Showing 15001 words to 18000 words out of 95068 words

Chapter 6 - FEERYAL BOOK3 COMPLETE

da kayan yaji d'an dai-dai ta sulala mai dai-dai kima, ta rufe ta rage wuta.

ta fere dankali ta zuba mai a wuta tasoma suya.

tana gamawa ta fasa kwai da kayan Spices da sokar kifi,ta soya.

a gefe guda

kuwa ta wanke hanta ta zuba a tukunya ta d'aura a wuta, batare da ta tafasa shi ba,

ta sulala masa mai ta zuba masa kayan kamshi da nikakken kayan miya, gami da kayan d'and'ano.

tarika d'an jujjuyashi har sai da ya soyu shi da kayan miyar, suya mai kyau k

ana tad'an zuba masa ruwan zafi yasake jikin sa, ta barshi ya turara kad'an sannan ta sauke.

nan da nan sashin nata ya kaure da dadad'an kamshin girkin.

a gefe guda kuwa ta d'aura Sudan tea a wuta.

karfe 11 da rabi ta kammala komai ta kwasa ta shirya su a

kan dinning.

kana ta dawo ta tsaftace kitchen d'in.

ta kunna masa turare sannan ta koma d'aki.

tayi wanka ta shirya cikin riga da wando Arabian dress rigar mai fad'i tsawon sa ya wuce guiwarta, wandon ma daga kasa tana da fad'i.

tayi rolling na gyalen kay

an tafito tamkar balarabiyar asali.

wani irin dad'i kuma sassanyar kamshi ne ke tashi a jikin ta.

Daga cikin parlour tajiyo muryar Miemie tana fad'in.

"Wow wani irin kamshi ne haka Restaurant aka bud'e a gidan ne."

da sauri tayi parlour tana fad'in.

"Oyoy

o Miemie."

Miemie na ganin ta taware ido da baki tana kallon ta kamar wata sabuwa ce a gaban ta ba Feeryal d'in ba.

baki Feeryal ta turo ta kwab'e fuska

"Ina miki oyoyo ma kin yi banza da ni."

Miemie takuma waro ido tana cewa

"Ke kin ganki kuwa wlh auren

nan kyau yake dad'a kara miki, sai da nayi da gaske na gane ke d'in ce na zata wata balarabiyar ce."

murmushi Feeryal tayi tace

"Ke ko Miemie hmm, yau dai kin zo mu kwana ko."

"Ke rufamin asiri yanzun ma sai da na tabbatar na tambayi security suka ce min

bai jima da fita ba, kafin na zo,

wai wata mai aikin kika samu ne take miki girki a kitchen."

"Laa fa na sa turare, kuma kitchen d'in a kulle nayi aikin."

"Wai kina nufin ke kikayi girkin, duk wannan d'in kamshin girkin ki ne?."

cewar Miemie tana rike hab'

a.

cikin muryar dariya ta ce

"Eh mana."

Miemie ta ce

"Allah kamar ban yarda ba bari dai na gani da ido na babu kowa a kitchen d'in."

ta rafi ta leka kitchen ta juya tayi kan dinning tana fad'in

"Kuma fa ba kowa."

ita dai dariya ta bita da shi.

Miemie na bu

d'e kuloli da kwanukan dake jere kan dinning d'in tawani ja numfashi tare da shakar kamshin girkin.

tayi mamakin ganin had'ad'd'un girki irin haka duk da tasan rainon Aunty ce ita.

Feeryal ta karo dinning d'in tana cigaba da mata dariya.

ta ce

"Zo muje muc

i gashi can nakai wani bedroom."

"Au wannan d'in duk na babban yaya ne?."

juyawa Feeryal tayi batayi magana ba.

Miemie ta biyota tana cigaba da fad'in

"Ah to gara dai da kika fara ankare wa, kika tuna da Ya Abdulrahim baya cin abincin masu aiki, dama naji

Ammah tana cewa Aunty ta ce mata baza a baki mai aiki ko d'aya ba sabo da Ya Abdulrahim baya so, kuma dama itama Aunty'n kin gani ba son mai aiki take ba,

amma naga wannan matar tasa Kuraiba kullum sai masu aiki har rai uku sun shigo mata,

kuma fa ranar in

a sashin Mommy, ta kai karansa wai ya mareta akan ta kira masu aiki side d'in nan, wai karo na biyu ke nan yake marinta akan su,

kuma bata fasa ba dake 'yar jaraba ce ita, Allah yasa watarana ya ba'alla 'yar banza,

ko da shike Mommy'n ce ta mara mata baya,

wai bata saba aiki ba dan haka dole masu aiki su mata;

karkiga kallon wulakancin da take min dataga zan shigo nan,

can farfajiyar side d'in nan na ganta da wata kawarta tazo a mota,

ko ta d'auka idonuwa na suna haila ne tuni na maidawa shegiya."

Feeryal t

arike hab'a tana zama kasan carpet.

"Miemie to ke ina ruwanki da ita."

"Meye ruwana dama da ita,

ita tafara min kallon banza nima na maida mata,

kin san dai bana barin bashi a take nake ramawa, dan ni ba ke bace."

kai ta girgiza ta ce

"Zauna muci dai."

Mi

emie ta zauna tana ci tana santi, ita dai Feeryal cake da yogurt ta matso da shi gaban ta.

A can gefen Kuraiba kuwa, suna gado da kawarta data kawo mata ziyara. sun kulle kofa a kansu, sunyi zigidir a kan gado suna aikata tsiyarsu.

sai tashin muryoyin su

kake ji.

sai da suka gama tsotsar junan su da kwakular junansu, sukayi shame-shame.

Kawar tata mai suna Numsy ta shafo kirjinta tana fad'in

"Kai gaskiya Bestie kin tara ruwa da yawa, kamar baki da mai zubar miki."

fuska Kuraiba ta yamitsa ta ce

"Um wannan

da shi da babu ai duk d'aya, ni ina tunanin mafa kamar bashi da cikakken lafiya, bai damu da mace ba da nad'auka ko ni ce yake min haka, amma kinga yau kwana 8 da kawo masa wata kullum ina sa ido ko sau d'aya ban tab'a ganin yaje gurin ta ko tazo bedroom d

'in sa ba,

yakan je na gansa da abinci sabo da uwar goyon ta tana girko abinci ta kawo mata, shi baya cin abincin masu aiki, baya fin 10min zakiga ya fito,

kinga kuwa babu abun da yake faruwa,

shifa ko jikin sa naje ina romance d'in sa yadda kisan baya jin

komai, kiga yayi ta ture ni,

kuma kar kiga tarin kayan aikin sa wannan in da mai lafiya ne shiru zaku jini,

dan wlh ba karamin zuma yake da shi ba, idan yad'an latsa min karkiga yadda nake ji kamar kar ya daina,

kin san har yanzu ban koshi ba, sex nake bu

kata irin zazzafar nan,

nakira BB naso mu had'u jiya yake ce min wai baya kasar."

Numsy ta ce "BB baya kasar, amma Shamo nanan ai."

tsaki taja "BB ya fi Shamo kayan aiki, zan dai jira shi ya dawo, kici gaba da had'uwa kawai, kafin ya dawo."

Numsy ta mike

ta soma saka kayan ta tana fad'in

"Lallai kina hanu da yawa, gobe mu had'u a hotel, dan naga gidan nan naku akwai matakan tsaro da yawa."

Kuraiba itama ta mike ta saka kayanta ta rako kawar tata, ta shige motar ta ta tafi.

A b'angen su Feeryal kuwa bayan

sun gama cin abinci, hira suka soma, wanda rabin hirar Miemie ce ke yi, Feeryal na binta da dariya gami da murmushi.

agogo Miemie ta kalla ta ce

"Azahar ta kusa bari na tafi kar Ammah ta neme ni."

Feeryal ta marairai ce fuska.

"Ayya Miemie ki ce mata kina

nan, ki zauna dan Allah kibari sai anjima."

Miemie ta mike tana cewa

"Yanzu haka nasan Ya Faisal ya na nan yana jirata, kayan gugonsa da aka kawo ba'a same shi ba, ni na karb'a,

kin san shi yanzu sai muje muyi fad'a."

Feeryal ta bi bayan ta suka fito har f

arfajiyar side d'in.

gani tana kokarin biyota har wajen gidan.

ta ce "Feeryal tsaya daga nan babu ruwana kar Ya Abdulrahim ya ce nafito masa da mata."

fuska takuma marairaicewa

"Ayya Allah so nake naje naga Ammie na amma ina zuwa zatace na koma."

takarasa

maganar kamar zatayi kuka.

Miemie zatayi magana mai gadin side d'in ya wangale get.

Abdulrahim yasako hancin motarsa ciki.

cikin Miemie ne ya d'ura ruwa.

ta dafe kirji da fad'in

"Nashiga uku."

ya karasa parking lot ya gyara parking.

Miemie ta dubi Feerya

l a tsorace ta ce

"Ki koma nikam na tafi."

tana kokarin isa get ya bud'e mota yafito.

dole ta tsaya ya fito a parking lot.

kame-kame Miemie ta soma sai kuma ta ce "Ina kwana Ya Abdulrahim."

kamar bazai amsa ba, cikin ta yakuma d'ura ruwa ganin kallon da y

a mata.

sai kuma ya amsa da

"Lafiya." a takaice.

ai da sauri tasa kai jin bai kuma yin magana ba, tayi waje da sauri har tana cin tuntub'e.

Feeryal daga inda take tsaye ta saki murmushi ganin yadda tayi tuntub'e kamar zata kife kasa.

tayi saurin janyo g

yalenta daya zame yana kokarin zamowa kan kafad'arta, gashi babu d'ankwali ko hula a kanta.

da d'an sauri ta gyara zaman gyalen, tana d'agowa ya wurga mata wani irin kallo, tayi saurin juyawa tanufi ciki......!

Tana shiga ciki tawuce bedroom.

in da ta t

adda kawayen ta suna jiran ta...

Karfe 2 tafito bayan tayi sallar azahar tayi sallama da su Chuchu.

kitchen ta nufa ta soma shirin d'aura girki.

ba wani abu mai wuya ta girka ba kuskus da miyar hanta da kwai tayi ta zuba masa yankakken kayan lambu irin su

Carrots da pis.

tana kammalawa ta zubashi cikin kyakkyawan kula mai matukar kyau da tsada wanda ta ciro daga cikin kwalinsa.

ta jera kulolin kan wani tray na musamman.

har zata d'au tray'n ta fito ta tuna da Ammie'n ta bata girki batare da ta had'a da abin

sha ba.

cikin mintuna kalilan ta had'a lafiyayyen lemun abarba da apple, ta juye cikin had'ad'd'en cup ta jefa kankara, ta d'aura kan tray'n ta d'auko tafito.

ta kaishi dinning.

tayi mamakin ganin an d'ibi girkin da tayi d'azu komai sai da aka d'iba aka b

ar saura,

flask d'in Sudan tea d'in kamma baya gurin.

batayi zaton zai zo ya d'iba ko zai san ita tayi ba Aunty ba...

ta d'au kwanukan safen ta kaisu kitchen ta wanke, ta gyara kitchen d'in tafito.

ta koma d'aki tayi wanka ta kwanta.

bata farkaba sai bayan

la'asar.

yamma lis ta koma kitchen karfe 7 da 'yan mintuna tagama girkin dare, ta kwasa ta kaisa dinning.

sannan ta koma ciki, sai da tayi sallar isha kafin ta shiga wanka...

"Deen kabar kanka ya huta mana, 8 days kana narkawa kanka kwayoyi da barasa,

t

un da anfi karfinka bakasamu lu'ulu'un nan ba, ka hakura mana, ka fantama cikin gari da wajen kasarnan zaka sami kamar ta ko wacce ta fita ma,

mttss naso ace kai ka auri yarinyar nan ka bani aron ta na more kayan alatu,

amma brother naku ya yi tsawon kafa

ya yi gola ya tsare,

wannan ba karamin kaya yake d'iba ba."

Zaraddin ya janyo kwalbar giya, ya kafa a bakin sa sai da ya sha rabi kafin ya d'aga kwalbar ya yi wurgi da shi sakiyar parlour'n Ziyad kwalbar ta tarwatse.

ya shiga dukan table d'in gabansu yana

fad'in

"Bazan bar masa ita ba! dole ya sake ta na aure ta!."

ya mike zumbur yana cigaba da fad'in

"Abdulrahim dole naji abin da kake ji a jikinta, yazama dole kuma kasake ta na aure ta."

ya d'aga kafa yana kokarin fita Ziyad ya taro sa yana cewa

"Deen me

zakayi kabi ko mai a hankali fa, dan wannan Dr d'an zafin kai ne kar aje a sami matsala."

cikin hargagi da ihu ya ce

"Yau nine zan kwana da ita ba shi ba, daga nan zuwa gobe kuma idan bai saketa ba, sai na kashe shi na aure ta."

da sauri Ziyad ya rike hann

unsa ya ce

"Deen ka dakata, kajira ka sauka a network kayi tunanin hanyar da zakabi wajen d'aukar wannan mataki, kaga yanzu a shaye kake, wannan lamari ba irin sauran da muka saba tinkara bane, katsaya kwakwalwar ka tagama caji, nima ina goyon bayan yasake

ta mu samu, idan kuma ba haka ba mu sace ta."

hannunsa ya fizge yajuya da karfi yayi waje yana fad'in,

"Bazan bari sai gobe ba yau zan aiwatar da komai." yashiga motarsa da gudu yabar gidan, ya nufi AA FIYA STREET.

Ana idar da sallar isha yana isowa gidan

a babban parking lot yayi parking.

ya zauna cikin motar bai fito ba, idanunsa a hanyanyar wucewa yana kallon matasan gidan da suka fito daga masallaci suka wuce side d'in su.

yakai minti 10 a zaune kafin yaga shigowar Abdulrahim.

sai da yakusa da side d'i

n sa kafin yafito a motar

a hankali yake tafiya yana d'an waige-waige, yana ganin shigewar sa dide d'in ya d'aga kafa da sauri.

yana isa bakin get d'in side d'in.

yatura karamar kofa,

mai gadi nazaune ya yi saurin mikewa, ganin d'an gida ne sai ya koma ya

zauna, dan zaton shi tare suke da Abdulrahim d'in ganin yanzu shigowarsa.

ya ce

"Yallab'oi ya wuce gefen sa."

kai Zaraddin ya jinjina kana

yasa kai yanufi gefen Feeryal yana d'an waige-waige.

sai da ya iso bakin kofar gefen nata yaja ya tsaya.

yakuma wai

gawa, yaga mai gadi ma sha'anin sa yake, hankalin sa nata wani gurin.

ya kai hannu kan handle duk da bai sammace kofar a bud'e take ba, sai ko yajita a bud'e.

ai ko da sauri ya murd'a handle d'in yasa kai cikin hanzari ya shige.

yana shiga ya maida kofar y

a rufe tare da murza key.

tsayuwa ya yi yana kalle-kalle, sai kuma da dauri ya nufi cikin parlour'n, yabud'e kofofin bedroom's guda biyu bai ganta ciki ba, ya juya da sauri ya nufi kofar da take ciki.

Tana tsaye gaban wardrobe fitowarta daga wanka ke nan

.

towel ne kad'ai d'aure a kirjin ta, babu ko d'ankwali a kanta.

da sauri ta waiga a kuma razane jin an bud'o kofar da karfi.

ganin wanda ya shigo d'akin da yanayin yadda ya fad'o d'akin nata, tashiga mamaki kwarai da gaske.

murmushin karfin hali ta sake,

da sauri ta mika hannu tana kokarin janyo hijabi, tare da fad'in

"Ya Zaraddin kai ne inayini."

wani irin mayataccen kallo yake binta da shi yasoma takowa yana fad'in

"No no no! basai kinyi wahalar rufa wannan kyakkyawar jikin ba, yau kwana zanyi ina kallon

sa."

a razane ta dube shi, ganin yana dumfarota gadan-gadan, tashiga ja da baya tana cewa

"Me kake fad'a ne Ya Zaraddin?."

bata kai ga rufa baki ba taji ya damko hannunta, wani irin sauti yaja

"Ahhh hannu kawai da irin wannan laushin, ina kuma dana lume

cikin wannan kyakkyawa had'add'en jikin, baki gane yaren ba ne, shi wancan da kike kwana da shi bafa wani abu yafini ba,

yau zaki gane ni jarumi ne sai kin raina jarumtar sa."

wani irin bala'in tsoro ne ya kamata, da iya karfinta tayi kokarin kwatar hannun

ta.

sai ji tayi ya rungumo ta.

kara mai karfi ta sake

a take wutan side d'in ya d'auke gaba d'aya.

tsaoro mai tsananin ya kuma lullub'e ta, tashiga ihu da musu-musun kwatar kanta.

Da karfi aka banko kofar ji kake kyass! karan yanka wani irin gigitaccen ka

ra Zaraddin ya sake ba shiri ya sake ta.

tayi baya a tsorace, duk da bata ganin abun da yake faruwa d'akin duhu sai hasken screen d'in waya da mai ita ya shigo, wanda bazata ce ko waye ba, tsoron da ya shige ta yanzu ya girmi na farko.

jin ta shige lungun

wardrobe tadad'a makalewa tana b'ari.

Wani irin duka yashiga yiwa Zaraddin kamar zai rabashi da ransa.

tun yana ihu har ya dawo yin wani irin gurnani.

Feeryal ta kankame idanunta gam-gam a cikin duhu jikinta na kakkarwa, tana kuka da kiran sunan Ammie'n

ta.

Janyo sa ya yi yafita da shi a d'akin, bai fasa bugun sa ba har ya fita da shi, daga gefen nata gaba d'aya.

ya yi parking lot da shi ya bud'e bot ya turashi ciki sannan ya rufe.

yajuyo yana huci, mai gadi ya karaso gurin da 'yar tocilan sa da sauri ya

na fad'in

"Yallab'oi haka kawai wutan ta d'auke, nayi iya kokarin gyarawa yaki."

baiyi magana ba ya soma tafiya, ya shige gefen sa yana shiga wutar ta kawo.

Wuta na kawo wa Feeryal ta kuma wani irin zamura ta mike, jiki na rawa.

a matukar razane takuma yi

n baya ta garu da jikin garu, jiki na kyarma.

ganin jini malale a kasan d'akin, ga kuma wuka a gefe.

takai hannu da karfi ta toshe bakin ta, nan da nan taji kanta na juya mata, a hankali ta sulale kasa, bata kuma sanin abunda yake faruwa ba...

Da sauri ya

fito ga yadda yake taka kasa zaka fahimci tsagwaran b'acin rai tare da shi.

ya isa parking lot ya yi wa motar key, da sauri mai gadi ya bud'e masa get yafita.

tun kafin ya kara babban get yake hon,

a guje security suka wangale masa get, ya fice da mugun g

udu.

Can gidan gona ya nufa yana isa ya bud'e yafito, yazo ta bayan bot ya bud'e ya janyo shi ya fado kasa.

ihun wahala yayi can kasan wuya, ko kansa baya iya d'agawa, sai juya fuskarsa yake akasa.

su Jaq da Tag suka karaso da sauri suka ciccib'eshi suka

shi ga da shi ciki.

suna shiga suka sake shi kasa.

Abdulrahim ya sunkuya a gabansa fuska a shinfid'e da tsagwaran b'acin rai.

hannu ya mika musu tare da fad'in

"Kawo kayan d'inki."

da sauri Jaq ya je ya had'o kayan aiki ya miko masa.

wasu lafiyayyun maru

ka biyu ya d'auke sa da shi,

cikin kakkausan murya mai nuni da zallan b'acin rai, ya ce

"Zan jinyataka kafin nayi maka hukunci dai-dai da laifin da ka aikata!

kar ka d'auki wannan a matsayin hukinci zanyi ma hukunci bayan ka warke."

ya mirgina sa ta baya

yankan da ya yi masa a baya sai fidda jini yake, yankan ya shiga kuma ya yi girma.

yasa hannu yakara yaga rigarsa ya masa allurar tsaida jini, dan tun a gida jinin yake zuba har kuma yanzu.

nan ya soma kokarin dinke gurin daya yanka shi.

Zaraddin sai juya

kai yake ba bakin magana.

Ya b'ata lokaci wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login