Showing 12001 words to 15000 words out of 95068 words

Chapter 5 - FEERYAL BOOK3 COMPLETE

saurin ruko hannunta tana fad'in

"Ke Feeryal me ya fito dake ke da jiy

a aka kaiki? maza koma d'akin ki, kar ki sake fitowa sai in shi yace ki fito."

baki takuma turowa cikin yanayin ta gami da shagwab'a ta ce

"Ammie ni dai so nake na ganki, ni dai zan zauna a nan kawai, ni kad'ai babu kowa tsoro nake ji."

Aunty ta d'anyi jim

sai kuma ta saki murmushi tana cewa

"In banda abin ki Feeryal nima bakiga ni kad'ai ce a nan side d'ina ba, haka nayi ta rayuwa a lokacin da babu ke bakima zo duniyar ba, da haka zaki saba har ke ma ki haifo 'yar ki, ko 'yanmatan Ammie."

ta karasa maganar

da jan kumatun ta.

baki ta kuma cunowa tana make kafad'a.

Aunty ta janyo hannunta

"Zo ki koma d'akin ki anjima Miemie zatazo ta tayaki hira,

basai kin fito ba ma, ke baki san kin girma ba yanzu,

yanzu duk abin da zaki aikata a d'akin ki na alkhairi ninki

n lada za'a rubuta miki,

lallai zaki sami lada da yawa amma zamu raba ladan ne ko, ko rowa zakiyi min?."

ta gyad'a kai tana sakin kyakkyawar murmushin ta,

Aunty ta yi murmushi itama.

haka tayi ta lallab'in ta gami da 'yan dabaru, har ta rakata kusa da sid

e d'in ta.

tana tsaye sai da taga shigarta kafin ta juya ta koma nata side d'in...

A hankali take takowa tana wasa da bakin mayafin ta.

kamar ance ta d'ago karaf suka had'a ido da shi yana tsaye cikin garden, rike da mug yayin da d'aya hannunsa ke zure c

ikin aljuhun sa.

da sauri ta janye idanunta takara sauri,

ta shige ciki.

a hankali yakai mug d'in bakin sa ya kurb'i Sudan tea d'in sa, kana ya soma takowa ya nufi gefen sa.

Tana shiga direct bedroom ta shige.

ido ta waro cike da murna take kallon wad'an

da suke cikin d'akin, tayi ihun murna tare da rungume su tana tsallen murna.

Chuchu da Chulu suna tayi mata dariya.

fuska ta d'an kwab'e ta cuno baki tare da marairaice murya tana cewa

"Dama kunsan ina nan ne, ni dai bana son zaman nan nafi son zama gun Am

mie na."

Chuchu ta ce

"Ai nan ma da dad'in zama gashi komai na gurin yana da kyau."

fuska ta kuma kwab'ewa ta ce

"Ni dai nafi son zama gun Ammie na,

bana son zama side d'in Sahab d'in nan, kawai bana son nakasa yiwa Daddy biyayya har ya yi fushi da ni ne."

Chulu ta ce

"Ai kuwa idan baki zauna ba bazai ji dad'i ba, ba gamu ba zamu rika zuwa muna tayaki hira anan d'in."

"Kun tabbata?."

ta fad'a tana d'aura yatsar ta kan bakin ta.

duk suka amsa da "Eh mun tabbata."

suka zauna suka soma hira, nan da nan taji k

ad'aici ya gusa a gareta...

wunin ranar da su Chuchu tayi,

abincin rana da dare duk Aunty ke turo Baba Rabi da su.

washegari kamar jiya yau ma Aunty takuma aiko mata da breakfast.

Baba Rabi ta shirya kulolin kan dinning, ta kwashi na jiya ta tafi da su.

F

eeryal bata fito da wuri ba bayan ta tashi a bacci sai da ta gyara bedroom zuwa bathroom. kafin tayi wanka ta shirya ta fito.

tana isa cikin parlour da sauri ta waiga can saman dinnin jin karar fad'uwar abu daga gurin.

shi tagani sunkiye yana kokarin d'auk

ar plt d'in da ya fad'i kasa.

kai ta kawar da d'an sauri dan bata sammaci ganin sa a gunba.

tsayuwa ta d'an gyara jin takunsa yana matsowa cikin parlour'n.

tana d'agowa ta gansa rike da plt a hannunsa guda d'aya hannun nasa kuma yana rike da Mug.

kai ta su

nkuyar tana wasa da 'yan yatsunta.

wuceta yayi ya nufi ta kofar da zai sadashi da gefen sa dake ta cikin parlour'n nata.

tabi bayansa da kallo har ya b'acewa ganin ta.

sai kuma ta cuno baki gaba sannan ta juya ta wuce dinning.

tana zama Miemie ta turo kofa

ta shigo.

tun daga bakin kofa Miemie ta soma yi mata kirari.

"Kaga a marya a gidan AA FIYA, ke kad'an ki kin zame musu kashin kifi a wuya, kinyi gaba kin bar karnuka suna ta haushi a baya."

Feeryal ta rike hab'a tana cewa

"Oh ni Miemie Allah ki rabani, ai

babu ruwana na da ke tun jiya baki nime ni ba."

tayi maganar tana cuno baki gaba.

Miemie ta karaso tana fad'in

"Ke yanzu waya gaya miki ana zuwa gidan amare a washegarin ranar da aka kaisu, ai sai kaje ka gane wa idanunka damuwa, gara dai ka bari ayi kwan

a biyu zuwa sati, yanzu ma kawai nayi missing naki ne da yawa yasa nazo, amma sati nayi niyyar kiyi kafin nazo."

takai hannu ta toshe bakin ta tana cigaba da fad'in

"Um Allah dai yasa ba Ya Abdulrahim ango, kar yajini yayi ball da ni waje."

"Ai kuwa yana n

an."

Feeryal ta fad'a tana waro ido.

Miemie ta juya da sauri tana fad'in

"Nashiga uku bari na tsere kafin ya fito."

dariya tayi ta ce

"Ke karya ne me zai zaunar da shi a nan yanzu dai ya d'ibi abinci yafita."

Miemie ta dawo tana cewa

"Na isa yanzu na karbi

dukan da ban shirya masa ba, Murad na zuwa anjima yazo ya same ni da kumburarren jiki."

taja kujerar dinnin ta zauna ta dubi Feeryal data soma cin cake d'in ta tana yiwa Miemie dariya ta ce

"Ban gane ba kamar naji kin ce ya d'ibi abinci ya fita,

yaje ina

dan yau dai weekend ba aiki bare nace asibiti yaje."

Feeryal takai cake bakin ta na tauna ta ce

"Ina zan sani nima ganin sa nayi a dinning d'in dana fito parlour'n, yana d'iba kuma yayi tafiyarsa."

Miemie ta ce

"Ba dai anan ya kwana ba ke nan?."

Feeryal t

a waro ido kad'an ta shake da cake tayi tagwayen tari tare da cewa

"Ya kwana anan kuma Miemie?."

"Dalla jita daga magana ta rud'e shine me, bazai kwana anan ba akan ke ba matarsa bace, ki zauna noke-noke karki san yadda zakiyi ki janyo mijin ki gareki ba,

waya gaya miki yanzu ana haka ai duk wani kunya da sauransu ya kare da zallar kirsa zaki janyo mijinki, ki zauna dai garin kallon ruwa waccan kwad'on matar tasa tayi miki kafa."

Miemie ta karasa maganar da yamutsa fuska.

Feeryal ta bita da kallon mamaki,

sai kuma ta girgiza kai tare da yin murmushi ta ce

"Miemie Allah bazan tab'a iyawa ba Sahab ya zauna a inda yake nima na zauan a in da nake, nayiwa Ammie'na alkarin zan zauna dan na cikawa Daddy burinsa, amma bazan tab'a iya abun da kike nufi ba."

Miemie t

a mara baki ta ce

"Ai sai kiyi ta rashin iyawa, zaki sha kallo idan akayi auren mu da Murad d'ina, kizo gidan mu kiga yadda ake soyayya."

dariya ita dai ta bita da shi...

Abdulrahim na shiga parlour'n sa, Kuraiba na shigowa daga kofar gefen ta da ke ta ci

kin parlor'n nasa.

ya nima guri ya zauna kan kujera, tare da d'aura plt da Mug d'in kan table.

Kuraiba tasoma takowa tana yamutsa fuska ta tako gabansa ta tsaya tarike kugu tana fad'in

"Kamar Mommy ta sani tace narika sa ido sosai kan abincin ka, dan itam

a wancan uwar goyon ta, da barbad'en magani cikin abinci, ta gama mallake Daddy, shine take biyoka da abinci har nan ai ina gani jiya ankawo yau ma an kawo, to gara na sanar wa Mommy tun wuri kafin kai ma a gama da kai,

dama yaushe zaka so cin ko wani abin

ci bayan ga inda ake dafawa da barbad'en magani, ai dole kaji yafi ko wanne dad'i, ga abincin da za'a kyamata nan bana masu aiki ba."

wani kallo ya d'ago ya watsa mata, batare da ya yi magana ba ya gyara zaman sa ya soma cin abincin a hankali.

wannan kallo

da ya mata tasan gargad'i ne dan haka taja kafarta tana mita takoma gefen ta.

Miemie ta mike tana fad'in

"Ni bari na tafi, ina gaya miki kisan me kike kisan wani irin miji kike aure na mijin da ba kowata mace ke samin irin sa ba,

dan wlh ko Kuraiba aro t

a samu dan batayi kala da matar auren sa ba,

irin ki d'in ce dai ta dace da shi wlh mata ribibinsa suke, gara ki janyo kayanki ki killace sa, in kikayi wasa kuma kina ji kina gani wata zatayi miki huff da shi."

dariya maganar ta baiwa Feeryal.

Miemie ta ce

"Au dariya ma kike ko zakiyi bayani ne, ke wlh bansan irin ki ba ace ni ce a matsayin ki, ai wlh za'a sha kallo."

baki ta tab'e ta ce

"Wai tafi zakiyi Miemie tun yanzu?."

"Tafiya zan dan bazan iya ganin abin haushi ba."

"Dan Allah ki zauna mu kwana."

ido

Miemie ta waro

"Wa na kwana anan rufamin asiri, bana ma so muyi ido hud'u da Ya Abdulrahim dan jiya ya yi wa su Ameerah kashedin shigowa side d'in sa,

ai bana fatan ma mu gamu, zan dai zo gobe."

ta juya da sauri tayi waje.

Feeryal tabi bayanta da kallo kam

ar zatayi kuka, ta taka zuwa d'aki a hankali.

tana kwanciya su Chuchu suka zo.

Da daddare tana d'aki taji motsi koda ta leko shi ta gani kan dinning yana serving

ta koma tayi kwanciyarta.

washegari.

batayi nisan bacci ba 7 ta fito d'aukar Yogurt da cake.

tana daf da karasawa dinning ya shigo.

da alama shirin fita yayi kuma sauri yake.

yana rataye da jakar aikin sa, yana tafe yana duba agogon hannunsa.

tsayuwa tayi bata karasa ba shi ya wuce, da d'an sauri ya d'au Food flask d'aya da d'an karamin flask ma

i d'auke da Sudan tea.

yazo zai gota ta a hankali cikin yanayin ta mai samyi ta ce

"Ina kwana."

picking call din da ya shigo wayarsa ya yi ba tare da taji ya amsa gaisuwar nata ba.

baki ta tab'e ta karasa dinning ta d'au abin da zata d'auka ta koma ciki.

Kuraiba data kasa bacci sai juyi take.

tana jin wani irin fitinannen sha'awa na taso mata.

sakamakon tadawa junan su hankali da suka gama ta cikin waya da mutanen ta.

wani dogon mika tayi ta mike n matse idanunta, ta ja kafarta ta fito.

ta nufi d'akin Abdu

lrahim duk da bata da tabbacin samin sa.

yana cikin bedroom d'in sa yana shirin kwanciya.

taji dad'in ganin sa.

ta karaso da sauri ta rungume shi ta baya.

ta saki kukan makirci tana fad'in

"Mijin Kuraiba cikina ciwo sosai ina jin yana harbamin ta kasan mar

ata, ash kad'an daddanna min idan ina tab'awa ina jin sassauci."

hannunta ya yi saurin rukowa da take shirin turashi cikin wandon sa.

ya d'an tureta gefe, da sauri takoma jikinsa tana kuma narke masa.

a rud'i cikin matukar jin masifar sha'awa ta ce

"Cikin

nan dai naka ne kayi min abin da nake so dan gujewa asarar sa, kai likita ne ai kasan duk abin da mai ciki take so yimata ake."

janye jikin sa yayi ya nuna mata kofa ya ce

"Fita!."

kamar zata ihu ta juya tana fad'in

"Kai da yin ciki ni da wahala, dan naji

nace zan zauna duk da

bawani kaini har geji kake ba,

ko awa 3 baka iya kaiwa,

sai me in ka kore ni dan zatazo d'akin ka, girman abin ne kawai ba aiki, 'yar da ta saba da maza ina zata iya jurewa ma."

tsaki yaja ya rufo kofarsa..

Sati guda Aunty ta d'auka

tana aiko musu da abinci.

safe da rana da yamma,

kullum kuwa zai shigo da kansa ya d'ibi abin da yake bukata.

abin da ta lura yana matukar son Sudan tea dan flask d'in gaba d'aya yake d'auka.

sai dare ya dawo da shi yakuma d'aukar wani da Aunty ta sa a ka

wo.

wani lokacin har ya fita tana jin motsin sa bazata fitoba,

har sai ya gama ya fita.

wani lokacin kuma suyi kicib'us a parlour zata tsaya sai ya d'au abin da zai d'auka yafita kafin ta wuce tayi abinda zatayi itama.

ranar da ta cika satin kuwa Aunty t

a kira Feeryal a waya ta video call, ta d'aga cikin yanayin ta mai sanyi da muryarta mai fita da yanayin shagwab'a, ta soma gaida Ammie'n tana,

yayin da ta sako shagwab'ar a zahiri irin yadda d'a yake idan yaga uwansa.

daga cikin wayar Aunty ta ce

"Feeryal

kuna lafiya dai ko?."

fuska ta marairai ce cikin yanayin ta mai sanyi ta ce

"Ammie ba kin ce kar nazo ba, kuma ni ina so na ganki."

murmushi Aunty tayi ta ce

"To Feeryal ba gani muna ganin juna ba, karki fito batare da izinin mijin ki ba kinji."

rau-rau t

ayi da ido.

Aunty ta kuma murmushi mai sauti ta ce

"Kina jina ko Feeryal?."

baki ta turo tare da gyad'a kai.

Aunty ta ce

"Amsa mana d'iyar kirki."

ta ce

"Ina ji Ammie."

"Yauwa bacci mai tsawo ya kare daga kan yau, dan daga yau na sake miki ladarki, ke zaki

cigaba da hidima da gidan ki, idan gari ya waye banda nisan bacci Feeryal ki tabbatar da kin tashi kinyi breakfast kin aje a kan dinning, abincin dare da rana kar ki bari ko d'aya ya wuce ki, ba kinga yadda nake yi ba ko Daddy baya nan side d'ina bana tab

'a yanke yin girki, to kar ki sake kiyi wasa da samin wannan ladar ko da wani bai ciba, ke kika ci zaki sami lada,

karkiyi wasa da gyaran sashin ki, nasan duk abin da na fad'a miki kin iya dan duk na koyar da ke su,

yanzu ne zaki bud'e iyawar taki kiyi amf

ani da shi a gidan ki, kada kiyi wasa Feeryal ladabi da biyayya girki gami da tsafta shine mace, dan haka ki kula,

a kwai komai na amfanin girki a kitchen da store d'in ki,

ki d'aura aniyar farawa da bakisan ranar dainawa ba."

kai ta jinjina.

Aunty tayi mu

rmurshi ta ce

"Ko so kike naci gaba da kwasar ladan duka?."

kai ta girgiza ita ma tana maida mata murmushin.

"To ayi rige-rigen tara lada aga wa zai riga tarawa da yawa."

Aunty tayi ta mata nasiha da jan hankali cikin dabara ta yadda zaifi yin tasiri a gar

eta a 'yan shekarun ta, daga bisani sukayi sallama......!

"Babu editing ban sami damar yi ba zaku had'u da kura-kurai da yawa*

Washegari karfe 10 na safe kiran Aunty yashigo wayan Feeryal

da ke bacci. sai da tayi mata miss call 5 kafin ta farka.

Aunt

y tana jin muryarta cike da bacci ta ce

"Feeryal bacci kike kar dai a ce baki tashi ba?."

hannu takai ta mussuke idanunta cikin muryar bacci ta ce

"Um."

Aunty ta ce "Feeryal bacci har karfe 10, me kike samu cikin baccin da baki tashi kin girkawa mijinki ab

in kari ba?

kin sane da cewa baya cin duk wani abincin da zai fito daga hannun masu aiki, haka kikasa ya tafi gurin aiki batare da ya karya ko ya tafi da abin karin ya yi breakfast d'in a can ba?

wani dad'i zakiji mijinki ya fita tare da yunwa,

haka kikaga

nake yi? ko sau d'aya ban tab'a hutu wajen yiwa Daddy girkiba, dan nasan babu in da zai je yaci sai a nan, Feeryal karki sake haka ina jiya mukayi maganar nan da ke, ki aje wannan cikin kwakwalwarki shine abu na farko kuma na gaba-gaba a cikin gidan ki da

zaki fara d'aukarsa da muhimmanci,

kar ki sake yin sake wajen wasa da yin girki, kina jin abinda nake fad'a ko?."

kai ta gyad'a tare da cuno baki ta ce

"Eh."

Aunty ta ce "Maza tashi kije ki kula da gidan ki, kar ki sake bari hakan ta faru,

karki yi sake

wajen shiga kitchen kar kice dan jiya kinyi yau kinyi gobe bazakiyi ba,

kiyi girki ko da wani bazai ci ba,

Feeryal Abdulrahim gadon Daddy yayi kamar yadda shima Daddy'n ya gado mahaifin sa,

basa cin abinci wata idan har sunan ta 'yar aiki ce,

da jajircewa

wajen ganin Daddy bai wahala wajen samin abinda yake so daga abinci ba ake cewa na mallake sa, kar kiyi wasa ki kula sosai."

kai ta kuma gyad'awa kamar tana gaban ta kana ta mike sanda Aunty ta kashe wayar.

Kallon agogo tayi taga goma har ya gota, ta shi

ga bayi ta wanko bakinta ta fito ta nufi parlour da kayan baccin jikin ta.

tun da tazo bata tab'a shiga kitchen ba bata ma san ta ina kitchen d'ina yake ba, nan ta soma niman ta in da yake,

nan ta gano wasu bedroom na alfarma guda uku cikin parlour, wata k

ofar da ke kusa da dinning ta nufa ta bud'e nan taga ashe shine kitchen d'in.

kitchen mai girman gaske da ya tara kayan da duk ake bukata na amfani a kitchen, har da wanda ma bata san da su ba, sai da da yawa ko mai a rubuce yake.

daga cikin kitchen d'in t

aga wata kofa, nan ta bud'e taga makeken store ne, shake da kayan abinci kala-kala.

ta d'ibi duk abin da take bukata ta dawo kitchen.

ta bud'e freezer tad'au kaza guda d'aya da suke cike ciki a gyare duk sunyi kankara.

ta saka a roba ta zuba masa ruwan zaf

i da ta d'aura kan gas.

ta matso da fulawan da ta d'ibo ta soma sarrafashi cikin kankanin lokaci ta had'a cake d'in ta na musamman, ta saka shi a oven.

bayan kankaran jikin kazar nan ya narke ta yayayyanka ta wanke shi saf ta zuba a tukunya bayan ta d'aura

a gas.

ta zuba mishi kayan kamshi da na d'and'ano gami

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login