Showing 12001 words to 15000 words out of 450388 words

Chapter 5 - Gudun Aure Complete Hausa Novel

16 Jul 2026

4099

wa Allah, amma ba zai yiwu ba sai dai ya je can wani wuri ya nema.
Hajja ranta ya yi mummunan baci har sai da ta zubar da hawaye akan kyamar da 'yar uwarta ta nunawa jininta. Daga karshe sai kawai ta ha'kura ta barwa Allah sai dai koyaushe cikin tsananta addu'a take yi a kansa akan Allah Ya magance masa matsalarsa.

Shi ma tun daga lokacin sha'awar aure ta fice masa daga rai domin shima ya tsorata ainun har ya fara zargin kansa yana hasashen kada dai maganar da jama'a suke yi ta zama gaskiya.
Dalilin ciwon mahaifiyarsa kenan Hajja hawan jini mai k'arfi ya kamata. Ashe da sugar a kwance sai shima ya tashi duk a lokacin aka dinga dau'ki ba dadi da ita ana neman rai 'kasa-'kasa har dai Allah Ya sassauta mata aka dawo da ita. Sai dai sa'i da lokaci ciwon yana tashi mussaman idan ta shiga yanayi na b'acin rai da fargaba. Amma da yake macace mai tawakkali bata ta'ba gazgata maganar mutane akan yaronta ba. Ta amince Allah ne yake saukar da ikonsa a kansa, kuma duk wanda ya mutu lokacinsa ne yayi har yanzu bata yarda yaronta yana tare da makaru ko wata aljana ba. Allah ne me yi kuma shi ta mikawa lamarin gabakidaya. Wannan dalilin ne ya sanya take yawan zuwa kasa mai tsarki domin ta yi masa addu'a akan Allah ya kawo karshen matsalarsa. Girma da manyan shekaru sun hau kanta tana so kafin rayuwarta ta kare taga yaransa.
Ganin Amina na ro'kon Allah akan miji nagari a take ta ji a ranta Allah ya kar'bi adduarsu bakidaya dalilin da ya sanya kenan ba ta yi shiru ba ta nemi alfarmar yarinyar wanda ta hangi dacewar auran nasu da samun albarka mai tarin yawa.

Wannan kenan...

Wani irin numfashi take fesarwa idanuwanta a rufe jikinta gabad'aya ya saki.
Gabad'ayanmu muka gigice! Mussaman shi uban gayyar ya tararrayota jikinsa ya rungume yana kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Ni kam Ina daga zaune amma kafafuwana sai karkarwa suke yi. Sai na nemi kukan da nake yi na rasa tsabar tashin hankali da d'imuwa. Ban san lokacin dana je na rungume kanta a kirjina ba ashe na hada da hannunsa. Ya cire da saurin gaske. Ya tashi da sauri d'akin da ya fito ya shiga Hajiya saratu ta zauna a wurin da ya tashi tana share hawaye. Ganin yadda na d'uka kanta ina yi mata addu'a sai itama ta fara yi. Tana tofa mata kamar yadda nake yi. Hannuna a saman kirjinta ina dan shafawa a hankali a hankali numfashinta ya daidaita. Jikin nata kuma ya daina karkarwa.
Babanmu na gefena a tsaye ya rasa yadda zai yi in banda kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un babu abinda yake yi.

Ya fito yana waya da harshen larabci kimanin minti uku ya gama wayar ya je kusa da 'yar'uwarsa ya tsaya ita dashi duk suka ba ni tausayi ganin yadda suka d'imauce.
Falon ya yi tsit! kowa da irin abinda yake sa'kawa a zuciyarsa.

Wannan littafin dai na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina na, duk kankantar hakki sunansa hakki mu kula sosai!

Kai na shiga rud'u ba k'arami ba. Ni tsorona Allah da Annabi kada ta mutu na zama ina da hannu a ciki. Har likitan ya zo ya gama abinda zai yi bana cikin hankalina.
Na dai tsinci kad'an daga cikin bayanin da yake yi akan tashin ciwon wani labari taji ya firgitata ko dai taga wani tashin hankalin har jinita ya haura ka'ida dole a kiyaye."
Baba ya ce ba zamu tafi ba har sai ta tashi daga bacci ya tabbatar mata da cewa aure kamar an yi shi an gama. Ni ma ban bada goyan bayan tafiyar ba dalili na san hankalina ba zai ta'ba kwanciya ba in ba gani nayi ta tashi ba.
Anan muka kwana sai gefin asuba tukkuna ta motsa.
Da yake ina kusa da ita da sauri na ri'ke hannunta ta fara yun'kurin tashi zaune Hajiya Saratu ta zo ta taimaka mini muka tayar da ita. Ta zuba mini ido tana kallo. Sai na rike hannunta da kyau na ce." Sannu Hajja ya jikin naki?"
Muryata rad'au ta furta." Na ji sauki ina Tajo?"
Da sauri na daga kaina yana can saman wani gado a kwance wata'kila bacci ne ya shammace shi.
Hajiya saratu ta ce ." Gashi can a kwance wata'kila bacci ne ya d'auke shi."
Sai ta girgiza kanta kawai ta tashi tana fad'in." Sallah zan yi." Muka kamata muka kaita bandaki ta kama ruwa ta dauro alwala. Jikinta yayi kwari sosai a tsaye tayi sallarta cikin nutsuwa.
Hankalina ya kwanta sosai ganin yadda Allah ya rufa asiri ciwon bai tsananta ba.
Bayan duk mun gabatar da salla an gaisa da juna. Babanmu ya dubeta yana fad'in." Hajiya maganar nan tana nan in sha Allahu za a daura auran Alhaji Tajo da Amina muddin Hakan shine kwanciyar hankalinki. Yau Juma'a kamar yadda kika buk'ata sai a nemi albarkar ranar. Duka ni da ita mun mikawa Allah lamarin shine yake da iko damu bakidaya."

"Ta d'an dube ni a hankali kafin ta ce." Amina na janye maganata, ba zan sanya ki kiyi abinda ranki baya so ba. Kamar yadda ki ka fad'a kina da za'bi a rayuwarki. Allah Ya za'ba muku abinda yafi alheri gabad'aya. Za mu cigaba da zumunci daku in sha Allahu rabbi."

A lokacin da ta fad'i maganar rasa abin yi nayi duk sai na diririce! Magana nake so na yi amma bakina ya yi nauyi.
Ban ta'ba ganin tsananin fushin Babanmu ba sai a lokacin. Ya rufe ni da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. yana cewa shi ya haife ni ba zai yi mini baki ba, ammafa da wahala na samu miji kamar wannan. Hawaye masu zafi suka dinga gudana a kumatuna. Duk yadda na so na fahimtar dashi halin da ake ciki ba zai gane ba, idonsa ya riga ya rufe da cewa babban mutum zai auri jininsa. Babanmu a sanin da nayi masa bashi da kwadayin abin duniya amma yanzu tashi guda ya aminta da auran mutumin da bai tsananta bincike akan halayensa ba.
Kuka nake sosai na gaza cewa komai Ina dai jin hajjan tana ce masa ya bar maganar haka ai don ba a yi auran ba zumunci ba zai yanke ba.
Da kyar na furta." Hajja ku gafarce ni, akwai 'kudurori da manufofi da uzurirrikana da nake so na cika a rayuwata shine dalilin da ya sanya na k'yamaci aure a yanzu. Ba wai ina 'kin jininki ba ne. Ni ya kamata ku k'yamata amma baku yi ba, wallahi na amince ayi auran nan saboda farincikinki. Yadda lokaci daya kika nuna mini k'auna ni kaina na san idan na nuna 'kyama ga alherin da kike nufina dashi ban yi miki adalci ba. Na yarda na amince Koda hakan zai zama karshen numfashina kenan." Na rushe da wani irin kuka mai karfi. Sai ta kamo ni ta rungume tsam a jikinta tana kuka take fad'in." In sha Allahu zaku zauna lafiya da juna kuma za a samu zuria mai albarka na gode sosai da wannan karamcin da kika yi mini Allah Ya yi niki albarka. Na gode, na gode na gode sosai."

Abin mamaki da al'ajabi. A ranar aka d'aura auran bayan an idar da sallar Juma'a. Shi kuma uban gayyar wanda tunda ake turka-turkar bai tofa tasa ba kawai dai yana ta bin mu da ido, duk abinda mahaifiyarsa ta ce masa ya yi zai ce mata to. Ganin hakan yasa ni ma na sasauta kyamatar lamarin a gabansu. Idan na cigaba da yin tutsu hakan zai nuna cewa na fi karfin mahaifina kamar yadda mutane suke zargi.
Manyan mutane ne suka halarci d'aurin auran a massalaci bayan an idar da sallar juma'a wanda sarki mai zamani a lokacin shi ya daura auran a massalacin Annabi Muhammadu S.A.W.
Na samu gudumuwa sosai daga wurin abokanansa larabawa da suke hurd'a kudi da gold masu yawa.
Kafin kice kwabo labari ya watsu a duniya gidajan yada labarai jaridu da social media sun samu abin yi. Sahihin gidan jaridar da jama'a suka aminta dashi sune suka fara sanarwa a shafinsu na fecebook.
Alhaji Tajudden Ibrahimu shararran dan'kasuwar nan ya auri 'yar gwagwarmaya kuma 'Yar kasuwar nan Amina Salisu mai-hula. Mahafiyar yaron nan Kamalu wadda a kwanakin baya ta yi dogon rubutu na zagi da 'batanci a kansa ashafinta na fecebook. An d'aura auran ne yau juma'a a madina massalaci Annabi Muhammadu S.a.w inda shahararrun mutane suka samu damar halarta. Amarya ta samu gudumuwa sosai daga hannun abokanan ango. Allah Ya basu zaman lafiya.
Wannan dogon bayanin sun yi shine tare da hotona da nashi a had'e......
'?
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram akwai normal What'sapp group #700 ga wad'anda karatu a talgrm yake yi musu wahala hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN=?N?*

*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay


*6*
Lamarin da ya janyo hayaniya da kace-na-ce, mussaman a social media kowa na fad'in albarkacin bakinsa. Wasu na ganin Alhaji Tajo alfarma ya yi mini ya aure ni. Wad'anda kuma suka san tarihinsa na baya suna ganin kawai kwanana ne ya k'are tunda har kud'insa suka rude ni na aure shi bayan nasan matsalarsa.
Ni dai tunda aka d'aura auran nake ta zubar da hawaye gabad'aya na rasa a da wane ma'auni zan auna lamarin. Wace irin k'addara ce wannan mai sammatsi. Ina zaune a wani d'aki da yake cikin gidansa domin tun jiya da muka zo ni da Baba Hajjan tace mu zauna kawai kayanmu ma dake can masaukinmu sai turawa akayi aka d'aukosu. Ina jin messages (sakkoni) na ta shigowa wayata ban duba ba dalili na riga na san ba ni da nutsuwar da zan bada amsa abinda dai na yanke a zuciyata shine duk wanda ya tambayi ya akayi hakan ta faru zan ce masa ban sani ba. Shigowar Hajiya Saratu d'akin da kaya a hannunta ya sanya da sauri na goge hawayen kumatuna.
Sai ta girgiza kanta ta karaso wurin da nake tana fad'in." Ki yi hakuri don Allah ki daina wannan kukan Amina. Wallahi tallahi kin ji rantsuwar Muslimi ba zamu cutar dake ba. Duk abinda hajiyarmu ta kaunace shi ya zame mana dole mu 'kaunace shi. Kuma albishirin da zan yi miki shine kin yi miji, ba don Tajo d'an'uwana ne ba nake gaya miki haka, mutum ne da rabin mutum. Zai baki kulawa sosai, kuma zaki samu jin dadin rayuwa dake da yaranki. Ki kwantar da hankalinki, kuma jita-jita na mutane ya daina damunki ki barwa Allah lamarinsa tunda ke kanki idan ki ka yi wa lamarin nan duba na tsanaki za ki san shirin Allah ne."

Murmushi kawai na iya bakina ya yi nauyin da ba zan iya ce mata ba na son d'an'uwanta ba. Gashi kuma ina jin nauyinta domin tana da irin sunan Mamana. Kawai sai na sunkuyar da kaina kasa. Ta ajiye mini kayan da ta shigo dashi tana fad'in." Ki shirya yanzu nan ya kira ni a waya na gaya miki za su shigo tare da abokanansa za a yi hoton tarihi."
Tana gama maganarta ta juya ta fita daga d'akin a gaggauce.
Ledojin na bude dogayen riguna ne manya irin na larabawa da hijabai masu kyawun gaske. Da band'aki a cikin d'akin na shiga na yi wanka na fito na zura d'aya daga cikin dogayen rigunan a jikina. Na d'auki karamin hijabi iya kafad'a nasa. Turare na d'auka akan madubi na fesa a jikina na nemi wuri na zauna zuciya gabad'aya a cunkushe.

Sa'kkonin da aka turo mini ta inbox na fara dubawa. Wanda na yi wa duban tsanaki na Anti Yagana da Sahura. Tambayata suke yi shin labarin da suka ji yana yawo a gari da gaske ne. Kuma ya akayi hakan ta faru.
Na basu amsa da gaske ne. Amma ni ma ban san yadda aka yi ba, kawai su taya ni da addu'a. Idan kuma kwanana ya kare suka kula mini da yarana."
Nasa hannu na goge hawayen da ya shiga zarya a kumatuna wanda ya yi daidai da lokacin da aka turo kofar d'akin a bazata na daga kaina muka yi Ido hudu. Ya mayar da kofar ya rufe ruf. Ya nufo wurin da nake cikin shigar larabawa harda alkyabba irin tasu.
Gabana ya dinga bugawa da k'arfi da k'arfi. Zuciyata tana harbawa kamar zata faso kirjina ta fito.
Daf da ni ya tsaya masifaffen kamshin turaransa ya fara surnanowa hancina.
"Amaryar Tajo." Maganar ta daki kunnena. Hanci na ja ban dago kaina ba balle na kalle shi.

Wannan littafin dai na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini muddin ba ki biyani hakkina ba, mu kula sosai hakki komai kankantarsa sunan hakki.

"Na gode sosai, da wannan sadaukarwar taki, kin daraja mahaifiyata. Kin kar'bi ro'konta, wannan dalilin ya sanya na baki gurbi mai girma a zuciyata. Ba ni da ra'ayin aure a yanzu saboda tarin matsalolina. Amma ba ni da k'wanjin yin turjiya ga umarnin mahaifiyata. Kada ki damu yaranki ki zo tare dasu, ai d'a duka na kowa ne, Allah Ya raya su, ke kuma Allah Ya ba ki hakuri da juriyar zama da ni."

"Ba zan iya zama da mazina ci ba. Ba zaka same ni ba har abada. Aure an d'aura dai amma zai zama na kwangila. Zan zauna a gidanka zan cigaba da hurd'odina na yi hakan ne saboda mahaifiyarka, amma ni ba ni da burun auran irinka, abinda yake cikin zuciyata na fito na gaya maka. Kana da damar auro wata, amma ni kam ba zan iya had'a jiki dakai ba."
Ido cikin Ido na gaya masa haka domin tun yanzu gwara ya san manufata. Haka kawai nake masa kallon mai cutuka a jiki. Domin duk mutumin da yake zina ba zaka raba shi da matsaltsalu ba.

Ya jima yana kallona kafin ya nisa. Ya daga kafadarsa yana fad'in." Ai aure ba abin wasa ba ne, ni ba munafiki ba ne, kuma ba zan fara a kan wannan karamin dalilin ba. Ni ya kamata na kyamace ki saboda mazan da ki ka yi tarayya dasu a baya. Amma har kina da bakin fad'a mini magana. Ki zauna a shirye duk lokacin da na tashi kar'bar sadakina zan turo miki likita ta auna ki. Domin ni har yanzu saurayi ne babu wata mace da na sani."

Wani irin kallo na yi masa a watse na ce." Sai dai a auna mu a tare don wallahi ba zan yarda ka shafa mini 'kanjamau ba."
Sai ya fashe da dariya irin wadda ban ta'ba ganin ya yi ba. Ya nuna kirjinsa da hannu yana cewa." Ni ne mai kanjamau!"
Murgud'a bakina na yi na kawar da kaina gefe.

Ya nisa kafin ya ce." Okey to shikkenan yanzu dai ki tashi muje abokaina suna falo wai sai an yi mana hoton tarihi Ina ce Hajiya Saratu ta gaya miki ko?"

Shiru na yi ban bashi amsa ba, kuma ban tashi ba.
"Kin ji ni ko?" Ya fad'a can kasan makoshinsa. Ban motsa ba.
"Amina."
Ya furta sunana a hankali tare da dora hannunsa a kafada. Na goce tare da mikewa tsaye ina gyara karamin hijabin din wuyana. Kawai na tsince shi yana satar kallon kirjina. Da sauri na dan gicciya gabana na faduwa. Ya miko mini hannunsa.
"Sa hannunki a cikin nawa, ai ko ba ma son juna ba za mu nunawa duniya ba ko?" Yafad'a yana matsowa jikina. Na matsa da saurin gaske. Sai ya gyara fuskarsa babu fara'a. Ya furta." Ba na son sakarcin banza, ko kin shirya ba ni kunya ne a cikin mutane? Duk abinda za ki nuna a yanzu kamar kina gayawa duniya yadda akayi auran nan ne, kin san matsayina

Chapters

Related Ebooks
03, August 2026
Aisha kabir iliyasu

Please book for gudun aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login