Showing 87001 words to 90000 words out of 95068 words

Chapter 30 - FEERYAL BOOK3 COMPLETE

kwaikwayar muryar t

a.

ido ta rufe da karfi wato Sahab haka ya iya zolaya shima, kamar ba shi ba idan ka ganshi zakace babu magana bakin wannan,

dan a fuskarsa kad'ai ka kalla zaka cire rai da samun magana cikin bakinsa.

idan yana mata wasu abubuwan takan sha mamakin sa,

a d'

an zaman su ta fahimci mutum ne mai mugun saukin kai sam baya son hayaniya magana kuma bata dame sa ba,

baya dogon magana amma da ita yakan yi magana mai tsowo.

kafa ta shiga shurewa da shagwab'a.

ya d'agota ya rungume yana manna mata kiss, ya yin da yake

dad'a jinta sosai cikin zuciyarta.

Dr Imran ya yi knocking sai da ya gyara mata jikinta ya rufa mata mayafi, kafin ya ce ya shigo.

Dr Imran na shiga idanunsa ya sauka kan computer.

baki ya washe yana cewa

"Wow! gaskiya mutumina kai d'in bana wasa bane, wa

ni babyn ka samo mana, Allah ya raba lafiya, to bari nayi sauri na sanar a gida a bani tukuici."

Abdulrahim ya harare shi.

ya kamo hannunta ya saukar da ita.

suka nufi kofar fita.

shiko Dr Imran dariya ya yi yana dan na wa lambar Ajmaal kira.

"Gara dai na

sanar musu da wuri dan nasan kai kam bazaka fad'a ba, sai dai in sun gani da idon su."

ya yi maganar yana kai wayar kunnensa.

Ajmaal na d'agawa Dr Imran ya sanar masa Feeryal na da ciki har da watan cikin.

Ajmaal da ke tare da su Mommy a parlour'n Hajiya

ya yi ihun murna.

yana fad'in

"Yes yes yes masha'allah!."

da sauri Hajiya ta ce

"Kai Ajimi lafiyar ka ai sai kasa mu ruga da gudu."

cikin matukar farinciki ya ce

"Hajiya Feeryal na da ciki wata d'aya da sati biyu."

Hajiya ta ware ido ta ce

"Ya haka kuma b

ayan batayi ko wata da dawowa ba."

Goggo bishira ta ce

"Hajiya kin mance san da ya karb'ota daga hannun 'yan kidnapping, bafa gidan nan ya dawo da ita ba, sai da sukayi kwana uku kafin ya dawo da ita,

kuma kiyi lissafi wata biyu da sati biyu ke nan da faru

war hakan."

Hajiya ta rike hab'a

"Oh 'yan zamani zasu kasheka da sauran kwanan ka, wato can ya lallab'a ya kai ta ya yi mata cikin."

Mommy kam sai tsunkuyar da kai abun da ta aikata ya zo mata sabo,

bakin mayafin ta ta kai ta shere hawayen da suka zubo mat

a,

ta ce

"Allah sarki Allah ya sauke ki lafiya Feeryal, ashe ba karshen koyayen Albulrahim na kashe ba, ka gafarceni Abdulrahim Feeryal ki yafe ni, ya Allah na tuba."

ta fashe da kuka duk aka dawo bata hakuri.

Ajmaal ya yi waje da sauri yaje ya sanar wa Au

nty.

Aunty kuwa bakinta yakasa rufuwa sai murmushi take.

itama Daddy na shigowa ta rungume shi da murna take shaida masa.

Daddy ya yi dariya da farinciki fal ransa ya ce

"Oh Fad'imatu babu kunya ana murnar anyi jika."

duk sukayi dariya zuciyoyi cike da far

inciki.

Wannan ciki na Feeryal taga gata da tarairaya, agun Mommy Aunty da kuma Daddy Hajiya ma ba'a barta a baya ba,

haka Ajmaal kullum a lissafin kwanakin cikin yake, wai yana alla-alla abun cikin yazo duniya,

su Farida da sauran kannen sa da 'yan gidan

kowa na mararin isowar baby duniya,

har da Mom da yanzu taga babu wani sarki sai Allah ta yada makamanta, ta rufawa kanta asiri ta zau na cip dan miji kam yana nan a rufe an yanke masa shekaru 10 a gidan yari.

sannan shi kansa mai cikin,

tamkar a goya ta

motsi kad'an za'a waiwayeta.

labarin cikin ba iya Yelwan Shendam da Abuja ya tsaya ba har Beirut Lebanon.

kusan kullum sai sunyi video call da 'yan Abuja da Lebanon suna jin lafiyar cikin nata.

Goggo Bishira kullum tana gurin ta idan Abdulrahim yatafi asi

biti ita zataje ta zauna da ita, ita da su Miemie da Ameerah.

baya kai awa uku zai dawo gida ya d'aura daga in da ya tsaya a rainon cikin nasa.

kayayyakin amfanin asibiti na kula da mai ciki musamman ya shirgesu a wani d'aki na gefen bedroom d'in sa, harda

computer scanning,

duk bayan sati yake duba lafiyar ciki.

a sanu a sanu cikin Feeryal ke girma, haka ma kulawar da ake bata ke kara hab'aka.

dan kuwa yanzu Aunty bata iya hakuri duk bayan kwana biyu zataje ta gano ta.

Akwan a tashi babu wuya a gurin Alla

h yau Feeryal ta tashi da ciwon nakuda.

tun da ya gane nakuda ne bai matsa ko nan da can ba,

bai kuma sanar wa kowa ba, sukayi ta nakudar su su kad'ai,

abun tun azahar har dare Feeryal na abu guda.

ta bashi tausayi matuka yarasa ina zai sakata ina zai saka

rayuwat sa,

ta kankame shi tana fad'in

"Wayyo Sahab zan mutu ka cire min cikin nan na huta, zai kashe ni."

ya rungume ta yana cewa

"Sorry Beauty kin kusa saura kad'an ki haihu."

ido ta matse da karfi ta ce

"Tun d'azu haka kake ta fad'a kuma haihuwar yaki,

wayyo Allah Ammie na zan mutu."

da sauri ya dad'a rungumo ta yana shafa bayanta.

haka sukayi ta yi,

idan abun ya motsa ya rungume abarsa suyi ta salati da addu'o'i idan ya d'an lafa mata ya d'auke ta da cikin yayi mata rukon jarirai.

sai wajen karfe 12 na

dare nakuda mai gaf-gaf ya zo a hanzarce ya shige da ita,

d'akin da ya mai dashi gurin kula da lafiyar ta dana cikin.

ai kuwa ko minti biyar basuyi da shiga ba ta suntulo katuwar jaririyarta.

zokaga murna gurin sa ya had'e ta da jaririyar ya rungume su.

d

ole sai da yayi mata d'in ki dan ta karu sabo da girmar 'yar.

ya gyara ta ya gyara jaririyar su, ya shiryata cikin kaya masu kyau da tsada.

ya gyara gurin sannan ya kamata ya kai ta bayi yana ta masa sannu cike da tausayawa dan ta galabaita, ya mata wanka

da ruwa mai d'umi ba mai zafi sosai ba dai-dai kima.

a d'auke ta ya kai ta d'akinsa ya dawo ya d'au jaririyar, da take ta musu-musu tana niman tura hanu a baki.

yana ta kallon yarinyar cikin wani irin so da kauna.

Feeryal na kwance jiki ya yi laushi.

ya

yi mata alluran da zasu taimakawa jikinta, da kuka akayi allurar ya bata tea mai kauri tad'an sha, ta koma ta kwanta ba jimawa bacci ya yi gaba da ita.

ranar Abdulrahim bai rumtsa ba ya saka Feeryal a gaba yana aikin kallonta, yana kuma runmuge da kyakkyaw

ar katuwar 'yarsa girmar 'yar bazakace yau aka haife ta ba.

Washegari da asuba a gida ya yi sallah, bai fita masallaci ba yana idar da addu'o'in sa,

ya dawo bakin gadon da ita da 'yarta suna bacci cikin kwanciyar hankali.

ya kwanta a gefen su ya ya rungum

o su duka a haka shima wani bacci mai matukar dad'i ya d'auke sa.

11 jaririyar ta farka tayi kuka ta farkar da su duka.

ya mike da sauri ya d'auke ta yana jijjigata.

Feeryal ta mike zaune tana kwab'e fuska.

wani kayataccen murmushi ya bita da shi yana fad'

in

"Beauty akwai in da yake miki ciwo."

kai ta girgiza tana turo lips d'in ta gaba.

murmushin ya kuma ya matso kusa da ita sosai ya rungumeta ta gefe,

ya ce

"See Beauty kama da ni tayi, hasken kuma naki."

tsintar kanta tayi da sakin murmushi har hakoran t

a suka bayyana ta kwantar da kanta jikin kafad'ar sa, idanunta akan yarinyar da take ta juya kai tana bud'e baki,

yatsarta ta d'aura kan kumatun 'yar ta ce

"Wannan fa?."

gira ya d'aga mata ya ce

"Oh dimple naki."

murmushi duk sukayi.

"Mu gani ko nonon ya

kawo ruwa yunwa take ji."

dad'a shigewa jikin sa tayi tace

"A bata tea ta sha."

ido ya waro ya ce

"Tea ai ko ruwa bazata sha ba daga nan har 6mon bare tea."

ya janyo wayarsa ya kira lambar Hajiya, Hajiya ta d'aga da sallama.

tana cewa

"Abokin turawa kun ta

shi lafiya."

ya ce "Lafiya lau Beauty ta haihu."

Hajiya tayi kambara ta ce

"Yanzu haka to gani zuwa."

Goggo Bishira da ke kusa da ita ta ce

"Ikon Allah wlh yarinyar nan tana raina tun jiya nake ta ganin alamun haihuwa tare da ita."

Hajiya tayi waje da sa

uri tana fad'in

"Je ki gaya wa iyayen su."

Gefen sa Hajiya ta shiga tana kwad'a sallama.

ya fito ya tsaya daga can sama ya ce ta hauro.

Hajiya ta ce

"Yoo a sama ka barta take nakudar, ni ina zan iya sintiri a sama kamar tsuntsuwa,

gwuiwa na ciwo."

da kya

r ta haura tabi bayan sa da sauri suka shige d'akin tana fad'in

"Ikon Allah madadin ka fad'a tun d'azu a nemo magani a tafa mata na nakuda."

shiru Hajiya tayi da maganar ganin Feeryal zaune cikin nutsuwarta,

jaririyar ta na kwance a gefen ta.

Hajiya ta rik

e baki tana fad'in

"Aa wai dama har anyi haihuwar ne, ni sai naji kamar kace zata haihu,

ikon Allah."

ya ce

"Tun jiya ta haihu mace da daddare."

Hajiya ta kuma rike baki

ta karaso bakin gadon tana fad'in

"Au haihuwar tun jiya har azahar ta kusa sai yanzu

muke sani,

lallai an gaisheka Abokin turawa,

bazaka kira azo a taimaka maka maka da wani abun ba,

ai ko d'an itacen rage saukin nakudar nan za'a girko a bata, sannu kinji 'yar nan."

baki ya tab'e jin wai itacen nakuda.

Hajiya ta d'au yarinyar tana fad'in

"

Masha'allah wannan katuwar haihuwar jiya, kai sannu kin ji Feeryal sannu da kokari duk wannan 'yar ke kika iya haifa

ikon Allah ga yarrinya tubar kallah,

yoo taso muje d'akin ki ka barta anan, in ba rowar ganin su zakayi wa mutane ba,

wannan hawa da saukar

ai sai kai."

Hajiya ta gyara rukon yarinyar tayi waje.

ya kamo ta suka bi bayan Hajiya yana rungume da ita ta gefe.

suna shiga gefen ta suka tadda Mommy da Aunty Ammah Mom da kannen sa duka a cikin parlour'n.

bai sake ta ba yana tallafe da ita har suka s

hige bedroom d'in ta.

su Ameerah suka rufu a kan Hajiya suna rige gigen karb'ar 'yar.

Hajiya ta ce

"Duk ki tsaya bari tayi wanka tukun."

yana fita su Aunty suka shige d'akin nata.

har ya kai bakin kofa ya dawo ya leko d'akin yana fad'in

"Hajiya kar a bata

ruwa ko wani iri ne."

Hajiya ta rike hab'a ta ce

"Yoo jimin d'a, nifa banson wannan karyan turawan nan, da kai da kasha ruwan me ya kashe ka, ba gaka nan digirgir da lafiyar ka ba, a rika zaluntar yara suna jin kishi a hanasu ruwa."

"Please Hajiya kar a b

ata."

ya fad'a tare da juyawa.

Goggo Bishira tayi murmushi ta ce

"Baza'a bata ba Abdulrahim."

Aunty ma murmushin tayi tana girgiza kai.......!

Duk suka cika da mamakin jin tun jiya da 12 na dare ta haihu.

ya karb'i haihuwar ya yi komai da kansa.

bai sanar

ba kuma har sai da rana tayi.

suka rika yi masa sannu suna yaba mata da kokarin haifo katuwar 'ya haka.

Hajiya tasa Goggo Bishira taje ta d'auko gabaruwa da lalle, tazo ta saka cikin babban tukunya ta zuba ruwa ta d'aura kan gas.

ana ta hira

Mommy tayi s

hiru tana ta sakar zuci

"Ina zai gayawa wani tana nakuda yana gudun kada wannan karon ma na kuma kashe masa 'ya, kauco na hakika ni Halima nayi asara, na kashe jikokina maza biyu da hannunan."

lura da halin da Mommy ta shiga Aunty ta miko mata jaririyar ta

na cewa

"Karb'e ta Mommy'n Ameerah wannan zata karya min hannu."

murmushi Mommy ta yi tana b'oye yanayin da ta shiga ta karb'e ta tana fad'in

"Ai Feeryal ta sha fama wajen d'aukarta a cikin ta, gashi sai karkata baki take wannan za'ayi acici a nan."

Ammah

ta ce

"Ai kuwa dai ga baban ta ya hana a bata ruwa, idan maman tayi wanka tasha tea mai zafi, zata sami ruwan nono akan kari."

Hajiya ta fito daga bayi rike da bawun da ruwan wankan jaririyar ciki tana fad'in

"To taso Fatima kije ki wa mai jegon wanka, ga

ruwa na had'a a bayi,

Bishira je ki juyo gabaruwan ya rika shan iska kafin a gama mata wankan, sai ki sa ta shiga."

Aunty ta dubi Feeryal tun d'azu take like a jikinta ta ce

"Taso muje kiyi wanka."

Aunty na mikewa kiran Abdulrahim na shigowa wayar Hajiya,

Hajiya ta d'aga tana kwad'a masa sallama, daga cikin wayar ya ce

"Yau wa Hajiya na mance ban gaya miki ba, karfa kuyi wa Beauty wanka da ruwan zafi sosai."

Hajiya ta ce

"Yoo ai ba ni zaka gaya min ba sai ka gayawa iyayen ka, kai tun kan a haifi uwan ka da

ubanka nake karb'ar haihuwa,

kai zaka gwada min yadda ake wankan jego, yanzu zan tura Ajimi ma yaje ya ballo min dalbejiya, in dai so ake tayi kwari kuwa dole sai an bigi jikinta da ruwan zafi."

Hajiya ta kashe wayar tana cewa

"Jimin d'an nan ka rika sakow

a mutane bidi'a cikin lamari."

Ammah ta yi dariya ta ce

"Hajiya kin san fa yanzu sai a hankali cututtuka sunyi yawa,

shi likita ne yafi mu sanin me yasa ya ce hakan,

a dai bi abun da ya ce d'in."

Hajiya ta soma mita

"Mu da da akayi mana mun mutu ne, yara d

a kalen fitina."

Aunty dai batayi magana ba taja Feeryal sukayi cikin bayi,

ta kara ruwan sanyi cikin ruwan zafin da Hajiya ta tara cikin bathtub.

tayi mata wanka sosai sannan ta sata ta shiga ruwan gabaruwa da lallen da Goggo Bishira ta dafa.

koda suka fi

to daga bayin

Mommy bata d'akin,

dan tun shigar su bayi ta fita a d'akin a matsayin ta na suruka.

Ammah ce ta shirya jaririyar bayan Hajiya ta mata wanka.

Feeryal na gama shiri, Aunty ta had'a mata tea mai kauri ta sha.

sai a lokacin Hajiya tabar su Amee

rah suka shigo, dan ta koresu duka ta ce suyi waje sai an gama kafin su shigo.

suka rika d'aukar yarinyar suna santin katanci da kyanta.

Miemie ta matsa kusa da Feeryal tana fad'in

"Ke kinga wani kyan da kika kara kamar ba ke ce kika haihu ba, ke na fahimc

i ma fa haihuwa kyau yake kara miki."

murmushi Feeryal tayi tana hararar ta.

Ko da aka ragu a d'akin Aunty ta d'au 'yar ta ce ta bata nono, dan tun d'azu take ta kuka tana niman nono.

Aunty na tallafe da jaririyar, ita kuma ta saka mata nonon a baki,

ja

d'aya ta fizge a bakin ta da sauri tana fad'in

"Wash!."

Aunty ta ce "Bata kafin ya kara tsami in yakai anjima baki bata ba zafi zai kara."

fuska ta kwab'e ta ce

"Ammie a barta kawai a bata tea."

"Tea kuma Feeryal jaririyar, kina dai ji baban ta ya ce ko ru

wa bai yadda a bata ba,

daure dai ki bata tasha."

ansha dabi da ita kafin ta barta tana sha tana matse ido har da kwalla.

yarinya ko ta koshi har tayi bacci.

Bayan sallar azahar Ajmaal Shamsuddin da Faisal suka biyo bayan Daddy suka taho sashin Feeryal,

a

parlour suka zauna Aunty ta fito musu da jaririyar.

sai da duk suka d'auke ta kafin suka bai wa Daddy, Daddy dai murmushi ya yi ta yi, ya ce

sun nuna masa wariyar launin fata saboda 'yarsu ce.

Feeryal ta fito suka gaisa Daddy yana ta sanya mata albarka.

Farida har da nama ta girkowa mai jego, ta kawo mana.

da daddare Zaraddin da matarsa Saddiqa suka shigo gurin mai jego,

suma suna zaune lafiya da mijin ta ba'a tab'a jin kansu ba,

sunyi wa kowa bazata.

Aunty ke zaune a kan d'iyar ta,

akai-akai ya ke shigo

wa duba lafiyar matar sa da 'yar sa,

sai dai da ya shigo baya zama zai fita sabo da Aunty da kuma 'yan barkan da suke zuwa.

kwana uku da haihuwar da safe ya shigo ya yi wa yarinya hud'uba da suna Fatima.

wayyo zo kaga murna gurin Aunty anyi mata takwara,

taji dad'i kwarai da gaske na karamcin da ya nuna mata.

da zai fita ya ajiyewa Feeryal sabuwar waya a kusa da ita.

yana fita ta d'au wayar tana dubawa an saka komai cikin wayar.

tana rike da wayar kira ya shigo, ko da ta d'aga muryarsa ta jiyo yana fad'in

"Baby bata koshi da nono ba ki kara akan wanda kike bata, a gajeren kari tayi minti 20 tana sha, ki kula da kanki ki ci abinci sosai."

fuska ta kwab'e kamar tana gaban sa, ta ce

"Har minti 20 da zafi fa, ai zata iya shan tea a rika bata ta na sha kawai."

d

a karfi ya ce

"Beauty! sai kuma ya sassauta murya

"Please kar ki bata tea bata kai na shan tea ba."

shagwab'e fuska tayi tana sauke wayar.

Aunty ta dube ta ta ce

"Maganar tea d'in nan ya fita a bakin ki, kar watarana ki ce zaki bata."

fuska ta kwab'e ta g

yara kwanciyar ta,

itafa maganar bada nonon nan bata son shi zafi yake mata.

Aunty takira Daddy ta gaya masa Abdulrahim ya mata takwara.

Daddy yaji dad'i sosai.

Ana gobe suna Aunty Zainab wato yayar Aunty da Maryam suka zo daga Lagos.

'yan Yelwan Shendam

ma sun sami zuwa.

gidan ya cika ana ta shirya in da gobe zata kasance.

tun a yau d'in aketa yanke yaken shasu da raguna da aka kawo su daga gidan gona,

ma'aikata suna ta aiki.

da daddare suna tare a d'aki ya kirata a waya, ya ce ta zo ta same

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login