Showing 279001 words to 282000 words out of 450388 words

Chapter 94 - Gudun Aure Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

4234

sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*2k COMPLETE ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA 1K VIA 0542382124.... BINTA UMAR GTBANK.*
*07084653262*

Ta jima sosai kafin ta yi magana cikin yanayi na damuwa ta ce." Dangin matar nan dai a ciki suke da ku Amina domin gani suke yi bakincikinku ne ya kashe musu 'yar uwarsu duk wanda ya zauna ya tashi sai sun amayar masa da abinda yake cikinsu.
Anti Yagana ta ja tsaki tana fad'in." To, abinda ya fi sai kawai su d'auki lasifika su fara bi sa'ko da loko suna shela tunda ba su da hankali, wannan ba k'auna ba ce abinda suke nunawa tsantsar jahilci ne kuma za su hana yar uwarsu kwanciyar lafiya a kabarinta muddin suka ce za su tashi rigima abubuwa da yawa ne za su faru. Dama zaman tare ai ya gaji haka dole a samu matsaltsalu ma bambamta sai dai kawai Allah Ya kyauta, ta wace hanya kike ganin za su hade mata kai ko su ware ta. Matar da ta samu soyayyar miji fiye da su, Hajiya Saratu ki duba maganar nan don Allah kaf fa yaransu suna hannunta basu da iko akan komai kina kwance kina jina Allah Ya jikanki, idan sun yi magana akan nuna rashin yarda ya goyu da bayanta. Ai ma sun yi hakuri da ita wallahi kuma son su ta da zaman lafiya domin da wahala a ce wata uwa an yi mata fin karfin a kan yaranta ta iya dannewa sun yi namijin kokari anan kuma na yana musu. Mu dama tsakaninmu da ita alheri ne, wallahi koyaushe Amina ta gaya mini halin da take ciki na damuwa akan zamantakewar gidanta akan tausheta tare da nuna mata cewa haka auran yake gabad'ayansa jarabawa ce a ciki jin dadinsa kad'an ne kuma ibada ne, kokarinmu ta yi hakuri ta zauna a yau ba wai don yar uwata ba ce ina yabonta sosai dalilin abubuwa da yawa da ta dinga cin karo na b'akinciki da b'acin rai amma ta yi hakuri ta jure. Don haka idan 'yan uwan Maryam sun zargi Amina da Hauwa wajen gumawa Maryam takaici har ta rasu to sun so kansu kuma zahiri ba su bukataci zaman lafiya ba domin dai duk mai hankali ya san matar nan ta sha jinyya kafin ta rasu. "

Ta girgiza kanta tana fad'in." Hakane amma Yagana daidai ne Hauwa ta ajiye jariri sabuwar haihuwa ta shilla wata duniya ko a waje Tajo ya je ya auri yarinyar nan ya kamata ta aikata mana wannan rashin mutuncin. Jininmu ce fa ciki daya fa ba wasa ba ne Hakan ne ma ya sanya duk muka ture komai da jin zafin abinda ta yi Hajja ta ce mu je a bata ha'kuri bisa bin umarinta muke je can bauchi Hauwa ta rufe idonta ta yi mini dibar albarka zagi na ne kawai ba ta yi ba, hakan ya sanya na yi alkawarin cewa muddin da yawuna da shawarata Tajo ya gama zama da ita har abada tunda ta za'bi ta tozartamu shikkenan sai dai zumuncin ya lalace ."
Anti Yagana ta ce." A a ba za a yi haka ba Hajiya, ai ko babu dangantaka ta jini an riga an zama daya tunda har yara suka ratsa tsakani. Don kyautawa Hauwa ba ta kyauta ba. A dai nuna mata kuskuran abinda ta yi a gyara ta dawo dakinta a ganina shine abinda ya fi dacewa."
Ta gyada kanta ba tace komai ba tabbacin maganar anti Yagana ba ta gamsar da ita ba.
Na ce." Anti Yagana idan Hauwa tana da lefi shima yana da lefi fa. Domin ya yi abubuwa sosai wanda ya kamata a ce ya gane kuskure ne a zamantakewa amma bai gane ba, ni na yi kokarin dannewa dalili nasan babu wani abun da yake dawwama sai ikon Allah wanda shi muka gani yanzu. Na yi ta ko'karin bata shawara kan cewa ta kawar da kanta ta kasa jimirin yin hakan har sai da bacin rai ya ratsa tsakaninsu. Ya kamata gaskiya a tsage Mamana. Shi kansa maigidan akwai tashi matsalar sai dai ace ta Hauwa ta rinjayi tasa."
Ta ce." Ni dai da yawuna ba zan bashi umarnin dawo da ita ba duk hukuncin da ya yanke daidai ne."
Tana fad'in haka ta tashi tana cewa." Zan je na watsa ruwa can wurin su Hajja jikina duk ciwo yake yi mini na samu nasa wani abu a cikina."
Na ce." To shikkenan Mamana dama na ce da Baba Tabawa ta tu'ka mana towo don zai fi man? dadin ci akan tsabar shinkafar nan."
Ta ce."Aikuwa kin yi shawara mai kyau Amina don tunda aka sanar da ni rasuwar nan wallahi ko na sanya abinci a gabana sai dai na kalle shi ba na iya ci. Kai rasuwar baiwar Allah nan ta ta'ba ni wallahi."
Anti Yagana ta ce." Ba ke kadai ba wallahi ni kaina na gigita kwarai da aniya Ubangiji Allah Ya yi mata rahama."
Muka amsa da amin gabad'ayanmu kafin ta yi mana sallama ta fita daga d'akin, anti Yagana ta dube ni tana fad'in." Na so na tambayi Ummansu Hadiza labarinta amma na sha'afa wallahi, kuma don dai Babanmu ya ce sai sun tafi amma da ko kwana daya sai su yi tunda yanzu dole ne su kwana a hanya
ina so mu sake samun lokoci mu je mu sake dubata ko ya ki ka ce."
Na ce." Hakane anti Yagana ni kaina Hadiza tana raina wallahi, dalilin da ya sanya kenan na ce da Hamusu duk k'arshen wata ya dinga yi mata siyayya yana kai mata, zuwan namu yana da amfani ai hannunka baya rubewa ka yanke ka yar."
Ta furta." Ni har fargabar ganinta nake yi wallahi saboda ina tuna irin kukan da ta dinga shirga a ranar da muke je kin san da kyar aka tura ciki muka fito, na jima ina kukan zucci duk sanda na tuna da halin da take ciki nakan shiga yanayi na damuwa mace a irin wannan wurin a ajiye Amina duniyar nan ta baci duk da ba ita kadai ba ce, amma su kansu ma'aikatan wurin wallahi wasu daga ciki ba su tsoron Allah."
Cike da damuwa na ce." Anti Yagana lefin Hadiza na kisa ne ta kuma tabbatarwa da kotu gaskiyarta ba mu da wani yun'kuri da zamu yi domin ceto ta. Hakkin rai ba abin banza ne. Idan Allah Ya kar'bi tubanta kuma tana da ragowar rayuwa sai ki ga ta fito ta hanyar da ba mu yi tsammani ba. Idan kuma sun kasheta shikkenan sai ta riski Ubangijinta a wankakkiya. Ubangiji Allah Ya kare mu daga fadawa jarabawa da mummunar kaddara."
Ta amsa da Amin Ya Allah da yanayi na damuwa da nadama.

Misalin goma da rabi maigidan ya shigo tare suke da Kamalu ban yi mamakin ganinsu su biyu babu Yusi ba domin sai na ce ganina da Yusi daya kafin a d'auki gawar marigayiyar na hange shi tare da Adam a rakube a bayan kujera yana rarrashisa yanzu ma su Hajja da Gwaggo sai tambayarsa suke yi ina jin Kamalu na basu amsa da cewa yana can tare da Adam. Maigidan bai tsaya ba suna gaisawa ya haye sama hankalina gabad'aya yana kansa don haka ban yi jinkirin bin bayansa ba.
Na same shi zai shiga wanka da babban towel a jikinsa.
Muka zubawa juna ido. Na isa dab da shi na tsaye a sanyaye na ce." Ya karin hakuri tun d'azu nake ta so na yi maka gaisuwa ban samu dama ba, Ubangiji Allah Ya gafarta mata, kai kuma Allah Ya baka hakurin jure rashinta, Allah Ya albarkaci abinda ta bari."
Ya dinga amsa da "Amin Ya Allah cikin jin dadi. Ya nufi bandakin na bi bayan shi na taimaka masa wurin had'a ruwan wanka. Kallo yake ta bi na dashi babu yabo babu fallasa, amma kallon ya fara sa'bata sai na tsargu na fara tunanin ko shima ya fara yarda da abinda 'yan uwanta suke fad'a akanmu wato da bakincikinmu ta rasu. Da na tuna kallon nasa babu harara da k'yama a ciki sai na d'an samu sassauci, na fito na bar shi a bandakin domin ya yi wankan. Na zauna jigum cikin zullumi.
Ya fito yana tsane jikinsa na tashi da sauri na bude wardrobe dinshi jallabiya na fito masa da ita da gajeran wando. Na mika masa ya kar'ba na koma na zauna yana kintsa jikinsa ya ce." Ki kawo mini abinci Amina."
Da sauri na mike ina fadin." Dama abinda zan tambayeka kenan, tun yamma na ce da Baba Tabawa ta yi towo zai fi dadin tafiya."
A takaice ya ce." Kin kyauta kuwa."
Ya d'auki turare yana fesawa a jikinsa. Na sauka kasa cikin nazarin abinda ya yi a ganina wane turare zai fesa a cikin wannan yanayin da matarsa ta rasu ko kwana daya ba ta yi a kabarinta ba
Na koma saman da tire a hannuna mai d'auke da kwanonin abincin da duk abinda nasan zai buk'ata. Yana zaune gefan gado
yana waya da Sukairaju na ajiye tiren hannuna a saman daddumar da yake zama domin cin abinci...

Ina binki bashi idan kin san kina karanta littafin nan ba ki biya ni hakkina ba.


Sai da ya kammala wayar tsaf tukkuna ya zo ya zauna saman daddumar da abincin yake a shirye. Na zuba masa guda biyu madaidaita ina ko'karin zuba miya ya furta." Wanene zai cinye miki wannan towon Amina?"
Na dube shi a tsanake kafin na ce." Kai ne za ka cinye?" Sai ya gyada kansa yana fad'in." A a d'aya ya ishe ni, kada ki zuba miya a kai a b'ata shi ki yi addu'a d'ayan ma na iya cinye shi."
Ban ce komai ba na cire dayan na mayar cikin fulas na fara ko'karin zuba miyar ya ce ki zuba ta yau'kin kawai kada ki sanya mini jar miyar, ki sanya mini man shanu akai wadatacce."
Na yi yadda ya umarta Ina fad'in." To naman fa." Ya ce." Ki tsamo sai ki sanya mini."
Ban ce komai na dinga tsamo naman ina zuba masa a saman towon har ya so yayi yawa." A nutse ya ce." Naman nan ya isa haka Amina, kina so na ci abinci jikina ya mutu ko?"
Na girgiza kai a hankali na ce." Kallo d'aya na yi maka d'azu na tabbatar da cewa akwai yunwa a tattare da kai wallahi."
Ya furta." Ba ki yi karya ba rabona da abinci tun yammacin jiya kuma ban wani damu ba wallahi."
A nutse na ce." To yanzu dai ka daure ka cinye wannan har naman duka."
Hannunsa ya sanya tare da bismillahi kafin ya ce." To ke ma sanya hannunki mu ci tare zai fi albarka.
Na sanya hannuna a hankali na gutsiro na kai daidai bakinsa.
Kallona ya yi na 'yan sakkoni kafin ya bud'e bakin na sanya masa towon ya fara taunawa a tsanake
D'akin ya d'auki shiru na wani lokaci kafin na ji maganarsa yana fad'in." Ina mai sunan abokina ya 'kara wayo ko.?"
Na ce." Ya yi wayo sosai su Hajja ma suka dinga mamaki girman da jikinsa ya yi suna fad'in kamar yana sha nono saboda jikinsa ya ginu babu motsewa ko wata matsalar gaskiya yana samun kulawa sosai a wurin Baba Tabawa ba shi da matsalar maraicin nonon mamansa."
Da d'an jin dadi ya ce." Na gode Allah na kuma gode muku Amina ina mutukar godiya Allah Ya saka muku da alheri

'Dan tausayi ya ba ni domin yanayin yadda ya yi maganar ya nuna mini cewa har yanzu yana jin zafin abinda Hauwa ta yi kuma abin ya dame shi abubuwa ne da yawa suka yi masa dabaibayi. Ta bakin Hajiya Saratun Hauwa ko a waje ya aurota bai kamata ta yi wannan sakarcin ba. yaro
d'anyar haihuwa ta ajiye saboda wani banzan dalili.
Na ce." Ni kam banga abin godiya ba duk abinda na yi maka ai kaina na yi wa."
Ya yi shiru bai ce komai ba yana dai ta kar'bar towon da nake bashi a baki har guda ya kusa k'arewa ya ce." Ban ga kin ci ba."
"Na ce." Sai ka koshi my love dina." Ya sa dariya wadda ban yi tsammani ba yana fad'in." Na ga sai wani ji ki ke da ni Amina."
Da d'an murmushi na ce." Tausayi ka ba ni." Ya gyad'a kansa da wani irin murmushi kwantacce a a tare dashi ya cinye malmalar towo daya na kara cire wani daga leda na cigaba da bashi bai hana ni ba. Jefi jefi muna d'an ta'ba hira mafi rinjaye kan marigayiyar ne. Da kyar na daure na soko maganar da take ta damuna na ce." Akan maganar da yan'uwanta suke yi akan mu ni da Hauwa wata'kila sun gaya maka kai ma ko?"
Ya ce." Wace magana ce kuma?"
Cike da damuwa na furta." Wai duk wanda ya shiga gidan domin yi musu ta'aziyya sai sun gaya masa irin zaman da muke da ita har suna fad'in bakincikin da muka jima muna guma mata ne ya yi sanadiyar rasuwarta."
Ya yi jim Yana kallona kafin ya ja siririn tsaki ya ce." Ke waye ya gaya miki haka?"
Kai tsaye na Mamana ce?" Ya san dama ina kiran yayarsa da sunan.
Sai ya girgiza kansa yana fad'in. " Mata dai ba a raba ku da k'ananun maganganu da fitina baiwar Allah ga sanadin mutuwarsa amma an jingina da wani lamari domin tayar da husuma ba ni so na ji bakinki a ciki wannan maganar duk abinda za su yi kada ki biye musu ku daga mini hankali don Allah domin na lura basu da kintsi dukkaninsu taron sakarkaru ne me yasa ga gaskiya 'kiri-'kiri a take gabad'aya da ni da su da ke mun san yadda ciwuka suka cinye Maryam har ajalinta ya sauka to me ya kawo wannan maganar kuma?"
Na ce." Ni ma abinda na gani kenan, kasan kuma dole ne na damu tunda ni ce a gidan yanzu, a ganina idan wasu basu yarda ba wasu za su yarda tunda Allah ne kadai ya san irin abinda suke fad'a a kanmu."
Ya ce." To kada wannan ya dame ki, tunda har maganar ta dawo kunnena zan yi wa tufkar hanci, na gaya miki dai kada ki kula su ku zubar mini da mutunci a gari."
A tak'aice na ce." In sha Allahu rabbi."

D'akin ya sake daukar shiru na wani lokaci kafin na sake yin kundubalar yin magana abin kamar wadda Hauwa ta sammace idan ma nace ba zan sake yin magana ba sai na kasa jurewa gabad'aya idan na tuna bata gidan sai na ji gabana ya buga kuma a raina sai nake ganin ai lefinta bai kai ace an rabu da ita gabad'aya ba tunda shima ai yanayi mata lefi me yasa shi da yayarsa suka fi bata rashin gaskiya.

Na ce." Don Allah tunda haka ta faru ku yi hakuri Hauwa...... Ban kai ga k?rasa abinda yake bakina ba ya katse ni da babban sauti." Amina." Ya kira sunana na amsa da "Na'am tare da zuba masa ido gabana na d'an fad'uwa ganin yadda ya yi bala'in shan kunu......
'?
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*


[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t

*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda

Chapters

Related Ebooks
03, August 2026
Aisha kabir iliyasu

Please book for gudun aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login