Showing 18001 words to 21000 words out of 95068 words
yi masa d'inkin, kafin yagama.
yana gamawa yasa su d'aga shi su shiga dashi cikin wani d'aki mai duhu, bayan ya yi masa duk abin da yakamata.
kana ya fito yashiga motar sa ya juya gida......!
Koda ya isa
gida gefen sa ya shige, yarage kayan jikin sa, yabar gajeren wando da singilet.
har yakai kofar bathroom sai kuma yaja ya tsaya, gajeren tsaki yaja kana ya juya yafita ya nufi gefen ta. yana shiga ya tsaya daga a bakin kofar bedroom d'in.
ganin in da d'aki
n yayi kaca-kaca da jini.
idanunsa ya sauka a kanta, tana kwance a kasa, kusan rabin jikin ta a bud'e yake dan towel d'in daga kasa ya bud'e amma ba duka ba, yanayin fad'uwar da tayi shi ya baiwa towel d'in damar bud'ewa ya zamo ta gefen cinyarta.
daga sam
a kuma ya kunce sai dai bai zame daga kirjin ta ba.
bata ko motsi da alama dai suma tayi.
gefe yabi yataka ya isa in da take.
ya sunkuya ya mika hannu ya ciccib'ota.
a hankali ya had'a ta da kirjinsa.
wani irin harbawa zuciyar sa tayi, ba shiri ya rumtse i
danunsa da karfi, sai kuma a sannu ya bud'e su a kan fuskarta.
a hankali ya soma d'aga kafarsa idanunsa a kan fuskarta bai janye ba, har ya tako bakin gado.
ya sauke ta a hankali ya kawar da kansa gefe tare da mika hannu ya gyara towel d'in yadad'a rufe ma
ta jikin ta.
ya share jinin ya goge gurin tass kamar komai bai faruba.
Ya na gamawa ya d'au wukan ya fita.
Jim kad'an ya dawo rike da allura daya rigada ya ja a sirinji.
ya tako bakin gado allurar ya d'ago tare da cire murfin Kansa, d'an tsayuwa ya yi ka
mar mai nazarin wani abu.
gajeren tsaki yaja yakai hannu ta kasan towel d'in yarike sai kuma ya sake, tare da furzar da fuci daga bakin sa.
ya juya da sauri har yakai bakin kofa yakuma juyowa,
yadawo bakin gadon.
ya janyo bargo ya rufe ta daga kafafunta z
uwa kugun ta.
sannan yajanyo towel d'in ya zaro shi daga cikin blanket d'in, ya d'an zamo bargon kasa kad'an dai-dai in da zai mata allurar yana luma allurar da sauri ya d'auke kai.
Ajiyan zuciya ta sauke sanda allurar ya shige ta, a hankali yake matsa
ruwan allurar a jikin ta.
zabura tayi dai-dai san da ya zaro shi, ya d'au cup da yagani kan bedside da ruwa a ciki ya tsiyaya a tafin hannunsa ya wasa mata a fuska.
dogon numfashi ta sauke,
ta kuma zabura tare da ware idanunta, suka sauka kanshi.
cikin ha
rhad'a kalmomi ta ce
"Kar..kar...kayimin allura."
tana fad'in haka jikin ta ya sake gaba d'aya bacci ya d'auketa cikin yanayin da take ciki.
ya juya da sauri yabar d'akin.
Sanyin asuba ne ya farkar da ita tayi mika gami da salati a hankali ta mike zaune
tana mussike idanunta.
a sannu ta zamo bakin gado.
ta na saka kafafunta kasa ta tuna da kamar wani abu ya faru.
da sauri ta ware idanunta tana rarraba ido cikin d'akin,
d'akin fess babu komai. shiru tayi tana juya abun cikin ranta.
tabbas wani abu ya faru
taga Zaraddin ya shigo d'akin nan, har yayi mata maganganu, daga nan kuma wuta ya d'auke wani ya shigo, taji ihun Zaraddin takuma ji alamun ana dukan sa.
daga baya wuta ya kawo taga jini a d'akin.
tana ta son tuna abun da ya faru bayan nan, amma duk iya tu
nanin ta nan ya tsaya.
ido ta dad'a warowa cikin d'akin babu jini hasali ma fess ya ke.
kai ta girgiza a fili ta furta
"Ko mafarki ne?."
sai kuma ta kwab'e fuska
"Mafarki ne ma me zai kawo Ya Zaraddin nan."
takuma fad'a
tare da kallon jikinta towel d'in
dai data d'aura jiya ne bayan tayi wanka, ke nan bacci ne ya d'auke ta ke nan har ganin da ta wa Sahab ma a d'akin nan da allura a hannunsa duk mafarki ne?.
takuma kwab'e fuska, mafarkin sam baiyi mata dad'i ba.
ta mike a hankali ta shige bathroom.
sai da
ta yi wanka da ruwa mai zafi dan tana jin jikin nata yana yi mata nauyi.
ta d'auro al'wala ta fito, ta saka kaya sannan ta haye sallaya ta tada sallah.
bayan ta idar tayi azqar, ta kuma kwanciya.
Karar ringing d'in waya ne yata da ita daga baccin da take.
a hankali ta mike zaune tana waige-waigen ta in da sautin ke tashi.
ta janyo wayarta tana mamakin ta yadda akayi sautin wayar nata ya koma haka.
da sauri ta waiga ta gefen da ta ji sautin na tashi.
ta zamo bakin gado ta sunkuya ta in da take jiyo sautin.
wayar ta gani a ta d'an karkashin gado, ta d'auko tana juya shi a hannunta da mamakin me yakawo waya nan.
kiran na yanke wa fuskar wayan ya bayyana, da mamaki take kallon hoton da yake fuskar wayan, yana zaune turawa sun sashi a tsakiya, dukkanin su da sh
igan likitoti.
fuskarsa d'auke da kyakkyawan murmushi mai burgewa.
mamaki yakuma kamata, a hankali abun da ya faru jiya yashiga dawo mata, Zaraddin ya shigo da gaske bayan nan kuma shima Sahab d'in ke nan tagani rike da allura azahiri ba mafarki ba.
to me
ya kawo shi har ya bar wayarsa anan?.
baki ta cuno a kasan ranta ta ce
"Ai Sahab d'in nan mugu ne allura yayi min ina bacci, shiyasa naji nan namin zafi,
alhalin lafiya ta lau."
ta tab'a gefen mazaunan ta.
ta aje wayar ta mike tana tuno kalaman da Zaraddi
n yayi amfani da su a kanta, duk da har yanzu takasa banbance shin hakan yafaru ko mafarki ne,
to in dai mafarki ne to ya akayi wayar Sahab ya shigo d'akin ta.
fuska ta kwab'e jin tunani nason hargisa mata kwakwalwa.
ganin goma saura
ta mike rike da wayar
ta tafi kitchen.
ganin lokaci ya tafi batayi wani breakfast mai wahalaba,
Sudan tea ta girka, sai chips. tana cikin yanka albasan da zata soya kwai wuka ya zarce ya yanke ta.
kara tayi tare da sakin wukan da albasan kasa, tashiga yarfe hannu...
Da shirin
fita ya shigo d'aukar Sudan tea d'in sa, baya yayi tare da leko kitchen d'in kasancewar kofar kitchen d'in a bud'e yake.
idan ta kalli hannun sai taji ya kara zafi, sai yarfe hannu take d'an jinin da yake fita duk ya b'ata mata jiki.
tuni hawaye yacika id
anunta, kad'an ya rage su zubo.
tana d'agowa suka had'a ido, a hankali ta sunkiyar da kanta tare da kwab'e fuska tana mai dad'a yarfe hannun.
kamar zai wuce dinning sai kuma ya juyo ya tako zuwa cikin kitchen d'in.
da d'an sauri ta d'ago tana duban shi, g
anin yana takowa cikin kitchen d'in.
sai kuma ta kuma sunkuyar da kai, san da ya iso in da take.
hannun da tayi yankan ya ruko.
da sauri ta d'ago da idanunta da suka ciko da kwalla sai sheki suke kad'an yarage su zubo.
suka had'a ido, fuskarsa a d'aure.
a
hankali ta kuma sunkuyar da kanta.
sakin hannun nata yayi sannan ya juya ya fita.
bayan sa tabi da kallo tana kuma yarfe hannun, ta jingina da jikin cabinet, tana son yin kuka.
jim kad'an ya dawo har lokacin tana tsaye tana sharar kwalla.
baki ya tab'e ba
iga wani yankan kirki ba sai raki take.
da sauri ta dago jin ya kuma kamo hannunta, taji ya manna mata abu a kan yankan.
'yar karamar kara tayi, ya sake mata hannun, ya juya yafita......!
Aikin da bata karasa ba kenan ta koma d'aki.
mintuna kalilan ta n
imi zafin ta rasa.
Ko da ya fita sashin Daddy ya tafi.
yana zaune suna gaisawa su Ajmaal Shamsuddin da Faisal suka shigo.
a kasan carpet suka zauna, kana suka shiga gaida Daddy.
sannan suka juya ga yayan nasu.
Daddy ya dube su yana fad'in
"Zaraddin yau ma
bai kwana a gida ba ko, na tambaye security sunce min shine kad'ai bai shigo ba."
Shamsuddin ya ce
"Eh Daddy bai kwana ba tun jiya da safe da ya fita bai dawo ba, yana can gurin gantalinsa, Daddy dama nace zan gaya maka har giya ranar yashigo da shi gidan
nan."
Ajmaal yad'an tab'a shi ta kasa kan ya yi shiru, shiko yaci gaba da fad'in.
"Kuma wlh Daddy saran da ya samu yanzu, idan ya tabbatar da kasan ya dawo,
cikin dare yake fita ya tirsasa security sai sun bud'e masa get, sai gari ya waye kafin ya dawo."
D
addy ya yi shiru yana saurarar sa kana ya jinjina kai tare da fad'in
"Allah kashirya Zaraddin daya zamo jarabawa cikin ahali, zansa aje a nemo sa idan ba anyi masa hukunci ba bazai dai na abunda yake ba, daga nan musa ayi ta masa addu'a da saukan alkur'an
i, Allah ya shiryar da shi."
Abdulrahim ya yi kwafa ya mike tare da taune gefen lips d'in sa, yanufi kofa.
Daddy yabi bayan sa da kallo.
su Ajmaal ma suka mike suka fita.
A kusa da sashin Hajiya Ajmaal ya iso shi suka shige sashin nata tare.
in da su Fai
sal kuma suka nufi b'angare iyayen su.
Hajiya na zaune a parlour suka karaso sai da ya fara zama kafin Ajmaal ya zauna.
Hajiya ta bishi da kallo tana fad'in
"Wai kai kam abokin turawa ko yaushe zaka sauya oho, kullum ya kullum fuska turnuke ba'a gane farin
cinka;
ko da yake iyayen ka su suka ja maka, kai kuma gaka mai jin maganar iyaye, bazaka iya tuburewa kace ba haka ba,
sai an karka da ranka anga bayanka,
ko d'iyar sarkin aljanu aka aurama zaka aminta,
bazakayi musuba duk rashin adalcin da aka maka haka
zaka d'auke shi ka aza a kanka,
ba garama uwar taka mutum ta zab'a maka ba, shiko uban ka d'iyar ifiritu ya aura maka,
ina zaka sami farin ciki,
ai saukin ka d'aya ka fito da matar da kake so ni muka nasa dole uban ka ya aura maka ita."
Ajmaal ya ce
"Ke Ha
jiya daga shigowar mutum ko gaisawa ba'ayi ba, kibi ki ishe shi da magana, ai ke ma haka su Daddy suke yi miki biyayya, ke nan shi so kike ya bijire yaki yi masa biyayya,
dan Allah kibar mutane su huta."
"To dun uban ka bazan bar mutanen su huta ba, rashin
hutu na nawa kuma, yawuce wan da ubanku ya d'aura masa, ai nan gaba sarauniyar aljanu zai kuma aura masa, iya shegen banza a hanani magana ga abun maganar,
kai ma in baka maida hankali ba jinnun za'a had'a ka da ita, duk ku taru kuyita kumburi kuna cika k
una batsewa kamar kububuwa." Jamal
"Idan ba a suffar aljanun zasu zo ba me zai hana mu iya zama da su, biyayya ga iyaye kuma ai wajibine, haba ki barmu haka mu huta ko mu tafi mu fasa gaisuwar."
"Yo ku tafin mana mai mugun baki, ana fad'i tashi a kanku id
an aka barku da aljanun zaku iya ne."
"Me zai hanamu iyawa da su, a barmu da su d'in kawai."
Hajiya ta harare shi tana kai loman nama bakin ta.
Ajmaal ya ce "Ke dai kici namar ki, bama Ya Abdulrahim ya ce ba kowani irin nama zaki rika ci ba, kuma ba kullum
zaki rika ci ba, amma kullum duk sanda za'a ganki da kwanon nama a gaban ki."
"Yo in ban da abokin turawa ma ai nama kara lafiya yake."
cewar Hajiya tana kai loman nama bakin ta.
"In ji wa? shi likita ya gaya miki kice ba haka ba."
Ajmaal yayi maganar yan
a rike hab'a.
Hajiya tace
"Ko d'azu ma sai da nasa Kulu ta kamo min tashar da ake saka shirin, haka matar take cin nama kuma da bakin ta tace nama lafiya yake karawa,
itama likita ne yagaya mata."
"Hajiya in ban da abun ki shirin film gaskiya ne, ai ba kom
ai ne ake fad'ar sa kuma ka samu da gaske ne hakan ba, shirin film ne kawai, gara dai ki kiyaye, kafin ki kasa iya tafiya."
da sauri ta ware ido ta dubi Abdulrahim ta ce
"Abokin turawa ba wani da yawa nake ci ba, sai nafi sati banci ba, ai bazai zamo illa
ba ko."
Ajmaal ya yi dariya
"Hajiya anji batu kan lafiyar jiki, ba'a kaunar lafiya ta tab'o, to ai sai ki rika kiyaye wa."
mikewa Abdulrahim yayi cike da kosawa da surutun nasu, yanufi kofar fita.
Hajiya ta bud'e murya tana fad'in
"Kai abokin turawa tafiy
a ma zakayi, ina tambayar ka bazaka bani amsa ba."
bai ko juyo ba yayi gaba abinsa.
ta kalli Ajmaal tana fad'in
"Kaga wannan d'an'uwan naka ban tab'a ganin mara alkibla irin sa ba, bazaka tab'a gane me ya dosa ba,
dan Allah kaje ka tambaya min shi ka gano
min bazan kasa iya tafiya nan gaba bako."
Ajmaal ya mike yana dariya gaba d'aya Hajiya ta rud'e, in dai lafiya ce ba'a kaunar ya tab'o..
Bayan sallan la'asar Feeryal ta foto zata shiga kitchen.
Kuraiba ta shigo tana yi mata kallon sama da kasa.
Feeryal ta
ja ta tsaya a kofar kitchen.
Kuraiba tashiga karewa parlour'n kallo tana takowa gami da wasa mata harara.
tana kuma fad'in
"Sati guda dama na d'iba naga wani irin shiri kika shigo da shi, sai kuma naga akasin haka ashe ma fanko ne."
ta sheke da dariya ta t
afa hannu kana ta ci gaba da fad'in
"Sai gashi har kwanin ki goma yau da tare wa, ban tab'a ganin yakai minti 10 da ke ba,
kash ayya ashe dai duk buge ne sorry fa."
d'akunan cikin parlour'n tashiga bud'e wa tana lekawa sai da ta leka duka d'akunan hud'u, k
o ina har kitchen da store kana ta fito tana tafa hannu da fad'in
"Da kyau mana ko ni da akasan waye ubana kayan d'aki na bai kai wannan ba, sai ke da ba'a san asalinki ba, wai wannan shine duka kayanki,
saboda karya, ko da shike aiki da asiri meye baza'a
iya ba."
Feeryal na tsaye tana kallon ta bata tanka mata ba.
ta tako gabanta ta dafa kafad'arta, tayi mata wani kallo tare da yamutsa fuska sannan ta saki dariyar makirci ta ce
"Laa karki damu da wannan fa ai ke kanwata ta ce tun da muna auren miji d'ay
a ai munza 'yan uwa, duk mun zamo abu guda, naga cucumber a cikin d'in nan naki bari na d'auka amma fa babba zan d'auka,
kin san laulayin ciki tun da yayi min cikin nan bani da abincin ci sai cucumber."
ta shiga kitchen d'in ta zab'o babba ta fito ta d'aga
mata hannu ta ce
"Bye."
Feeryal na tsaye har sai da taga ficewar ta kafin ta shige kitchen.
Dad ne ya shigo side d'in sa yana kwalawa Mom kira.
da sauri ta fito jin kiran da
yake kwad'a mata.
ya dube ta yana fad'in
"Kin gani yaron nan Zaraddin
bai kwa
na a gida ba, yana so ya jamin abun magana, gashi Yaya Abubakar ya tare ni yana
tambaya ta ina yaje bai kwana a gida ba?."
Mom ta yamutsa fuska ta ce
"Sai kace an mai da Zaraddin d'in d'an tayi da beyi kwana
d'aya a gida ba, a taru ayi ta magana, ansan m
atasa da wannan
yanzu haka suna tare da
abokansa ne, zaka samu gidan
wani abokin sa yaje ya kwana,
wannan ai ba sabon abu bane a gun matasa, aje gidan aboki a
kwana, haba dan Allah duk kabi ka tada hankalin ka kawai daga
ya yi magana."
Dad ya zauna ya
na fad'in
"Wannan yaro duk abun da zan
fad'a masa bazai ji ba,
ya natsu yajira lokacin da
komai zai dawo karkashin ikon
mu in yaso duk abunda zaiyi ya yi amma ya tsaya dole sai ya b'ata min shiri, zamu gamu da shi bazai dawo ba duk in da
yaje ai zai da
wo ai,
wai yaron nan shaye-shayen
nasa yakai har da giya yake
shigowa gidan nan."
Mom ta ce
"Narasa me Zaraddin ya tsare
wa mutane ayi ta maganar shi
kamar shine kad'ai mai abun
fad'a, ni dai kar a tambad'a
min yaro da mugun baki."
Mom tayi ta suruta
i da
zage-zage.
Feeryal ne tsaye cikin
parlour'n ta tana gyara shi.
da sauri ta waigo jin an turo
kofa.
Kuraiba ce ta shigo tana wani taku ta iso cikin parlour'n.
ta zube kan kujera tare da fad'i
"Wash Allah wlh na gaji."
sai kuma ta kalli Feeryal ta c
e
"Barka dai amarya ana ta gyara ne haka, wlh duk a gajiye nake daren jiya ko rumtswa Mijin
Kuraiba bai barni nayi ba, oh
sorry Abdulrahim mai gidan namu, tun d'azu naso shigowa
mud'an yi hira baccin gajiya
ya kamani dole na kwanta,
to ykk."
tageren mur
mushi tayi sannan
ta ce
"Lafiya lau."
Kuraiba ta mike tana cewa
"Um bari na barki kiyi aikin
ki zan shigo muyi hira sanda
bakya komai."
a bakin kofa sukayi kiliya da
Miemie zata shigo.
kallon banza Miemie tayi mata
kamar yadda itama Kuraiba tayi
mata
.
Miemie ta karaso ciki da sauri, ta harari Feeryal ta
ce
"Me wannan tazo yi a nan?."
Feeryal ta ce "Nima ban sani
ba yanzu shigowar ta kuma ta
fita, amma dai ce min tayi hira taso muyi bacci ya kamata
bata zo ba sai yanzu, amma gobe zata zo."
a hatsa
le Miemie ta ce
"Wannan ba karamar munafuka
bace, ni haka kawai bana son
ta, idan kika sake mata sai
tayi shanya a