Showing 9001 words to 12000 words out of 95068 words
kayan sa kar wani d'an
hau ya gane masa kayansa,
ikon Allah har shima ya gane bakya son sa bra ke bakisan idan kina tafiya kirjinki matsawa suke ba, ko a cikin gyale ne kuwa."
Feeryal tayi rau-rau da ido sai ga hawaye.
wato hakan ne yasashi lalub'arta ya tabbatar wa kansa babu
bra'n a jikin ta.
hawaye suka dad'a zubo mata.
Miemie ta kuma kwashewa da dariya ta ce
"To meye na kukan ya gwada miki baya son ki rika yawo haka sai ki kiyaye."
ture kayan tayi ta mike ta shige bathroom, Miemie ta bita da dariya.
tayi wanka tafito d'aure
da towel, ta saka kayan baccin Miemie,ta haye gado ta kwanta gefen ta
Miemie dake rungume da pillow tana waya Murad d'in ta.
Washegari sai dare Aunty ta dawo shima dakyar Daddy ya barta.
a daren ta shigo sashin Ammah ta d'auki d'iyarta suka koma sashin s
u.
washegari da safe Miemie ta biyo ta da laidar kayan ta.
Aunty tabi kayan da kallo sai kuma ta girgiza kai tayi murmushi.
kwanan Daddy 8 sai sannan Abdulrahim ya sallame shi.
tun zuwan Feeryal sau d'ayan nan kuwa bata kara zuwa ba.
satin Daddy guda da da
wowa yasa aka akayi odar kayan d'akin Feeryal daga waje, dan yace a satin zata tare.
sai da kayan ya iso Nigeria sannan ya sanarwa Abdulrahim za'a zo a shirya mata kayanta a d'aya gefen b'angaren sa.....!
Kaya na isowa Daddy yasa aka wuce dashi direct b
'angaen Abdulrahim.
a d'aya plat d'in da ke gefen nashi aka zuba kayan.
wanda sashi uku ne cikin side d'in nasa, nashi upstairs a tsakiya sai na Kuraiba a gefe ta hagu sai wanda aka zubawa Feeryal kayanta a ciki ta b'angaren dama,
in da ko wannen su da kof
a sakanin su da b'angaren nasa.
ma'aikatan da aka taho dasu daga kasar da aka siyo kayan suka soma Arrangement d'in kayan yadda ya kamata, abunka da aikin mutum basu d'au wani lokacin kirkiba suka gama shirya komai a inda ya kamata.
kama daga babban parlou
r bedroom's guda hud'u zuwa bathroom's babban kitchen da sauransu.
nan da nan guri ya d'auki kyalkyali tamkar a turai.
Kuraiba tun da taji shigowar mota tafito ta leka.
ganin kaya cikin babbar mota hankalin ta ya dugunzuma.
ganin goggo Bishira kanwar su D
addy da Ammah sun shigo suna nunawa wad'anda suka kawo kayan in da zasu shiga da shi.
da tabbata da gaske ne jita-jitan da take ji game da tarewan Feeryal d'in.
da sauri ta juya ta koma ciki, ta zari makullin motarta, da mayafi ta fito ta shiga motar ta ba
r gidan.
A b'angaren Umma Karima da Siyama kuwa.
damuwa yataru ya dame su, Siyama ta dubi Aunty'n nata da duk nutsuwa ya kaurace musu ta ce
"Aunty Karima yanzu shike nan komai yatashi a banza shi ke nan, na kara narasa Abdulrahim a karo na biyu, na shiga
uku ina zan sa kaina, ji nake kamar naje na kashe Feeryal sannan na kashe kaina kwa ya rasa gabad'an mu."
"Uhum nafiki shiga tashin hankali Siyama,
tashin hankalin da nake jina ciki yanzu yafi na lokacin aurenshi da Kuraiba,
sannan babban bakincikina ma bo
ka ya gaza ganin su cikin kwaryar tsafinsa, bare yasan matakin da ya kamata ya d'auka a kansu,
wanan sinanniyar yarinyar wlh sai naga karshenki a duniyar nan!
yadda kike ta b'ata min shiri sai kin biduniya ba takalmi in zanyi yawo tsirara wlh sai na sa kin
tsani kanki."
Hajiya na samin labarin shigowar kayan gidan tasa a kirawo mata Daddy.
Daddy ya shigo ya sameta a parlour'n ta.
bayan ya gaishe ta tayi masa ya jiki ya ce da sauki.
Hajiya ta gyara zama tana fad'in
"Naji labarin wai an kawo kayan d'akin da
yarinyar nan, ashe kasan turawa ka aika aka siyo,
to ni dai damuwa ta karka mance da ko waye ita, kar ka zauna kayita wahalar banza a kanta, 'yar da ba wani asali take da shi ba,
tun da ka nace kace sai ka had'a ta da abokin turawa to shi ke nan ni dai ina
gudun wani abun da zaizo ya biyo baya."
"Hajiya insha'allahu babu abin da zai faru sai alhaki, Allah dai ya wuce mana gaba."
Hajiya ta kawar da kai tana fad'in
amin.
Daddy ya yi saurin mikewa dan ya gano so take takuma b'aud'e hanya gara ya yi azama tun k
an, ta karkace hanya...
Kiran wayar Mom d'in Kuraiba ce yashigo wayar Mommy.
Mommy ta d'aga da sallama gami da fara'a tana fad'in
"Hajiya Luba an wuni lafiya ya gidan."
daga cikin wayar Hajiya Luba ta ce
"Ina ko lafiya tun daga gidan ki rashin lafiya ya s
oma har zuwa gida na,
yanzu fisabilillahi Hajiya Halima irin sakayyar da d'anki zai mana ke nan,
a tun tarihin kawayen mu babu wata wanda aka tab'a mata haka, ace aure ko shekara baiyi ba d'anki ya kuma karo aure,
haba wace irin rayuwa ce wannan; ga shi ta
shin hankali ya haifar mata zuban jini tana da ciki, gata a kwance ta shigo min a firgice, haba Hajiya Halima taya za'ayi mana haka gaskiya baku kyauta mana ba."
Mommy ta ce
"Allah ya baku hakuri Hajiya Luba wlh wannan auren ba da son raina aka d'aura shi
ba, nayi duk iya bakin kokari na ganin hakan baifaruba amma an nuna min fin karfi,
amma ina mai tabbatar miki auren nan babu in da zaije za'a watse dan wlh Abdulrahim bazai tab'a zama da yarinyar nan ba,
yanzu ina Kuraiba'n take Allah dai yasa cikin bai
fita ba."
"Gata nan kwance tana numfarfashi a gaya masa yazo ya d'auke ta ya jinyata ciwon da ya sa mata,
kuma a gaskiya idan kika bar auren nan ya zaunu bakiyi mana adalci ba."
"Haba Hajiya Luba kar ki damu yarinyar nan bana kaunarta sam-sam a rayuwa ta,
babu abun da zaisa na barta tayi zaman aure da d'ana, yanzu kuwa zaizo ya d'auko ta."
Mommy na kashe wayar ta lalub'o number Abdulrahim dan tasan yau weekend yana gida.
yana d'agawa ta ce yazo yanzu tana nimansa kada ya b'ata lokaci.
bai b'ata lokaci da y
awa ba yashigo kiran Mommy.
tun kan ya zauna Mommy ta rufe shi da bala'i.
"Baku isa ku kunyatani kai da mahaifinka a cikin kawaye na ba, ga matarka can Kuraiba tana kokarin yin b'ari, ka fita kayi gaggawar zuwa gidan su kaje ka d'auko,
ka magance maysalar
da ke kolarin aukuwa kada ka sake cikin nan ya b'are,
ina ga irin ta and'agawa yarinya hankali har ya kaiga tana kokarin yin b'ari, to wlh bazan yadda ba,
yazama dole a kiyaye cikin a hakura da abin da bata so,
akan karin banza auren aljana a halakamin jik
a wlh bazai sab'uba,
maza kaje ka d'auko ta yanzu."
kafad'a ya d'aga ya juya ya fita.
Hajiya Luba tayi ta zuba idon ganin sa shiru, takuma kiran Mommy,
Mommy tayi mamakin da taji ance bai je ba, duk da tasan hakan ba wani abun mamaki bane a halin sa.
tayi
ta baiwa Hajiya Luba hakuri, daga karshe dai ita taje ta dawo da Kuraiba dan shi kam yaki zuwa.
Sashin Daddy Mommy ta wuce ta tarar da shiko zama bayiba ta ke fad'in
"Yanzu Alhaji kaji ka aminta auren nan sai an zauna sai Abdulrahim ya zauna da yarinyar
nan,
mene ne ajikin auren wannan yarinya da kake so ka jonawa Abdulrahim ita,
yanzu gashi can damuwa nason sa cikin jikin Kuraiba zuba,
nifa ban aminta da auren nan ba z
bazai taba'a sab'uwa ba."
"Ke Hajiya Halima ki maida hankalin ki kada ki sake zuwa min
da wannan shirmen,
d'ana ne ko naki? haka naga dama dashi,
idan baki dai-dai ta hankalin ki ba zaki iya kaucewa ki bamu guri a gudanar da komai lafiya, kar ki sake zuwa min da wannan zance."
"Au haka zakace ma Alhaji, to sai me ko mai ma kayi."
ta juya fu
uu tayi waje.
Mommy tayi sashin Hajiya da kukan ta wai Daddy ya ce zai koreta ta akan auren, ga shi kuma
cikin Kuraiba na shirin fita sanadin damuwar auren.
Hajiya ta ce
"Ai ko bai isa ba sai dai in a fasa tarewar, dama Kuraiba'n tana da ciki ne, amma dai
bai fita ba ko?
ikon Allah ashe dai tana kunshe da abun, ai yafi aure kusan shekara babu motsin ciki ai ba kanta,
jeki zan kira shi ai karma ya soma."
Kwana uku da shirya kayan Feeryal a side d'in Abdulrahim Daddy yasa su Ainty da goggo Bishira da Amma
h suka shiga babban kasuwar su suka had'o wa Feeryal lefe.
kud'in da Daddy ya narka wajen had'o lefen Feeryal sai da ya baiwa Aunty tsoro.
kwana uku sukayi suna shiga kasuwa, inda gidan gaba d'aya ya d'auki zancen, masu habaici sunayi masu mugun fata sunay
i.
Aunty zaune tana waya da Hajja Umma. Mommy ta b'ankad'o kofar parlour ta shigo.
tana bin Aunty da kallon banza tana fad'in
"Hajiya Fatima burinki ya cika kinyi kutun-kutun kin sa an jona d'ana da d'iyar tsintuwarki, tsintacciyar aljanar ruwa mara asali
,
amma kisani har a gobe nice nan uwar da ta haifi Abdulrahim nayi nakudar sa nasan zafin sa, wanda har a gobe bakisan ya ake nakuda bare nishin haihuwa ba;
ina so na sanar miki cewa baki isa kisa ayi wani shagalin biki ba dan d'ana bazai jera da aljanar r
uwa ba,
idan kuma kikace zakiyi to mu zuba mu gani, mttsss!."
taja dogon tsaki kana ta juya tafita tana banko kofa.
Aunty ta bi bayanta da kallo tare da sauke numfashi.
tana dad'a gyara rukon wayar da ke kunnen ta.
Hajja Umma dataji komai ta cikin waya ita
ma ra sauke numfashi tare da fad'in
"Fatima Allah dai ya miki albarka da baki tanka mata ba, dama kin shirya wani shagalin biki ne a tarewan nata?."
"Aa wlh ban shirya komai ba Hajja Umma, ta daiyi tunanin ko hakan zai faru ne."
Hajja Umma ta ce
"Yauwa to
kada ma ayi dan gujewa wani tashin tashina,
muma babu wanda zaizo daga nan idan Allah yasa ta tare Allah ya kawo rabo in da rai zamuzo suna, zamuyi musu fatan zaman lafiya daga nan, zamuyi ta tayaku addu'a Allah ya kad'e fitina."
Aunty ta ce "Amin ya Allah
amma Hajja Umma ni dai zanfi jin dad'i idan na ganku kusa."
"Fatima kiyi hakuri bazai yuwu muzo a irin wannan halin da ake ciki ba, kar azo a b'ata goma d'aya bai gyaruba, 'yan'uwanki bazasu zuba ido ayi musu cinkashi su share ba, to maganin bari kar a so
ma, kiyi hakuri kawai zamu zo ai nan bada jimawaba idan Allah ya nufa."
Aunty ta girgiza kai kawai, sukayi sallama.
Da yamma Daddy ya shigo.
jikin Aunty ya yi sanyi san da Daddy ya sanar mata a karshen satin nan Feeryal zata tare.
Aunty ta dubeshi jiki a
sanyaye ta ce
"Daddy beyi wuri ba baza'a bari a kara lokaci ba."
"Fad'imatu karki ce komai dan Allah kiyi musu addu'a da fatan alkhairi, bana so najinkirta, ina so nayi amfani da wannan damar ne kafin Hajiya takuma waiwayowa kan lamarin,
yadda taga naji sa
ukin nan zata iya kuma tada bori ta ce bata amince ba."
Aunty ta girgiza kai
ta ce
"Allah yasa hakan shine mafi alkhairi."
"Yauwa ko ke fa amin ya rabbil izzati, shin kinshirya wani hidima ne Fad'imatu?."
"Aa babu abun da na shirya Daddy ayi addu'a a kaita
Allah ya basu zaman lafiya."
kai Daddy ya jinjina tare da kuma amsawa da amin amin.
Miemie zaune da Feeryal a d'akin ta, Miemie ta b'ata rai tana fad'in
"Ni wlh naji haushin da akace babu wani shagali a auren nan ni da nagama hasasho yadda shagalin zai g
udana,
Allah ban so ba."
Feeryal ta bita da ido dan ita da ido take kallon duk wani mai magana kan auren nata da har yau take ganin kamar karya ko mafarki.
Ranar da ya kasance rana ce da Feeryal zata tare a side d'ib Abdulrahim, ranar ta tsinci kanta cik
in tashin hankali sosai. ranar wuni tayi sukuku daga bisani kuma tasoma kuka,
Aunty ta sunkuya rarrashi.
Abdulrahim ne zaune a parlour'n Mommy da tayi masa kiran gaggawa.
ta dube shi tana cewa
"To bawai kaga an kaima wancan kyalkyal banzan sashin ka, ka
saki jiki da ita ba,
tun da ya matsa sai ka aure yarinyar nan, ka bud'e kunnen ka da kyau kajini,
kar ka soma gangancin kusantarta dan kyan d'an maciji ne gareta, kasan takunka idan ba haka ba wallahi sai ta fasa kai duk ta wasa mana dafin tsiya, kaji na g
aya maka ke nan."
baki ya tab'e ya mike ganin ta gama maganar nata ya yi gaba.
Hankalin Feeryal bai kara tashi ba sai da dare yayi, Aunty Ammah suka sata a gaba suna mata nasiha.
kuka sosai take da gaske dai mafarkin nason zamowa gaskiya.
Aunty ta gaza d
aurewa itama ta fashe da kuka, ta rungume Feeryal suna kuka kamar wacce mutuwa zata rabasu da d'ayan su.
Ammah ta rika baiwa Aunty baki itama tana share hawaye dan duk wanda ya gansu sai sun bashi tausayi.
Daddy da kansa ya shigo ya kama hannun Feeryal tan
a tirjewa tana mikawa Aunty hannu.
da kyar ya lallab'a ta tasassauta kukan,
ya dubi goggo Bishira da Ammah ya damka musu ita a hannunsu ya ce
"Ku kaita d'akin ta."
Feeryal takuma fashewa da kuka.
wannan karon sai da Daddy shima ya share guntun kwalla.
gogg
o Bishira da Ammah suna rike da hannunta har sashin Abdulrahim suka shige da ita gefen ta.
nasiha suka kuma yi mata kana sukayi mata saida safe suka janyo mata kofa.
Feeryal ta fad'a kan lafiyayyen gadon ta ta kuma fashewa da kuka tana kankame pillow......
...!
Allah ya bamu aron rai ya nuna mana bayan sallah da rai da lafiya.
Abun da take ganin sa kamar mafarki sai gashi ya zamo gaskiya, yau ta rabu da Ammien ta gata a side d'in Abdulrahim kuma wai a matsayin matarsa.
wani kukan takuma fashewa da shi,
tana dad'a kankame jikin pillow gami da kiran sunan Ammie'n ta.
a haka bacci yasami nasar d'aukar ta,
sai dai tayi ta juyi dan sam bata saba bacci da kaya masu nauyi ba,
dole ta mike ta isa jikin wardrobe tashiga bubbud'ewa tana lalumo ta in da Sleeping d
ress yake.
bata sha wuya wajen nemaba kuwa ta gani sabbi cikin kwalaye da laidodinsu, a jere kamar za'a bud'e kanti.
ta d'au d'aya mai riga vest da wando har kasa.
a sannu ta nufi kofar da take hango shi na glass.
a hankali takai hannunta jikin kofar gila
shin da take tunanin nan ne bathroom.
tana kai hannunta jikin gilashin ya zuge, tasa kai ta shige a hankali.
ta tub'e kayan jikinta ta wasa ruwa kana ta saka kayan baccin, ta fito.
a hankali ta kwanta gefen gado ta rakub'e.
takai zamani guda da tunani ire-
ire kafin bacci ya sami nasarar d'aukar ta...
Ab'angaren Kuraiba kuwa, ta kasa zaune ta kasa tsaye.
tun da taji an kawo Feeryal hankalin ta yayi mugun tashi.
karfe 12 ta fito ta nufi bedroom d'in sa.
ganin sa kwance yana bacci bata san san da ta saki wani
ajiyar zuciya ba, dan tayi zaton yana can gurin ta ko ita Feeryal d'in tazo d'akin nasa suna tare.
ta janyo masa kofar ta juya tana jin dad'i a ranta.
Feeryal ba ita ta farka ba sai asuba.
bayan ta idar da sallah a hankali ta kifa kanta jin gado tana azq
ar, takai awa guda zaune sai da ta fara gyangyad'i. kafin ta mike a hankali ta kwanta bakin gado batare da ta cire hijab d'in jikinta ba.
Sai wajen karfe 10 da rabi ta farka.
ta shige bayi tayi wanka tafito, ta shirya cikin doguwar rigar atamfa data d'auk
a cikin sabbin kayan da suke cike tam cikin wardrobe din d'akin.
rigar ya zauna sosai a jikin ta yamata kyau matuka.
turarukan dake gaban mirror ta shafa masu dad'i gami da sanyin kamshi.
daga su bata kara komai ba, abinka da me kyau tamkar ta zauna ta tsa
ra wani rantsastsen kwalliya haka take kyalli.
karfe 11 dai-dai ta shafa cikin ta data fara jin yunwa, wanda rabon ta da tasa wani abu a cikin tun jiya da rana.
ta mike a hankali ta je ta d'au gyale ta yafa a kanta ta nufi kofa, da zumbar tafiya sashin Amm
ie'nta.
Tana fitowa Baba Rabi na shigowa niki-niki da kulolin abinci, gami da flax's.
tayi saurin isa ta taimaka mata da wasu.
tana fad'in
"Sannu Baba Rabi ina kwana."
"Lafiya lau 'yar nan ya kwanan bakunta?."
batayi magana ba suka karasa saman dinning su
ka jera kulolin.
Baba Rabi ta d'ago ta dube ta tana fad'in
"Ammie'n ki ta ce na gaida ki ga breakfast d'in ku."
kai tad'an langwab'ar
tayi rau-rau da ido cike da yanayin ta mai kama da shagwab'a kamar a gaban Ammie'n nata take.
Baba Rabi tayi murmushi ta j
uya tana fad'in
"Nabarki lafiya."
har Baba Rabi takai kofa tana tsaye jiki ba kwari, sai da taga ficewar ta kana
a hankali taja kujera ta zauna.
Kulolin tashiga bud'e wa had'ad'd'un abinci ne kala-kala d'aya daga cikin flax's d'in kuwa Sudan tea ne a ciki
.
sai da takai kan abun da tafi bukata wato cake da Ammie'n ta ta shirya mata shi a mazubi na musamman.
tayi serving
tasoma ci da tea d'in da tad'an had'a rabin mug.
tana kammalawa ta mike ta gyara mayafin kanta ta fita, ta nufi sashin Aunty.
Aunty n
a zaune cike da kewar ta sai ganin ta tayi.
ta mike tsaye tare da rike baki tana binta da kallon mamaki.
itako kai ta langwab'e tare da cuno d'an karamin kyakkyawan bakin ta.
Aunty tayi