Showing 54001 words to 57000 words out of 95068 words

Chapter 19 - FEERYAL BOOK3 COMPLETE

ba yasan wannan halin nasa tun yana d'an karami,

idan yana cikin b'acin rai haka zufa zatayi ta karyo masa daga cikin sumar kansa yana gangara fuska

rsa, jijiyoyin jikinsa zasu mike rad'a-rad'a.

sai dai na yau yafi na duk sauran lokutan dan kuwa yau karkashin jajayen idanunsa sai da sukayi damshi alamun ruwa nason fita daga cikin su.

Daddy ya damke hannunsa da kyau ya dube shi yana fad'in

"Ka yarda da

Allah kayi imani da kaddara mai kyau ko mara kyau, muje gida Abdulrahim."

ya janyo hannunsa motar Daddy suka shiga shi da Daddy gidan baya,

direba ya ja su.

Ajmaal ya shiga motarsa da suka zo da shi yabi bayan su suka nufo gida.

Su Shamsuddin da Faisal d

a suka d'auko hanyar zuwa, bayan sunyi waya da Ajmaal ya sanar musu abun da ke faruwa, kafin su fito suka sanar a gidan, tuni gidan ya d'auki labarin.

suna hanya suka kuma kiransa ya yi musu kwatance, ya ce su juya gida gasunan suma dawowa.

Wani irin gud'

a Umma Karima ta rangad'aga, tayi tsalle ta tafa hannaye, tamkar anyi mata albishir da aljanna.

"Hajiya Halima kinyi abun da ya dace, da baki farka ba da ni zan mike dan ni bana bacci."

Bilkisu data kawo mata labarin ta ce

"Umma wai murna kike wlh ni jikin

a yayi sanyi, ko da bani son Feeryal amma 'ya'yan nan na Ya Abdulrahim ne shi kuma yayan mu ne,

ai bazai so ace yau ayi masa haihuwa a yau d'in kuma yana ji yana gani akashe masa yara ba,

gaskiya Mommy bata kyauta ba, kashe rai ai musifa ce, ranma na jarir

ai wanda yau aka haifesu basu d'auki hakkin kowa ba haba dan Allah."

Bilkisu tayi waje tana Kuma fad'in rashin kyautawar Mommy.

Tun da suka hau hanya Daddy ke bubbuga bayan hannunsa da hannun nasa ke rike a hannun Daddy alamun rarrashi, duk da shima yana

jin kuna da b'acin ran a tare da shi.

har suka karaso gida.

suka sauko a motar ya zame jiki ya wuce side d'in sa.

Daddy ya nufi sashin Mommy rai b'ace, a tsaye ya tadda ita a parlour Mommy tana ganin sa ta b'ata rai.

tana fad'in

"Haka kawai a dukeka a hana

ka kuka, a wani dalili aljanu suje can su karata."

bata yi aune ba yana karasowa ya wanke mata mari cikin kakkausar murya ya ce

"Allah wadai da hali irin naki Halima wlh nayi nadamar kasancewar ki a matsayin uwar 'ya'yana,

kije na sake ki, kuma bazan kyale

ki ba sai nayi shari'a da ke akan jikoki na da kika kashe!."

muryar Hajiya suka jiyo a bayan su tana fad'in

"Mai da ita yanzu nan maza ka mai da ita, in dai ina numfashi baka isa ka saki Halima ba, 'yar uwar taka ko me tayi maka banyar da ka sake ta ba,

y

ara kuma sunzo kan lokaci ne dama ba masu rayuwa bane su, ka mai da ita na ce ko ka biyani nono na!."

Hajiya ta karaso tana kuma fad'in

"Ka mai da ita nace."

Daddy ya ce "Amma Hajiya."

da sauri Hajiya ta tari numfashin sa

"Ka mai da ita na ce, duk shari'a

r da zakayi da ita kuyi tana d'akin ta."

Daddy ya ciza yatsa tare da fad'in

"Na mai da ke amma kar ki sake kizo in da nake."

ya juya yafita cikin matukar b'acin rai.

Mommy dake dafe da kuncinta da alamun jikinta ya yi sanyi.

Hajiya ta dube ta ta ce

"Yanzu

ke Halima bakiji ko d'ar ba, da har zaki iya kashe kikokinki da hannunki?

yau ko bare ai bazata aikata hakan ba,

bare ke da kike jinin Abubakar,

ai 'yar nunel ta nuna basai an fad'a ba, da ka kalli yarannan kallo d'aya kaga Abokin turawa,

ko makaho ya sha

fa yasan 'ya'yan nan na abokin turawa ne,

yo zance ya kare tun da har yabi dare yaje ya had'a shinfid'a da ita,

ai dole mu karb'i 'ya'yan nan, bare ga babban shaida da sukayi kama da uban su,

wannan ai niman jawa mutane magana ne."

Hajiya tayi waje tana bo

mbomi.

Mommy ta zauna kan kujera jiki a sanyaye.

Daddy na fita asibiti ya tafi.

Aunty na tsaye a kan kafafunta hankalin ta a matukar tashe.

tun da tayi waya da shi ta sanar masa, Mommy ta d'auki yaran daga baya tana ta kiransa baya d'aga wayar.

tayi ta ki

ran Ajmaal shima haka.

Sumayya da Miemie hankalinsu ya kasa kwanciya suka nufo gida,

kasancewar babu motar gida dole taxi suka bi, suka b'ata lokaci a hanya.

Feeryal na kwance tayi shiru, Aunty na tsaye da kafafunta.

Daddy ya turo kofar da sallama,

kallo d

'aya Aunty ta masa gaban kirjinta ya yanke ya fad'i.

tafi kowa sanin halin mijinta,

kallo d'aya take masa ta karanci farinciki ko bakinciki ke tare da shi.

da sauri Aunty ta nufo shi tun kafin ya karaso, ta ruko hannayen sa hankali a bala'in tashe take fad

'in

"Daddy ina yaran suke ina ta kaisu?."

Daddy ya rumtse idanunsa yana jin zafi cikin zuciyarsa.

Aunty ta kuma jijjiga shi murya na rawa ta ce

"Daddy kayi magana, dan Allah ina ta kai su, dan Allah a dawo mana da su, ko nono basu shaba, a kawo mana su ta

basu nono kar yunwa ya dame su."

Daddy ya kifa kansa a jikin kafad'arta.

duk yadda yaso ya daure ya gagara, sai kawai ya rushe da kuka mai cike da kuna da matukar tausayin su.

sai kawai itama ta fashe da kukan da tun d'azu take ta danne shi.

Daddy yayi sau

rin d'ago kansa a kafad'ar ta ya rungumeta.

yana bubbuga bayanta tare da fad'in

"Kiyi hakuri Fad'imatu nayi duk iya yina yau na gaza."

Aunty ta d'ago da sauri ta ce

"Daddy me kake so ka ce."

"Nagaza taimakon jikoki na Halima ta jefa su a ruwa ta kashesu."

ya yi saurin sakin Aunty ya jingina da jikin garu ya dafe kirjinsa yana tari, da sauke numfashi da sauri-sauri.

wani irin rumtse ido Feeryal tayi, jin kanta ya yi wani irin sarawa.

wasu siraran hawaye suka gangaro gefen idanunta.

Aunty da gaba d'aya ta fir

gice ta d'aura hannu a ka tana salati da fad'in

"Me sukayi miki Hajiya Halima idan ku bakwason su, kun wadata da 'ya'ya mu bamu samu ba, yanzu ke nan Allah ya bamu, mu muna son su."

gaba d'aya ta daburce cikin d'akin tana ta kaikawo da sambatu gwanin ban t

ausayi.

Daddy na dafe da kirjinsa ya mika d'aya hannunsa ya kamo nata sannan ya furta

"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un."

ai ko da sauri ta cab'e kalmar da furtashi ya samar mata da nutsuwar da har ta juya ga Feeryal dan son ganin halin da take ciki.

ta

karaso bakin gadon da sauri ganin hawaye na gangara a fuskarta, ta shafa kanta tana cewa

"Kiyi hakuri, ita wannan kalmar bayan an cutar da kai ake gaya maka ita, idan kayi hakurin kuma zakaga ribar yin ta Allah yana bayan gaskiya."

Feeryal ta bud'e idanunt

a a hankali, idanunta ya sauka kan inda Daddy yake,

ta d'aga hannu ta nuna inda yake tana cewa

"Ammie Daddy."

da sauri Aunty ta juya numfashin sa na dad'a sama-sama idanunsa yana yin sama-sama.

da sauri Aunty tayi gurin sa ta rike shi tana kwad'awa likita

da nurse's kira.

a guje suka shigo jin irin kiran bana kwanciyar hankali bane.

Aunty ta ce "Ku taimake ni ciwonsa ya tashi."

a ka kwashesa akayi da shi wani room d'in.

ranar Aunty taga tashin hankali mara misaltuwa.

ana shiga da shi Ajmaal na isowa, shi y

a zauna a gunshi ita kuma ta komo gun Feeryal.

tana kaiwa da kawowa sakanin room d'in da Feeryal take da na Daddy......!

Cikin dare Daddy ya dawo hayyacin sa.

washegari da safe ya bukaci a sallame sa ya

koma gida.

Bappa Salihu da asuban fari ya baro Yelw

an Shendam ya shigo garin Jos.

yabi jirjin da ya taso daga Jos ya sauka a airport na Lagos da karfe 9 dai-dai, na safiya.

bai fad'awa kowa zai taso ba shiyasa mota bata je domin tarar sa ba,

taxi ya shiga ya taho AA FIYA STREET.

yana isa ya buga get securi

ty suka leko ganin shine sukayi hanzarin bud'e masa karamar kofa ya shiga, suna yi masa sannu da zuwa.

sama-sama ya amsa musu ya shige ciki.

da su Nabila da Sahala da Ameerah suka fara cinkaro sun fito daga sashin Daddy.

shiko kai tsaye sashin Mommy ya wuc

e.

Ameerah tayi gudu taje ta gayawa Hajiya ga Bappa Salihu ya zo.

tun daga bakin kofar side d'in Mommy Bappa Salihu yake kwad'a mata kira har ya shigo parlour'n ta yana fad'in

"Ina kike mutumiyar banza shashasha wacce ta girma har yau batasan ciwon kanta b

a."

Mommy ta fito daga cikin bedroom nata jiki na rawa

Bappa Salihu ya nufo ta ya na cigaba da fad'in

"Halima ke d'in nan da a asibiti aka haife ki da wlh cewa zanyi an canza min 'ya aka bani wacce zata kashe ni,

ban haifi 'yar da zata zo ta zame min fitin

a cikin ahali ba, gara tun marmaza na cire ki cikin 'ya'ya na tun kafin ki hallaka min ahali,

mutumiyar banza ni ban haifi makashiya ba!."

Bappa Salihu ya rufe ta da duka da hannu bibbiyu yana cigaba da fad'in

"Bani ba ke Halima kada ki sake ki d'aga ido k

i kalleni a matsayin mahaifinki,

ke baki isa ki zame mana fitina cikin ahali ba, meye amfanin rayuwar ki ke baki cancanci zama uwa a gurin 'ya'yan ki ba, ke azzalumar uwace mai son kanta."

Sumayya Ameerah da Hajiya suka taho da gudu,

Ajmaal da ya shigo ya

nzu shima ya taho da sauri.

Hajiya ta shiga sakanin Bappa Salihu da Mommy tana cewa.

"Haba Malam Salihu mene ne haka, mata da girman ta ai ko 'ya'yan ta yanzu sun wuce duka."

Bappa Salihu ya ce

"Ai kin banza abun da ta aikata ai ko 'ya'yan nata bazasu aik

ata ba, wacce irin kwakwalwa ce da ita irin na dabbobi,

na cire ki a 'ya'yana Halima ke ba 'yata bace, ni ban haifi makashiya ba,

dad'in me zakiji ki kashe jikokin ki da hannun ki wace irin azzaluma ce ke,

na yafe ki Halima na yafe ki,

me ma kika zauna yi

anan hukuma basuzo sun tafi da ke ba, hukuma zasu zo su d'auke ki yanzu,

bayan na nuna miki na isa da Abubakar na sashi ya sake ki,

sannan hukuma suyi gaba da ke!."

Bappa Salihu ya fita rai b'ace.

Hajiya tabi bayansa tana fad'in

"Kar ka kira mana huku

ma anan, tun da abu ya faru ai shike nan, me ye na kiran hukuma."

sai da suka fito waje Bappa Salihu ya juyo rai b'ace ga Hajiya ya ce

"Ai ya kata hukumar su had'a har da ke su tatta, dan banga amfanin zaman ki a gidan nan ba,

ke Hajiya Hanne kina cikin gi

dannan b'arna daban-daban yana afkuwa ace har da kisan rai, meye amfanin zaman ki a tare da su, gara ma ki tattara ki koma can gida Yelwan Shendam, ki zauna babu amfanin zaman ki a nan, tare da su."

Hajiya ta mara baki tana fad'in

"Ahap ba yau aka saba min

gorin na tafi ba,

idan abu Allah ya kadda zai faru ko ku mazan baku isa ku hana ba."

Bappa Salihu ya yi gaba yana cewa

"Duk hankalin ku d'aya ne da Haliman, Allah ya sawake irin wannan rayuwar."

ya wuce sashin Daddy.

Mommy ta zube kasa zuciyarta ya kari

ya,

tun da take da mahaifin nata bata tab'a ganin b'acin ransa irin na yau ba.

jikinta ya yi sanyi matuka.

Ajmaal da ya share kwalla yake fad'in

"Mommy meye hakan wlh baki kyauta wa Ya Abdulrahim ba, kin cutar da zuciyarsa dan kin san a zuciya yake barin k

o wacce irin damuwar sa,

ba Ya Abdulrahim ba har da mu kika cutar Mommy, domin damuwar sa namu ne bazamu so ganin d'an'uwan mu cikin damuwa zuciyar mu ta sami nutsuwa ba,

muna murna da samin 'ya'ya kika hallaka mana su, Mommy kin san zafin da naji kuwa,

to

ina ga shi Ya Abdulrahim mai 'ya'yan, da kuma uwar 'ya'yan,

da wacce ta raini uwar 'ya'yan,

da Daddy da ya zame mana garkuwa,

Mommy kin cutar da zuciyoyi da yawa,

kiji furucin da Bappa yake fad'a a kanki,

ina mu zamu saka rayuwar mu, ace muna tsaye mu 'y

a'yan ki, mahaifinki yana kai hannu jikinki da munanan kalamai,

taya kike son mu goben mu tayi kyau, baki daidai ta sakanin ki da mahaifin mu da mahaifin ki da babban yayan mu ba,

Mommy bakiyi mana adalci ba!."

Ajmaal ya fashe da kuka yana kuma fad'in

"Mo

mmy bakiyi mana adalci ba."

Sumayya da tuni ta fashe da kuka ta na cewa

"Ni gara ma na bar gidan nan natafi Yelwa, wlh tun da naga yarannan naji sonsu a raina, Mommy me yasa zaki kashe su,

Mommy da baki kashe su ba,

me yanzu mutane da kawayen mu zasu rika

fad'a Mommy'n mu tayi kisa."

Sumayya ta kuma rushewa da kuka.

Ajmaal yayi waje yana share kwalla.

Ameerah da hawaye ya ciko idanunta ta zube jikin Mommy tana share mata hawayen da ke gangara kan fuskarta.

yayin da itama jikinta yayi sanyi..



Bappa Salihu

ya shiga gurin Daddy.

anan ya tadda su Dad da Abbieh.

sunyi mamakin ganin sa suka mike suna yi masa sannu da zuwa.

Daddy da har yanzu jikin sa da saura ya ce

"Bappa baka sanar mana zaka zo ba bamu tura mota domin taron ka ba a gafarce mu."

Bappa Salihu ya

ce

"Zauna Abubakar."

ya dubi Dad da Abbieh yana cewa "Tukur Sulaiman ku kirawo hukuma azo a tafi da Halima."

Abbieh yayi saurin cewa

"Allah ya huci zuciyan ka Bappa da dai anyi maganar a cikin gida daya fi."

"Hakane kuwa kayi hakuri Bappa kuskure kam anyi

sai dai fatan a gyara nan gaba."

cewar Dad.

Bappa Salihu ya ce

"Babu maganr gyara kuskure, baza'a rufe maganar a gida ba dan suma raine da su, hukun cin kisa kuma kisa ne, dole kuma a hukuntata,

Abubakar ka sake ta kafin a tafi da ita."

Daddy ya gyara zam

an sa yana cewa

"Bappa na saki Halima amma na maida ita, abisa umurnin Hajiya,

da fari nima hukuncin dana so zartarwa ke nan, kiran hukuma azo a tafi da ita,

sai dai yin hakan bashi ne zai sa, yaran su dawo ba."

Bappa Salihu ya ce

"Ko da bazasu dawo ba huk

unci ya rayata a kanta, kuma dole a zartar da hukunci."

Abbieh ya ce

"Bappa a bar maganar zuwa yarinyar ta sami sauki, a halin da ake ciki yanzu shima kansa Yaya Abubakar ba balafiyar ne da shi ba, kayi hakuri a aje maganr tukun."

Daddy da Dad duk suka sa

baki akan bar kiran hukuma tukun.

Bappa Salihu badun ya so ba ya

hakura amma da tabbatar musu da cewa, zai zauna tare da su a nan har lokacin da za'a yanke wa Mommy hukunci.

ya fita yana tambayar Ajmaal ina Abdulrahim yake?.

ya ce tun jiya daya shige side

d'in sa bai ga fitarsa ba har yau.

Bappa Salihu ya nufi sashin nasa Ajmaal na biye da shi.

mai gadin side d'in a ya shaida musu yana ciki.

suka karasa kofar parlour'n sa Ajmaal ya ya babbuga.

ya d'au tsawon ninuna 5 kafin yazo ya bud'e.

yana sanye da gaje

ren wanda da singilet.

fuskarsa babu annuri.

Bappa Salihu ya bubbaga kafad'ar sa yana cewa

"Sannu kaji najimin duniya, Allah ya huci zuciyar ka."

baiyi magana ba har Bappa Salihu ya juya daga bakin kofar suka fice daga side d'in yana tsaye.

kana a sannu ya

taka ya koma ciki.

A b'angaren Bappa Salihu kuwa suna fita

Ajmaal ya d'auke sa, zuwa asibiti in da Feeryal take.

sosai Bappa Salihu ya bawa su Aunty hakuri ya koma ga Feeryal itama yakuma bata tabbacin za'a bi mata kadinta.

Aunty dai har yanzu hawaye bai

bar zuba a idanunta ba, sai dai tace masa ba komai, dan Abba'n Abuja ya gargad'e ta da d'aukar mataki a hannunta, shima kuma baiyi magana ba har lokacin duk da sunji matukar zafin abun da ya faru..

A b'angaren Mommy kuwa jikinta ya sanyaya matuka zafi bi

yu ta ko ina, gana Daddy gana mahaifinta.

tana zaune tayi jigum a d'aki kiran Hajiya Luba ya shigo wayarta.

kamar bazata d'aga ba harya kusa yankewa kafin ta d'aga.

"Hajiya Halima ikon Allah ashe haka kika kware a iya kisan kai,

amma anji kunya atarihin mu

mu kawaye babu wacce ta tab'a aikata irin abunda kika aikata yanzu, to ina laifin ki had'a da babban d'an naki duk ki kashe sakarai mara lissafi."

Hajiya Luba tana kaiwa nan ta kashe wayar.

Mommy tabi wayar da kallo jikinta na dad'a jin sanyi, wanda har y

a kai da jin kamar abun kunya ta aikata,

dan tun da abun ya faru take amsa kira daga kawayen ta suna masu mamakin abun da ya faru.

Kwanan Feeryal biyu ita ma aka sallame ta.

tun da suka dawo gida Aunty a zubda kwalla take, ta kasa iya daure zuciyarta.

a y

ammacin ranar da suka dawo Aunty na zaune a gefen Feeryal tana had'a mata ruwan zafi da milo, jifa-jifa tana share hawaye.

ganin hawayen nata yake sa Feeryal d'in yin hawaye.

a hankali Feeryal ta kwantar da kanta jikin kafad'ar Aunty,

takai bayan hannunta

ta goge hawayen da suka zubo mata.

cikin muryarta mai sanyi ta ce

"Ammie to wai mu meye damuwar mu ma, ba kin ce idan na haihu za'a basu d'ansu ba,

to ai 'ya'yan su suka kashe mu babu ruwan mu, Ammie ki daina kuka ni ma kina sani kuka, daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login