Showing 51001 words to 54000 words out of 95068 words

Chapter 18 - FEERYAL BOOK3 COMPLETE

ya fito yana warware hannun rigarsa.

Aunty ta bishi da murmushi da farincikin daya gaza b'oyuwa a fuskarta, tana fad'in

"Sannun ku da aiki Abdulrahim."

Daddy kuwa bai kalli in da yake ba, idanunsa akan jikarsa, d

aya gaza janye ido a kansa.

kai ya jinjina ya wuce ya tafi can gefe yana d'aga kiran yada shigo wayarsa.

aka fito da Feeryal a ture a kan gado aka wuce da ita wani room.

su Daddy suka bi bayan su da sauri, yana tsaye yana kallon wucewar su.

Ajmaal da Shams

uddin da Faisal ne su shigo da sauri suka karoso in da yake cike da matukar farinciki suke fad'in

"Ya Abdulrahim ina baby's d'in mu, ina twins d'in mu suke!."

sukayi maganar cike da matukar farinciki sosai.

dan tuni Daddy ya kira ya fad'a musu tun kafin a

fito da ita.

murmushin gefen baki yayi ganin yadda suke maganar kamar kananun yara suna wani tsalle ya ce

"Suna can."

ya nuna musu kofar room d'in da aka shige da Feeryal.

ai ko da sauri suka juya suna rige-rigen shiga.

shiko ya fice ya shiga motarsa ya b

ar asibitin.

su Ajmaal

suka karb'e yaran a hannun su Aunty kamar zasu had'iye su dan farinciki.

sai yabawa da zuzuta kyan su suke.

Daddy yayi murmushi yana kallon yadda suke yi kamar zasu had'iye yaran.

ya ce "Iye anyi 'ya'ya sai murna ake."

sukayi dariya

Shamsuddin ya ce

"Wayyo kalle su fa kyawawa wlh duk kama da Ya Abdulram suke, suka d'auko farin Feeryal."

"Asalin kama ma kuwa."

cewar Ajmaal da Faisal.

Aunty tayi murmushi dan ko ba karya 'ya'yan asalin kama da uban su suke.

sai sannan suka masa bakin ga

do in da Feeryal ke kwance suka gaisheta suna yi mata ya jiki.

murmushi tayi musu tana lumshe idanunta tare da juya fuskarta ta jikin garo.

Daddy ya ce

"To mu fitan ku waje likita ya ce a barta ta huta, ku bawa Aunty'n ku yaran ta kwantar da su suma suna

bukatar hutu."

suna shirin fita Hajiya da Goggo Bishira Ammah Miemie Kulu mai aikin Hajiya da Sumayya suka shigo.

Miemie kamar zatayi tsalle dan murna Sumayya ma haka, dan ita halinta da sauki dan wani lokaci bata d'aukar zugar Ameerah.

ko da suka fito za

ta biyo su Hajiya Ameerah ce mata tayi wai zataje kallon 'ya'yan aljanu ita ba inda zata.

ita Sumayya na son yaran tun bata gansu ba, tana ji a ranta ko ba komai dai 'ya'yan yayansu ne, dan bata daga cikin 'yan'uwan ta masu cewa ba cikin yayan nasu bane.



Miemie da Sumayya suka riga kowa d'aukar yaran.

da kyar goggo Bishira ta karb'i na hannun Sumayya dan Miemie kam ta rike na hannunta gam.

Hajiya ta leko fuskar su ta tana fad'in

"Eh to ga kamar abokin turawa a jikin su, ah to yanzu kam hankali zai kwanta

."

Ammah ta girgiza kai.

Aunty ko Murmushi kawai tayi.

sai da likita ya shigo ya ce su bata guri ta huta kafin kowa ya fita aka bar Aunty da ita.

da zasu tafi Sumayya da Miemie suka ce su bazasu tafi ba,

suna tare da Aunty a asibitin.

Sumayya tana like da

yaran da har cikin ranta take jin kaunarsu.

Aunty ta kira su Hajja Umma ta video call.

Abba da Hajja Umma sunyi matukar farinciki Aunty ta hasko musu yaran sunata yabawa da fatan Allah ya raya.

lokacin bacci ya d'auki Feeryal suka ce idan ta tashi zasu ki

ra.

Aunty na kashewa ta kira Maryam, Maryam kamar zata fasa wayar da ihu

"Wai da gaske Aunty Faty Feeryal twin's ta haifa?."

cewar Maryam cike da zallar farinciki.

Aunty tayi dariya tana fad'in

"Gasu kuwa kina gani."

ta ce "Jibi ina hanya inasha'allah."

A

unty ta kashe tana mata dariya.

Umma karima ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta shiga wani mummunar bala'in tashin hankalin da bata b'a shigan irin sa ba.

tayi sintiri ta zaga cikin parlour'n ta yafi a kirga.

Siyama ce ta shigo kamar an jefo ta tana haki da

fad'in

"Aunty Karima ta haihu an cire 'ya'ya biyu duka maza, yanzun nan su Ajmaal suka shigo da idona na gana hoton yaran!."

Umma Karima ta buga kirji ta d'aura hannu a ka tana fad'in

"Nashiga uku!."

takuma dannan lambar da tun d'azu take ta gwada shi ya k

i shiga.

jin wayar tashiga yanzu ta sauke numfashi sanda aka d'aga kiran.

"Dr ya zakayi min haka, ko nawa nagaya maka zan baka in har ka aiwatar da abun da na fad'a maka."

daga cikin wayar ya ce

"Hajiya matsala aka samu muna tsaka da aikin Dr AA FIYA ya sh

igo, karshe ma dai shi ya karasa aikin, abun da ya bani mamaki kuma, kince min bata gidan bai ma san da cikin ba, to ya akayi yasan biyu ne a cikin ta, bayan ya ciro d'ayan da mahaifarsa, a yadda ya koma domin ciro d'ayan yasan da akwai wani a cikin,

naso

da ya kauce da ragowar d'ayan zansan yadda zanyi da shi, in yaso sai asan yadda za'ayi ma dai duka."

Umma Karima data cire d'ankwalinta tana fifita da shi ta ce

"Ya b'ata komai yama akayi yasan an kaita asibitin bayan baya gidan san da aka fita da ita!."

ta kashe wayar tayi zaman 'yan bori a kasa, tare da d'aura hannu akai ta kurma ihu tana fad'in

"Wallahi tallahi bazan barka haka ba Abdulrahim, Feeryal gidan nan ba naki bane,

dukiyar Alhaji Abubakar AA FIYA nawa ne, da na dad'e ina farautarsa yau zankara

sa farautar dana d'au tsawon shekaru ina yin sa."

Siyama ma zubewa tayi kan kukera, tana jin kamar itama tayi ihun ko zata sami sassauci daga d'acin da take ji cikin zuciyarta.

burin ta dana Aunty'n nata da banbance ita burin ta ta aure shi su zauna inuwa

d'aya ne,

duk wani abun da 'yar'uwan nata zata fad'a jinta kawai take,

ba so take a kashe shi ba ita so take ta aure shi ya zamo mallakinta.

Umma Karima ta mike da sauri ta fita ta nufi sashin Mommy.

tun kafin ta shigo parlour'n Mommy take jin yadda Mommy

take cewa

"Wlh karya ne in har kuwa akace 'ya'yan nan nasa ne, to bazai rike 'ya'yan aljanu ba, ai dole ma su san yadda zasuyi yayan suyi kama da shi,

wani suffa ne aljanu bazasu iya juyawa ba, d'ana bazai zamo uban aljanu ba kuwa!."

ta wurgawa Ajmaal waya

r sa kad'an ya rage ya fad'i yayi saurin cab'e wa, yana cewa

"Mommy ki bar wannan maganar tun da ta haihu ai ya kamata yanzu ko mai ya wuce, basai an fad'a ba ana ganin yarannan an san na Ya Abdulrahim ne, yara gwanin sha'awa ya kamata kiyi maraba da jikok

inki."

"Dan uban ka bazan yi ba fita ka bani guri anan!."

Ajmaal ya juya ya fita.

Umma Karima ta karaso tana rike baki.

"Hajiya Halima mai jikoki an haifo miki manya-manyan sarakunan aljanu, sai ki cigaba da rainon su suzamo gamashekar da zasu girma su sar

e wuyarki."

"Haba Hajiya Karima wace irin fatar tsiya ce wannan, ai wlh 'ya'yan nan baza su kwana a duniyar mutane ba sai dai duniyar aljanu, can in da suka fito."

Mommy ta shige bedroom d'in ta tana zuba uban masifa.

Umma Karima ta juya ta fita tana zaman

jiran sakamako idan baiyi mata ba ta d'au mataki da kanta a yau d'in nan ba sai goge ba.



Motarsa ne yakuma shigowa asibitin.

suka fito shi da Dr Imran suka nufi room d'in da Feeryal take yana rike da laidar magunguna,

Dr Imran kuma yana d'auke da wani

katon laidar shopping .

Sumayya da Miemie suna ganin su suka mike suna musu sannu da zuwa,

Aunty ko shigarta toilet d'in room d'in ke nan zatayi al'walar sallar azahar sukayi sab'ani.

Dr Imran ya tsaya suna gaisawa da su Sumayya, shiko ya tako bakin gadon

.

ya tsaya a kanta idonta a lumshe tana bacci yaran a jere a gefenta suma baccin suke.

sosai ya zuba musu ido ita da yaran, a fili ya sauke ajiyan zuciya.

a hankali yakai hannu ya shafi gefen fuskarta, ajiyan zuciya ta sauke tare da juya kai ta kwantar da

fuskarta atafin hannunsa.

a hankali ya lumshe idanunsa tare da bud'e su a kanta.

ya zare hannun nasa a hankali ya kai fuskan yaran ya shafa zuwa kawunan su.

Dr Imran ya karaso yana fad'in

"Wow masha'Allah see beautiful baby's I congratulate you."

Dr Imran

ya masa kusa da shi cikin yin kasa da murya sosai ya ce

"Gaskiya mutumi na kayi kokari fa ka zuba jarumta sai da ka samo masu kama da kai."

ya yi kamar baiji abun da Imran ya fad'a ba ya juya yafice.

har ya tada mota Dr Imran ya iso da sauri dan yasan hali

nsa sarai sai ya iya tafi ya barsa.

suna fita Aunty na fitowa daga toilet, Sumayya ta nuna mata kayan da suka kawo.

Aunty ta fita ta ce zataje masallacin cikin asibitin tayi sallah.

Mommy ta fito da sauri tana gyara mayafinta, ta shiga mota direbanta yaj

a suka nufi asibiti.

suna isa ta fito da sauri ta ce wa direban

"Jirani yanzu ina zuwa juya da motar ta hanyar fita."

ta nufi ciki tana tambayar wata nurse wanda akayiwa C'S da safen nan tana nuna mata d'akin da take,

Mommy ta tura kofar babu ko sallama.

lokacin Feeryal ta farka tana kallon su Miemie da suke ta zayyano sunayen da za'a rika kiran yaran da shi.

Aunty kuwa bata dawo daga sallah ba.

Mommy ta bugawa Sumayya harara tana cewa

"Uwar me kika tsaya d'auka anan?."

Sumayya ta turo baki.

Mommy ta karas

a bakin gadon ta rike kugu tana kallon yaran,

tare da aikawa Feeryal da mugun kallon .

sai kuma ta jinjina kai kana ta sa hannu ta d'auki d'aya ta rike shi ta gefe, sannan ta kuma d'aukar d'aya ta juya ta fita, Feeryal tabi bayan ta da kallo.

su Miemie ma

haka.

tana fita ta shiga mota ta ce direban yaja su tafi da sauri..

Mommy na fita ba da jimawa ba Aunty ta shigo.

da mamaki ta kalli kan gadon ta ce "Ina yaran."

Miemie ta ce "Mommy ce tazo ta d'auke su."

da sauri Aunty ta ce "Ta kai su ina?."

"Mu ma bamu

sani ba."

cewar Sumayya.

Aunty zata kuma magana aka turo kofa Ajmaal ne ya shigo cike da d'okin ganin yaran.

Sumayya tayi saurin cewa

"Ya Ajmaal Mommy ta zo ta d'auki yaran ko kuna tare da ita ne?."

"Mommy'n ina ta kai su!?."

yayi maganar hankali tashe.

S

umayya tace

"Muma bamu sani ba kawai zuwa tayi ta d'auke su ta fita, kafin Aunty ta dawo daga sallah."

da sauri ya aje shopping bag d'in hannunsa yafita da sauri.

yana kiran Abdulrahim a waya.

"Ya Abdulrahim kana ina Mommy fa tazo ta d'ibi yaran nan, yanzu

na shigo asibitin wai bata jima da fita ba ta d'ebe su."

d'ip ya katse kiran.

Ajmaal ya zaro wayar yana binsa da kallo.

sai kuma ya juya da sauri ya koma room d'in.

yana kuma tambayar su Miemie yadda akayi.

Aunty ko hankalin ta ya kasa kwanciya ta kira Da

ddy ta sanar masa.

Abdulrami bai d'au minti 20 ba ya iso asibitin.

da karfi ya turo kofar room d'in yana ware idanunsa akan gadon.

Feeryal na kwance tun da ake maganar bata furta ko kalma d'aya ba.

da sauri Ajmaal ya ce

"Ya Abdulrahim nayi ta kiran wayar M

ommy bata d'auka."

da karfi ya juya ya fita Ajmaal yabi bayan sa........!



Cikin hanzari ya shige mota, Ajmaal ya bud'e d'aya gefen ya shiga yana cigaba da kiran Mommy da har yanzu bata d'aga ba.

da karfi ya fige motar da mugun gudu, suka haura titi.

da

sauri Ajmaal ya kunna computer motar yasoma tracker ya shiga lalub'o ta in da Mommy take.

da sauri ya d'ago yana nuna computer yana cewa

"Ya Abdulrahim kilomita 15 ta hanyar titi ta baya kilomita 10 tazaran mu da su, sun doshi Cea, sun sauka a titi suna b

in hanyar kasa a lamu ya nuna ta baya zasu bi,

idan mukabi hanyar titi yafi garanti sai dai za'ayi jinkirin isa, ta baya hanyar ba kyau bazai yuwu ayi gudu ta hanyar ba."

kafin Ajmaal ya rufa baki ya juya sitiyarin motar yabi ta hanyar da yake gaya masa b

abu kyau, yaja sit belt ya d'aura.

Ajmaal ya kwalalo ido yana kallon yadda ya figi motar kamar zai watsar da su, ba shiri ya ja sit belt shima ya d'aura, yana gyara zaman sa idanunsa akan d'an'uwan nasa ganin yadda jijiyoyin hannun sa suka firfito damatsan

sa suna bud'awa, yayin da fuskarsa ta juye ta rikid'e izuwa na tsananin b'acin rai, idanunsa sukayi jajir.

gudu yake baya sanin inda yake saka tayun motar tasa.

Ajmaal idanunsa akan computer yana gaya masa adadin sauran lokacin da ya rage su cim musu, da

ta inda zaibi.

kiran Daddy ya shigo wayar Ajmaal, Ajmaal ya bashi adireshin in da su Mommy suke.

yana kashe wayar

da sauri Ajmaal ya d'ago yana cewa

"Ya Abdulrahim sun tsaya a kusa da gab'ar Cea!

muna daf da cimmusu."

kure gudun motar yayi wanda duk tsana

nin gudun da yake, ganin nawar gudun yake, da karfi ya naushi sitiyarin motar badun ingantacciyar mota ce mai tsadar gaske ba, da tuni ya tarwatse sitiyarin nasa.

sai da Ajmaal ya razana..

Mommy tafito daga ciki motar da sauri rike da yaran a hannunta.

d

a sauri ta nufi bakin gab'ar ruwan tana fad'in

"Zo ku koma in da kuka fito, bazaku zauna cikin jinsin mutane kuna aljanu ba, ku ko ma can in da kuka fito."

da sauri direban ta ya fito ganin abun da take shirin aikatawa ya biyo ta yana cewa

"Hajiya dan All

ah kiyi hakuri kar ki aiwatar da abun da kike shirin aikatawa."

tsawa ta buga masa ta ce

"Ka tsaya a matsayin ka na direba, kada ka sake ka shiga lamarin cikin gida."

ai ko ya ja ya tsaya ya nad'e hannu jiki na rawa cike da d'inbin fargabar abun da take sh

irin aikatawa.

ta dad'a matsowa bakin gab'ar.

ta d'aga d'aya ta na kokarin wurgashi a ruwan, dai-dai san da motar Abdulrahim ya sharo kwana in da suke iya hango tekun.

wani irin wawan burki ya taka dai-dai sanda ta jefa d'aya yaron cikin kogin.

direbanta y

a d'aura hannu a kai yana salati.

da karfi ya b'alle murfin motar ya duro kasa batare da ya kashe motar ba.

a hargitse Ajmaal ya zare sit belt d'in jikinsa ya yi azaman ruko sitiyarin ganin motar tana kokarin gangarawa cikin ruwan.

yayi kwana da ita ya kas

he motar.

wani irin gudu Abdulrahim yake cike da zafin nama yake taka kasa, cikin wani irin murya mai nuni da tsantsar tafasar zuciya gami da amon sauti, mai fita da karaji,

ya ke fad'in

"No! Mommy kada kiyi haka!."

yana daf da isowa inda take tayi saurin

dad'a masowa bakin ruwan, ta d'aga zata kuma jefa d'ayan.

ya mika hannu yana fad'in

"Aa Mommy a'aaaaaa!."

bai rufa baki ba kaji bundun, ta jefa shi yaron ya calla kara.

yana wutsil-wutsil kamar yadda d'anuwan sa yayi kafin ya nitse a daina ganin sa.

da gu

du ya wuce ta zai yi tsalle ya dira cikin ruwan.

Ajmaal da direban ta sukayi hanzarin ruko shi ta baya.

Ajmaal da tuni hawaye yashiga wanke fuskarsa ya ce fad'in

"Aa Ya Abdulrahim kada ka shi ga."

"Yellab'oi ruwannan da zurfi sosai tanan gefen kada ka shig

a."

da jarfi ya fizge yakuma yunkurin shiga suka juyo muryar Daddy a bayan su

"Ka dakata Abdulrahim!."

Daddy ya yi maganar cikin d'aga murya.

wani irin durkushewa yayi da gwuiwowin sa a bakin gab'ar tare da cusa hannanyen sa cikin gashin kansa da karfi ya

yi wani irin ihu mai kara gami da karajin gaske,

yana yamutsa gashin yana wani irin huci tamkar namijin zakin daya kwana baiciba.

Daddy ya nufo su da sauri mai kama da gudu, in da direban sa shima ya rufa masa baya.

Ajmaal ya juyo yana hawaye murya na raw

a yake fad'in

"Daddy Mommy ta kashe su ta jefa su a ruwa, ta kashe su Daddy!."

ya fashe da kuka kamar karamin yaro.

Daddy ya karaso ya dafa kafad'ar Abdulrahim dake durkushe yana bubbugawa, yayin da idanunsa ke kan ruwan da babu alamun yaran a ciki.

idanun

Daddy suka kawo kwalla sai ga Daddy na hawaye da idanunsa.

kan kace me aka nimi Mommy a gurin aka rasa, ta zame ta shiga mota tasa direba ya juya da ita gida.

tana ji a ranta ta raba su da fitinar aljanu.

Nan da nan Daddy yasa aka kirawo masana ruwa, aka

shiga jirgi akayi ta yawo cikin ruwan ana nima,

amma ko gawarsu ba'a samu ba, daga karshe aka samo abun d'aukar d'aya jaririn.

ma'aikatan suka bawa Daddy tabbacin gawarsu baya kusa, ruwa ya tafi da su amma zasu tura sanarwa a tare su acan rariya idan suka

isa can za'a neme su.

Jiki ba kwari Daddy ya juya gurun Abdulrahim, ya ruko hannun sa da tun d'azu ya masa ya zauna gefe kan wani dutse ya sunkuyar da kai kasa.

Ajmaal da tun d'azu ya kasa tsayuwa guri guda ya zo gon d'an'uwan nasa ya koma bakin ruwan y

ana lekawa ko za'a ciro yaran.

ya taho da sauri sanda Daddy yake mikar da shi tsaye.

tausayin d'anu'wan nasa ya kuma baibaye shi.

idanunsa sunyi jajir jijiyoyin jikinsa sun mike rad'a-rad'a,

zufa yana gangarowa daga cikin sumar kansa zuwa fuskarsa.

Daddy

ya dubi d'an nasa da d'inbin tausayawa dan yasan yakai makura a b'acin rai ko bai furta ba, basai ya furta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login