Showing 21001 words to 24000 words out of 95068 words

Chapter 8 - FEERYAL BOOK3 COMPLETE

kanki."

Feeryal ta ce "Ni ina ruwana ma da ita, Ammie na ta ce kar

na sake nashiga sabgarta,

zauna Miemie dan Allah kar ki tafi yanzu."

"

Ke ni yanzu zan tafi dama nazo nuna miki ashoben Yaya Yusuf ne,

Daddy ya

bada kud'i a yi mana odan kayan, dukan mu har da ke."

baki Feeryal ta washe tana kallon kayan a wayar Miemie ta ce

"Ai kuwa sunyi kyau."

"Idan ya iso zan kai mana

gurin d'i

nki, yanzu zanje wa Ammah aika ne direban ta na

jirana."

tayi waje da sauri..

Yusuf d'an yayan Mommy ne da suke ciki d'aya, wanda suke kira da Kawu Sani.

Kawu Sani shine babban d'an Bappa Salihu, yana zaune da iyalansa a Yelwa.

Yusuf shine babban d'an K

awu Sani, shi yana da zama a cikin garin Jos in da gidan sa da gun aikin sa yake can cikin garin Jos.

Daddy ne zai karb'a masa aure a nan Lagos za'ayi bikin.

matar anan cikin Lagos take,

bayan an gama biki zasu koma Jos.

biki na saura sati jama'an Yelwan S

hendam suka taho.

in da shima tuni ango Yusuf yana nan.



Ana saura kwana uku bikin Miemie ta karb'o musu d'inkin su. a parlour suka baje kayan Feeryal tana ta yaba kyan d'inkin.

bayan fitar Miemie Feeryal ta mike zata koma d'aki, ya shigo

rike da waya a

kunnen sa, sai da ya wuce dinning kafin ta shige d'aki. wayan sa data gani ranar a d'akinta ta d'auko ta fito,

dai-dai lokacin da yazo zai wuce rike da karamar flask mai d'auke da Sudan tea a ciki.

ta moko masa wayar

a hankali cikin muryarta mai sanyi ta c

e "Ga wayar ka......!

Kallon kyakkyawan hannunta fari tass mai dauke da zara-zaran yatsu da tayi musu kwalliya da jan lalle ya yi, gami da wayar da take miko masa.

sannan ya mai sa idanunsa kan fuskarta.

da sauri ta yi kasa da kanta jin yadda idanunsa

ya yi mata mugun kaifi da ganin ta.

lips d'in ta ta turo gaba ganin bai karb'i wayarba sai idon da ya tsare ta da shi.

ta kuma miko masa wayar, tana kuma cuno lips d'in ta.

ya miko hannunsa ya karb'i wayar kana ya sa kai ya shige.

Tana ganin shigewar sa t

a kofar dake sakanin parlor'n ta da nasa, ta gyara mayafin kanta tawuce ta fita ta ainahin kofar fita daga gefen nata zuwa farfajiyar side d'in.

ta nufo get mai gadi ya gaisheta tare da bud'e mata kofa, ta fice.

sashin Aunty ta nufa tana ta kiliya da 'yan

biki da gidan ya fara d'aukar jama'a.

wad'an da suka santa suka san da auren ta da Abdulrahim suka rika nuna ta, wasu su yaba wasu su kushe suce 'yar tsuntuwa ce ba'a san asalinta bama.

wad'an da basu santaba kuwa ta zame musu abin kallo da burgewa.

tana

daf da isa side d'in Aunty suka had'u da Ajmaal.

murmushi tayi masa tun kafin suyi kusa da juna.

shima murmushin ya yi mata.

"Feeryal an fito ne."

"Ina kwana Ya Ajmaal."

"Lafiya lau Feeryal antashi lafiya."

murmushi ta kuma tana fad'in

"Lafiya lau."

da sa

uri yasa kai yawuce yana jin zuciya na kokarin kawo masa abin da bai dace ba a kan ta, da sauri ya kwab'i zuciyarsa da take bijiro masa da yanzu ita ce mallakinsa.

ya sanarwa zuciyar

ita d'in haramiya ce a gare sa mallaki ga d'an'uwan sa.

Da sauri ta shig

e parlour'n Aunty cike da son ganin ta, tun daga bakin kofa take kwad'a mata kira

"Ammie Ammie Ammie."

Aunty ta fito daga cikin bedroom da sauri jiyo muryar ta.

da sassarfa Feeryal ta tafi ta rungume ta tana dariyar murnar ganin ta.

Aunty ta rike baki fusk

a d'auke da fara'a ta ce

"Ke Feeryal waya ce ki fito?."

baki ta cuno cikin muryarta mai sanyi gami da shagwab'a ganin ta gaban Ammie'n ta ta ce

"Ammie ai ina so na ganki ne, idan nazo sai kiyi ta ce na koma, ni dai kwana zanyi yau, kullum ni kad'ai zanyi t

a zama, danma Chuchu da Chulu suna zuwa, Miemie ma tana zuwa amma bata jimawa, ni kawai na dawo zan zauna a nan tare da ke."

Aunty tayi dariya ta ce

"To ke da kike da 'yan taya hira ma, kawayen ki suna zuwa kullum suna tayaki hira, bakiga ni kad'ai nake r

ayuwa ta ba, sai in Daddy ya zo ni nake samin mai taya hirar,

sai kuma idan kin haifo 'ya'ya dozen duk zan kwashe su na rike, kinga na sami 'yan hira ke nan ni ma."

kafad'a Feeryal ta make tana b'oye fuskarta jikin Aunty.

Aunty ta kuma yin dariya ta ruko h

annunta tana cewa

"Zauna dai ki ci cake da yogurt yau bazan mai da ke a kan kafarki ba."

ta zauna kan kujera Aunty ta shige kitchen tana jin kewa gami da kaunar d'iyar tata,

bataki ace ta zauna sucigaba da rayuwar su ba, amma ina sawun giwa ya kere na raku

mi.

ta fito mata da Cake da yogurt mai sanyi dai-dai misali, ta aje a gabanta kana ta zauna gefenta aiko da sauri ta gyara zaman ta ta soma ci, suna d'an tab'a hira irin na d'a da uwa.

a hankali take ci dan bata so taci da sauri Aunty tace ta tafi.

ai ko A

unty ta gane wayon ta ta tasan cikin ta duk son cin cake d'in nata bata ci yawuce yanka uku zuwa hud'u.

Aunty tana ganin ta ci yanka uku

koma kitchen ta d'ebo da yawa ta kawo mata tace.

"Tashi muje na rakaki ga wannan sai kije ki aje ki wuni kina ci."

kam

ar zatayi kuka tashiga bubbuga kafa kasa tana fad'in

"Ammie ni dai zan zauna."

Aunty ta ce

"Aa Feeryal ki koma d'akin ki, ta so maza."

ta ruko hannunta ta mike suka nufi kofa tana bubbuga kafa a kasa.

a bakin get na side d'in Aunty ta tsaya ta ce

"Maza ki

koma d'akin ki karki kuma fito wa sai kinyi fin wata kafin ki to."

ido ta waro ta ce

"Ammie har wata to ai jibi ma zamuje dinner."

"Aa Feeryal ki zauna a d'akin ki a bin ki me zai kai ki wani gurin dinner."

"Ammie Daddy ne fa da kansa yamana ashobe."

"Ke

dai jeki maza kar ki tsaya ko ina."

ta fita badan ta so ba.

a b'angaren Aunty itama ji take kamar karsu rabu, sai dai ta b'oye gudun kada Feeryal d'in tasami mafakar tuburewa..

"Ke Feeryal."

taji an ambata a bayan ta, da sauri ta waigo, Nabila ta gani.

Na

bila ta wurga mata kallon banza sannan ta ce

"Kije ana kiran ki a can."

Feeryal takalli in da Nabila take nuna mata, mutane da yawa a gurin wanda ta gane cikin su Umma Karima da Siyama ce kad'ai.

Nabila ta juya a hankali tabi bayanta.

tun kafin ta karaso S

iyama da Umma Karima suke aika mata kallon tsana.

har ta karaso gurin Umma Karima takuma wasa mata kallon banza tana fad'in

"Kunganta nan wannan kyawun duk na gaibu ne,

in banda aikin asiri me Abdulrahim zaiyi da tsintacciya, wacce tagama bin maza har cik

in gidan nan an kamata da wani, wai ita ce surukar Hajiya Halima, ai Hajiya Halima ta bada mata wlh datayi sake aka mallake mata d'an da ta haifa a cikin ta,

in nice tuni ban shafe babin su ba, mujen ku dan Allah."

Umma Karima tayi gaba bayan ta kuma wasa

mata kollon wulakanci.

Siyama ma haka harda jan dogon tsaki.

Feeryal tabi bayan su da kallo kana ta juya.

Umma Karima tun kafin su shige sashin Mommy take yab'a magana mai nuni da kaskanci gami da wulakanci, kan Feeryal har suka shige sashin nata.

Mommy

ta tare su tana fad'in

"Meke faruwa ne Hajiya Karima?."

Umma Karima ta yamutsa fuska tana cewa

"Saken da kikayi ne ya bani mamaki, har yaushe zaki bar nagartaccen d'anki ya cigaba da zama da wancan kaskantacciyar yarinyar data gama tambad'e wa a waje, wlh

Hajiya Halima kina bani mamaki."

Mommy ta ce

"Hmmm Hajiya Karima kibar wannan maganar tukun a gama bikin nan, ni nafi kowa son ganin naraba yaron nan da yarinyar nan, dan wlh ni banyi na'am da ita a matsayin sirikata ba, dole zai saketa dan ban shirya had'

a jini da aljanu ba,

shiyasa ma na gargad'e sa kada ya sake yace zaije gareta da wata bukata ta aure, bari jama'a su watse daga gobe zuwa jibi gata zakiga hukuncin da zan yanke."

Umma Karima ta ce " Da dai ya fi gara ki farka daga baccin da kike."

kawayen

nasu kuwa kowa ya cigaba da tofa albarkacin bakin sa wasu na fad'in

gara ta farka gida kamar wannan ace sirikar gidan ta kasance haka, wasu ko cewa suke tun da har an bari ta aure shi to a hakura kawai a barsu,

masu fad'ar haka kuwa Umma Karima ji take kam

ar ta nitsa musu mashi a zuci.

In da sabo ta saba tana shiga gefen ta takama wasu tsabgogin ta mance da duk tozarcin da Umma Karima tayi mata.

Bayan kwana uku ta kasance ranar d'aurin auren Yusuf da amaryar sa.

anata shagalin biki Feeryal tana gefen ta

ko sha'awar fita bataji.

magana tajiyo a parlour tana kwance a bedroom,

ta mike tafito, ta tsaya daga bakin kofar bedroom.

su Ameerah ta gani da wasu 'yan'uwan su da sukazo daga Yelwa, 'ya'yan Kawu Sani ne kannen angon Yusuf.

duk 'yammata ne kansu d'aya, s

u uku sai ita na hud'u.

"To gata nan da kuke ta dami na nazo na kai ku ku ganta, ni fa kar kusa yarinya ta rainani."

cewar Ameerah tana yamutsa fuska.

tare da ci gaba da fad'in

"Idan kun gama kallon ta kamar TV sai ku fito."

ta juya tayi waje.

Feeryal tabi

bayan ta da kallo tana mamakin yanzu Ameerah bata cika tsayuwa a gaban ta tana mata rashin mutuncinta data saba ba, sai dai ta tsaya daga nesa, tana mata kuma zata juya, ta kauce daga in da take.

hankalin ta ta mayar kan 'yammantan da taji suna cewa

"Ai k

uwa da gaske ne kamar balarabiyar."

murmushi tayi musu ta ce

"Kuzauna nakawo muku ruwa."

ai ko suka zauna, ta shiga kitchen ta ta d'ebo musu drink's da donut da nama ta kawo musu.

suka karb'a suka kuma yi mata godiya.

tayi murmushi tare da zama a gefe.

su

ka kusa cinyewa kuwa kafin suka mike sukayi mata sallama.

tun kafin su fice daga side d'in suke maganar ta,

d'aya daga cikin su ta ce

"Ni kam banga aibunta ba da su Ameerah suke kushita ba, gata kyakkyawa kamar ita tayi kanta."

sauran suka ce ai kuwa kam

suma basuga makusa a tare da ita ba.

suna koma sashin Mommy Ameerah ta harare su tana fad'in

"Ku har wani iya zama kukayi a gurin ta."

"Wlh tana da kirki har abinci ta bamu, ta zauna mukayi hira, ita wacce kike yabon nata ma ko kallo bamu isheta ba."

suka

had'a baki wajen fad'a.

hararsu tayi ta ce

"Kwad'ayayyu sai kun ci abincin aljanu ai."

Ana sallar magriba Miemie ta shigo side d'in Feeryal da sauri.

tana zaune a kan sallaya ta idar da sallah ke nan.

Miemie ta rike hab'a tana fad'in

"Wai ke Feeryal ko

da yaushe in dai za'aje wani guri kullum ke ce karshen shiri, dan Allah ki tashi ki shirya kafin ayi isha, 12 fa za'a tashi dan yau zasu wuce Jos."

"To yanzu zan shirya."

Miemie tafi tana fad'in

"Kiyi sauri zan kira ki idan muka fito."

ta ce tom.

A hanka

li take shirin dan har cikin ranta bata jin zataje gurin dinner, dan tasan zata fuskanci kalubale a gun Mommy da Umma Karima da wasu daga cikin danginsu.

kiran Miemie ne ya shigo wayarta, Miemie ce ta

"Kiyi sauri ki fito Feeryal gamu mun fito."

ta ce "Tom.

"

ta sauke wayar, tayi ta lalawai, Miemie tayi ta kiranta a waya tayi ta ce mata gatanan fitowa, daga bisani ta ce mata itafa su Mommy take tsoron abun da zasuje su mata.

Miemie ta ce

"Ina ruwanki da su muna gefe suna gefe."

kai ta girgiza kana ta ce

"Gan

i fitowa."

sai sannan ta d'auko ashoben nasu tasaka pant da underwear batare da ta sa bra ba, tayi tayi ta tasaka doguwar rigar tasama takasa, dole sai ta kasa ta saka ta janyo sama ya wuce da kyar.

d'inkin ya kamata sam bataji dad'i ba, dan bata saba sa k

ayan daya matse ta ba.

ta d'au gyale ta saka akan ta,

ta zura takalmi mara tudu sosai.

ta d'an feshe jikin ta da turare ba masu karfi ba.

kana ta d'au handbag da wayan ta fita..

Tana fita ta hangoshi yana fito daga gefen sa,

tana kokarin wucewa yayi mata

alama da hannu ta koma ciki.

tsayuwa tayi kamar zatayi kuka, takuma duban shi ya tsare ta da ido, fuskarsa bawasa.

kasa tayi da kanta tana jin hawaye na taruwa mata, sai dai ta kasa iya kuma kallon sa.

a hankali ta juya ta koma ciki ta fad'a saman bed.

Sa

i da yaga shigewar ta kafin ya fita.

motoci nata fita da mutane yawanci a daren zasu wuce, dan daga gurin dinner ango da amarya zasu wuce Jos da wasu daga cikin 'yan biki da yawa.

dan akwai wani gaggarumin shagalin da za'a gudanar a washegari a can Jos d'i

n.

tuni anyi bukin jiri na jiran su 11:30 zasu tashi, shi yasa 11 za'a tashi a gun dinner.

Daddy da ya fito daga side d'in Aunty ya tsaya suna sallama da wasu 'yan'uwan shi.

Abdulrahim ya karaso gurin san da motar ba'in ya tashi.

Daddy ya dube shi tare da

amsa gaisuwar da yake masa,

ya ce

"Ina Feeryal ga 'yan'uwan ta nan duk kowa yafita za'a tafi."

shiru ya yi baiyi magana ba

Daddy yakuma duban sa tare da karantar sa kana ya ce

"Idan kai bazakaje ba, to ita kabarta taje, akan me yasa zaka hanata, wata kila

tasa ranta tana son zuwa."

nan ma baiyi magana ba sai nad'e hannayensa da yayi a kirji.

A b'angeren Feeryal wayanta tajanyo tana share d'an guntun kwallan da suka zubo mata.

ta danna numman Aunty, tana d'agawa cikin muryar shagwab'a ta ce

"Ammie Sahab ya

hanani zuwa."

da sauri Aunty ta ce

"Ban amince kiyi gardama ba ki zauna, ban sanki da kafiya ba kar naji kinyi masa gardama"

baki ta cuno ta sauke wayar.

itafa ba gun biki take son zuwa ba so take tasamu ta fita taje b'angaren Ammien nata..

da sauri ta k

alli kofa jin an turo kofar.

daga bakin kofar ya tsaya ya ce

"Ki tashi ki sa hijab kije."

aiko bai rufa baki ba ta mike.

ya tab'e baki yajuya.

babban hijabin sallar ta ta zura tayi waje.

Yana tsaye daga sama yana hango cikin gidan.

motoci duk sun gama taf

iya.

akan idon sa ta shige sashin Aunty.

Aunty ta bud'e baki cike da mamakin ganin ta ta ce

"Ke Feeryal bana ce kar ki fito ba."

"Ammie shi yace naje."

"Feeryal yaushe kika koyi karya?."

"Allah Ammie da gaske Sahab shi ya ce nasa hijab naje."

Aunty tayi

shiru tana nazartar ta kana ta ce

"To me ya hanaki binsu Miemie ku tafi kika zo nan?."

zama tayi kan kujera tana cewa

"Nifa dama Ammie ba zuwa zanyi ba ni bazan je gurin dinner ba."

"Ai ko sai ki tashi ki koma d'akin ki, tun da ba tafiya zakiyi ba."

"Ayya

Ammie kibari sai anjima, idan suka dawo sai na koma, nima nayi dinner na anan."

tayi maganar tana cire hijab d'in.

Aunty tayi murmushi tana girgiza kai....karfe goma nayi tace ta tashi ta tafi dare ya yi.

Feeryal ta shagwab'e fuska,

"Ammie kaina ciwo yake

min kuma ina jin yunwa."

Aunty ta ce

"To tashi maza mijin ki likita, shi yasan maganin da ya dace ya baki,

fad'a min dai yanzu me kike son ci, sai na dafa na baiwa Baba Rabi ta kawo miki yanzu,

gobe idan Allah ya kaimu ma ki huta na d'auke miki girkin gobe

duka, ni zan dafa nabayar a kawo miki, kinji ko 'yammatan Ammie."

takuma shagwab'ewa tana fad'in

"Faten dankali da kifi kuma zan jira kiyi."

dakyar talallab'ata tace yanzu zatayi tabada akawo mata.

suka fito ta yi mata rakiya har bakin side d'in su sai da

taga shigarta kafin ta juyo.

Feeryal na shiga d'aki ta kwab'e hijab tashiga kokarin cire kayan jikinta, dan ba karamin damunta yake ba.

tayi-tayi ta cire ta gagara,

tarika kokawa da rigar kamar zatayi kuka.

da sauri ta shige bathroom jin fitsarin da tak

e ji yana kokarin fitowa, tayi ta fito tacigaba da kokarin cire rigar ga zip d'in rigar can sama kuma yayi tauri sosai.

zama tayi bakin gado tana maida numfashi kamar wacce tayi wani aikin.

ta janyo waya ta dannan number Aunty tana d'agawa ta ce

"Ammie na

kasa cire rigar, zanzo ki jamin zip d'in."

Aunty ta ce

"Me ya kaiku yin matsastsen d'in ki, karki fito ai ba ke kad'ai bace a side d'in mijinki na nan sai kije yaja miki, haka kawai kamatse kanka da kanka kahana kanka jan numfashi da kyau."

Aunty ta kashe

wayar Feeryal ta kwab'e fuska kamar zatayi kuka.

taya za'ayi ma taje tace yaja mata zip ai gara ta kwanta haka.

ta gyara ta kwanta.

tana sa kafad'arta akan gado taji rigar yana cizon ta, gashi ko numfashi mai dad'i bata iya ja dan bata sama ba sa irin mats

astsun kayan nan ba,

uwa uba kuma bata iya bacci da kaya masu nauyi ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login