Showing 1 words to 3000 words out of 95068 words

Chapter 1 - FEERYAL BOOK3 COMPLETE

Da sauri Aunty ta waro ido ta ce

"An d'aura fa kace Daddy!."

"Kwarai kuwa an d'aura yanzu, cikin yardar Allah Fad'imatu,

Bappa Salihu ne ya ce a d'aura yanzu dan wani jinkirin ba alhaki bane, musamman a gab'ar da ake yanzu."

jiki a sanyaye Aunty ta ce

"D

addy ni dai ina fargabar abin da zaije ya dawo."

Daddy ya katseta

"Kiyi fatan alkhairi Allah zai wuce gaba,

yanzu abin da nake so dake je ki kira min Feeryal d'in."

Aunty ta mike jiki ba kwari ta nufi d'akin Feeryal ta tarar da ita tana bacci, ta dawo ta s

anar masa ya ce a barta sai ta tashi.

Kaf matasan gidan suka fito daga masallacin, dake kofar gidan jiki a sanyaye.

dan lamarin d'aurin auren ya zo wa kowa a matukar bazata, shi kansa Daddy bai san a take Bappa Salihu zai ce a d'aura ba.

Zaraddin ne yabi

yo Dad d'insa da sauri kamar wani zararre yana cewa

"Yanzu kana ji kayi shiru aka d'aura auren yarinyar da nake so, na rantse bazan yadda ba,

wannan munafurci ne kawai ai an sanni ni nake son ta saboda shi yana da kud'i shine za'a bashi ita, to wlh bazan y

adda ba sai an juya aurennan yadawo kaina."

Dad ya harareshi ya ce "Shashashan banza matsa kabani guri, wanda baisan abin da yake yi ba, anata kokari a kanku bakwa gani,

ina ruwanka idan an bashi ita,

kar ka sake naji wani magana ka yadda ka b'ata min shir

i kagani,

shashasha kawai."

Zaraddin ya tsaya daga hanya, Dad ya shige sashin sa bai fasa surutu ba.

Mom ta ce

"Kai da waye kuma kake fad'a?."

ya ce "Ni da wancan shashashan d'an naki mana, wai dan an d'aura wa Abdulrahim aure da wancan yarinyar da suka so

kashe kansu a kanta, shine yake hauka wai sai an maida auren ya dawo kansa,

jimin shashanci fa auren da babu wanda yasani kamar auren munafurci ana idar da salla Bappa Salihu ya miko goro da minti ya ce a d'aura yanzu."

Mom ta rike baki ta ce

"Feeryal d'i

n aka d'aurawa Abdulrahim aure da ita?."

sai kuma ta shiga tafa hannu tana fad'in

"Tabd'i jam lallai akwai babbar matsala,

yanzu shi Yaya Abubakar d'in har ya lamunce ya d'aurawa d'ansa aure da 'yar da ba'asan asalinta bama,

'yar da aka tsinta cikin ruwa,

yarinya mara daraja ya yadda ya amince ya had'ata aure da mutum kamar Abdulrahim,

ai ko shi Zaraddin d'in da akewa kallon mai rawar kai bazan yadda na lamunce a had'a shi aure da ita ba,

kuma Hajiya Halima tana gidan ta zuba ido akayi wannan aure."

"Can mu

su suje can su karata, ni yanzu hidimar dana sa agabana kad'ai nake kwarara."

Mom ta zauna tana ta jinjina lamarin...

Can bakin masallaci kuwa.

Ajmal yayi kokarin dai-dai nutsuwarsa,

yana ta kokarin yaki da zuciyar sa.

ya iso in da Abdulrahim ke sunkuye g

aban Bappa Salihu da ke zaune kan dakalin masallaci,

yana masa magana kasa-kasa.

murmushi Ajmal ya yi yana fad'in

"Congratulations bro."

Faisal da Shamsuddin ma suka karaso gurin suna fad'in

"Muna tayaka murna Ya Abdulrahim."

bai yi magana ba sai fuska day

a dad'a murtukewa.

Bappa Salihu ya ce "Shiga ciki Abdulrahim Allah dai yamaka albarka yasa 'ya'yanka suyi maka biyayya fiye da yadda kakeyiwa iyayen ka."

ya mike ya nad'e hannunsa a kirji ya soma takawa zuwa ciki.

Daga masallaci in da aka gama d'aurin aur

en, Bappa Salihu ya tafi sashin Hajiya.

ya kai mata goro da minti yakuma shaida mata an d'aura auren Abdulrahim da Feeryal, shi yabada umurnin a d'aura nan take bayan an idar da sallar asuba.

Hajiya dake kan kujera ta zamo kasa tayi zaman dirshem, ta kwala

lo ido tare da buga kirji ta ce

"Auren ka d'aura masa da yarinyar da rabin ta mutum rabin ta aljana, kasan waye wannan yarinyar kuwa,

to wlh ni dai ban amince ba,

ta in da aka hau tanan za'a sauka yadda kuka d'aura haka zaku kunce, dan kunyi aikin banza ne

,

dan billahillazi, abokin turawa bazai zauna da yarinyar nan ba."

Bappa Salihu ya mike yana fad'in

"Idan ke baki aminta ba ni da 'yan'uwa na Jibir da Ali duk mun amince,

kuma mun yanke hukunci akan d'anmu Abubakar da jikan mu Abdulrahim, dan baki fimu kar

fi da iko a kansu ba."

Bappa Salihu ya juya ya fita.

Hajiya da harbakin ta na kumfa ta ke fad'in

"Zancen banza kai wlh bazata sab'u ba, yadda kuka d'aura haka zaku kunce."

Bappa Salihu na fita sashin Mommy ya tafi.

Mommy ta tarbi mahaifin nata, bayan ta c

ika shi da kayan karin kumallo ta zauna suka shiga gaisawa, kasancewar daren jiya da ya iso bata samu sun gaisa ba.

Bappa Salihu bai tab'a komai daga cikin abincin ba.

gani bai ci komai ba Mommy ta ce

"Baba ga abinci fa an kawo maka."

ya ce

"Aa bar wannan

yanzu haka nasan Abubakar ya kai min abinci can d'aki na, idan naje zanci acan."

Mommy ta d'anyi dariyar yake a kasan ranta kuwa haushi ne tam dan tasan abincin daga gun Aunty zai fito.

dan duk iyayen nasu idan suka zo Daddy ke d'awainiya da su da kansa,

daga sashin Aunty kuma yake fita da abincinsu.

tayi kwafa a kasan ranta ita da take 'yar su wai sai wata ce can za'a rika d'aukar abinci daga gurin ta ana kai musu.

ta wani jijjiga kai tana kuma jan kwafa a kasan ranta

Mommy ta d'an muskuta tare da kwakulo

murmushi ta ce

"Baba ko kazo yin wani abu ne, naga baka shigo da wuri ba jiya sai dare,

ko jirgi ne aka rasa sai na dare?."

ya ce

"Tafiyar ce dai da ba'ayi masa shiri ba, shi yasa ban sami jirgi mai tasowa da rana ba,

lokacin da na iso Jos jirgi har ya ta

shi,

na bari sai gari yawaye kuma ina ganin b'ata lokaci ne, shiyasa nabi jirgin da zai taso da daddare,

dan nazo na aiwatar da abin da ya kamata da wuri."

Mommy tayi murmushi ta ce

"Ai kuwa kasha hanya mutan gidan kowa lafiya."

ya ce "Lafiya lau suke."

ya

saka hannu a aljuhu yana cigaba da fad'in

"Yauwa ga goron auren d'anki da aka d'aura d'azu da asuba d'in nan."

wani irin mike wa a haukace Mommy tayi ta buga kirji

"Aure Baba! wai dama abun da ya kawo ka garinnan ke nan? wlh Baba bazai yuwuba yazama dole

a wargaza auren nan!."

Mommy tana maganar a haukace tana jin kamar kanta zai bud'e.

Bappa Salihu ya ce

"Ke Halima zauna wani haukar banza ce wannan,kamar wanda aka fad'a miki mutuwar d'an naki,

abun da Allah ya hukunta kin isa kice ba haka ba, shirmen ban

za kawai."

Mommy ta zauna tana fad'in

"Baba a gaskiya ni ban yadda da wannan auren ba, ni kwata-kwata yarinyar ce bana kaunar ta."

"Au haka ne shine ke kika iya nemo masa mata ya aura, dan mahaifin sa ya bashi zab'in sa, sai ya zamo abin tada hankali,

shi

yasa nace a d'aura auren nan take sabo da irin wannan shiriritar taku,

ke zaki zauna masa da matar,

shi Abdulrahim d'in da akayiwa dirar mikiya cikin rayuwar sa, ba'a jira jin ta bakinsa ba, ba'a jira jin ko da wacce yake so ba, aka zab'ar masa bai yi irin

wannan haukar ba,

to ki maida hankalin ki baki isa ki hana abin da Allah ya hukunta ba."

Mommy da gaba d'aya kwakwalwarta ya cakud'e ta ce

"Baba wannan abun fa makirci ne kawai, duk shirin Hajiya Fatima ce, so take ta juya shi ta juya ubansa,

ban san me

yasa ake son lallai sai ya aure ta ba, in dai auren ake son a kara yi masa a nima masa wata amma ba ita ba."

"Kaji shirmen banza kawai ita mahaifinsa yaso ya aura masa, karki kuskura kice zaki d'agawa mutane hankali kinji nagaya miki,

shirmen banza kawai

shi yasa na d'aura auren d'iyanin sabo da gudun irin wannan shirmen,

zaku hana abin da Allah ya hukunta ne."

Bappa Salihu ya mike yana cigaba da fad'a.

Kuraiba ta fad'o parlour Mommy a hargitse tana fad'in

"Mommy wata magana nake jihaka, wai da gaske Abd

ulrahim aure yayi?

yaushe ne mukayi auren ko shekara bamu rufa ba shine zai kuma aure, wai kuma wannan yarinyar mai kama da aljanun,

Mommy kice min karya ne bama auren ya yi ba bare ace ita yarinyar ce ya aura."

Bappa Salihu ya daka masa tsawa

"Wace irin s

hashanci ne wannan zaki fad'o guri babu sallama, haukar banza kawai shine me idan ya yi aure matan ubansa nawa ne gasu nan kina ganin su rai uku,

kuma har yanzu yana da ikon karo d'aya bare shi mai mata d'aya,

haukar banza kawai."

Bappa Salihu ya fita yan

a cigaba da fad'a.



Bappa Salihu na fita Mommy ta kamo Kuraiba tana fad'in

"Zo nan aikin banza sukayi dan wlh ba abun da zai sa Abdulrahim ya zauna da yarinyar nan,

kwantar da hankalin ki kar ki wani tada hankalin ki ki sawa ranki damuwa,

muga yadda za'a

yi su kai masa ita, yadda aka d'aurashi a titi haka zai watse a titi,

koma b'angaren ki kije ki kwanta ki huta kibarmin komai a hannuna."

"Mommy kin tabbata?."

"Aa ba ni na gaya miki ba ai ni yarinyar ce sam-sam bani kaunar ta, dan me zaisa na zuba ido a h

ad'a ta da d'ana,

kije nagaya miki ke dai."

Kuraiba ta juya ta fita

gefen Abdulrahim ta nufa, tana shiga ta ganshi ya fito cikin shirin tafiya asibiti.

tasha gabansa tana taunar cingam tana yi masa wani kallon sama da kasa sannan ta ce

"Abdulrahim auren mu

baiyi shekara ba aka kuma yi maka aure, baka gaya musu cewa ba wani isasshen lafiya ce gareka ba,

kai kana likita ma baka fahimta ba,

in ba haka ba zuwana gidan nan zan iya kirga sau nawa ka kusanceni, shima sai nayi tattaki nazo gare ka,

saboda ina maka

kallon namiji mai lafiya da bazai iya rike kansa batare da mace kusa da shi ba, baka tab'a yin awa 3 a kaina ba,

a hakanne za'a kuma baka mata, wannan yarinyar da tasan mazama ina zata iya zama da kai."

"Bani hanya na wuce!."

yafad'a cikin tsawa fuska babu

wasa.

duk da rashin mutunci na gaban goshin ta sai da ta girgiza da tsawan daya buga mata.

ta matsa gefe tare da sakin kukan makirci sannan ta rungume shi ta baya tana fad'in

"Ban tab'a ganin haka ba aure bai shekaraba ace za'a kara aure, me kawaye na zas

u d'auke ni, please mijin Kuraiba kace baka son auren nan."

fezge jikin sa ya yi yasa kai yafice a a parlour.

yashiga motarsa yabar gidan.

Umma Karima da labari ya isar mata ta garzaya sashin Mommy a bujajan.

ko zama batayi ba, ta soma fad'in

"Amma kin ba

ni mamaki Hajiya Halima, kina da ranki a cikin gidannan ki zuba ido a aurawa d'anki aure da wannan annobar yarinyar da take son ganin bayan mu,

kuma kina zaune kin rungumi hannu kin yi shiru,

shikenan burin Hajiya Fatima ya cika, ta mallaki mijin ki ta ma

llaki d'anki,

to me yayi saura baki da wani amfani kin zamo 'yar kallo."

Mommy ta ce

"Zauna Hajiya Karima, wlh na rasa yadda zanyi ne sun d'aure ni da jijiyata, Baba ya tsaya tsayin daka cikin lamarin, jira nake ya tafi wlh bazan tab'a zuba ido na bar aure

n nan ya yuwuba tun da aka d'aura wlh sai ya sake ta,

zan nunawa Hajiya Fatima ni na haifi Abdulrahim."

Umma Karima da gaba d'aya hankalin ta ya kai kololuwa wajen tashi ji take tamkar zatayi hauka.

ta zauna tana fad'in

"Uhm yanzu naji batu, idan baki sa a

uren nan ya watse ba, ina mai tabbatar miki ke zaki watse, dan wlh Hajiya Fatima da wannan mayyar aljanar ruwan sai sun kora mu a gidan nan mun zama 'yan kallo daga can bakin get."

Mommy ta buga kirji ta ce

"Ai insha'allahu sai dai su subar gidan nan ba da

i mu ba,

yau Baba zai bar garinnan ai wlh bazan kyale ba bazan tab'a bari d'ana ya zauna da yarinyar nan ba."

Umma Karima ta jijjiga kai tana jan kwafa zuciyarta na wani irin tukuki abin mamaki wai Feeryal ce aka aurawa Abdulrahim.

idan ta tuna haka sai ta

ji tamkar tayi ta kururuwa ko zataji saukin lamarin, bata tab'a sammani ko hasashen hakan zai iya kasancewa ba,

da tuntuni tayiwa tufkar hanci.

ji tayi zaman parlour'n Mommyn yamata kad'an ta koma sashinta tasa direbanta ya kai ta gurin bokanta.

Umma Kari

ma na zube gaban boka Mali tana haki, cikin matukar tashin hankali.

baka Mali nata zane-zane da buga kasansa,

idonsa na kan katon kwaryar tsafin dake gabansa.

ya d'ago yana cewa

"Mun kira su daga shi har ita basu bayyano ba, meke faruwa ne a duk sanda muka

kirasu bama ganin su, duk iya makircinmu mun gaza ganin su da ido,

idan muka gwada wannan sa'ar ta gagara to tabbas sai anyi babban gaggarumin shiri a kan su."

"Boka koma meye a yi kai nifa in da halima a kawar da yarinyar tabar duniya ko zan huta, wlh bo

ka ji nake kamar nayi hauka wannan shegiya tambad'ad'd'iyar yarinyar, bana kaunar bud'e ido na ganta daga ita har uwar goyon nata,

boka dan Allah ka taimaka min kamar yadda kasaba taimako na,

wlh bansan ina zan sa rayuwata ba idan auren nan ya zaunu, duk y

adda za'ayi a wargazara auren asa ya yi mata saki uku basai an kai ga tarewa ba, ka fi kowa sanin matsala ta."

wani kazamin dariya ya sheke da shi.

kana ya d'au wani bakin ruwa ya na zirarawa cikin kwaryar tsafin nan, yana yi yana kiran sunan Feeryal da Ab

dulrahim.

har ya juye ruwan duka.

ya d'ago a daburce yana fad'in

"Basu amsa kiranye ba me suka takaaaa!

dole sai munyi aiki cikin duhu da bakaken aljanu."

Umma Karima ta ce

"To boka ni dai ko ma meye ayi bukatata kada auren nan yayi tasiri ya wargaje cikin

gaggawa."

"Tashi kije cikin duhuwar dare zamu soma aikin ki."

ta mike tana fad'in

"Nagode boka dan Allah a wargaza auren na, wlh ban san ina zan sa rayuwa ta ba idan auren ya zaunu."

A hanyar komawar ta gida Umma Karima sai fifita take da d'ankwalinta, d

uk AC da ke motar ita gumi take.

ta gyara zama tare da jan tsaki gami da kwafa a karo na sau ba adadi, tana fad'in

"Tsintacciya tambad'ad'd'iya da ni Karima kike narantse in zanyi yawo tsirara sai na wargaza auren nan, bake ba zama a matsayin matar Abdulra

him baki isa ki kuma b'ata min shirina a wannan karon ba."

direbanta ya juya ya kalleta yana cewa

"Ayi hakuri dai abi a hankali Hajiya, kar ki kwashi kud'i kiyi ta dankarawa mutumin nan mu tashi a tutar babu."

wani uban harara ta dankara masa tare da jan d

ogon tsaki

"Mtttsss in kud'ina gaba d'aya zai kare wlh sai na hana Feeryal zama da Abdulrahim, yi sauri muje gida da'alla."

Tun a daren ranar Bappa Salihu ya yi shirin tafiya,

Daddy yayi-yayi ya bari ya yi ko da kwana uku ne,

ya ce ina aje kawai a shirya

masa tafiya, da safe zai tafi.

akwai abin da zaije ya yi a gida.

washegari

Daddy Dad da Abbie suka fito rako shi zuwa sashim Hajiya dan yaje ya mata sallama.

a waje suka had'u da Abdulrahim zai shiga gaida Bappa Salihu.

cikin girmamawa duk ya haishe su.

Bappa Salihu ya dafa kafad'arsa tare da bubbugawa ya na fad'in

"Babban mutum Allah ya maka albarka."

"Amin."

ya furta a kan lab'b'ansa idan ba idon ka na kallonsa ba bazaka san ya amsa ba.

ya nad'e hannayensa a kirji suka taka zuwa sashin Hajiya.

Hajiya

ta karkata baki tana fad'in

"Um to Allah ya tsare hanya ina ka d'aura auren ya tamku gudun kada ya warware nan gaba."

Bappa Salihu ya ce

"Idan bazaki fad'i alkhairi ba kiyi shiru, babu ruwan ki kicire hannunki cikin lamarin."

"Na cire hanu na ai na cire ha

nuna kuje ku karata, ni ina ruwa na idan yaso kuje ku aura masa 'yar sarkin aljanu ma ni ina ruwa na."

Bappa Salihu ya ce

"Eh hakan ma yafi ki cire hannun naki, to ni natafi Allah ya sada mu da alkhairi."

Hajiya ta kawar da kai tana fad'in

"Allah ya tsare.

"

Bappa Salihu yayi gaba su Daddy suka bi bayansa.

a waje ya tsaya yayi ta sawa Abdulrahim albarka tare da nasihohi, da ban hakuri kan ya yi hakurin zama da zab'in iyayensa.

har airport Daddy ya rakashi sai da jirgin su ya tashi kafin ya juyo gida...

Momm

y tana ganin dawowar Daddy tasan Bappa Salihu ya tafi.

ta kira Abdulrahim ta ce duk abin da yake yabari ya zo.

yana shirin fita office ya nufo sashin ta.

bedroom d'in ta ya wuce ya sami guri ya zauna saman kujerar da ke d'akin, yana duba agogon dake d'aure

a hannunsa, da alama dai sauri yake.

Mommy dake zaune bakin gado ta gyara zama tana dad'a tamke fuska ta dube shi da kyau sannan ta ce

"Me kake jira da auren yarinyar can da aka kakaba maka,

baka guntule shi haryan zu ba, har kabari ya kwana a kanka."

ta

jefo masa takarda da biro tana cigaba da fad'in

"D'auka yanzu ka rubuta mata saki uku nakaiwa uwar gayyarta da hannuna, na nuna mata na isa da kai."

kallon takarda da biron ya yi kana ya kalli Mommy sannan ya ce

"Mommy lokacin da kika nuna min Kuraiba a ma

tsayin zab'in ki, ban bijere ba nayi miki biyayya,

to dan me zan bijire

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login