Showing 261001 words to 264000 words out of 450388 words

Chapter 88 - Gudun Aure Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

4023

shigowa jikina. Ya kamo daya hannun na yana duba lallan yasa bakinsa ya sumbuta yana fad'in." Ko wannan da ki ka yi mini na ji dad'i har na ce Allah Ya shi albarka abinda za a ru'banya miki lada ne. Yanzu za ki cika she ladanki ina so ki nuna mini kwanzonki a wannan daran mai albarka."
Na dube shi duk ya kanainayeni. Na ce." Wane k'wazo zan nuna kuma?"
"Ya dago da sauri yana fad'in." Ki cinye ni a wasan gabad'aya hajiyata."
"Umm" Kawai na iya cewa jikina duka ya shika. A hankali ya mik'a hannunsa ya kashe fitilar gefan gadon da ta d'an haske d'akin. Sai ya yi duhu sosai. Ya rike ni da kyau tare da d'an tura ni na kwanta ya yi mini rumfa shikkenan daga lokacin ni ma na kwarkwace muka zama kamar tuburarrun mahaukata.


Da safe da wayar Hajja ya karya. Ga yanayin yadda yake amsa mata magana ya sanya mini kasala. Suna gamawa ya dube ni yana fad'in." Zan je kano yanzu Amina Amma ina sha Allah zan dawo yau idan kuma wani dalili ya sanya ni kwana zan kira waya na sanar dake in sha Allahu."
Na ce." To shikkenan." Na yi shiru ina kallonsa yana kimtsawa. Na dai kasa daurewa da nace ba zan sake sanya musu baki ba, amma na gaza ha'kuri na ce." Ka ga abinda nake ta guje muku kai da Hauwa ko?"
Ya dube ni yayin da yake sanya links a hannun rigar da take jikinsa ya ce." Ai dole dama za a zo wannan ga'bar na sani, kada ki damu ni babu abinda zai faru sai alheri ni dama ai ban ce ina sonta ba, sune suka dage za kuma ta san ni ta yi wa wannan wulakancin ai."
Na ce." Kenan a ganinka itace mai lefi kafi ta gaskiya, ko da suka dage suna son auranka ka fad'i tsakaninka da Allah da annabi cewa kai ma baka sonta."
Kai tsaye ya furta." Wallahi Samira nake so ba Hauwa ba Amina, ai na gaya miki tuntuni Samira da ita na fara soyayya nasan menene so, Allah Ya k'addara ba mu zauna ba ta rasu. Hauwa kam ba ni yi mata soyayya fitacciya gaskiyar magana"
Na ce." To mai yasa ba zaka maye gurbin soyayyar da kake yi wa Samira zuwa ga 'yar uwarta ba, ka ji tsoron Allah wallahi yanzu da bakinka kake furtawa baka sonta. Amma mai yasa kake rayuwar aure da ita har ku haihu, menene bambacin Samirar da Hauwa tunda duka uwa daya Uba daya suke."
Ya girgiza kansa yana fad'in." Da bambamci Amina, babu dalilin da zai sanya ni maye gurbin son da nake yi wa Samira akan Hauwa, me yasa lokacin da ta rasu ta'ki maye gurbin 'yar uwarta, na fa san komai Amina, don haka ba ki da ruwa akan wannan abinda yake faruwa tsakaninmu. Ba a yi macan da za ta yi mini wannan iskacin ta kwana lafiya ba."
Na ce." To ai zumuncin da yake tsakaninku za ka duba."
Ya furta." Ita ta duba zumuncin ne?"
Na yi shiru ina kallonsa. Ya girgiza kansa kafin ya bud'e ma'adanar da yake ajiye gilasansa ya d'auko daya ya sanya kafin ya kwashi wayoyinsa ya zuba a aljihu. Ya dube ni sai kuma ya kama hanyar zai fita na bi bayansa ina fad'in." Za ka tsaya ka yi breakfast ko?"
Ya ce." A a yanzu wurin Momi zan shiga mu gaisa na wuce kawai zan ci abinci a can gidan Hajja in sha Allahu."
Muka sauko a tare ina fad'in." Shikkenan to don Allah a ce ina gaishe da Hajja da kyau tare da su Kamalu." Ya furta." Za su ji, zan gaya musu sa'konki in sha Allahu sai na dawo." Ya fice da saurin gaske. Na juya na shiga d'akina jikina duk a mace. Ubangiji Allah Ya sa mu ji alheri.....
'?
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

"Yanzu don Allah Hajja abinda Hauwa ta yi shine zumunci? nasan duk wannan fad'an da ki ke yi akan hakan ba zai wuce ace kina gudun lalacewar zumunci ba. Amma ki yi nazari akan wannan abinda Hauwa ta yi Hajja ko mahaukaciya fa ta san d'anta ki ga yadda ake yi musu ciki akan titi A
Amma su haihu a yi ta dambarwa da su wurin 'karbar jaririn daga hannunsu. Sannan kin ga yadda dabbobi idan sun haihu suke tattalin abinda suke haifa ai ko babu dangantaka ta jini a tsakaninmu da yarinyar bai kamata ta yi mana haka ba. Wannan wulakanci ne da rashin mutunci da kuma rashin tarbiya."
Hajiya Saratu ce take wannan maganar cikin yanayi na damuwa da bakincikin abinda yake faruwa.
Hajja ta d'an gyara zamanta tana fad'in." To tunda gashi nan a zaune sai mu ji menene dalili saboda ai k'arfe d'aya baya amo! ba wai ina goyuwa da bayan Hauwa akan abinda ta yi ba, ban ji dad'i ba kuma bata kyauta ba amma wata'kila duk ta yi hakan ne domin huce fushin abinda ya aikata mata. Ai ya nuna mata iyakarta ni ma kuma ya nuna mini ba ni da wani muhimmanci dangane da rayuwarsa tunda har zai iya yanke irin wannan hukuncin ba tare da ya nemi shawarata ba. A ganina kome Hauwa ta yi masa ta ci albarkacin jini da dangantaka ko."
Ta girgiza kanta tana cewa." Hajja Hauwa fa bata da kunya ba wai ina 'kin ta ba ne a a halayenta munana sun rinjayi kyawawan domin duk mai zuciyar imani da tausayi ba zai aikata abinda ta yi ba a yanzu kamar yadda na gaya miki ko daga waje Tajo ya auro Hauwa ba mu cancanci wannan iskancin ba."
Sai ta dube shi tana fad'in." Ka na jin mu baka ce komai ba, wai shin mai ya yi zafi ne tsakaninka da Hauwa da har ka saketa ko kana so ka nuna mini cewa ni ban isa ba ko kuma na ce ka d'auki hanyar lalata zumuncin da yake tsakanina da 'yar uwata da ta rage mini a duniya."
Ya ce." Hajja a yi hakuri amma ina ganin zan ha'kura da Hauwa kawai domin wallahi ban da tayar mini da rikici babu abinda take yi a gida."
Ta ce." Akan wane dalili shine abinda na tambayeka, kai yanzu baka ji kunya da nauyin gaya mini hakan ba da wane ido zan kalli Uwani.''
Ya yi shiru bai ce komai ba. Sai ta cigaba da fad'in." Ka gaya mini mai ya had'a ku da har ta yi wannan fushin ta ajiye jariri d'anyar haihuwa ta gudu, duk abinda za ka ga uwa ta aikata haka ba k'aramin abu ba ne ."
Cike da b'acin rai ya shiga warware mata duka matsaltsalun da suka dinga faruwa wasu ta san da faruwarsu wasu kuma bata sani ba mussaman akan rikicinta da Maryam da kanwarta duk ya gaya mata abinda ta dinga yi har sakin ya ratsa. Ta ce." To ai kai ma kana da lefi me yasa za ka raba su da yaransu hakan bai isheka ba ka had'a da duka da cin mutunci don haka ta gayawa uwarta ni ma ta gaya mini shin jaka ce ita da zaka dinga dukanta ko ka manta cewa diyar wani ce itama, kana so ka aurar da yaranka a dinga dukansu."
Ya ce." Wallahi Hajja sau daya na mare ta, amma ni ba ni dukan iyalinsa sharri ne kawai irin nata."
Ta ce." To marin ma kada a sake yin sa ban yarda ba, dukansu amana ne aka bamu bakidaya Hauwa ko ba ta ci darajar komai ba sai ta ci albarkacin zumunci da haihuwa ai ta zama kai ka zama ita haihuwa uku ba wasa ba ce."
Ya gyad'a kansa yana fad'in." In sha Allahu ba za a sake ba. Falon ya d'auki shiru na wani lokaci kafin ta ce." Menene matsayin auranta a yanzu? Ya furta." Tuntuni na mayar da ita ai tun kafin ta haihu har yanzu tana nan a matsayin matata."
Ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in." Alhamdulillahi yanzu ka je can bauchi wurin Uwani ka basu hakuri don ta fusata sosai har suna fad'in ka aiko musu da takarda domin su ajiye sheda."
Ya ce." To yadda ki ka ce haka za a yi in sha Allahu."
Tare da 'yar uwarsa Hajiya saratu suka shirya tafiya Bauchin da wajan la'asar bayan sun yi sallah tafiyar mota za su yi suna fitowa harabar gidan Hajja Yusi ya shigo akan sabon machine wanda Hamusu ya saya masa domin shige da fice zuwa makaranta da kasuwa tunda sun bud'e sabon shagon sayar da takalma na mata da maza a kasuwar kwari to Yusin ke kula da shagon shi da Saminu.

Cike da kwarin gwiwa ya je ya kafe babur din shi kuma Baban sai dariya yake yi ya zuba hannuwansa duka biyun cikin aljihun tazarcen dake cikinsa. Gabad'aya hankalinsa yana kan yaron fuskarsa kamar gonar audiga. Ya 'karaso wurin da suke tsaye da sassarafa sai suka rungume juna. Ya d'an dinga dukan kafadarsa yana fad'in." Abokina." Shi ma yana abokina?"
Suka cika juna amma hannunsu a hade yake ya risina yana fad'in." Baba barka da yamma yaushe ka zo ne?"
Ya dafa kafadarsa yana fad'in." Ban ji ma da zuwa ba, ni ma ina zuwa na tambayi Hajja tace mini ka fita tun safe mutumin ya zama d'an kasuwa."
Yasa dariya yana cewa." Wallahi ai da na san da zuwanka da sai na zauna domin mu gaisa sosai."
Ya ce." Idan kana so mu gaisa sosai ka zo abuja idan ka d'an yi free tunda nasan kana karatu ga kasuwa ko ta hana ka zuwa ne?"
Ya yi shiru yana murmushi kafin ya juya gefan da Hajiya saratu take tsaye tana ta dariya ganin yadda suke cafkewa dama tuntuni akwai wannan sha'kuwar mai karfi a tsakaninsu.
Ya d'an risina yana gaisheta ta amsa tana dariya kafin ta wuce wajan motar da Sukairaju yake tsaye yana jiran zuwansu ya bud'e mata gidan baya ta shiga ta zauna.

Ya ce." Yanzu Bauchi muka nufa amma ina so ka zo abuja kamar yadda na gaya maka duk lokacin da baka da wani uzuri ka duba Momi bata da lafiya, ta kwanta a asibiti jiya muka dawo gida. Amma alhamdulillahi ta ji sau'ki akwai buk'atar ka zo ka dubata ko?"
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Zan zo in sha Allahu Baba, mun yi magana da Adam kwanciyarta ta farko asibiti shi ya kira ni ma yake gaya mini ban samu zuwa ba. Ya yi fushi bai gaya mini ba yanzu, in sha Allahu idan Kamalu ya dawo da daddare zan gaya masa."
Ya ce." Hakan yana da kyau, amma baka ba ni amsar dana tambayeka ba mamanka ce ta hana ku ziyartarmu."
Ya ce." Ko daya wallahi Baba, ba ita ba ce kawai dai tunda muka dawo nan din ne ba mu samu zama ba shine kawai dalili amma idan ya dawo zan gaya masa zan kuma sanar da Baba Hamusu."
Ya ce." To madallah aboki Allah Ya ba da sa'a, Allah Ya sa ina gari lokacin da kuka shirya zuwan."
Ya amsa da "Amin Baba."
Wajan motar suka nufa a tare Sukairaju ya d'an matsa da sauri kafin ya bud'e masa motar Yusi ya yi saurin riga shi. Ya shiga ya zauna kusa da 'yar uwarsa da bismillahi yana fad'in." A gaishe mini da Kamalun idan ya dawo a gaya masa sa'kon Mamanku cewa tana gaisheku gabad'aya."
Cike da ladabi ya ce." In sha Allahu zan sanar dashi Allah Ya tsare Baba."
Ya d'aga masa hannu Yana amsawa da "Amin."
Koda suka sauka a garin bauchi Hajiya Saratu ce kadai ta yada zango a gidansu Hauwa domin shi kam tun a mota ya ce tunda dare ya yi Sukairaju ya kai shi hotel din da ya saba sauka idan ya shiga garin suka kwana da safe a hadu. Hajiya Saratu ita kadai Sukairaju ya kai gidansu Hauwa bayan ya zartar da umarin da aka yi masa.

masu karanta littafin nan ba ku biya ni hakkina ba ina binku bashi ba wai don baku dashi ba ne. Na kudi ne yi kokari ki sauke hakki domin abu kad'an da ake rainawa sai ya hana ki kwanciyar hankali. Allah Ya datar damu.

Dama Hajja ta sanar da Inna Uwani zuwan na su don haka da ta ga Hajiya saratu ita kadai ta shiga tambayarta mai gayya mai aikin ta ce mata tare suke Amma da safe zai shigo kamar yadda ya fad'a. Inna Uwani sosai ta marabceta ta yi wanka ta yi salloli ta ci abinci Hauwa tana kwance a cikin d'aki ba ta fito ba ta gaisheta ba kuma tana jin motsinta. Itama kuma inna Uwanin ba ta yi mata magana ba ai ko babu komai tunda ta ganta a gidan tasan akwai dalilin zuwanta Kuma ko banza ta girmeta ta kuma girmi mijin nata yayarsa ce.
Hajiya Saratu abin ya yi mata ciwo sosai amma sai ta share tunda sulhu suka zo bai kamata ta yi wani abin da zai sake harzuka zuciyoyinsu ba.
Da yake d'akuna uku ne a d'akin d'aki daya inna Uwani ta gyara mata da katifa da mashinfidi ta shiga ta kwanta sai da asubahi tukkuna da suka gaisa suka fara tattauna maganar inna Uwani tana fad'in." To dukansu dai babu yaro idan sun yi hakuri sun rungumi auransu sai sun fi kowa mora kuma yaransu su tashi cikin annashuwa tare da tsalle da dara a gidansu domin duk inda uwa da uba suka rabu yara sukan kasance a lalace. Kuma ban ga dalilin da zai sanya Tajo ya dinga kwashe musu yara yana bawa wata ajiya ba, Saratu ki dubi lamarin nan fa da kyau ki ga ni akwai son zuciya, ba ni so na fiye magana a ga kamar ina goyon bayanta, tana da gaskiya a wannan ga'bar domin abu ne mai wahala uwa ta yarda a d'auki danta a bawa kishiyarta cikin gadara da iko, a kuma biyo ta da ba'kar magana da zagi."
Ta ce." Ni kaina ban goyi da bayan hakan ba Inna wannan dalilin ne ma ya sanya da Hajja ta ce masa ya zo nan din ya baki hakuri na ce ya bari mu zo tare domin bibbiyu tafi dad'i amma tsakani da Allah ita abinda ta yi ta kyauta Inna ki fadi gaskiya. Daga kowane bangare fa akwai lefi ko musulunci abinda ta aikata rashin imani ne da yin butulci ga Allah."
Inna Uwani ta ce." Umm! to ni dai gaki nan ga Hauwa Saratu idan tana ganin ta gaji da zama da Tajo bisimillah sai ta share d'aki ta zauna. Idan kuma za ta koma auransa sai ki tambayeta ni dai babu wanda ya isa ya shiga tsakanina da 'yar uwarta a cikinsu."
Tana gama fad'in haka ta tashi tana fad'in. A dama miki kunu ko kuma shayi za ki sha."
Ta ce." Kunun dai zai fi dama-dama Inna amma a turo mini Hauwan mu yi magana."
Ta juya ta fita tana fad'in." To bari na turo miki ita."
Ta shigo sanye da hijabi babu yabo babu fallasa ta zaune gefan katifar da take zaune ba ta kalle ta ba ta ce." Ina kwana."
Hajiya Saratu ta'ki amsawa tana fad'in." Ba zan amsa ba Hauwa ai kin nuna mini matsayina kamar ni na zo gidanku domin ke amma har na kwana ban isa ki fito ki gaishe ni ba, ke ba za ki canza dabi'u ba ko."
Ta yi shiru ba ta ce mata komai ba. Sai ta girgiza kanta tana fad'in." To magana ce akan abinda yake faruwa ta kawo ni nan, Hauwa duk wani abu da ki ke jin an yi miki ki yi hakuri ki koma dakinki domin shine farincikin iyayenmu, tare muke da Tajo nasan an jima kadan zai shigo, ya tabbatarwa da Hajja cewa ya mayar dake tun kafin ki haihu kin ga yanzu baki da wata hujja da zata hana ki komawa." Ta nisa kafin ta cigaba da cewa." Yanzu ke ba ki ji kunya ba a ce bare wad'anda aka auro a waje sun fi ki matsayi da shiga zuciyarsa. Ke ya kamata fa ace kin fifita a cikinsu amma kina wasa da damarki. Zan gaya miki gaskiya ba ki kyauta ba, abinda ki ka yi ba daidai ba ne,

Chapters

Related Ebooks
03, August 2026
Aisha kabir iliyasu

Please book for gudun aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login