Showing 81001 words to 84000 words out of 95068 words

Chapter 28 - FEERYAL BOOK3 COMPLETE

sai gashi ta tsinci kanta cikin jin nutsuwa mai cike da tarin farincin kasantuwar ta da mahaifinta.

haka Uncle Aliyu ko motsi tayi sai ya tambaye ta tana lafiya.

Jerginsu na sauka a Beirut na kasar Lebanon, tun daga airport

taga tsantsar tsagwara

n kauna da sosayya,

zuga guda 'yan taran su motoci sunfi goma.

maza da mata rungumar Feeryal suke, kamar zasu had'iyeta, ganin ta ya tuna musu da 'yar'uwar su.

wani gida ne da girman sa ya kai girma tsaruwa bazai fad'u ba,

nan Feeryal ta tsinci kanta.

suna

shiga gidan wasu zugan suka kuma yiyowa kanta,

kamar bazasu barta ta taka kasa ba tsabar kauna.

wata dattijuwar mata ta fito tunda ga can take yi mata murmushi hawaye kuma na sauka a idanunta,

ganin Feeryal ya tuna mata da d'iyarta Sheehra,

itama Feeryal

ta gane ta ta waya da ta ganta sanda Uncle Aliyu ya had'asu ta waya.

ta taho ta rungume Feeryal tana mata maraba da zuwa tana murmushi gami da share hawaye.

nan ta ruko hannunta ta jata sukayi ciki da ita.

Uncle Aliyu yabi bayan su.

wani babban kayataccen

parlour suka bayyana cikin sa,

bayan sun wuce wasu palukan sama da biyar.

dattijo sarki Al'Ayzaan na ganin ta ya mike daga kan kujerar sa ya mika hannu yana cewa

"Taho nan jikata lale marhaban da zuwa masarautar Beirut."

cikin harshen larafci yake maganar

.

ta fahimci abun da yake nufi ta tafi izuwa gare shi, ya rungumeta yana fad'in

"Sarki ya tabbata ga ubangijin halitta daya sanya kamannin Sheerah Al'Ayzaan a gare ki, hakiki muna farinciki da zuwan ki, nan gidan ki ne Feeryal Aliyu Sheehra Al'Ayzaan."

Unc

le Aliyu ya yi murmushi yana gaya mata abun da ya fad'a.

Dattijon ya sake ta yana dafa kanta, tare da sanya mata albarka.

yana jin ta a ransa sosai ya yi farincikin ganin ta matuka.

Ranar Feeryal sai da taji a ranta ashe itama wata ce,

dan kuwa taga kaun

ar da ya sata jin itama wata ce ashe.

Nigeria

Legos

Mommy ce ta shigo parlour'n Daddy yana zaune yana duba wasu takardu.

ta nimi guri ta zauna tayi masa barka da warhaka.

ya amsa batare da ya janye idanunsa daga kallon takardun ba.

Mommy ta d'an muskuta

bakin ta na d'an motsi alamar magana ce d'auke da ita,

ta ce

"Alhaji dama magana nazo muyi akan batun Abdulrahim da Feeryal, na ce me zai hana a maida auren su idan ta dawo,

kayi hakuri Alhaji ina mai kara baka hakuri amma wlh nayi nadama nayi danasa mara

misaltuwa, sharrin shaid'an ne da Hajiya Karima."

Daddy ya d'ago ya dube ta yana fad'in

"Sabo da yanzu kinsan asalin ta shiyasa zakice a maida auren ta da d'anki ko."

da sauri ta ce

"Ba haka bane Alhaji wlh na jima da wannan abu a raina narasa ta ya zan ti

nkare ka da batun ne, bansan taya zaka fuskanci lamarin ba,

amma Allah ne shaida wlh tun ranar dana gano gaskiya nayi nadamar abun da na aikata,

wlh Alhaji nayi na dama."

Mommy ta saka bakin mayafin ta tana share kwalla da gaske yake hango nadama tare da i

ta.

Daddy ya girgiza kai sannan ya ce

"Abdulrahim bai saki Feeryal ba, lokacin da kika matsa masa sai ya sake ta, ba saki ya rubuta cikin takardan ba kalmar hakuri ya rubuta ya mika mata."

Mommy ta d'ago da sauri tana murmushi da fad'in

"Allah na gode mak

a daka takaita yawan zunubaina."

ta mike da sauri tana share hawayen fuskarta ta fice da sauri tayi sashin Hajiya.

tana zuwa ta rungume Hajiya tana fad'in

"Hajiya Abdulrahim bai saki Feeryal ba, ashe da na ce ya sake ta ba saki ya rubuta mata ba."

Hajiya t

a ce

"Ah to madallah aikuwa dama ina shirin sa Abubakar ya kuma d'aura musu aure, ai ko fad'uwa tazo dai-dai da zama."

Ajmaal Shamsuddin Zaraddin Faisal, Goggo Bishira Bilkisu Rahma da suke zaune, suna hira da Hajiya duk sukayi farinciki da jin labarin,

Mo

mmy baki ya kasa rufuwa kowa sai da yasan da labarin Abdulrahim bai saki Feeryal ba.

ta kira 'yan Yelwa tarika sanar musu..

Lebanon

Feeryal

kwanan ta biyu a masarautar aka d'auke ta akayi ta zagawa da ita, ana nuna mata inda dangin mahaifiyar ta suke,

du

k in da sukaje kuwa sai sunyi kuka da farin ciki wai ta tuna musu da 'yar'uwar su Sheehra.

haka zasuyi ta riritata kamar zasu goyata.

A ranar da tayi kwana uku kuma Uncle Aliyu da kansa ya d'auke ta a mota, ya kai ta gidan da sukayi rayuwa da mahaifiyarta

har da d'aki da gadon da aka d'auke ta akai,

ya nuna mata hotunan sa da hamaifiyarta.

Feeryal tasha kuka sosai dan taji kewar mahaifiyar tata.

Suna dawowa cikin masarauta, Feeryal ta kule

babban d'akin da a ka yi mata masauki, ta kira Aunty tana ganin ta

taji kewar uwa daya baibaye ta ya gushe,

tayi ta zuba mata shagwab'a kamar yadda ta saba, Aunty na biye mata.

Aunty ta ce yaushe zata dawo dan tayi kewar ta Feeryal ta ce

"Bari Uncle yazo na tambaye shi yaushe zai mai dani, d'azu ya ce min wai kakana ya c

e sai nayi musu wata, nima ina so na dawo Ammie nayi kewar ki."

Aunty ta rike baki ta ce

"Baban naki ne Uncle."

sai kuma tayi dari ta ce

"Wata guda kuwa yakamata kiyi musu, suma suna bukatar ki a tare da su."

hira sosai sukayi Aunty tana tambayar ta ya kas

ar yake, dan duk fitar da take kasashen waje bata tab'a zuwa kasar ba.

daga bisani sukayi sallah.

Ranar da Feeryal ta cika kwana biyar, aka fita da ita ganin kadarorin mahaifiyarta, da kamfanonin mahaifinta da mahaifiyar ta,

sai yamma suka dawo gida.

ta

na shiga parlour'n kakarta mace ta tadda mutane da yawa cikin parlour'n kamar ko da yaushe,

tana kokarin karasowa cikin parlour'n

tayi burki da mamaki take kallonsa, suna zaune da wani da akace mata d'an kawun ta ne shi, suna hira cikin harshen larabci,

ga

yadda suke hirar zaka fahimci ba sabon rana d'aya bane, sun jima da sanin juna.

Duk suka d'ago suka kalleta.

dattijiwa kakarta Ummuh da ke zaune a gefen su tayi mata alama da hannu ta karaso.

a hankali take d'aga kafarta idanunsa a kanta har ta karaso ge

fen ta ta zauna.

kakar nata take cewa

"Munyi farincikin da shi ya kasance mijin ki, dan yaron kirkine shi abokin d'an 'uwan ki ne shi, tare suke aiki a can kasar Germany."

Rubah dake gefen su take maida mata abun da take fad'a da turanci.

shiru tayi batay

i magana ba.

zuwa can ta mike ta tafi masaukinta.

Washegari tana fitowa ta hango shi shi da Uncle Aliyu, ta kauce bata bari sun had'a ido ba.

san da ta shiga gaida sarki Al'Ayzaan, takuma ganin su tare.

mamki take ganin yadda shi ya fita shiga da fita a c

ikin gidan.

suna gama gaisawa ta koma.

karfe goma da rabi dattijiwa kakarta Ummuh ta shigo ta ruko hannunta kamar kullum tun san da ta zo gidan,

suka fito kan babban dinning mai zagaye da kujeru talatin, an jera abinci kala-kala kan dining d'in,

jikoki da

'ya'ya sune zagaye da gurin,

tun kafin ta karaso ta hangosa zaune shi da wannan d'an uwan nata abokin aikin sa, da wasu mazan suna zagaye da shi suna ta yi masa magana da harshen larabci,

ga takardu a gaban sa da alama dai hannu yake saka musu cikin takard

un.

a sannu ta karaso suka rika mikewa suna rumgumar ta, kamar yadda larabawa suka saba wajen gaida d'an uwan su,

har da mazan gurin.

fuska ya d'aure yana aika mata wani kallo.

ta kawar da kanta kusa da Rubah ta zauna aka zubo mata abinci kala-kal,

batawa

ni ci abincin kirki ba dan dama ita ba ma'abociyar cin abinci bane, sannan bata saba da cin kalar abincinsu ba,

abun da zata iya ne ta d'an tab'a, ta tsulale ta bar gurin, dan kallon da yake ta jefa mata ya hanata nutsuwa.

Da rana suna zaune da 'yammatan

gidan, dattijiwa kakarta Ummuh tazo ta ruko hannunta suka tafi parlour'n Al'Ayzaan.

anan suka tadda mahaifinta zaune.

kakar nata ya dafa kansa yana sanya mata albarka, kana ta nimi guri ta zauna.

ya dube ta da kulawa ya na cewa

"Yake jikata ki shirya gobe

zaki koma da mijinki, zai kuma dawo mana da ke bayan wani lokaci."

Feeryal ta d'ago da sauri dan ta ji wani abun da ya fad'a.

Uncle Aliyu ya ce

"Gobe idan Allah ya kaimu zaki koma da mijin ki, idan an kwana biyu zai dawo da ke ki kuma ganin danginki."

Feer

yal ta sunkuyar da kai tana tankwashe 'yan yatsun ta, ko ba'a fad'a ba tasan shirin nan na Sahab ne.

Goma na arziki suka had'a mata

in da aka mallaka mata dukiyar mahaifiyarta.

akace idan suka dawo Nigeria za'a transfer dukiyar ta dake aje a banki zuwa ba

nkin Nigeria.

Ummuh ta bata wani sarkar gold ta ce ta kaiwa Ammien ta.

motoci goma na masarauta suka fito rako su airport.

tana rike a hannun dattijuwa kakarta Ummuh ta bud'e motar da yake ciki shi kad'ai ne a baya sai direba ta ce ta shiga, ta shiga ta za

una Ummuh tayi musu fatan isa gida lafiya,

yana amsa mata da larafci.

Ummuh ta share kwalla dan ba shakka bataji dad'in rabuwar su ba.

motocin sukayi layin fita suna haurawa titi ya juyo inda take,

ya janyo ta jikinsa cikin yin kasa da murya ya ce

"Kar na

sake ganin kin tsaya wani kato ya rungume ki."

da sauri ta d'ago ta kalle shi ya jinjina mata kai alamun tabbar wa.

kasa tayi da idanunta bata ce ko mai ba, yana rungume da ita har suka isa airport.

ai kuwa da suka sauka ana ta rungumar juna na bankwana d

uk namijin da zai rungume ta sai ta matsa ta bishi da murmushi,

ji tayi an sakalo ta ta gefe ta juya da sauri shine ya rungume ta ta gefe a haka suka shiga jirgi.

Karfe 6 na yamma suka iso Nigeria.

sai da suka sauka ya kira Ajmaal ya ce ya zo airport da m

ota.

Ajmaal na kokarin fita da d'aya daga cikin motar Abdulrahim d'in, Daddy ya tsare shi ya ce

"Ina zakaje da motar nashi, wai ina shi Abdulrahim d'in ne, yau kwana biyu ke nan ban sashi a idona ba, ko yana wani aikin ne a asibiti?."

Ajmaal ya ce

"Nima tu

n shekaran jiya dana ganshi ban kara ganin sa ba, yanzun nan ya kira ni ya ce nazo da mota airport, inaga ya d'anyi tafiya ne."

Daddy ya ce

"Jeka ka d'auko shi."

Ajmaal ya ja motar ya fita.

Ko da ya isa airport d'in yayi mamakim ganin sa da Feeryal,

wan d

a yaji ance sai tayi wata kafin ta dawo wato shine yaje ya d'auko ta ya dawo da ita.

Ajmaal ya yi murmushi yana girgiza kai.

ya sauka ya bud'e musu motar yana yi musu barka da hanya, kana ya d'auki kayan su ya sa a bayan but.

ya shiga ya jasu suka nufi AA

FIYA STREET.

Aunty na zaune sai ganin ta tayi, mamaki ya cika ta tace daga sama ko kasa,

sai kuma ta rungume ta tana yi mata oyoyo.

"Feeryal wani irin dawowa ne wannan babu sanarwa, ya akayi haka, ko Yaya Aliyu fa bai sanar min da dawowar naki ba, ke da z

akiyi wata guda sati d'aya kuma sai ki dawo."

"Ammie nima bansan ya akayi ba Uncle da tsohon nan suka ce wai nabi Sahab mu dawo, in an kwana biyu zai kuma mai dani."

Aunty ta rike hab'a da mamaki tana murmushi.

muryar Daddy suka jiyo

"Au shi Abdulrahim d'i

n dama can Lebanon d'in ya tafi, shi yasa kwana biyu ban ganshi ba ashe yaje d'auko ki ne,

ina ruwan sa ga yadda akayi zakije ki zaga cikin 'yan'uwa shi ne shi zai je ya rushe shirin, zai gamu da ni kuwa."

Feeryal ta zame a jikin Aunty tana gaida Daddy.

Au

nty ta ce ta shiga ciki ta wasa ruwa ta rage gajiya.

Feeryal na shiga d'aki, Aunty ta dubi Daddy tana cewa

"Daddy dama fa ba'ayi shawari da shi wajen tafiyar nata ba, yakamata kuma aji ta bakin sa kafin tafiyar nan."

Daddy ya ce

"Dan ba'aji ta bakin sa ba,

shi ne zai bita har wani kasa yaje ya d'auko ta, shekara 18 sukayi suna kewar ta da mahaifiyar ta,

shine bazai iya hakuri ya bar musu ita na wata d'aya kacal ba,

sabo da rashin hankali."

Aunty tayi murmushi tana cewa "Uhum Daddy ai gado ya yi, baka tab'a

barina nayi sati a gida ba, tun da nazo gidan nan, in na jima nayi kwana uku, duk hidimar da ake kuwa."

Daddy ya yi karamar dariya yana fad'in

"Nashi gajen hakurin ai ya yi yawa, ya kamata ya barta tukun suma suma bukatar ta."

Aunty dai murmushi tayi dan

tasan yana bukatar matarsa.

A waje suka had'u da Daddy yana kokarin wucewa side nashi.

Daddy ya dube sa yana cewa

"Ka kyauta da ka je ka dawo da ita."

yad'an sosa bayan keyar sa, yana gaida Daddy.

Daddy ya amsa yana wucewa.

A ranar da suka dawo da dadd

are karfe 8, Ajmaal ya shigo sashin Aunty suna zaune a parlour da Feeryal.

ya gaida Aunty Feeryal kuma ta gaishe shi, ya amsa yana yi mata murmushi sannan ya ce

"Aunty wai inji Ya Abdulrahim a bashi sudan tea."

Aunty ta ce

"Babu a kasa amma bari a girka."

tana mikewa kira na shigowa wayar Ajmaal ya d'aga ya kai kunnen sa sai yace

"To Daddy."

ya sauke wayar yana cewa

"Daddy na kira na bari na je na dawo kafin an gama."

ya juya da sauri ya fita.

Har Aunty ta gama Ajmaal bai dawo ba, sai can ya kirata a waya

ya ce

"Aunty naje wa Daddy aika ne, dan Allah ki bawa wani ya kai masa."

Aunty ta ce "Tom bari a ba wani ya kai masa."

Aunty ta dubi Feeryal da ke zaune tana game a wayarta ta ce

"Feeryal je ki sa mayafin ki ki kaiwa Abdulrahim tea d'in nan."

ido ta waro t

a ce

"Ammie akwai mage a hanya."

"Babu mage yana sashin Hajiya, har ki tafi ki dawo bazaki gansa ba."

ta mike ta shiga d'aki ta fito da hijabi a jikinta.

tana kwab'e fuska da tsoro ta ce "Ammie bazanga magen ba ko?."

Aunty ta ce "Bazaki ganshi ba Feeryal,

ki sa a ranki bazaki gansa ba."

ta gyad'a kai ta karb'i flas d'in ta fita.

a can farfajiyar gidan ta had'u da Shamsuddin, ganin yadda take ta waige-waige ya ce

"Lafiya Feeryal ina zuwa da daddaren nan?."

ya kalli abun da ke rike a hannunta ya na kuma fad'

in

"Ko zaki kaiwa Ya Abdulrahim ne."

da sauri ta gyad'a kai ta ce

"Eh kuma akwai mage a hanya."

ya yi murmushi ganin yadda tsoro ke d'awainiya da ita ya ce

"To kawo na kai masa."

ai ko ta mika masa da sauri ta juya ta koma.

tana shiga Aunty ta ce

"Wai har

kin kai masa?."

marairaice fuska ta yi ta ce

"Ai naji kukan mage."

"Au da kikaji kukan mage sai kika aje tea d'in a ina."

"Na bawa Ya Shamsuddin ya kai masa."

tayi maganar tana kwanciya kan kujerar da Aunty ke kai tayi pillow da kafar ta..

Washegari da mi

salin karfe 7 na safe, Aunty na kitchen tana had'a breakfast.

kiran Abdulrahim ya shigo wayarta.

ta d'aga da sallama ya amsa sallamar tare da gaishe ta ya d'aura da fad'in

"Aunty ko zan sami sudan tea?."

ta ce "Eh bari a kawo maka."

fita tayi ta shiga d'a

kin Feeryal ta tashe ta a bacci, Feeryal ta tashe tana mussuke ido.

Aunty ta ce "Tashi ki kai masa breakfast zai tafi asibiti, yi sauri ki fito kafin na gama had'a masa."

Aunty ta fita ita kuma ta mike ta shige bathroom.

sai da tayi brush tayi wanka sannan

ta fito.

ta zauna gaban mirror ta shafa mai da turare masu sanyin kamshi, sannan taje ta ciro pant da dogon riga normal riga mara nauyi, tasa pant d'in sannan ta zura rigar, batare da ta sa bra ba, ta d'au hijabi har kasa ta zura, ta fito kuwa dai-dai san

da Aunty ta fito daga kitchen rike da basket data shirya masa breakfast ciki,

ta mika mata tana cewa

"Yanzu kam dai ba kule a hanya maza ki kai masa."

ta karb'a tayi waje.

A hankali take tafiya har ta isa bakin get na side d'in sa.

tayi knocking mai gadi

n get d'in ya bud'e mata.

ya shiga gaisheta cike da girmamawa.

ta wuce ciki tana bin sashin da kallo tun da ta barshi sai yau ta kuma saka kafarta cikin sa.

gefen sa ta nufa ta isa bakin

kofar parlour'n sa tayi knocking sannan ta murd'a handle ta tura ta s

higa, d'auke da tsiririn sallama a bakin ta.

yana zaune a saman kujera da laptop a gabansa,

yana sanye da gajeren wando da singlet.

tun da ya d'ago ya zuba mata ido har ta karaso bai d'auke idanunsa a kanta ba.

a kasa a gefen sa ta aje basket d'in.

a hanka

li cikin tsiroriyar muryarta mai sanyi ta ce

"Inakwana."

zaman sa ya gyara tare da mika hannu ya janyo ta, ya yi mata masauki kan cinyarsa.

ya zare hijabin jikinta yana cewa

"Wato jiya baza ki iya kawo min ba sai dai ki ba wani ya kawo min tea d'in ko."

f

uska ta kwab'e ta ce

"Ai akwai mage ne a hanya."

ya ce "Okay to ai yanzu ma akwai magen a nan."

wani irin zabura tayi, ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login