Showing 6001 words to 9000 words out of 95068 words
ce
"Baza'a kawo gawar Daddy gidan nan ba kiyi masa addua'r daga nan zai iskeshi."
ya shige motarsa yaja ya bar gidan.
Hajiya ta zube a gurin tacigaba da kururuwa.
Da sauri Aunty ta koma ciki ta sauya mayafi, ta fito ta umurci direban ta, daya ka
i ta asibitin,
hankalin ta bazai kwanta ba sai ta sa Daddy a idon ta, taga halin da yake ciki.
motarta na fita Mommy da Umma Karima suka shiga mota guda suma sukayi asibitin.
Shamsuddin na kokarin a mota, Hajiya takuma fasa kara tana fad'in
"Shamsuddini ka
ini naga gawar Abubakar nafad'a masa wlh na janye duk wani abun da na fad'a, ya yafeni na yafe masa duniya da kiyama."
Shamsuddin ya bud'e mata mota Hajiya ta shiga tana sharb'e hanci kafa ba ko takalmi.
Hankali a matukar tashe Dad da Abbieh da labari ya
iskesu, suka garzaya asibitin dan an ce musu gawarsa yana can.
a kusan tare duk suka iso asibitin.
Hajiya tana fad'uwa ana d'agata tana kururuwa da buga hannaye a cinya tana fad'in
"Abubakar ka tashi kajini wlh in dai akan maganar auren nan ne, wlh na ami
nce har abada, tashi ka karasa abun da ka fara,
Abubakar na yafe maka na yafe maka,
kaiceno ni Hanne nayi sanadin mutuwar d'ana mai tausayi na wayyo Allah ina zan sa rayuwata naji sanyi, Abubakar yatafi ya barni!."
Hajiya ta zube a sakiyan parlour'n asibit
in tana cigaba da ihu da kururuwa gami da fad'e-fad'e.
Ajmal ya dubi Shamsuddin ya ce
"Me yasa ka kawo matar nan nan tazo ta d'agawa mutane hankali kawai."
bai kai ga bashi amsa ba su Abbieh dake cikin d'akin da Daddy yake suka fito da sauri sukayi kan ma
iafiyar tasu,
Abbie ya ruko ta yana fad'in
"Hajiya taso kije ki gani Yaya Abubakar bai mutu ba."
Hajiya ta taso a dibirbirce da sauri ta soma Abbieh dake rike da hannunta tana fad'in
"Allahu Akhbar Abubakar, ina Abubakar d'ina yake? taso kaji wlh na kanye
maganata na yafe maka idan baka d'aura musu auren bama kaje ka d'aura na amince."
tana ganin Daddy na numfashi ta fashe da kuka ta karasa inda yake ta ruko hannunsa tana cigaba da fad'in
"Abubakar bud'e idanunka wlh na janye maganata ta tashi kaje kasa yar
inyar ta tare sashin abokin turawa,
kayafe ni d'ana karka mutu idan ka mutu ina zamu shiga ina wannan tarin iyalen zasu shiga,
tashi ka yafe ni Abubakar."
Daddy da maganganun Hajiya ke yawo cikin kwakwalwatsa yad'an motsa,
allurar bacci na jikin sa idanuns
a a rufe amma sai da ya yi murmushi.
Abdulrahim dake tsaye hannayen sa suna sufe cikin aljanu,
ya tab'e baki tare da zaro d'aya hannunsa dake d'aure da agogo, ya kalla kana ya fubi su Dad ya ce
"A barshi ya yi bacci."
da sauri Abbie ya janyo hannu Hajiya y
a na cewa
"To to Hajiya zo muje waje mu jira."
Hajiya da gaba ki d'aya take a firgice ta ce
"Amma dai zai tashi ko bazai tafi daga baccin nan ba, ku tayani fad'a masa wlh na janye duk wani abun da na fad'a ya tashi ya gafarceni."
"Hajiya bazai mutu ba insh
a'allah Yaya Abubakar zai tashi, muje mu jira a waje."
suna fita ya matso ya d'an duddubashi, kana shima yafita yaja masa kofar.
Inda su Ajmal ke tsaya ya karaso yadan dube shi.
"Kaine ko?."
ya fad'a yana kallon Ajmal.
Ajmal ya ce
"Ai in ba an mata haka b
a bazata bar mutane su huta ba, mata da fitina haka, kullum sai ta d'agawa Daddy hankali."
ya yi kwafa yana taune lips.
"Be careful ana wasa da mutuwa ne."
ya fad'a yana wurga masa kallo mai kama da hararar, yana nade hannun rigarsa.
kwafa Ajmal ya kuma t
are da taune lips gami da girgiza kai.
Nutsuwa da jin dad'i ya ziyarci Aunty sai godiya da tasbihi ta ke wa Allah subhanahu wata'ala.
Mommy ta matso in da Hajiya take tana cewa
"Hajiya cewa fa kikayi kin amince da auren, Hajiya ko kin mance wa aka aura
masa ne."
Hajiya da hankalin ta yafara kwanciya ganin Daddy na da rai bai mutuba ta ce
"Ke da'alla Halima rabani koma wa ya aura masa in dai har bazai mutu ba."
Umma Karima da maganganun Hajiya ya shanye mata ruwan kai,
da sauri ta zame jiki tabar asibitin
, dan tana jin idan tacigaba da zama zuciyarta zata tarwatse a yadda take jin kanta..
Sai daf magriba Daddy ya farka, har yanzu su Aunty basu gusa ba, saima kara tuttud'o wa dangi suke,
sai dai da sun zo za'a dakatar da su awani keb'ab'b'en parlour, dan
ba'a so a dami shi da surutu.
Daddy na farkawa ana sanar da farkawar nasa, Hajiya ta suri kafa tayi room d'in da yake.
Abdulrahim na tsaye yana cire masa ruwan da yaka re yanzu.
Hajiya ta karaso bakin gadon tana cewa
"Abubakar ka tashi? sannu kaji kayi hak
uri ka gafarce ni, in Allah ya yarda bazan sake wata magana ba,
rayuwar ka da lafiyar ka yafi min ko mai, ya jikin naka Abubakar?."
Daddy ya yi murmushin jin dad'i ya ce
"Jiki da sauki sosai Hajiya."
"To madalla zamu tafi gida ba anjima ko."
Daddy ya kalli
Abdulrahim yana cewa
"Zan iya tafiya gida anjima ko?."
"After 7 days kafin mu gani ko zaka iya koma wa a kwanakin."
ya fad'a yana gyara rukon ruwan allurar daya zuko cikin Syringe ya kamo hannunsa yana masa ta cikin cannula.
Daddy ya ce
"Hajiya kinji sai
nayi kwana bakwai kafin a sallame ni na koma gida."
Hajiya ta ce
"To-to ai shike nan in dai zaka sami lafiya ko wata guda ne ai za'a zauna,
kai abokin turawa zai warke dai babu abun da zai same shi ko?."
baki ya tab'e ba tare da ya yi magana ba ya zare sy
ringe'n.
Aunty ta turo kofar da sallah Ajmal da Shamsuddin su na biye da ita.
wani murmushin farin cikin gani Daddy zaune Aunty ta sake.
daga in da Daddy ke zaune shima ya maida mata murmushin.
Mommy ta turo kofa ta shigo tana wani shashshan kamshi tana ci
ka tana batsewa.
Abdulrahim ya dubi Aunty yana cewa
"A sama masa wani abun ya ce yanzu."
kana ya maida dubansa ga Daddy ya ce
"Daddy zaka iya yin sallah bayan ka d'an tab'a wani abin."
kai Daddy ya jinjina, da sauri Aunty ta fita.
Mommy tabi bayanta da har
ara, Aunty ta isa in da ta aje basket d'in abincin data koma ta girka masa, dan tasan dama idan ya farka dole zai bukaci abinci.
ta d'auko ta koma d'akin ta soma had'a masa abunda tasan yafi bukata.
bayan Ajmal ya taimaka masa yaje ya wanko bakinsa ta aje
masa saman gadon ya soma ci.
"Kai dun gidan ku ina tambayar ka yaushe zaiji sauki kayi burus da ni."
Abdulrahim ya tarkasa 'yan kayakin sa yana cewe
"Ki jira lokacin mana."
ya sa kai ya fice.
Daddy ya ce "Hajiya zanji sauki ai in Allah ya yarda."
Hajiya
ta ce "To Allah ya kawo manzon sauki da gaggawa."
Kwanan Daddy uku a asibiti kullum a can su Aunty suke wuni, kwana kuma Ajmal da Shamsuddin ne suke kwana a kanshi.
Umma Karima kam tun da tazo ranar farko bata kara zuwa ba, sai ta fake da wai itama bata
jin dad'i ne.
sai yau Feeryal itama ta sami zuwa duba Daddy, dan kullum in tace zataje ta gaishe shi, Aunty takan ce tabari tukunna.
yau Aunty da kanta tace ta shirya suke.
Feeryal bata sake ba dan su Farida da su Ameerah Nabila Sahla yau duk suna gurin, g
ashi Miemie bata zo ba,
sukayi ta mata habaici tana gefe.
dataga zaman shirun ya dame ta sai ta d'au wayarta tasoma sana'ar ta wato buga game.
magana taji a kanta tayi saurin d'ago wa.
wani saurayi ne yana tsaye a kanta ya kurawa kyakkyawan surar ta ido ya
na fad'in
"Sarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci wannan sura."
"Feeryal zo ki rike min wannan."
ta jiyo maganar Aunty daga bayan su.
ta mike da sauri tana d'agowa suka had'a ido da Abdulrahim.
da sauri ta bi hanyar da Aunty take.
Da daddare kamar ya
dda suka saba, direba ya kwashi su Hajiya da Mommy da wasu daga cikin 'yan gidan.
Aunty ta d'au jakar ta tana kokarin fita taje ta same su su koma gida.
Daddy ya ce
"Fad'imatu yau banda ke a tafiyar ki zauna ki taya ni zama kad'aici na dami na."
"Daddy nag
a gasu Ajmal da Shamsuddin, basu wadatar ba."
"Su ba sa'an hirata bane basusan wace irin hira nafi so ba, ke kad'ai kika sani dan haka ki zauna ko kuma mutafi gidan tare."
"Aa Daddy baka gama warkewa ba, ai da Abdulrahim ya sallame ka, to Daddy Feeryal fa
da wa zataje gida, kasan bazai yuwu ta bisu ba."
Daddy ya ce
"Baga mijin ta ba in zai tafi sai ya d'auki matarsa su koma gida tare."
Daddy na rufa baki Abdulrahim na shigowa yana rataye da jakan kayan system nasa da wasu 'yan tarkacen sa.
ya karaso yana fa
d'in
"Daddy ya jikin akwai wata matsala ne?."
Daddy ya ce
"Babu komai jiki da sauki sosai Abdulrahim zaka iya tafiyarka, amma ka d'auki matarka tana waje ku koma gida tare."
bai yi magana ba ya sa kai yana fad'in
"Sai da safe.........!
Yana fita Dr Imra
n ya taho inda yake.
"AA na kiraka baka d'aga ba ashe kana gurin Daddy."
tafiya ya soma yana dad'in
"Ya akayi?."
Dr Imran ya ce
"Dr Daniel ne ya kirani yace ya kiraka baka d'aga ba."
"Kace masa Daddy na is seriously ill, next week zan shigo."
Dr Imran ya
ce "Okay zan sanarasa."
Nurse Samira ke takowa tana nufo in da suke.
Dr Imran ya ce "Oh yau tana night ashe, anya bazakayi na uku da ita ba kuwa?."
Dr Imran ya yi maganar cikin zolaya.
bai kulashi ba ya ci gaba da tafiyarsa.
Samira ta karaso da sauri tana
narke murya
"Sir the patient of that room his BP is higher."
"Je ka duba shi."
ya ce wa Dr Imran, fuska tad'an kwab'e bata so haka ba ta so a ce shine zaije da kansa dan ta samu damar tsayuwa kusa da shi, ta shaki kamshinsa mai dad'i.
Dr Imran ya yi hanya
r room d'in tabi bayan sa.
Feeryal na zaune ta nad'e hannayen ta cikin mayafin ta, da alama sanyi take ji dan gurin akwai sanyi sosai kanta a sunkuye.
"Let's go."
da sauri ta d'ago jin maganar daf da ita.
shi ta gani yasa kai ya wuce tabi bayansa da kall
o.
sai kuma ta waiga gefe da gefen ta zaton ta da wani yake.
har yafita harabar asibitin bata motsa ba.
yakai 10mit da fita Aunty ta fito, baki ta rike ganin ta zaune, sai mammatse ido take da bacci ke cike tap cikin su.
ta karaso in da take tana fad'in
"Ke Feeryal baku tafi ba ashe ko Abdulrahim d'in bai gama abin da yake bane?."
baki ta turo
"Ammie ni bacci nake ji."
"Daddy ya ce kutafi da Abdulrahim wata kila bai gama abun da yake bane, munyi waya da Ammah'n Miemie tana jiran ki idan kun isa, can zakij
e ki kwana sashin ta."
"Ammie kwana zakiyi a nan?."
"Eh Feeryal sai gobe zan dawo."
Feeryal zata kuma magana Dr Imran daya fito daga duba Patient, ya karaso yana gaida Aunty ta amsa tana tambayar sa.
"Abdulrahim fa ko wani aikin yake?."
ya ce
"AA ya fita f
a bai jima da fita ba bari muga ko ya tafi."
ya leka ta waje ya juyo yana fad'in
"Ga motar sa can bai tafi ba."
Aunty ta ce
"Jiranki yake kije ku tafi taso maza, ga Daddy na kirana bari naje sai da safe ko 'yanmatan Ammie."
Aunty ta juya tana d'aga kiran D
addy da ya shigo wayarta.
"Gani zuwa Daddy."
tayi maganar tana nufar room d'in da yake da sauri.
A hankali tasoma takawa tana wasa da bakin mgyalen ta.
ta sako kafarta a step d'in karshe na sauka daga kofar da zata sadaka da farfajiyar asibitin,
idan kunn
en ta ya jiyar mata dai-dai tabbas taji maganar sa amma batayi zaton da ita yake ba.
yanda ta ke sauka gaba d'aya ilahirin jikin ta motsawa yake, musamman kirjinta da nonuwanta da bata sa musu bra ba suke rawa cikin rigarta.
a hankali take takowa cikin yan
ayin ta mai sanyi.
"Wow kai kaga wata halitta kuwa."
cewar d'ya daga cikin wasu maza uku da ke tsaye a farfajiyar asibitin.
duk suka maida dubansu gare ta kowa na fad'in albarkacin bakin sa.
d'aya daga cikin su ya ce
"Kai gaskiya bari naje na tsala wannan.
"
ya soma takowa gareta ya sha gabanta yana fad'in
"Hi 'yammata ga mota can ko zaki shiga murage miki hanya, kema dubiyan kika zo ne?."
ido ta bisa da shi tare da girgiza kai, ta kauce tabi gefe ta karasa jikin motan.
taja ta tsaya jiki a sanyaye.
yana za
une cikin motan waya a hannunsa yana daddannawa. aje wayar yayi tare da yiwa motar key batare da ya kalli inda take ba ya ce
"You are waisting my time! ."
a hankali ta saka hannu zata bud'e gidan baya, tajisa a rufe ta matso ta bud'e
gaba ta shiga tana r
ufe murfin ya fige motar yayi hon masu gadi suka bud'e masa get ya fita.
a hankali ta gyara zamanta tare da jan numfashi ta sauke.
wani sassanyan kamshi na bugar hancin ta,
a hankali ta juyar da fuskanta ta jikin glass tana kallon gefe.
Sunyi tafiyar da y
akai na 20min babu wanda ya yi tari cikin su.
a sannu bacci ke fizgarta ta d'an lumshe ido bacci nason d'aukarta.
da sauri ta ware idanunta afirgice jin yadda ya taka burgi zaton ta karo sukayi, jikin ta ya kama cirawa, ta d'ago a zabure tana ware ido kan
titi.
ganin ba karo ba ne ta juyo da sauri ta kalle sa.
ganin idanunsa a kanta a hankali ta sunkuyar da kai tana wasa da 'yan yatsunta.
ji tayi ya fisge mayafinta a razane ta waro ido.
tana binsa da kallon tsoro.
ido ya kura mata fuskarsa babu wasa, ya mi
ka hanu ya fisgota ta matso daf da shi.
dibirbircewa tayi nan da nan idanunta suka kawo kwalla.
ya saka hannu saman kafad'arta yad'an ja rigarta. ya tura yatsa yana zaga gurin kamar mai niman wani abu,
da d'an sauri ya ciro hannun sa ya sauke shi kan kirji
nta ta saman rigarta ya laluma shi.
wani irin waro ido tayi jin hannunsa saman nonuwanta, kamar dai yadda yayi a kafad'arta, kamar mai niman wani abu.
sake ta ya yi yana fad'in
"Stupid Be careful!."
saurin matsawa tayi tana binsa da kallon tsoro.
ya bud'e
mota ya fita.
tabi bayansa da kallo wani katon Mll da suke tsaye daf da shi ya shiga.
sai sannan ta sauke numfashi ta kai hannu ta tab'a kafad'ar ta zuwa saman kirjinta,
ko me yake nima oho.
ta kwab'e fuska hawaye na shirin zuba, gaba d'aya a mugun tsorac
e take.
bai wani jima ba ta hango sa ya fito daga ciki yana tahowa hannunsa rike da bakar laida mai girma.
ya karaso ya bud'e gidan baya ya saka laidar ciki, kana ya dawo mazaunin direba ya shiga yaja motar.
kankame jikinta tayi har suka isa gida.
yana gy
ara parking tayi saurin kai hannu zata bud'e gefen da take, taji sa gam.
ta d'an juyo ta dube shi jiki a sanyaye.
hannu ya saka ta baya ya d'auko laidar ya saka mata shi kan cinyar ta, sannan ya bud'e motar.
bin laidar tayi da ido kana ta kai hannu ta bud'
e ta fita rike da laidar.
Miemie dake tsaye tana zaman jiran isowarsu dan Aunty ta kira Ammah ta sanar mata sun taso, ta turo Miemie tazo ta jira isowarta.
Miemie ta nufo ta da sauri tana binta da da dariya, ta karaso ta karb'i laidar hannunta tana fad'in
"Kawo na karb'e ki Aunty Feeryal."
hararar ta Feeryal tayi.
Miemie ta saki dariya tana cewa
"To ya zanyi tun da kin aure min Yaya dole na kiraki Aunty, dama wayon na kiraki Aunty ce yasa kikace sai Yaya na."
baki Feeryal ta bud'e Miemie ta ce
"Karya na fa
d'a ne? muje gashi can tahowa kada ya ce na tsaida mishi mata tana shan wuya."
Feeryal ta kwab'e fuska kamar zatayi kuka.
da sauri ta sa kai dan alla-alla take ta ganta cikin d'aki ko zata ji nutsuwa ya zo mata.
Ammah na parlour tana ganin su ta mike tana
cewa
"Yauwa kun iso Feeryal? to bari naje na kwanta, kuyi bacci da wuri dai kar ku zauna hirar shiririta ku kasa tashi da asuba."
sukace to.
Ammah ta shige d'aki suma suka shige bedroom d'in Miemie.
Feeryal ta zube bakin gado tare da sauke numfashi.
ta za
me gyalen kanta ta jefashi gefe.
Miemie ta zauna gefen ta tare da aje laidar a tsakiyar su, tana fad'in
"Wai tsarabar me aka kawo mana ne, najisa da nauyi da alamar munyi babban kamuwa."
Feeryal batayi magana ba sai zubawa laidar ido da tayi, tunanin abin
da yamata a mota ne yake ta mata yawo cikin kwakwalwa, tsoro mai had'e da fargaba suka sami nasarar lullub'e ta.
ta gaza fahimtar me hakan yake nufi.
Miemie ta soma cicciro kayan da suke cikin laidar.
da mamaki duk suka waro ido kan kayan.
manyan hijabai
ne kala gomo duk a cikin laidodinsu.
sai bra dozin uku mai guda shabibbiyu.
Miemie ta kalli Feeryal Feeryal ta kalleta.
dariya ta kwashe da shi cikin muryar dariya take fad'in
"Yafi so ya ganki cikin hijabi, gaskiyar sa ya yi kishin