Showing 144001 words to 147000 words out of 450388 words

Chapter 49 - Gudun Aure Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

4042

da ina Legos. Ni kuma jikina duk ya yi la'asar hankalina na can tunanin abinda zai faru domin kuwa nasan ko likita bai gaya masa wata magana ba na tabbatar da cewa sai ya tuhume ni dalilin da ya sanya na yi shiru ban gaya masa samuwar cikin ba tsayin wattani uku da satika.
La'asar a gidana ta yi mana tare gabad'aya muka dunguma har dasu Hajja a ka yi sa'a kuwa Baba Tabawa tana ta hidimar abinci koda ta fito suka gaisa cikin barkwanci take cewa da maigidan towo take yi saboda ta ji labarin zai zo kuma ta sanya an samo mata daddawa da kuka masu kyau tunda ta fahimci ya fi k'aunar miyar kuka fiye da sauran abin ka'di.
Ya dinga godiya kuwa cikin kulawa da sakin fuska wannan dabi'ar tasa ta rashin 'kyama tana kara masa martaba. Hajja fadi take yi kin kyauta kuwa Tabawa sai ki tu'ka towon da yawa ni ma na tafi dashi na d'umama da safe.
Tashi ya yi ya nufi d'akinsa dake saman bene wanda ya jima a rufe tunda ni duk dabdalata a kasa nake yi ban sake hawa saman ba tun washe garin ranar da na tare a gidan.
Duk da rashin jin kwarin jikina hakan bai hana ni tashi na bi shi bayan shi ba.
Waya yake yi da Sukairaju a lokacin da na shiga d'akin tare suke zo dama tunda shi ya d'auko mu a mota ma. Na nemi kusa dashi na zauna a hankali Ina nazarin d'akin bai yi wata 'kura ba tunda ko'ina rufe yake da tagogi irin na gilashi da narka narkan labuleye a kewaye babu ma wata kofa da k'ura za ta shigo sai dai idan an dan gyara wasu guraran hakan ba zai zama lefi ba.
Ya kashe wayar yana dubana a tsanake ya furta." Ya gajiya da jikin kuma?"
A hankali na furta." Na ji sauki kai ma ya gajiyar hanya."
"Ban gaji ba." Yafada idonsa a tsaye a kaina. Sai na yi kasa da nawa idon ina dan jin fargaba kad'an zan yi kokarin ganin na kare kaina ta kowace siga domin kuwa na fahimci zallan rikici da fitina a cikin kwayoyin idonsa."
"Ina so ki gaya mini abinda ki ka taka, kada ki rufe ni Amina domin kuwa babu abinda na tsana a rayuwata sai zamba cikin aminci. Na kan ji na tsani mutum tsana ta har abada muddin na fahimci cewa yana zaune da ni da wata zuciya ta daban. Ki fito fili ki gaya mini me kike nema a wajena? Menene a can kasan zuciyarki dangane da zama da ni."
Cikin nutsuwa na furta." Ban gane inda maganganunka suka dosa ba Baba."
Ya tsira mini ido da b'acin rai a tare dashi kafin ya gyad'a kansa ya ce." Kin san idan wani likita zai b'oyewa kowa wani lamari da ya shafe shi tsakaninsa da mara lafiyarsa ni dai alfarmata da yadda Ubangijina ya karramani a nan gidan duniya ba za a rufe mini wani lamari da ya dangance ni ba. Likitan da ya yi tsaye a kanki a daran jiya ya yi mini bayanin da ke kanki bai yi miki shi ba, ya sanar da ni dalilin zubewar cikinki wanda ki ka boye mini samuwarsa bincike ya nuna cewa lallai an yi yun'kurin fitar dashi ta kar'fi da ya ji, hakan ya haddasa matsala babba cikin ya canza mazauni, shi bai fice ba haka zalika kuma shi ba zauna daidai yadda ake so a mahaifar ba. Ya gaya mini biyu ne na farko ya fita jim kad'an bayan zuwanku asibitin na biyun ne sai da aka kai ruwa rana kafin su fitar dashi ko kina da ja akan hakan, ni dai na san Dr Iliyas haka kawai ba zai 'kir'kiri 'karya domin ya 'bata ki a wajena ya gaya mini ba, ya sanar mini ne domin akan akinsa yake ni kuma na aminta da bayaninsa sanin da na yi miki za ki yi aikata fiye da abinda ya fi haka. Na ro'ke shi ya rufe maganar ba don Ina gudun tozarci da tiriri na jama'a ba, nasan ni dai babu wanda zai zage ni, sunana kuma ba zai 'baci ba, na yi hakan ne kawai saboda idan maganar ta fita dole idan an rubuta sunanki za a rubuta nawa a gaba. Kuma da sauran igiyoyin aurena a kanki ba ni da yadda zan yi na 'karyata domin sakamako ne daga wajen mahukuta wad'anda suka san abin. In banda ke dashi Dr Iliyas din da ni na uku babu wanda ya san yunkurinki na fitar da cikin ta k'arfi saboda haka mu yi magana ta tsakani da Allah da annabi dake anan, na san matsayata lullub'e mini gaskiya kuwa zai iya janyo miki miki b'acin rai da fushi mai tsanani daga wurina."
Cikin dauriya da ko'karin aro jarumta na ce." Ni wannan maganar ban santa ba. Sharri ya yi mini domin neman suna a wurinka to wai akan me zan zubar da cikin da Allah Ya ba ni, me ka yi mini ko ma ka yi mini wani lefi shi cikin Ina ruwansa da zan zubar dashi, kawai Allah Ya k'addari fitarsa ne a wannan lokacin amma ni kam ban san da wannan maganar ba.

Ya gyad'a kansa yana kallona ido cikin ido sai na kasa dubansa na yi k'asa da kaina gabana na bugawa da k'arfi. Ya sanya hannunsa ya dago fuskata yana cewa." Ki rantse da girman Allan da ya hallice ki a wannan duniyar ba ki yi yun'kurin zubar da cikin nan ba Amina."
Shiru na yi ban ce komai ba zuwa wannan lokaci kuwa kafafuna sun fara rawa saboda fargaba da zullumi domin kuwa ban hangi kwanciyar hankali da yarda da kaddara daga gare shi ba.
Ya tashi ya je ya dauro alwala duk Ina zaune Ina kallonsa ya bude drowa ya d'auko al'kur'ani izu sittin ya dawo ya zauna a kusa da ni yana fad'in." Zan iya rantse miki da Allah cewa baki da gaskiya Amina, kuma bayanin da likita ya yi shine gaskiya."
Na ce." Me ya yi zafi da har sai an yi rantsuwa da al'kur'ani, kafi kowa sanin hakan babban hadari ne, kuma al'kur'ani ba abun wasa ba ne."


Littafin nan na kudi ne kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

"Ban d'auko al'kur'ani da zummar wasa ba Amina, wallahi Allah daya ne kin yi yun'kurin zubar mini da ciki, ina so ki tashi ki je ki d'auro alwala ki yi yadda na yi ki d'auki al'kur'ani ki dora a saman kanki ki rantse da Allah muddin ki ka yi haka wallahi zan aminta dake d'ari bisa d'ari."
"Zan yi dai alwala amma ba ni da hurumin rungumar al'kur'ani domin ba ni da tsarki, ko ma ina dashi ni ba zan yi wannan gangancin ba gaskiya."
Ya jima yana kallona kafin ya furta." To na ji ki ba ni amsa me yasa ki ka rufe mini samuwar cikin ba ki gaya mini ba."
Shiru na yi ina d'an duban yatsun hannuna kafin na ce." Babu wani dalili mai k'arfi na bari ne kawai idan ka zo garin sai ka gani da idonka, kuma anti Yagana ta ce mini hakan kuskure ne don Allah ka yi ha'kuri."

"Ba ha'kuri na ce ki ba ni ba Amina gaskiya na ce ki gaya mini, tun muna mu biyu dake a d'akin nan idan kin yi mini gardama zan sanar da 'yar uwarki sannan na gayawa Mahaifiyata abinda ki ka yi mini na zalinci da ha'inci."
Na zuba masa ido da yanayi na damuwa na ce." Na gaya maka gaskiya baka yarda ba to karya kake so na yi maka, zalinci da ha'inci kamar yaya? wai me zai sanya ni na zubar da cikin ne ai ba shege ba ne, na sunnah ne akan wane dalili."
Cikin zafin nama ya tashi tsaye a fusace! "Ai kin shegantashi tunda ki ka zubar mini da shi, Allah Ya isa tsakani na dake ban yafe miki ba Amina."
Ya fad'a jikinsa na karkwarwa idonsa ya kada jajawur.
Tsaye na mike ni ma jikina ya fara 'bari
da yanayi na ko'karin kare kaina na ce." Menene abin Allah Ya isa, shikkenan 'kaddara ba za ta faru ba sai a jingina mini ita, ai musulma ce ni nasan abinda addini ya koyar ko cikin da ba a same shi ta hanyar mai kyau ba haramun ne zubar dashi balle wanda aka same shi ta hanyar halak, ban ga dalilin da zai sanya ku dinga kokarin dora mini lefi b......Ban 'karasa ba ya kawo mini hari na 'barin makauniya a kuncina sai na yi kasa da mugun sauri har sai da kafata ta gurde na kusa fad'uwa saboda dama jikin babu kwari ga kuma fargabar da ta yi mini dabaibayi.
Lamarin da bai taba ratsa tsakaninmu ba ko da wasa bai tab'a yun'kurin kai hannunsa jikina da zummar duka ba.
Jikinsa na rawa yake ce wa." An jingina miki lefin, ai ba ki da imani kuma baki da kyawun zuciya Amina, ke din muguwa ce mara tsoron Allah na jima da sanin za ki iya aikata abinda ya fi haka akaina tunda baki zaune da ni da zuciya daya. Ki bar ganin kina cikin hali na lalura hakan ba zai hana ni na huce takaicina ba. Abinda nake nema ruwa da iska rani da damuna na samu har guda biyu kin zubar mini me na yi miki Amina Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!"
Ya kai 'karshen maganar da kiran sunan Allah kafin rigijib ya zube a kan gadon ya rufe fuskarsa da tafukan hannayensa gabad'aya yana nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! da baban sauti.......
'?
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=?N?*

TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

https://chat.whatsapp.com/K944WIHnBaKHDrZS6snUky

*TALLAH!*
*Albishirinku mata ?an ?walisa matan da suka amsa sunansu mata, waWanda suka san sirri da fa'idar gyaran jiki domin ta da komaWar sha'awarsu. To ku matso kusa kuji, wai kuna da labarin shahararren kamfaninnan na ?awa da ?awa Waya tamkar da dubu, sha ?undum, mai suna?*
*DUNIYAR LAFIYA ISLAMIC NATURAL PRODUCT & WOMENS CONSULTATION*
*Daga aunty Fatima Buhari rijiyar lemo 7ano state*
*Cibiyace da tai fice wajen gyaran ma'aurata*
*Wannan kamfanin basu fito ba saida suka shirya tsab domin taimakon mata ta hanyar samar musu da magunguna ingantattu nagartattu wanda aka haWa da natural kaya cikin tsabta da inganci, komai a kwali yake ?ar uwa cikin tsabta da nutsuwa aka shirya muku*
*ina masu son soma kasuwanci ku matso Anty Fatima tana bada kaya a sari akan farashin da zaki gode mata, tana raba kayanta ga manyan shagunan saida magunguna dake cikin kasuwar kurmi dake kano, tana tura kayanta izuwa gari_gari ?asa_?asa. Kayan sari kona miliyon nawa kike da bu?ata zasu iso hannunki a cikin kwana biyu da izinin Allah*
*Ni Badiat Ibrahim Mrs Bukhari ?awar Sabuwan maigogul, Aminiyar Iyabo, uwar Wakin Tani Shanono na gwada na san amfaninshi, kema ?ar uwa ki kwada zaki bani labari siyan nagari maida kuWi gida.*
*Mun sani yanzu yana da kyau duk abinda zamu siya musan ingancinshi da nagartarshi bawai muita siyan magungunan mata kara zube ba.*
*Wannan kamfanin kayansu babu algus ko almundahana a ciki, da tsoron Allah da ?wa????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? rewa gami da gogewa ta sanin* *yadda ake sarrafa magunguna suke aikinsu, cikin nagarta da gangariyar tsabta.*
*Abu mafi sha'awa komai a cikin kwali yake a rufe kirib*
*ga kaWan daga cikin abubuwan da kamfanin yake samarwa*=?G? *Tsumin dadi har Madiga tareda gunbarshi*
*Tsumin no excuse mela?abin bita zaizai*
*Gumbar dare daya wanka goma, dana gari da zumarta da tsuminta duk muna dashi*
*Zumar hana bacci gumbarta da garinta*
*Munada Arabian sabaya tare d Sudanese sabaya*
*Da zumarta*
*Sabaya ce dake cuko da ?a mace duk ramarta, da ?anjamewarta*
*Itama da zumarta*
*muna da mummuna da aiki*
*Akwai tsumi da gumbar ta da zaune tsaye*
*muna da kogin daWi*
*Abangaren sanyi sun samar ma mata maganin matsolilinsu*
*muna da fitattun maganin sanyin da yake fata_fata d sanyi yayi mishi korar kare*
*Khanzur Rahman herbal formular*
*Sanyi clear syrup*
*7 days for chronic infections flusher*
*Sannan kuma muna da* *Package amarya*
*Package Uwargida*
*Package irin na zawarawan da suke shirin sabon aure*
*Bugu da ?ari wannan kamfani yana sarrafa magungunan maza ba a iya na mata ya tsaya ba, wannan kamfani magungunan da yake samarwa suna da yawa wannan tsakurene daga cikin kayansu*
*Da sauransu da sauransu wanda bamu ambata ba.*
*Ba fa a iya haka muka tsaya ba muna d cancada cancadan zannuwan Gado da carpet*
*Domin neman ?arin bayani ku tuntuSeta a kan lambar wayarta kai tsaye*
+2348032089456

*29*
Ina tsammanin Hajja ce ta yi masa maganar tafiyarmu saudiya domin ni ban samu kofa ba tunda ban ga fuska. Kwanan Hauwa biyar da tarewa ya kira ni a waya, lokacin ina bandaki ina wanka, na ji ringing har sau biyu kwata kwata ban tsammaci shi din ba, domin kafin shigata bandakin na kira Anti Yagana a waya ba ta daga ba, sai nake tunanin ko itace ta kira.
Ina fitowa na dauki wayar ina dubawa wanda ya yi daidai da lokacin da ya sake kira na dan ji faduwar gaba kad'an dalili na san ba kasafai yake kar'bar uzuri idan ya kira waya ba a daga ba.
Cikin nutsuwa nasa a kunne kafin na ce komai a hasale ya furta." Kina ina ne ina ta kiran waya."
Na tausa harshena na ce." Wanka nake yi."
Tsaki ya ja wanda ya ta'ba mini zuciya sosai, tunda nake dashi bai ta'ba yi mini tsaki ba, sai yau don kawai ban daga waya ba, a ganina tsaki yana daya daga cikin nau'ika na wulakanta mutum, kuma wata'kila tana zaune a kusa dashi ya yi mini haka.
Raina ya 'baci sosai zafin zuciyata ya motsa na dinga ji kamar na kashe wayar ma domin ban san wane kalar wulakanci zai yi mini a gaba ba.
Ya ce." Hajja ta yi mini magana akan tafiyarku jibi na ce ni ba ki gaya mini ba, ban sani ba ko kina da wani mijin bayan ni kin gaya masa."
'Kafafuna ne suka dinga kyarma jin maganar da ta fito daga bakinsa sai na ji wani gumi ya yanke mini kamar ba daga wanka na fito ba. Gabana na bugawa cikin kaduwa da furucinsa na ce" Ban gane abinda ka ke nufi?"
"Kin ji abinda na fad'a ai ba sai na maimaitamana ba, ba ni da wani mutuncin a wurinki, da ni da banza duk daya."

Na ce." Ka ga Baba, har yanzu ban fahimci inda maganarka ta dosa ba, in banda neman fitina kai ka ba ni kujerar nan ba tare dana roka ba, haka zalika kuma ka fini sanin yaushe ne tafiya, to me zai sanya haka kawai saboda kana jin haushinsa ka nemi daga mini hankali. Me nayi maka?ka jima kana zargina saboda kawai ka aureni bazawara baka tauna magana motsi kad'an zan yi sai ka mayar da abin wata manufa, idan ka gaji da ni kana da dama a hannuna fa."

"Ki zage ni kin ji ko, ai fitsara da rashin kunya ba sabon abu ba ne a wajanki Amina, kowa yana shura ya gagara ta fannin alheri amma ke duk wanda zai bude bud'e baki aibunki zai fad'a. Ina so ki sani wallahi tallahi ba zan juri wannan sakarcin ba, ba zai yiwu da mutuncina da k'imata a gari ki zubar mini da ita ba."

Na danne kukan da yake so ya kufce mini na ce." wani abun kuma aka ce maka na aikata? wannan cin mutuncin ya isa haka Baba, ko namiji ka kama ni dashi iyakacin abinda za ka yi mini kenan, idan ba ka sona yanzu don Allah kada mu 'batawa juna lokaci mu rabu cikin mutunci ba sai ka kayi mini 'kaharu ba."

Kashe wayar ya yi ba tare da ya sake ce mini komai ba. Na ajiye tawa wayar a gefena tare da rufe fuskata da tafukan hannayena kuka mai karfin gaske ya k'wace mini.
Cikin rashin kuzari na dubi wayata da na ajiye lambar anti Yagana ce. Sai zuciyata ta sake karyewa hawaye ya cigaba da zuba. Cikin kuka na daya jin yanayin muryata ya sanya jikinta yin sanyi a hankali ta ce." Menene kuma? Ina ce magana ta mutu tunda maigidanki da kansa ya fito ya wanke ki a idon jama'a, kukan kuma na menene?"
Na ce." Anti Yagana kisan mummuk'e yake yi mini wallahi na rasa gane inda ya dosa, ai kin ga dai ya fito ya nunawa duniya girma da matsayina, amma wallahi duk wannan k'aunar da kulawar a yanzu babu ita, a tsukin nan cikakkiyar gaisuwa bata wanzuwa a tsakaninmu abinda ya fi daga mini hankali yawan zargina da yake yi, motsi kad'an zai canza mini manufa, kin ga zargi a cikin aure haramun ne."

A sanyaye ta ce." Sai fa kin yi hakuri a wannan lukutan kin kawar da kai gefe guda, kin ki ji, kin ki gani, tunda yana da sabuwar amarya, ke ma kuma kishi yana damunki Amina, Ina ganin shine abinda ya hana ki zaman lafiya da mijinki."

"Wallahi anti Yagana ba wannan ba ne, nasan ina jin babu dadi a raina amma ya zan yi, bayan Hauwa zai iya auro wasu mu zauna, wulakancin da ya tsiro dashi ne ba zan iya jura ba."

"Amina ki yi hakuri na gaya miki, matsalarki ba ta kai wadda za ki tayar da hankalinki ba, mijinki yana sonki yayin da ya gama d'okin amarya komai zai sake shi, ke dai ki cigaba da kyautata masa kuma ki godewa Allah mahaifiyarsa tana k'aunarki to duk abinda za ki ga ni a wannan lokacin ki daure ba zai dawwama ba."

Shiru kawai na yi Ina jinta, na san ba don komai take kafe ni a gidan ba, sai dan gudun lissafin aure, yadda na san halinta hakan ta san nawa, ina da hakuri amma kuma duk ranar dana furje babu mai iya tankwarani, kuma idan na bar abu na bar shi kenan har abada.

Ta ce. " Kina jina

Chapters

Related Ebooks
03, August 2026
Aisha kabir iliyasu

Please book for gudun aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login