Showing 426001 words to 429000 words out of 450388 words

Chapter 143 - Gudun Aure Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

4002

mata da suke kawo masa caffa ba. Amma shi so babu ruwansa Hadiza ya hango cikin dubbanin 'yan mata da zawarawan da suke a wannan duniya.
Anti Yagana ta riga mu zuwa domin da muka isa kanon a gidana na sharad'a muka sauka sannan gari yana wayewa muka yi gidan GARKUWAR MATA yini muka yi a tare da ita ta sabunta ni ta kuma sabunta Hadiza da ciccibi tare da dahuwar 'yan shilla aure biyu da duk wani abinda ya kamata.
Kuma Koda muka gama da ita gidana muka sake komawa sai da gari ya waye bayan mun kintsa muka nufi can gidan na mu gabad'aya ni da ita da Baba Tabawa domin tare muka zo da ita saboda yaran Mairo da Taburni suna gida Abuja muka bar su.
Gidan an yi masa sabon fenti ciki da waje har da ties a tsakargidan da d'akunansu wannan aikin Usaini ne ya gyara gidan sosai bayan wanda na yi musu ya yi musu sabbin d'inkuna Babanmu tsaf da shi cikin manyan kaya ya sake murmurewa. Sosai hankalina ya kwanta ganin yadda aka samu daidaito tsakanin matan gidan duka sun daina abinda suke yi Ummansu Saminu ta fito ana ta hidima da ita yayin da 'yan uwan Ummansu Hadiza suka cika gidan zuwa na ya sake bud'e babin gaisuwa har da rige-rige a tsakaninsu lamarin nan dai ya tabbata da ake cewa kudi suna sayan girma kuma suna kankaro mutunci. Ma'kotan gidanmu da ada suke yin surutu a kaina a duk lokacin da Ummansu Hadiza ta yi musu gulmata sai na zama abar fadanci da gurfana tamkar wata basarakiya.
Ranar da aka d'aura auran da daddare ya kira ni yana gaya mini bai tafi ba sai gobe don haka Ayuba zai zo ya d'auke ni da yaran mu kwana can gidana na sharad'a.
Na ce masa ya bari gari ya waye domin duk mun gaji har yaran su Hassan ma sun yi bacci tun d'azu. Ya ce a a mu Ayuba zai zo. Haka na kintsa ina gayawa anti Yagana yadda muka yi da shi ta ce mu tafi din kawai tunda hakan ya bukata.
Wajan tara da arba'in Ayuba ya zo ya kwashe mu a mota amma banda amaryar tukkuna dole za ta yi sallama sosai da mahaifiyarta.
Kwanciyar aure zai yi da ni a daran ashe shine dalilin da ya matsanta lallai sai mun dawo dalili matar da yake d'an ragewa da ita tana can saudia basu dawo ba shi ya gaya mini tare ya biya musu da mahaifiyarta da kuma Kawunta da ya zo ya yi musu sulhu wattanin baya. Daga lokacin na gane dalilin da ya sanya ta sassauto har take taka kyasa da k'arfi ganin ta fara samun kansa kyautar umara ya yi wa iyayenta biyu wannan kuma shine karo na biyu tsakaninta da Inna Uwanin a shekarun baya tun kafin ya kai k'arfin haka ya ba su kujerar ita da Hajja da Samira duk su hudun suka je lokacin suna soyayya kafin auransu.
Ya yi yadda yake so ban hana shi ba dalili nasan ya jure tunda kusan kwanaki biyar kenan rabon da mu had'u da safe yake gaya mini gidan da ya mallakawa Sukairaju amma ba a cikin estate din da muke ba ya d'an yi gaba da mu. Ya nuna mini shi a waya maidaidaci ne plate wanda aka yi wa ginin zamani daidai gwargwado kuma ya ja kudi sabo ne kuma na yi masa murna sosai ya kuma tabbatar mini da cewa a shirye gidan yake shiga kawai za su yi.
Yini guda muka yi da shi a d'aki yana ta maimaita abu daya don a k'alla sai da ya neme ni sau uku bayan wayewar gari da safe bayan mun karya da azuhur ya yi sallah sai kuma da yamma wanda shi ya yi bala'in gabalabaitar da ni na yi kwance a gado ina nishi wai lallai sai an samu ciki bayan shi kansa ya san yawan yin wannan abu ba shine yake bada ciki ba. K'addara ma a samu d'in amma ai ba mu da hurumin nunawa Allah abinda muke so idonsa gabad'aya ya rufe har na rasa inda tunaninsa yake har da cewa yana ganin a shekarar nan zai mutu shiyasa ya damu da ganin na sake haihuwa.
Baba Tabawa ita ta dinga hidima da yaran gabad'aya domin ban sauko ba sai bayan biyar da rabi a gajiya tubis ga gajiyar bikin Hadiza ga wadda ya tara mini
Ta yi abinci tsaf ta gama shirya ko'ina da yaran gabad'aya suna zaune a falo suna kallon cartoon Hasan na wasa a kusa da ita shi kuma Usaini na dafa kujera yana mi'kewa tsaye Sultan na ri'ke hannunsa.
Na zauna cikinsu zamana kuwa ke da wuya suka rufe ni kowa da abinda yake fad'i mussaman Minal duk ta kanainaye ni ta ko'ina.
Yana dawowa daga sallar magriba yake gaya mini rasuwar Malam D'aha a lokacin ne Malam Rabi'u abokinsa ya kira shi a waya ya sanar da shi amai da gudawa ya yi kwana daya don asibitin zana ya rasu.
Na kadu sosai da rasuwar malamin jikina ya mutu na zauna ina Kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un babu babu shakka maza sun tafi Allah Ya kar'bi ayyukan alherin da aka yi dominsa.
Da sassafe mu ka dauki hanya ni da shi domin samun ta'aziyya a daran dama na kira Usaini na ce cikin hikima ya san yadda zai sanar da Hajara domin kuwa tsohon ciki ne da ita haihuwa ko yau ko gobe ya tabbatar mini da cewa da wuri za su tafi shi da ita inshallah.
Aikuwa a can muka same su gidan Malam ya kacame unguwar ma gabad'aya motocin manyan mutane ta ko'ina da yake karkara ce akwai filaye sosai da aka samu damar ajiye motacin.
Hajja ma can muka same ta lokacin an gama shirya gawar za a fito da ita domin a sallace ta.
Sai bayan da aka d'auke shi zuwa gidan sa na gaskiya tukkuna na samu sararin bin dakunan matan gidan ina yi musu gaisuwa da yaransa mata aurarru Hajara na cikinsu sun yi kuka har sun gaji na yi musu gaisuwa sosai kafin na koma na zauna wurin da Hajja take a killace muka sake gaisuwa tare da yi wa juna ta'aziyya. Wajan biyu na rana Babanmu anti Yagana Hadiza da su Fati da Ummansu Saminu suka zo Ummansu Hadiza ?????"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"#kawai a ka bari a gidan Saminu da Ashiru duka tare suke Hajara da kanta ta dinga bi da su d'akuna suna yin ta'aziyya sannan mazan suka fita waje su kuma su anti Yagana muka zauna a tare a wuri d'aya.
Hajja can muka barta da za mu tafi ta ce ba zata iya wannan kai kawon ba sai anyi addu'ar uku tukkuna. Amma ni da shi haka muka dinga wannan kai kawon muje mu dawo har sai da aka yi addu'ar uku tukkuna. Ranar sadakar bakwai kuma shi kadai ya tafi bai ce na shirya ba sai ya dawo tukkuna yake gaya mini tare suka je da Hajja.
Kwanaki goma da rasuwar Malam D'aha muka shirya komawa abuja lokacin Hauwa ta kwana kusan shida da dawowa kira shi a waya babu adadi ya kuma gaya mata babban rashin da aka yi ba wai jin dad'i ne ya zaunar da shi ba don a ganinta tunda muna tare wata'kila ni na hana shi dawowa bayan kwanakin da ta yi a saudia ya kamata a ce ya yi d'okinta.
Ranar da muka koma kuwa a gidanta ya kwana domin hura masa wuta ta yi babu kintsi ya tafi ba cikin dad'in rai ba.
Hadiza a can muka bar ta. Sai bayan sati daya tukkuna angon ya je ya daukota kai tsaye kuma gidanta ta sauka sai da ta kwana biyu da tarewa tukkuna na je na ga gidan alhamdulillahi Hadiza ta 'yantu ta yi gida gayun nan da ake ta nema yanzu ya samu an ci ado da kwalliya irin na amare abin dai gwanin burgewa da sha'awa nan take gaya mini Ummansu ta ce bayan ta dan yi wattani sai su shirya zuwa ganin d'aki dangin babamu da danginta na ce hakan ya yi Allah Ya sanya alheri.

Kwanaki talatin da uku da rasuwar Malam D'aha Hajara ta haihu mace tun daga haihuwar aka ce mini an yi mini takwara dole haka na shirya tafiya da gudumawar kayan baby kwanaki uku kacal na yi a daddafe domin da 'kyar ma ya bari na dawo gida tunda ba taron suna aka yi ba saboda rasuwar mahaifinta. Amma alhamdulillahi ta haihu lafiya lau ita da baby suna cikin koshin lafiya yarinya kamar Usaini ya yi kaki ya tofa saboda tsananin kammani.


Na kudi ne littafin kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.


****
Bayan wata hud'u zaman namu ni da Hauwa yana ta tafiya a waskace babu tsari sai dai zangon 'kasa da kuma bita da 'kulli tunda nake kafata bata ta'ba taka gidan Nusaiba ba wallahi don wasu lukutan har kunyarta nake ji yarinyar har ta gaji da tambayata yaushe zan zo nakan ce mata ina tafe in sha Allahu amma Hauwa ta riga ni saboda gulma tana cin ko'kon ranta kawai yarinyar ta kira ni a waya tana gaya mini wai Hauwa ta je mata ta yini har ta kai mata mayafai biyu da hijabai irin wanda ta zo da su daga makka har tana gaya mata cewa Hadiza ba tsaran auran Sukairaju ba ce dalili karuwa ce kuma 'yar kungiyar shan jini an cutar da shi kuma ta girme shi nesa ba kusa ba wataran za a wayi gari babu shi ta nemi wani sassa na jikinsa domin alamu sun nuna zaman da ta yi gidan gyaran hali bai koya mata darasi ba don haka dole za ta matsantawa maigidan ya dawo mata da yaranta saboda tana jin tsoro kada a wayi gari babu daya daga ciki mun had'a baki mun bawa dodon tsafi tunda ni kishiyartace kuma ba ni k'aunarta zan iya yin komai domin ganin bayanta da yaranta saboda ni da 'ya'yana mu gaje dukiya.
Wallahi bakina mutuwa ya yi na rasa abinda zan cewa yarinyar kaina ya yi bala'in d'aurewa wata'kila fahimtar hakan ta yi daga wajena yasa ta shiga ba ni ha'kuri tana fad'in ba ta san hankalina zai tashi ba kuma ta yi rantsuwa da Allah ba ta ta'ba gazgata maganarta ba domin ni din ma na fiye mata ita sau dubu.
Har muka yi sallama ban iya ce mata komai ba saboda mamaki lallai wannan al'amari ya daga mini hankalina ba kad'an ba. Duk wasu kaidi da sharri Hauwa ta yi mini na jure saboda dalilai masu yawan gaske amma ina ganin wannan kam ba zan iya ha'kura ba dalilin da ya sanya kenan yana shigowa ban ma bari ya huta ba saboda da abin na yini shima ganina a hargitse cikin rashin nutsuwa ya shiga hankalinsa na shiga gaya masa abinda kunne na ya ji wanda nake da tabbacin cewa yarinyar nan Nusaiba ba za ta yi mini karya ba.
Ya shiga mamaki kwarai shima jikinsa ya yi sanyi mussaman yadda ya ga hankalina ya tashi ina kuma sake jaddada masa cewa shari'a ce zata raba tsakanina da ita idan kuma bai yadda da hakan ba ya zama dole ya za'bi zama da ni ko'ita domin ba za a cigaba da tafiya a haka da ni ba ya zame mini dole na nemi mafita.
Kwanan rarrashi ya yi duk da girkinta ne sai ya kashe wayarsa ma gabad'aya domin kada ta kira shi ya rufe dakin da key ya boye shi saboda kada na fita rarrashina ya dinga yi sosai lamarin na sa'barsa shi kansa yanzu yadda yake nunawa lamarin Hauwa ya kai shi ma'kura akwai dalilan da ya sanya yake daga mata kafa wanda ni ma su nake duba mussaman yaranta Khalil dai biyayyar da yake yi mini kwatankwancinta ba ta samu ba ga Minal da take jarabar kulafucina uwa uba kuma ina duba Hajja domin duk lalacewarta tata ce idan na yi tutsu abubuwa da yawa marasa dad'i za su faru wanda za su sanya kunci da zubar hawaye a idanuwan yaran.
Wallahi kwana cur ba mu rintsa ba har sai da ya karya mini lagona da rarrashi da kalamai tare kuma da al'kawaruruka da tabbaci akan idan ta sake aikata abu makamamcin wannan da kansa zai d'auki mataki.
Sai da ya yi mata ya ji na sati d'aya bai je gidanta ba ta kuwa zama kamar mahaukaciya ta zo gidana ya fi sau hud'u ba ni ma sanin zuwanta sai dai idan na fito daga d'aki yara ko masu aiki su ce mini ta zo. Shi kuma ba ta ma riskarsa domin yakan fita da wuri kuma baya dawowa sai dare.
A ranar da ya cika sati guda ya koma gidan wanda na tabbatar da cewa wannan ba shine iyakacin horon ba akwai wasu mabambamta yadda ya yi wannan fushin kuma sai ta gayawa aya za'kinta.

Hakan da ya yi sai ya kara sassauta mini rai amma dai duk haka cikin k'unci da takaicin abin nake don sai da na sanya aka yi mini saukar al'kur'ani can makarantar allonmu dake cikin unguwar mu duka cikinta muka yi sauka al'kur'ani mai girma a duk lokacin da masifa ta tunkaro ni nakan sanya an yi mini sauka da addu'a sannan a yi sadaka Hamusu ne ya jagoranci al'amarin sati guda aka d'auka ana sauke izifi sittin a lokacin na fara jin sanyi a zuciyata. Maigidan ya kuma zo mini da albishirin kammaluwar ginin shagunana har ya nuna mini bidiyon wurin a waya waje ne mai darajar gaske a cikin kasuwar ta wuse market gini ingantacce na zamani mai tafe da 'kawa kamar yadda ya fadi madaidaiciyar plaza ce mai d'auke da shaguna sha biyu masu matsakacin girma kasa da sama ko'ina gwananin sha'awa ga Ac ta kowace kusurwa da manyan panal na solar haske ko ta ina yanzu shawarar yadda za a yi tana hannuna sai abinda na ce haka yake gaya mini yana lankwasar da kai da murya duk a k'okarinsa na ganin ya kashe guguwar wuta mai tartsatsi da take shirin kamawa a gidansa.
Ni kuwa na ce da shi yadda ya bada umarni haka za a yi amma dai ina so na yi amfani da 'bari d'aya sama da k'asa d'aya side d'in a bada shi haya ya ce hakan ya yi.
Bayan kwana biyu ya shigo har d'akina ya same ni ban jima da fitowa daga wanka ba ya dinga bina da kallo har sai da na tsargu na dube shi ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta." Ciki ki ka samu ne?" Na ji wani bala'in fad'uwar gaba domin kuwa akan ga'ba nake ina sanya ran ganin al'adata cikin kwanaki biyun nan.
Sai na girgiza kaina ina fad'in." A a mai ka gani?" Ya d'ora hannunsa saman kirjina da suke da towonsu har yanzu ba su langa'be ba ya ce na ga sun girma sosai kin d'an yi kumburi Giwa ina fahimta a duk lokacin da ki d'auki ciki kina canzawa fa har yatsunki.
A sanyaye na ce." To wallahi ba zan tabbatar ba amma don Allah ka daina kira mini shi yanzu ka taimaka mini na rantse da Allah na wuce haihuwa Allah Ya raya mana wanda muka samu."
Ya zuba mini ido fuskarsa ta canza da wani yanayi ya furta." Ni ba za ki taimaka mini ba kenan. Na jima ina gaya miki ina son samun uwata Halimatussadiya sai ki ce na tausaya mini indai ni ban wuce haihuwa ba Hajiya kema ba ki wuce ta ba, mu riko Allah Ya ba mu mai albarka na ce ko daga haka sai na godewa Allah."
A sanyaye na ce." Ai shikkenan." Ya rike hannuna yana dan murzawa ya furta." Ki ce Amin kin ji ko Allah Ya sa shi din ne, domin a jikina nake ji hakan!"
Na dube shi ganin yadda ya zura mini idonsa ya sanya na ce ." Amin Allah Ya sa shine."
Ya kuwa sauke ajiyar zuciya yana fad'in." Na gode miki sosai Allah Ya yi albarka."
Na amsa da Amin a takaice kafin ya sake kallona a karon da babu adadi.
"A game da abinda muka sanya a gaba ni dake a yanzu nake so na ji a ina aka kwana ina so mu wuce wannan wurin ne zan je Legos ina da uzuri a can din amma ni kad'ai nake son tafiya."
Na ce." Business din da nake yi cikin garin kano na zannuwa takalma da huluna nake so na kawo shi nan din kamar yadda na gaya maka da farko amma ina so shaguna biyu na zuba supplements ina so na jarraba ana samun alheri."
Ya d'an yi jim kafin ya ce."Supplements kayan gyaran jiki na mata da kwalliya ko?"
Na gyad'a kaina idona a kansa ya ce ." Hakan ya yi Allah Ya ba ki sa'a, amma ba ki sha'awar sayar da kayan maza ina nufin irin wanda muke sanyawa tunda harkar huluna ta kar'be ki sai ki sa hannu anan din domin mu ga abinda Allah zai yi."
Na ce." Hakan kuwa ya yi sosai na gode da shawara Allah Ya saka da alheri zan yi ko nan gaba don ba ni tsammanin abinda yake hannuna a yanzu zai ishe ni yin duk abinda nake buk'ata.
Ya ce." Ni zan yi miki order domin shirya shagunan tunda na bada shawarar yin hakan amma har yanzu ba ki fitar da sunan shops din na'ki ba. Ita kanta plazar akwai buk'atar a samar mata da suna na mussaman ko?"

Nan fa d'aya wallahi na manta shaf kuma dai da kunya na ce masa sauran shagunana suna d'auke da AminatuAminu collocation ne. Tun lokacin da na fara bud'e shagon d'inki na sanya masa A-A fashion designer hakan na nufin AminatuAminu sai Kuma da na bud'e shaguna tukkuna na bud'a sunan kowa ya gane abinda nake nufi kuma har zuwa yanzu wannan tambarin ne a jikin duka shops dina sai dai a sabunta idan ana so a sake 'kawata lamarin. Ina so a ko'ina ya cigaba da tafiya a haka domin cirewa customer's d'inmu shakku da kokwanto.......

Masu karatu ku ba mu sunan da ya kamata a kira shop's din Amina na Abuja don Allah kada a yi rashin adalci.......=??
Plazar dai na yi mata suna da (GIWA PLAZA) shin ta cigaba da

Chapters

Related Ebooks
03, August 2026
Aisha kabir iliyasu

Please book for gudun aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login