Showing 210001 words to 213000 words out of 450388 words

Chapter 71 - Gudun Aure Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

4098

ji ciwon irin tijarar da Hauwa ta yi mata.
'Dagowar da za ta yi kuwa sai ya yi daidai da kwaranyowar ruwan hawaye a dakalin fuskarta. Ba ta yi yun'kurin gogewa ba sai ta kalleni ta fara magana cikin karaya da zullumi." Amina ni na haifi Salim amma wallahi ba na goyon bayansa akan irin abubuwan da yake aikatawa na rashin kyautatawa. sannan na sake jadadda miki babu yawuna ka haifi d'a ne kawai amma ba ka haifi halinsa b..... Hauwa ta yi saurin cewa." Kuka ai yanzu ki ka soma in sha Allahu rabbi Hajiya kina
fama da gagararan d'anki da ki ka kasa sarrafawa ina ke ina iya yi wa yaran wasu tarbiya wallahi ki ji tsoron Allah da Annabi, ga shi dai da bakin ki kin fad'a cewa Salim baya jin maganar ki, sannan nan Nusaiba ta shigo har gida ta yi mana rashin kunya, ina tarbiya anan kina so ki lalata mana yaranmu ne, ko kuma kina so su yi koyi da abinda yaranki suke yi duk a had'u a yi mutuwar kasko gabad'aya ko ba haka ba ne."
Shiru ta yi ba ta ce mata komai ba. Na dube Hauwa da ta kasa zaune a kan kujera sai zabura take yi kamar ta yi tsalle a gabanta ta rufe ta da duka.
Gyada kaina na yi ban ce komai ba na mayar da hankalina kanta domin sauraran abinda take cewa." Na nunawa Salim takaici da 'bacin raina na kuma gargade shi akan kada ya kuskura abu mafi muni ya sake faruwa irin haka. Ina kwance cikin ciwo jiya na samu labarin doki-in-doka da ya shiga tsakaninsu. Wannan shine abinda ya fi tayar mini da hankali na ce kina ina har hakan ta faru. Ban haifi Kamalu da Yusi ba, amma yau zan gaya miki wani abu da nake ji game da yaran nan a zuciyata wallahi ina sonsu fiye da yadda ki ke tsammani. Yadda nake jin yaranku gabad'aya a raina haka nake jin wanda na haifa. Ina rokonki da Allah da annabi kada ki yanke kyakykyawar ala'kar dake tsakaninmu. Kada ki yi yun'kurin datse k'akkarfan zumuncin da yake tsakanin Adamu da Yusuf domin kuwa d'azu Adam ya je mini cikin damuwa cewa kin tura yaran nan kano, ki yi hakuri yara su dawo mu cigaba da rayuwa cikin aminci na yi miki alkawari wani abu makamancin wannan ba zai sake faruwa ba. Kuma in sha Allahu Salim zai shigo ya baki ha'kuri komai ya shige da izinin Allah."

Ta gama maganar tana sanya hannu domin share hawayen da yake ta tsiyaya a fuskarta. A nutse na ce." Ki yi hakuri ki daina kuka akan wannan lamari Momi wallahi ban k'ullaceki ba, kuma ni har abada akan yara ba zan yi rigima dake ba, amma ina so ki sani ce wa muddin Kamalu da Salim na tare a Inuwa daya to sa'bani ba zai daina giftawa a tsakaninsu ba. Abinda ba na fatan ya sake faruwa. Ba wai ba ki isa ba ne, kin fi karfin komai a wurina domin ban mance alherinki ba, ki yi hakuri yara dai har abada sun bar nan in sha Allahu suna can hannun dangin Babansu sai dai su zo da ziyara. kuma ban isa na yanke zumuci da ala'ka ba tunda ai ba ni na had'a ba......
'?
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=?N?*

*TALLAH!*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya


Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 ne kachal=?L?
*88*
Ta yi shiru tana gyad'a kanta kafin daga bisani ta yi wani murmushi da babu annashuwa ta ce." Shikkenan ba zan karya miki rantsuwarki ba Amina tunda har kin rantse amma ya za a yi da kayansu akwai takardun Yusi na makaranta shi ma Kamalu akwai wanda na sanya aka yi masa domin na gama shiri tsaf za su tafi jami'ar musulunci ta Madina makarantar da Salim ya kammala domin samun horo fannin addini da al'kur'ani tare da hadisan Annabi Muhammadu S.a.w."
A nutse na ce." Babu damuwa duk abinda ya danganci nasu ne za ki iya aiko mini dashi sai nasa a mota a kai musu in sha Allahu rabbi, na gode sosai Allah Ya saka miki da alheri."
A sanyaye ta amsa da "Amin." Kafin ta yun'kura da kyar ta tashi tana gyara madaidaicin hijab din da yake wuyanta ta ce." Zan shiga gida, Allah Ya ba mu alheri."
Ni kadai na amsa mata. Hauwa kam uffan ba ta ce mana ba har muka 'kare maganarmu. Ta kama hanyar fita jikinta a sanyaye.
Gabad'aya muka bi ta da kallo tana tafiya a hankali da rashi kuzari.
Sai bayan da ta fita ne Hauwa ta ja tsaki tana fad'in." Sai ta d'an ban tausayi wallahi."
Na dubeta a hankali na ce." Hauwa zan gaya miki gaskiya abinda ki ka yi wa matar nan ba daidai ba ne, don Allah ko don gaba kada ki sake kwatantawa ko so kike ki k?rasa gawar da ba ta ki ba. Kina kallon fa a yanayin da take ciki amma sai tsalle ki ke kina han'karo kamar za ki kai mata duka. Takaici abinda ki ka yi mata ne fa ya sanyata kuka. Ki duba shekaru da kuma d'awainiyar da take yi da yara don Allah."
Dan murmushi ta yi sai kuma ta ja tsaki a karon da babu adadi ta ce." Ta yi kukan jini ma, ni ina ruwana, sau nawa a sanadinta ana sanya ni kuka, munafukar banza kawai duk abinda take yi wallahi da niyya take yi ai sanin zuciyar mutum sai Allah."
Na gyad'a kai ina sake ce wa." Magana dai ta mutu Hauwa don Allah ni dai kada hakan ta sake faruwa kin ji."

Ta'be baki ta yi tare da furta." Haba ko yanzu na buga na bada ruwa wallahi zuciyata wasai nake jin ta. Murmushi takaici kawai na yi na yun'kura na tashi cikin zuciyata nake fad'in ba za ki ta'ba canzawa ba Hauwa, ba ki takali rigimar kina jin dad'i ba abinda zai biyo baya shine damuwar domin kuwa nasan akwai rikici akwance a tsakaninmu da shi uban gayyar. Shiga ta d'aki da kamar minti ashirin na fara jin hayaniya na tashi falo. Murya Hauwa a sama da wata murya da na kasa tantance ko ta wacece. Cike da zullumi da fargaba na fito falon na same su a tsaye cirko cirko har da yaranmu k'ananu a tsaye kusa da baba Tabawa dake ko'karin shiga tsakani.
Nabila ce 'kanwar Momi mutuniyata ce sosai kuma tun lokacin rasuwar Alhaji Amadu muka kulla zumunci don har musayar lamba muka yi. Sai ta d'an ja baya da ni ta rage kiran wayata bayan auran 'yar uwarta da maigidan. Ni kuma ban ta'ba nuna mata komai ba don wasu lukutan har magana nake yi mata idan na ga ta d'ora status a Whasap amma dai duk da hakan ta kasa sakin jikinta kamar lukutan baya.

Tana tsaye cikin shiga ta alfarma dama can 'yar gayu ce tunda itama tana taba kasuwancin irin na 'yar uwarta business take yi sosai zannuwan gado takalma da dogayen riguna har dashi take yi irin na manya maza da mata tunda ina gani a wasu lukutan tana dorawa a status dinta tana juya kudi itama yaranta biyu kacal duk maza tunda auranta ya mutu ta famtsa duniya itama har 'kasashen waje take zuwa sarin kaya..

"Ba ku isa ku kashe Momi da bakincinku ba Hauwa. Idan ba zata iya ba, ni zan kar'bi rigimar akan me? me ta yi muku da za ku tisa ta a gaba, masifar yau daban ta gobe daban tunda ta auri mijinku kuke yi mata bita da 'kulli kun had'e mata kai me ya yi zafi
mace tana sonku da zaman lafiya, tana d'awainiya da yaranku amma kuna cin dunduniyarta. Idan kun had'e mata kai sai me? Mijinta yana sonta fa, ai duk maccan da ta samu soyayyar namiji itace mowa kowa ya iya allonsa ya wanke
kuma ita alheri a jininta yake, wallahi ba za mu lamunta ba, za mu iya d'aukar kowane irin mataki akan abinda kuke yi."

Ido na zuba mata kawai kaina ya gama d'aurewa da maganganunta amma ba zan ce mata komai ba Hauwa kadai ta isheta tunda dama mai neman kuka ce.
Aikuwa ta bugi kirji har tana had'awa da tsalle tana fad'in." Karya banza da wofi an had'e mata kan don Allah ku d'auki mataki, matsafa masu kauce hanya domin neman duniya menene ba mu sani ba, dube ki don Allah sai kace tsohuwar karuwa tunda ki ka shigo falon nan ya game da 'karni da warin zunubi, kuna haura kan dutse fa ai ba abin mamaki ba ne don 'yar uwarki ta zama mowa a gidan nan, mun san komai mun ji labari
asalin dukiyar da uwar guzumar taku ta tara daga majiya mai tushe cewa kudin tsafi ne uwarku da ubanku ta bawa gumaka suka shanye jininsu. Sannan 'dan uwanku da aka tsinci gawarsa an kwakule masa Ido tare da cire masa 'ya'yan maraina haka aka ce da sanya hannunta. Tun a wancan lokacin kowa ya sheda matsafiya ce shine yanzu ta fake da gina gidan marayu taimakawa mabukata da sadaka domin yi wa Allah a dubara, in sha Allahu ba za ta yi karshe mai kyau ba
Har mu za a zo a yi wa wata burga, ko kuwa mun ce ta yi dawainiya da yaranmu ne? Ita taga zata iya. Mu dai in sha Allahu ba zamu rayu da kudin haram ba. Ba zamu fake da Allah da addini mu ciyar mu tufatar da kudin jinin mutane ba."
Nan da nan Nabila ta rikici sai ta fara rawar murya idanuwanta suka ciko da ruwan hawaye ta ce." Wallahi tallahi Hauwa sai mun yi shari'a dake sai kin tsaya a gaban alkali kin bada sheda akan abinda ki ka fad'a akan 'yar uwarmu wallahi ba zamu bar wannan maganar ba
ba za mu yarda."

Ta ce." Ashe babu dadi k'azafi ko. Mai yasa kuka take gaskiya da gangan, yanzu ke Nabila har kina da bakin da za ki zo ki tsaya a gabanmu da wata banzar magana. Ki je ki tambayi 'yar uwar ki irin zaman da muke yi da ita a gidan. Ai ba a banza ta ri'ke mana yara ba. A shirye nake ki kalleni da kyau babu wata 'yar iska da ta isa na ji tsoronta wallahi."
Nabila ta kasa cewa komai domin ta yi mutukar k'aduwa da jin maganganun da suka fito daga bakin Hauwa. Duk yadda ta dinga kokarin hana kanta kuka hakan bai samu ba cikin gaggawa ta kama hanyar fita ba tare da ta iya mayar da martani ba.

Cike da mutuwar jiki na dubi Hauwa da take ta numfarfashi na ce." Tsakani da Allah Hauwa idan rai ya 'baci yana da kyau a sanya hankali da tunani. Yanzu ke don Allah a ina ki ka ji wannan maganar kada fa ki d'auri kanki Hauwa mai ya yi zafi ne, ni dai idan har a kaina ki ke wannan balo'kokon to don Allah ya isa haka, yaran da suka asassa wannan rikicin na d'auke su da gidan fakat mu zauna lafiya, babu ruwanki da matar nan da duk abinda zai shiga tsakaninta da mijinta a kan hakkinki kawai ya kamata ki yi magana, amma ki yi kokarin kawar da kanki daga barin ji da ganin abinda yake yi a kanta."
Baba Tabawa ta jijjiga kanta cikin alhini da damuwa ta furta." Don Allah ku zauna lafiya, wallahi ba na jin dad'in abubuwan nan da suke faruwa."
Tsaki ta ja kafin ta ce." A shirye nake da abinda zai biyo baya Amina, wallahi yadda na tsani mutuwata haka na tsani matar nan, munufuuka ce, mai son zuciya gabad'aya ta juyar mana da kan miji, ai kafin ya aureta muna zaune lafiya da sauki akan abinda yake yi yanzu, babu wadda yake gani da mutunci face ita. Ta dabaibayi shi ta ko'ina ta asirce shi sannan ta zo tana sadda kai kasa tana magana cikin alhini kamar wata mai gaskiya wallahi zuciyarta babu Allah
kuma abinda na fad'a ai ba k'aharu ba ne, ni ma ji na yi ana fad'a a duniya." Daga haka sai ta tashi ta shige dakinta cike da neman tashin hankali.

Ni da Baba Tabawa muka bi ta da kallo cike da tsantsar mamaki. mai ya yi zafi haka, a ganina abinda take yi ai ni ya kamata na yi amma ban yi ba, ita lamarin nata yana nema ya wuce gona da iri fa, ba na so ta janyowa kanta gagarimin rikicin da zata yi nadama a gaba domin kuwa wad'annan maganganun sun yi tsauri kwarai da gaske kuma sun yi muni.

To ita rigima dama akwance take shiyasa tashinta bashi da amfani domin kuwa muddin ta tashi akan sha mutukar wahala wajan samun ruwan da zai kasheta. A wasu lukutan ma ana kashetan shaid'an da mukarrabansa suke shiga cikinta su yi kane-kane, su bugi wannan bangare su bugi wancan b'angare.

Lokacin da na ga kiran wayarsa hankalina ya tashi sosai dalili ban san mai yake 'kunshe a cikin kiran nasa ba, daga jiya zuwa yau abubuwa masu muni sun faru wanda na tabbatar da cewa muddin ba a kai zuciyoyi nesa ba to rayukan kowa zai 'baci har da wad'anda ma ba su ji ba, ba su ga ni ba.
Na daidaita yanayi kwarai da aniya ban bari raunina ya bayyana ba na d'aga wayar a nutse gaisheshi na fara yi bai amsa mini ba ya ce." Kai ni 'kara wurin Mahaifiyata bai gamsar da ku ba har sai kun had'a ba ki kun cutar da baiwar Allah ko Amina?"
Na ce." Ban fahimci maganarka ba."
"Nabila ta kira ni yanzu ta cikin tsananin damuwa tana fad'in irin abinda kuka yi mata yanzu daidai kenan Amina, ko kina so ki nuna mini hassadarki a fili domin Allah Ya suturta Maryam ta fi ku kyau da ilimi da gogewa ta fi ku dukiya da kyauta da tausayi, kana ta fi ku mutunci da karrama dan adam. Idan har za ku yi kishi akan soyayyar da nake yi mata wannan ba zai dame ni ba, tunda zuciyata ita ta za'ba a madadinku, amma ba zan lamunci cin zarafi da sharri ba, zan shige mata gaba domin ganin an hukuntaku bisa sharrin da ku ka yi mata mai mutukar muni da razanarwa......
'?
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=?N?*


*TALLAH!*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl

Momyn Hajara GHT supplements

Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah

Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya


Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah

Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 ne kachal=?L?
*89*
A nutse na ce." To shikkenan muna sauraran sammanci a shirye muke ita Maryam tana da kai Tajo, Amina da Hauwa kuma suna da Allah da Annabinsa sai maganar da ka ke yi akan cewa muna yi mata hassada wallahi tallahi ni ban ga abin 'kyashi da b'akinciki a tare da wannan kwalmad'addiyar matar taka ba mai kama da mai cutar kanjamau ba, kudi da kake magana tana da su
kasan daidai gwargwado nima ina da su na halali babu wata mummunar hanyar da na bi wurin nemansu gumina ne, halak dina ne, babu wani mahaluki da ya ta'ba ba ni kwabonsa da zummar na yi jari, Ubangijina ya rufa mini asiri sannan
Ya taimake ni ban ta'ba ro'konka abin hannunka ba ina ga dana ta'ba neman wata alfarma a wurinka to da
cin zarafin da za ka yi mini sai ya fi haka. Ban ta'ba cewa Tajo tallafa mini ba. Eh tabbas talaka ne ubana amma ba mai mutuwar zuciya ba, kuma kai kanka ka san ba a tsiyace ka aure ni balle ka goranta mini. Allah Ya yi mini rufin asirin da babu wani mahalukin da ya isa ya firgita ni da dukiyarsa. Kai kanka baka da abinda za ka burge ni ga gigitani dashi ta fannin arziki balle matarka. Ko yanzu ka sake ni ba ni da kaico wallahi domin ina da madogara don naga kamar kana tunanin zan yi b'akincikin rabuwa da wannan daular da aka ajiye ni a cikinta. Idan kana da ja akan maganata to jarraba sakina kaga abinda zai faru.
Na yi shiru ina sauke ajiyar zuciya cike da tsananin bacin rai na cigaba da ce wa." Tunda ka zama dan aike jani talau ka gaya musu mun shirya da

Chapters

Related Ebooks
03, August 2026
Aisha kabir iliyasu

Please book for gudun aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login