya sanya Baban Saude ya dube ni a tsanake ya ce." Ku yi hakuri ni bai gaya mini hakan ba, kuma in sha Allahu zan baku gudumuwa. Ke Hauwa za ki koma dakinki in sha Allahu rabbi."

Ganin mun yi shiru ya sanya ya sake sassautawa tare da furta "kuyi hakuri kun ji salihan mata ba a san su da irin wannan sakarcin ba, suna d'aukar kishiyarsu 'yar uwarsu kamar yadda ku ka d'auki lamarin junanku da muhimmanci to itama ku d'auketa hakan ku daina ware ta, ku yi mu'amula da ita tsakanina da Allah, idan ma tana cutarku a boye sai Allah Ya saka muku lefinta daya yaranku da suke hannunta to ku d'auki alhakin hakan ku dora shi akan mijinku domin da bai kai mata su ba ai ba zata zo gabanku ta kwashe muku yara ba. Kada ku munana zato a kanta ko kuma ku 'kyamace ta, ku zauna ku yi tunani sosai ku gano akan me yasa maigidanku ya fi shau'kinta domin tunda na zauna anan yake ta yabonta har sai da na ji wani iri a raina mai yasa ba za ku yi koyi da ita ba?"
Shiru muka yi gabad'ayanmu. Sai ya nisa kafin ya cigaba da ce wa." Ni ban zo gidanku domin na sanya ku koke-koke ba, ita Amina ta san wanene ni, ta kuma san halina ciki da waje babu yadda za a yi na goyi da bayan karya na take gaskiya ba na so a sake gaya mini kun aikata wani shashancin makamancin wannan, ku dinga sanar da maigidanku matsala idan ta taso tunda ai ba zaman kan ku kuke yi ba ko?"
Babu wanda ta ba shi amsa. Ya cigaba da cewa." Na gode da nutsuwar da ku ka yi kuka saurare ni, ina fatan a ce kada na zama dattijon banza a idonku bayan na gusa ku cigaba daga inda ku ka tsaya, Amina hakan ba za ta yi muku kyau ba."
Jin ya ambaci sunana na ce." In sha Allahu rabbi hakan na za ta sake faruwa ba."
Ya dube Hauwa yana fad'in." Amina ta baki lambar wayata duk ranar da ya sake dukanki sai ki kira ni ki sanar da ni."
Ta ce." To shikkenan Baban Saude na gode....
'?
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*


*Paid book 1k akan telegram via 0542382124.. Binta Umar gtbank. Ko 07084653262*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*99*
Cike da kulawa ya ce." Ni ma na gode Hauwa, kun tar'be hannu biyu kuma kun karrama ni, Allah Ya yi muku albarka bakidaya."
Muka amsa da "Amin a tare."

Maigidan ya rufe Loptop din gabansa yana fad'in." Ba za dai ka bari ka bi jirgin yamma ba kenan."
Ya ce." Motar ma za ta kai ni gida cikin k'oshin lafiya, abinda na saba da zamanta tunda ni ba mazauni ba ne. "
Ya gyada kansa kafin ya furta.'' To babu damuwa idan mun tashi sai mu shiga can wajan Maryam din ku gaisa ko."
Baban Saude ya furta." Ai ya zame mini dole ranka shi dad'e wannan alatun da aka shirya mini yana da kyau na je yin godiya."
Ya kuwa fashe da dariya yana d'an dukan kafad'arsa."
Takaicin abinda suke yi ya dinga nukurkusata don sai nake ganin kamar ma da gayya suke yin hakan. Abin mamaki da al'ajabi wai yau Baban Saude ne da mijina suke wasa da barkwanci irin na abokai. Na girgiza kaina a yayin da nake jin wani irin bala'in takaici na taso mini ban ankara ba na ji motsin Hauwa ta mike tsaye kafin ta d'an rankwafa tana fad'in." Baban Saude a sauka lafiya don Allah a gaishe da mutan nan gidan da kyau."
Da sauri ya dawo da hankalinsa kanta yana fad'in." Za su ji in sha Allahu rabbi Hauwa." Tashi na yi ni ma ina dan d'auke kaina domin gabad'aya ba na son kallonsu saboda b'acin rai, duk da kare mana mutuncin da ya yi a yanzu amma na ji haushin yadda suke raha har yana cewa zai je ya yi wa Maryam godiya
Na furta." Baban Saude ina zuwa yanzu akwai sa'ko da za a kai wa su Dada."
Ya ce." To, amma ki hanzarta domin na himmatu." Ban ce komai ba na bi bayan Hauwa wadda na hange ta can bakin kofa tana daf da fita.

Haka muka jera tafiya ni da Hauwa babu magana kamar wasu kurame. Abinda dai ya sanya na k'ara ganin mutuncinta bai wuce yadda ta jure cin fuskar da Baban Saude ya dinga yi mana da farko ba, don gaskiya ya gayyaya mana magana a fakaice. Ni nasan halinsa a ganinsa hakan ba komai ba ne, wai idan ma abinda aka ce masa muna yi da gaske mu ji haushi mu gyara yana yabon Maryam din tare da cewa mu yi koyi da ita. Lallai Hauwa ta yi mini kara sosai duk da nasan ko bata fad'a ba ta ji zafin hakan da farko daga baya kuma da ya fahimci gaskiya har ha'kuri ya dinga bata. Ta yi shiru har ya gama bata yi yun'kurin ta mayar masa da raddi ba, duk kuwa da cewa lefin ta bai kai a ce an yi mata wannan titsiyar ba, amma ta jure duk domin yi mini kawaici hakan ya sanya ni jin kunyarta kwarai da gaskiya wannan dalilin ne ma ya sanya muna shiga gidan na dube ta a nutse na ce." Hauwa ki yi hakuri don Allah bisa abinda Baban Saude ya yi da farko haka halinsa yake wallahi. Na kuma gode sosai da karar da ki ka yi mini."
Murmushi kawai ta yi kafin ta furta." Wallahi ko kad'an ban ji haushinsa ba Amina, idan da wanda nake jin zafinsa a raina bai wuce mijinki ba shine ma'kiyana lamba daya, kuma Baban Saude ai ya yi mana abinda iyayenmu suka kasa yi mana Amina, wallahi na tabbatar da cewa ko Inna Uwani na gayawa matsalata bai zama lallai ta dubi gaskiyata ba, shi za ta bawa gaskiya ta d'ora mini lefi, to balle na samu iyayena maza ina nufin 'yan uwan mahaifina wallahi a cikinsu babu wanda zai iya tunkararsa da sunan kwatar mini mutunci saboda yana da kud'i. ai ni Baban Saude ya yi mini kuma babu shaushinsa ko kad'an a cikin raina."

Tana gama fad'in haka sai ta shige dakinta ta barni a tsaye ina bin hanyar da ta bi da kallo. Na jima a tsaye a bakin kofar falon kafin na sauke zazzafar ajiyar zuciya na kama hanyar d'akina zuciyata cike da nazarin hanyoyin da zan bi wurin ganin mutumin nan ya yi kukan zucci. Idan da hali ma ya yi na zahiri zuciyarsa ta cika da damuwa tunda shi ya sayi hakan da kansa. Yadda ba ya so ana yawon tiritirin kai shi k'ara bayan yana aikata lefi, to ni ma abinda na tsana kenan a rayuwa kuma tun farko-farkon auranmu na gaya masa ba na so ya'ki dainawa. Zai gane idan kai ni kara shine zai daidaita ni.

Ranar dai gidan na mu tsit ya kasance kowacce tana d'akinta dama ni da Baba ne muke zaman falo Hauwa ba sosai ba kullum tana d'aki a kwance. Tunda na koma na kaiwa baban Saude sak'on su Dada
ban sake fitowa ba sai bayan magariba Baba ta kammala komai tana zaune ita kadai a falon tana kallo da carbi a hannunta. Gaisawa muka sake yi dalili ita haka dabi'arta take duk bayan sallar farilla sai an yi gaisuwa.
Ban fi minti goma da zama ba Hauwa ta fito da waya a kunnanta tana fad'in." E gata bari na bata sai ku gaisa ." Ta miko mini wayar tana fad'in." Inna ce take magana."
Cike da fad'uwar gaba na amshi wayar ina kallonta taje ta zauna saman kujera
Muka gaisa da inna Uwani cikin kulawa da sakin fuska har muka kare gaishe-gaishenmu ban ji ta yi wata magana ba wanda da farko na d'auka Hauwa ta gaza juriya ta sanar da ita abinda yake faruwa.
Wayar ta kar'ba suka d'an yi magana kafin su yi sallama ta kashe tana kallon baba Tabawa ta ce." Indomin nan nake so Baba duk dai tsugar mini da ciki take yi amma idan ba ita na ci ba na jin dadi. Amma ki hada mini da dankalin turawa ki sanya wadataccen kifi."
Na ce." Hauwa Indomee fa basir ce da atini idan kin manta na tuna miki gashi sai ki ce a sanya mini attaruhu ya ba zata tsugar miki da ciki ba, ki rage cin ta don Allah."

Littafin nan na kudi ne sister kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

"To mai zan ci Amina, ita kadai nake jin sha'awa wallahi ban ta'ba ciki mai azabar laulayi irin wannan ba, da farko fa shiru kamar ba zan yi ba Amma cikin sati biyun nan ina jin jiki k'warai."
Na dube ta sosai ta dashe lebanta duk ya bushe ta ba ni tausayi. Dama kuma can tana da laulayi wannan ne ya yi tsanani.
Baba ta tashi ta kama hanyar kicin din na ce" don Allah Baba Tabawa kada ki biye mata ki sanya attaruhu kad'an kuma kada ta yi da roman nan."
Tana yar dariya ta ce." Haka kuwa za a yi, Hauwa ni ma na daina biye miki gaskiya."
Ta dube ni tana ce wa." Kin san roman shine abinda ma na fi so na dinga lasa dad'i yake yi mini."
Na ce." Mu bar maganar nan Hauwa, ni fa jikina ya yi sanyi ina fatan dai ba ki sanar da inna Uwani wani lamari ba ko."
Girgiza kanta ta yi a hankali ta ce." Babu abinda na gaya mata wallahi, mun yi waya ne mun gaisa ta ce na ba ki wayar ku gaisa."
Ajiyar zuciya na sauke domin har cikin raina na yarda da maganarta.

To a ranar bai shigo mana ba sai da garin Allah ya waye tukkuna ban kai ga fitowa falon ba ya shigo yaran kaf dinsu a tare da shi da yake asabar ce suna gida babu makaranta sai sha biyu na rana suke tafiya tahafiz su tashi shida na yamma.
K'amshinsu ya cika mini d'aki da uban da yaran sun sha gayu. Ido kawai na zuba musu Khalil ya fara gaishe ni kafin sauran suma su tsuguna k'asa kamar yadda suka ga ya yi "Mama ina kwana." Suka dinga jerowa ina amsawa. Khalil din ya ja baya suma sai suka ja baya suka tsaya kusa da shi. Na jima ina nazarin abinda suka yi kafin na furta." Khalil ja su ku tafi wurin Mamanka ku gaisa."
Bai ce mini komai ba sai ya dubi Baban nasu da yake tsaye a jikin kofa shi bai shigo ba shi bai fita. Ya d'aga masa kai alamar su je can wurin

Chapters

Related Ebooks
03, August 2026
Aisha kabir iliyasu

Please book for gudun aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login