Showing 45001 words to 48000 words out of 95068 words

Chapter 16 - FEERYAL BOOK3 COMPLETE

masa ciki, baya tare da itan ma sai an bida da sharri, in dai cikin nasa ne da gaske me yasa ba'a gansa tu

n a nan ba sai da ta sa kafa ta tatafi dadironta tayiyo cikin sannan dan ana so ayi rufa-rufa kada duniya susan halin da ake ciki, ace wai cikin sa ne."

Hajiya ta ce "To nima dai shi ne na gani wanna zance babu lauje cikin nad'i kuwa, amma bari na nimi Abu

bakar dan ni bai zo min da zancen ba har yanzu."

"Hajiya idan kika bari aka karb'i cikin nan, wlh ke ce na gaba da za'a fara kwatancen ki dan ke ce gidan gaba d'aya, gara ki kwab'i zancen tun da wuri, suje can su nimi wan da ya mata ciki badai jikan ki ba.

"

Umma karima tayi ta iza Hajiya tana karawa wuta fetur nan da nan Hajiya ta d'au zugarta har tana fad'in

Ba'a isa a lakawa jikanta d'an shege ba, suje can su karata da tsiyarsu.

sai da taga ta gina Hajiya ta zauna daram kan maganar ta kafin ta koma sashin

ta.

in da ta tadda kanwar tata Siyama hankali duk a jagule, da bakin cikin lamarin.

A b'angaren Daddy ya shigo side d'in Aunty dan ya sanar mata, ya isketa tana waya da su Hajja Umma.

tana ganin shi ta rungume shi tana dariyar farinciki.

Daddy yaja kum

atun ta yana dariya da fad'in

"Um musu an girma za'ayi jika."

dariyar farinciki Aunty ta kuma ta ce

"Jika kafi d'a wuya hausawa sun fad'i gaskiya, ban samu ba gashi d'iyata ta samar mana, Allah ubangiji ya kawo jika lafiya."

"Oh Fad'imatu ba bu kunya ana m

urnar an sami jika."

Daddy ya yi maganar cikin zolaya.

Aunty ta zame jikin ta tana fad'in

"Tare dai muke murnar kai ma ga murnar a fuskar ka."

ya yi murmushi mai nuni da zallar farinci.

D'iyanin Hajiya ta sa aka kira mata Daddy a waya.

yana shigowa tun ka

n ya zauna, ta ke fad'in

"Wai wace magana ce nake ji ne ha, wanna yarinyar tayi ciki ake son d'angwalawa Abokin turawa, to wlh tun wuri ka kwab'i maganar nan, dan basu isa su miko mana d'an da ba namu ba, su nimi uban cikin tun kan dare ya yi musu."

Daddy

ya zauna yana fad'in

"Dama Hajiya ina da shirin zuwa gaya miki,

ai Hajiya bamu isa muce cikin nan ba nashi bane, dan likita ya tabbatar da cikin wata uku da sati biyu ke nan,

kin ga kuma yanzu wata d'aya ne da sati biyu da karewar auren su, sauran watanni

biyun a gidan nan tayi, basai an tsauwala bincike ba ciki ya tabbata nashi ne,

mu dai kawai muyi fatan Allah ya raba lafiya, kar muyi wata maganar da zai zubda mana kima a d'auke mu kananun mutane."

Hajiya tayi shiruuu sannan ta ce

"To me yasa basu fad'a b

a sai yanzu, ni fa kar aje a d'auki d'an wani a bashi, dan irin wad'an nan yayan su ke kashe iyaye ayi ta cewa d'a ya kashe ubansa alhalin dama ba uban sa bane."

"Babu ko mai Hajiya insha'allah hakan ma bazata faruba ciki kam nashi ne."

"Eh ai dama haka za

kace in dai magana akan abun da ya shafi Fatima ce, duk in da aka bi da kai zaka b'ulle."

Daddy dai bai kuma cewa ko mai ba dan yasan yana kuma cewa wani abu Hajiya zata b'alle.

Kuraiba kuwa hauka ne kawai batayi ba, data sami labarin.

ta shiga mota tayi

gidan su,

hankalin mamarta ma ya bala'in tashi, Hajiya Luba ta dubi d'iyar tata ta ce

"Wai ina cikin da kika ce min a kwai? shi wata nawa bai nuno kansa ba."

Kuraiba ta turo baki ta ce

"Ai zuban jini nake kullum dana je naga likita ya ce min wai zuban ji

nin da nake ne yasa cikin yake komawa baya, amma yana nan ina jin motsin shi."

"To tashi maza muje asibiti, na kai musu shaidar kina da ciki, taya zakiyi sake har wata tazo ta riga ki yin ciki,

kullum ina ta zuba idon jin kyakkyawan labari, sai kuma naji

shiru, ai yanzu ya ci a ce cikin nan ya baiyana kansa,

Kuraiba kar kiyi wasa kar ki bari cikin nan ya fita, akwai babbar matsala fa, ta shi maza mu tafi."

"Mom ni gaskiya bazan je wani asibiti ba, ai ba a b'oye bane kowa yasan ina da ciki,

ki kira Mommy ki

ce mata bazan zauna nan gaba akawo d'an shege gidan ace d'an Abdulrahim bane, tama san yadda zatayi tun da wuri."

"Ke dalla tafi can tashi muje na karb'o shaidar cikin ki, ba kiranta a waya zanyi ba, da kaina zanje na tabbatar mata nan gaba bazai yuwu a h

ad'a sunan d'aki da d'an shege a matsayin d'an uwa ba, gara tun wuri ta sani."

ta zari mayafi ta ce

"Muje maza."

da fari Kuraiba taso bijerewa tafi asibin, Hajiya Luba tace fa sai sun tafi.

suna zuwa asibiti,

ana gwada ta aka ce bata da komai.

Hajiya Lub

a dake tsaye cikin d'akin gwajin ta ce

"Sake gwajin nan likita ciki fa a kwai shi tun ba yau ba."

"Hajiya ki kalla scanning dai baya karya, hasali ma mahaifanta bai tab'a d'aukar ciki ba, sannan akwai matsala ma a mahaifar nata, wanda bincike ya nuna yawan

shashayen maganin hana d'aukar ciki barkatai ba'a kan ka'ida ba, shi ya kawo wannan matsalar, da kamar wuya ta iya d'aukar ciki."

Hajiya Luba ta shiga fifita da bakin mayafinta.

Likitan ya sallame su, suna fita Hajiya Luba ta ce

"Amma kin cuceni Kuraiba,

kin ruguza min mafarkin dana jima nake yin sa,

wanda shi yasa nayi ruwa nayi saki wajen ganin kin zamo surukar Hajiya Halima sabo da na nuna mata iyakarta,

naci alwashin sai na mallaki dukiya dan na kuntata mata kamar yadda a duk san da na ganta nake shiga

kunci,

sabo da tana auren mijin daya ninka mazajen mu dukiya shi yasa take fankama a cikin mu kawayenta, tana nuna ita mijinta mai dukiya ne,

shi yasa naci alwashin sai na mallaki dukiyar da take takama da shi, ni zan zamo mai dukiya ba nama son na kasanc

e a karkashi wani,

shi yasa na zab'i had'a ki da d'anta dan na cimma burina, sai gashi kin ruguje min duk wani abin da na dade nake buri."

fuska Kuraiba ta yamutsa ta ce

"Lallai ma Mom wani irin tunani ne wannan da ke, to ni na auri Abdulrahim ne dan shine

irin mijin da nake buri, bawai dan wani dukiya ba, duk da ban samu abun da nayi sammani tare da shi, ban damu ba dan gari da fad'i,

idan kayi ihu wani baiji ba wani zai jika,

ni kam dai nayi gidan mijina, ni nasan yadda zanyi na kwato 'yanci na, Mom ki aj

e wannan tunanin ma."

Hajiya Luba ta bud'e baki da hanci tana kallon d'iyar tata data wuce bakin get ta tari abun hawa ta hau ta tafi...

A cikin gidan gona ya gyara parking, kamar ko da yaushe Jaq da Tag suka iso gurin shi, bayan sun bud'e masa mota ya

yo gaba suka biyo bayan shi.

suna shiga ciki yaja kujera ya zauna ya ce

"Ku fito da shi."

da sauri suka bud'e d'akin da Zaraddin ya ke ciki.

da sauri ya kare fuskarsa da tafin hannunsa, sakamakon hanken da ya zoyarcin cikin d'akin, wan da ya ke duhu babu

ko kyallin haske, yana kwance a kasan turb'aya babu riga a jikin sa sa, sai gajeren wando kad'ai.

"Kai taso muje."

Tag ya fad'a yana janyo shi daga kwancen, ya mike tsaye ya tura shi waje.

suna isa gaban sa ya durkusar da shi kasa ya zube gaban sa.

ya mika

hannu yana fad'in

"Miko min bulala."

da sauri Zaraddin ya mike yasa gwuiwowin sa a kasa yana fad'in

"Dan Allah Ya Abdulrahim kayi hakuri Wallahi na shiryu kar ka duke ni yau, d'azu ma sai da suke ni, kuma duk ayyuka na na gama akan lokaci,

ka tambaye su k

o minti 20 banyi ba na share gidan gonan nan tas na nome in da ciyawa suka fito,

na canza ruwan kifi na wanke dem, na kwashe kashin kaji na zuba musu abinci da ruwa da magani, na share kashen shanu da raguna na zuba musu

abinci da ruwan sha, zabbi da d'awe

su da jimina Wallahi suma sai da na share gefen su na zuba musu abinci, kuma gasu nan ka tambaye su, kuma ka tambaye sauran ma'aikatan ma, daga nan kuma malam yazo ya koya min karatu, muna gamawa aka mai da ni d'akin nan ko minti 30 banyi da komawa ba yanz

u haka."

ido ya zuba masa fuskarsa a mirtuke.

Zaraddin ya juyo ya kalli su Jaq yana cewa

"Ku gaya masa da gaske duk abun da na lissafa nayi, dan Allah Ya Abdulrahim ka taimaka ka mai dani gida, na rantse maka bazan sake aikata ko mai ba wlh na daina,

Wall

ahi tallahi ka tambaye su gaba d'aya na gama shiryuwa, ni nake fara fad'a musu lokacin sallah ya yi, ka tambaye su kafin su tashi suyi sallah na riga su,

ni nake buga kofar nan idan naji malam ya tada sallah sai su zo su bud'e min,

lokaci biyar akan lokaci

baya wuce ni, ka taimaka ka mai da ni gida idan na sake aikata wani abun na yarda ka yi min hukuncin da yafi wannan, ni da shaye-shaye da 'yammata munyi hanun riga, har da abokan banzan ma har abada bazan sake ba, wlh na dai na kayi hakuri."

"Kira min mal

am."

Abdulrahim ya fad'a yana duban Tag.

da sauri Tag ya fita ya nufi gefen da sauran ma'aikatan gonar suke, batare da b'ata lokaci ba suka dawo da wani dattijo.

malamin ya mikawa masa hannu suka gaisa kana ya dubi malamin yana cewa

"Ya kai izu nawa yanzu

."

da sauri Zaraddin ya ce

"Wallahi nafi ashirin saura kad'an na haura izu talatin."

"Ban tambaye ka ba."

ya fad'a fuska ba wasa.

Zaraddin

yayi saurin kunshe bakinsa yana tsilli-tsilli da ido, ya kwantar da kai kamar maraya.

malamin ya ce

"Eh yana daf da k

aiwa izu talatin, kuma yana ganewa sosai yanzu."

kai ya jinjina sannan ya ce wa malamin

"Zaka iya tafiya."

malamin na tafiya ya mai da dubansa ga Zaraddin ya ce

"Idan ka kai izu sittin ka shirya zaka ko ma gida."

yana gama fad'in haka ya jefar da bulalan h

annunaa ya mike ya fita.

Zaraddin kamar ya fasa ihu yana ji yana gani suka jashi suka maida shi d'akin duhu suka kulle shi......!

"Feeryal yi sauri ki fito ki shirya mana mu tafi, sai juya jiki kike duba kiga 11 har ta gota, sai azahar kike so mu tafi."

cewar Hajja Umma data ke ciro mata kayan da zata saka, su tafi asibiti don yin awu.

Feeryal ta fito daga bathroom d'aure da towel, tana gyara zaman towel d'in da yaso kasa mata sakamakon cikin ta daya tosa, watannin cikin biyar ke nan.

Hajja Umma ta ciro

mata doguwar riga tana d'ago rigar, magani ya zube kasa.

Hajja Umma ta aje rigar bakin gado ta sunkuya ta tattaro maganin tana fad'in

"Me kuma ya kawo magani nan."

ta kwaso magungunan tana kallon su

"Wannan ai maganin da masu ciki suke sha ne,

wannan ne

ma ban san amfanin sa ba, Feeryal maganin ne bakya sha kike tarasu anan, ko ba su bane?."

Feeryal ta zauna kan kujerar Morro tana fad'in

"Ina sha fa Hajja Umma ba ke kike bani na sha ba."

"To ai shine nima nagani to ya akayi wad'an nan suka zo nan."

mai ta

d'auka ta soma shafawa tana cewa

"Wannan maganin fa Sahab ne ya bani ranar daya dawo da ni d'in nan, wai narika sha kullum ni kuma nasan lafiya ta kalau shine na ajiye."

Hajja Umma tayi shiru a ranta take fad'in

"Yama san da cikin, kafin mu mu sani ke nan

ma."

a fili kuwa cewa tayi

"To yi sauri ki shirya, mu tafi bari na zo."

tayi waje...

Lagos...

"Boka wai har sai yaushe bakin aljanin nan zai isa inda take ne,

dan Allah boka kayi duk yadda zakayi ka katura akashe abun da ke cikin ta lokaci nata tafi,

a lissafi na yanzu watannin cikinnan biyar ke nan, saura wata hud'u ya zo duniya, boka idan yazo kwai matsala fa a kashe shi tun kafin yazo, sannan a shirya auren Siyama da shi."

Boka Mali ya d'ago daga bugo kasan da yake ya ce

"Ai kin ki bazai karasa ciwu

wa ba har sai kin karasa jefa cikon na uku cikin kaskon can, ki tashi kije ki nemo cikon aikin ki,

ki tabbatar da biyu ne cikin sa ba d'aya ba, dan a wannan karon idan kika kuma kuskure to aikin ki ya rushe duka,

bazai tab'a gyaruwa ba, kin kuma tabba babb

an kuskure zaki fuskanci kalubale, mai girma."

kirji ta dafe ta ce

"Boka yanzu a ina zan samu kasan irin kasadar da nayi a wancan lokacin kafin na samo,

na karshen dana zo da shi sai da na narka kud'i kafin na samo, cutana yayi ce min yayi biyu ne a ciki,

amma Boka babu yadda za'ayi aljanu su samo min, ni ko mawa ne zan iya badawa in har zan sami biyan bukata."

Boka Mali ya kece da kazamin dariya yana cewa

"Babu halin yin haka in har kina son cimma burin ki to dole ke zaki samo da kanki."

shiru tayi sannan

ta gyara zama ta ce

"Boka zan samo kota halin yaya."

"Tashi kije ki taho da shi aikin ki ya gamu daga ranar duniyar ki tana hannunki."

Umma karima ta mike da sauri zuciyar ta abushe ta dasawa ranta ko ta halin yaya zata samo.

Yau Farida sanmakon zuwa A

A FIYA STREET tayi kamar yadda halinta yake bata zuwa sashin kowa daga na Daddy sai na uwar ta da kakarta.

daga sashin Daddy ta tafi side d'in Hajiya.

tana zaune suna hira da Hajiya, 'yarta data yaye ta da d'an jimawa nata tsalle-tsalle cikin parlour'n.

Ha

jiya tabi yarinyar da kallo tana fad'in

"Har yanzu uwarki ta kasa yin ciki ta kuma haihuwa kun zauna irin abun 'ya'yan zamani, wai baza'ayi ciki ba sai yaro ya shekara biyar."

Farida ta ce

"Wai Hajiya yanzu an karb'i cikin aljanar yarinyar nan a matsayin n

a Ya Abdulrahim ke nan?

taya ma hakan zata yuwu a ce mu had'a jini da kaskantacciyar da ba'a san daga ina ta fito ba, ba'a san su saye dan gin ta ba, ta yuwuma 'yar wani kaskantacce talaka ne, taya za'ayi mu had'a jini da ita, wlh idan ta haihu ma ba'a isa

a danganta mu da d'an da ta haifa ba,

dan cikin nan na tabbata bana Ya Abdulrahim bane."

Hajiya ta ce

"Um ni ma dai haka nagani, Abubakar ya tattare maganar ya hana yin sa, ba muna nan ba zamuga yadda d'an zai fito idan baiyi kama da Abokin turawa ba, to

bazai karb'e shi a d'a ba, suje can su nima masa uba."

"Hajiya maganar kama ma bata taso ba, kawai ciki ba nashi bane dan wlh baza a kawo mana shege cikin gida ba."

Farida ta had'eye ragowar maganar nata sakamakon shigowar da yayi parlour'n.

Wani kallo y

a wurga mata ta shiga taitayin ta.

ta mike da sauri tana gaishe shi bai amsa ba ya zauna.

ita ko ta ja 'yarta da sauri sukayi waje.

Hajiya ta dube shi tana cewa

"Abokin tuwa an shigo, dama ina ni man ka, cikin nan fa ni ina ganin ba naka bane,

kawai so ak

e ayi ma rufa-rufa a baka cikin da ba naka ba."

"Ni zan fad'i hakan ba ku ba."

ya yi maganar yana murtuke fuska.

da sauri Hajiya ta ce

"Yauwa ba naka bane ai dama nasan za'a rina, su rike kayan su a can, bari ma na kira Abubakar ya kira su tun da wuri, baz

amu karb'i cikin ba gara tun da wuri su sani, tun kafin ta haihu."

Fuska ya dad'a sukewa ya ce

"Cikina ne mana ba ku kukaje kukayi jinyarta a daren mu na farko ba."

"To fisararre zama da wancan shegiyar aljanar yarinyar ya saka zama mara kunya, sau nawa a

ke kamata da maza a cikin gidan nan Karima tasha zuwa ta fad'a min."

ya dago ya dube ta sannan ya ce

"Yanzu idan aka ta da ke kina da hujjar da zaki kawo akan ta tab'a zina."

Hajiya ta ce

"Zancen banza yarinyar da a cikin gidan nan ta kawo wani, ga shaida

an ganta da ido."

"Ni ne shaidar da yakamata a ji daga baki na, ba kurika yanke hukunci kaitsaye ba, Beauty bata tab'a sanin wani namiji ba, ni na fara sanin ta mace,

kada wani ya sake sheganta min d'a idan kuma ba haka ba zan d'auki mataki a kan kowa!."

yana gama fad'in haka ya mike yanufi kofar fita.

Hajiya ta saki uban salati

"Laha'ilaha'illallah Abokin turawa, Eh ba shakka anyi ma turen aljanu, dole na sa a nemo mai rokiyya."

Goggo Bishira data fito daga d'aki ta sinkayo zancen a sama ta saki murmushi

tana karasowa cikin parlour'n.

"Zo Bishira kirawo min Abubakar ina ga fa yaron nan ya sami matsala, Eh an masa turen aljanu."

Goggo Bishira ta zauna tana cigaba da murmushi ta ce

"Hajiya wani turen aljanu gaskiya ya fad'a, duk da shiru irin nasa sai da ak

a sa shi ya maganu, tabbas shine babban shaidar matarsa gaskiya ya fad'a, a budurwa ya sami matarsa dan haka babu wata hujjar da za'a ce ciki ba nashi bane, kuma dai na wannan maganar, yafi kowa sanin cikin nashi ne ko akasin haka."

"To ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login