Showing 78001 words to 81000 words out of 95068 words
kad'ai ke da irinsa, wanda yake haramun ne kera i
rin sa masarautar su ne kad'ai ke da ita,
kamar dai yadda sauran masarautu ke da irin nasu suma,
hakika wannan lu'lu'un Sheehra Al'Ayzaan ne data mallakawa d'iyarta Feeryal, wacce ta b'ace a lokacin da take da kwanaki goma a duniya."
wasu hawaye suka z
ubo wa Uncle Aliyu ya kuma mika hannu yana fad'in
"Taho gareni d'iyata mun rasaki a lokacin da muke farinciki da samin ki, sai gashi na kuma samin ki a lokacin da kad'aici ya zagaye rayuwa ta na rashin ki da mahaifiyar ki, da rashin ki ya haifar mata da b
ugun zuciya har ta kai ga rasa ranta."
Feeryal ta soma d'ago kafarta tana takowa in da yake.
Uncle Aliyu ya rungume ta yana hawaye da fad'in
"Hakika ke jinina ne Feeryal d'iya ga Sheehra Al'Ayzaan 'yar sarkin Beirut babban birnin kasar Lebanon,
ke ce muka
rasa shekaru 18 baya,
a ranar da kike da kwanaki goma da haihuwa, kina a kwance a kan gadon ki kina bacci, mu kuma muna parlour da mahaifiyarki,
muka shigo muka tadda bakya nan,
mukayi ta nima bamu same ki ba,
abun al'ajabi abin da ya shigewa kowa duhu, k
e da kike d'aki a kwance muka neme ki muka rasa, babu kuma wan da ya shigo gidan, dan gida ne mai matukar tsaro,
kakanki mahaifin mahaifiyarki sarki Al'Ayzaan yasaka bincike mai tsanani, ciki da wajen garin sakamakon b'atar ki,
amma ina ba'a sameki ba,
b
ayan niman ki da mukayi muka rasa da kwanaki uku itama mahaifiyar ki Sheehra Al'Ayzaan, ta bar duniyar sabo da bugun zuciyar da ta samu sakamakon rasa ki,
nayi kukan rashin ku nayi kukan rasa Sheehra data nuna min halacci duk da kasancewar ta d'iya ga sark
i Al'Ayzaan sarkin larabawa na Beirut babban birnin kasar Lebanon,
bata dubi kabila ko jinsi ba ko banbanci kasa ba,
muka kulla soyayya a makaranta in da mahaifina ya kaini karatu kasarsu,
soyayyar da take nuna min shi ya kaiga mahaifinta dattijon arziki b
ani ita a matsayin mata,
shima bai nuna banbancin kasa ko kabila ba,
amma ya ce da sharad'in zan zauna da ita a kasar su,
bayan mun kammala karatun mu
gwamnatin kasar ta bamu aiki
da muke d'aukar albashi mai tsoka,
da har ta kai mu gina manyan masana'antu
masu reshe daban da ban a fad'in duniya, wanda yake mallaki na ni da ita, mai tambarin sunan mu.
S.A
(Ø´ÙØ±Ø§) (عÙÙÙÙÙ)
Wan da har a yau gwannatin kasar bata fasa biyan Sheehra Al'Ayzaan albashi ba, duk da bata raye,
sannan
iyayen ta basu yadda su karb'i ko sisi cikin kud'in albashin ta da kuma wanda masana'antun mu suke kawowa ba, kud'in albashin ta yana nan a ajiye a wani banki na kasar,
duk wata nan ake tura mata albashin ta,
masana'antun kuwa mahaifinta ya ce na rike duk
a basu karb'i ko d'aya daga ciki ba."
Feeryal ta kifa kanta a kafad'ar Uncle Aliyu tana jin sanyi cikin ranta hawaye na gangara a fuskarta.
ta mike ta dawo jikin Aunty ta rungume ta, tana murmushi hawaye na zuba a idanunta,
Aunty bakin ta ya kasa rufuwa sa
bar farinciki.
Uncle Aliyu ya dube su yana cewa
"Ashe dama Fatima da kike gaya min kun tsinci yarinya a cikin ruwa ashe 'yar ki kika tsinta,
ta ya akayi ita da take Lebanon me ya kawota Nigeria, kuma a cikin ruwa."
da sauri ya daddana computer yana kiran w
ata lamba na kasar Lebanon.
wata farar dattijuwar balarabiya mai matukar kama da Feeryal ta bayyana tare da yin sallama.
Uncle Aliyu ya amsa sallamar yana gaisheta cikin harshen larafci, kana ya d'ago sarka da abun hannun nan ya nuna mata kafin ya yi magan
a ta rigashi magana cikin harshen larafci.
"Lu'ulu'ul Fahsia lu'ulu'un masarautar Beirut,
a kaf ahalin masarauta babu wanda nashi baya wajen sa, sai na Sheehra Al'Ayzaan, daya b'ace da jikata."
Uncle Aliyu ya je ya kamo hannun Feeryal ya kawo ta gaban lapt
op d'in,
dattijuwar tana ganin ta ta dafe kirkinta tare da fad'in
"Lahaula walakuwwata'illabillah, idona ne ke gane min Sheehra ko kama ce, wani irin kama ne wannan irin na Sheehra, hakika mutuwa d'aya ce kuma idan anyi ta ba'a tab'a dawowa,
na yadda Sheeh
ra ta mutu shekaru masu dama,
wannan ita kuma wace ce?."
ya ce "Jikarki ce Feeryal gatanan cikin dangina su suka tsince ta, tsintuwa mai ban mamaki."
ya bata labarin in da su Aunty suka tsinceta.
dattijuwar ta fashe da kuka ta soma tafiya cikin sauri,
ta b
ayyana cikin wani ramb'asheshen parlour, ba sai an fad'a ba kasan na masarauta ne irin na kasashen larabawa.
tun kafin ta karasa take fad'in
"Ya Al'Ayzaan ga jikarka Feeryal d'iya ga Sheehra."
dattijon ya mike zumbur da jin abun da ta fad'a ta karaso da sa
uri ta mika masa wayar tana cewa
"Feeryal ce tabbas ita ce."
sarkin Beirut Al'Ayzaan ya kura mata ido yana kallonta zuciya da fuska taf da farinciki mai gauraye da al'ajabi.
Uncle Aliyu ya d'ago gold d'in yana sakashi a hannun Feeryal.
dattijon balaraben y
a jinjina kai cike da kamala da dattako ya ce
"Tabbas Feeryal Sheehra Al'Ayzaan ce wannan, lale marhaban jikata."
larabawa maza da mata suka rika tuttud'owa suna zuwa bayan dattijon suna leka Feeryal,
tun da sukaji dattijuwa ta ambaci sunan d'iyar 'yar'uwa
r su data rasu.
'yarta kuma ta b'ace.
duk wan da yayi ido biyu da ita,
cewa yake tabbas jinin su ce koda babu Lu'ulu'un masarautar su tare da ita,
tabbas sunga Sheehra a jikinta,
iya haka ma ya tabbasar musu ita d'in d'iyar 'yar'uwar su ce.
suka rika d'a
ga mata hannu suna sanar mata da farincikin da sukayi na ganin ta.
Feeryal dai sai murmushi take musu itama tana d'aga musu hannu,
dan ba duka maganar nasu take fahimta ba tsinta-tsinta take jin larafcin wanda a islamiya aka koyar da ita.
Sarki Al'Ayzaan
ya yi wa su Aunty da Daddy godiya sosai da suka zame mata uwa da uba,
batare da sanin wace ce itaba.
ya ce ikon Allah ne ya jefo ta Nigeria, ta fad'a a hannun su mutanen kwarai, uwar da ta raine ta bata san cewa d'iyar d'an uwan ta ba ce ita.
ya kuma bukac
i Uncle Aliyu ya zo musu da ita, domin taga dangin mahaifiyar ta.
kowa ya cika da mamaki da al'ajabi, Daddy bakin sa ya kasa rufuwa sai fad'in
"Alhamdulillah Alhamdulillah."
yake, Abdulrahim yana tsaye daga bakin kofa.
Hajiya Mommy Mom Ammah da sauran m
utane kowa na tsaye da d'in bin mamaki.
Feeryal na tsaye sai gani akayi ta yanki jiki ta fad'i kasa.
salati parkour'n ya d'auka har da su Sarki Al'Ayzaan da sauran mutanen da suke tare da shi,
suke kallon abun da ke faruwa ta cikin waya.
wani irin d'ago k
afa ya yi ya karaso cikin parlour'n,
yana isowa kanta da sauri cikin wata iriyar murya na maza ta ce
"Aa Garkuwar god'iyar mu, mu ba macuta bane kuma bamuzo dan mu cutar da ita ba,
hasali ma mune masu bata tsaro a lokacin da baka tare da ita Garkuwa,
munzo
ne don mu fayyace duhun da ya shigewa kowa cikin lamarin b'atar god'iyar mu a lokacin da take jaririya,
sunana Waziri Kutup nine Wazirin Sarkin Aljanu."
A wani karni shekaru masu tsawo alokacin da zalunci ya yawaita,
baga bil'adama ba ga jinnu ba.
ta ko
wani fanni zalunci ya yi yawa,
kwasam aka haifo shugaba Matip ya taso da farar zuciya, yaci burin gyara al'umman sa,
ya yi yaki da karfin sa wajen ganin azzaluman aljanu da wad'an da suke baiwa jinsin bil'adama bokaye da matsafa sa'a,
wajen yin bokanci d
a tsubbace-tsubbace masu surkulle da 'yan bori, ya rushe sansanin su da karfin izzarsa.
yasa kowa ya rusuna bisa gwaiwowin sa, dan dolen su sukayi murabus da zaluncin da suke yi, cikin jinsin mutane da 'yan'uwan su aljanu.
ya shafe babin azzalumai aka dain
a zalunci, ya zame mana sarki.
tun daga lokacin adalci ya wanzu kwasam bayan shud'ewan wani lokaci.
aka sami munafukin shaid'ani daga cikin masarautar ashe ya dad'e yana munafurtar sarki Matip,
ya kafa sansanin sa a gefe batare da sanin sarki ba,
ya jone d
a bil'adama bokaye da matsafa, suna zalunci a bayan fage.
da labari ya zowa sarki Matip yasa aka hukuntashi sannan aka koreshi a fada, dama hukuncin duk wanda aka kama da laifin zalunci ke nan.
yana barin fada ya je ya kafa sansanin sa in da ya rika jan ra
'ayin wasu daga cikin mu duk suka tattara suka koma karkashin sa,
kafin wani lokaci ya tattara kusan rabin fada da iya makircin sa,
daga nan ya nad'a kansa a matsayin sarkin bakaken aljanu,
ya fara wanzar da zalunci, cikin Aljanu da mutane,
ya baiwa bokaye
lasisin cin karen su ba babbaka zalinci ya wanzu.
kafin wani lokaci yayi karfi fiye da sammani ya zamo shine mai fad'a aji,
fadarsa tayi karfi fiye da tunani.
a lokacin ya shirya yaki da sarki Matip ya shiga fadarsa da mayaka suka yake mu, aka karkashe da
yawa daga cikin mu in da wasu kuma da yawa sukayi mubaya a suka koma bayansa, wasu kuma suka sami nasarar gudu subar gurin,
daga nan ya shiga yakama sarki Matip da ni wazirinsa ya sa aka d'aure mu, ni aka jefani a kurkuku,
Sarki Matip kuma akayi masa keji
n karfe mai tsananin karfi, wanda in duniya zasu taru bazasu iya b'allashi ba,
kejin da aka kerashi da manya-manyan matsafa aljanu da mutane aka tsafe kejin karfen,
wanda bashi da makari sai abu guda, hawayen jaririya macen bil'adama 'yar baiwa mai idon ga
nin wasu jinsin da ba iya jinsin mutane ba,
shine kad'ai makarin sa,
da zai iya bud'e kejin karfen,
sai idan jaririyar tayi kuka hawayen ta ya d'iga a jikin kejin daga nan kejin zai bud'e.
aka d'auke sa aka jefashi a tsakiyar tekun Matip tsawon shekaru da
ri uku, Sarkin bakaken aljanu ya ke shinfid'a mulkinsa yadda yaga dama.
sai da nayi shekara d'ari uku a kurkuku sannan aka sake ni a matsayin bawa,
mai bautatawa fadar sarkin bakaken aljanu.
kwasam wata rana ina cikin aiki a fad'ar na tsinci maganar bakake
n aljanu da mabiyansa wanda suke kusa da shi sosai,
da kuma bil'adama bokaye, suna cewa sunyi bincike sun gano an haifo irin yarinyar da zata iya kub'utar da Sarkin Aljani Matip,
'yar baiwa da Allah ya halitta mai iya ganin jinsin da ba nata ba kad'ai, suk
a kuma tabbatar da cewa sun gano kasar da aka haifeta,
dan haka zasuje kasar domin bincikota, su kashe ta kafin ta zame musu matsala, dan sun san idan sarki Matip ya kub'uta bazai kyale su ba.
Tun da naji labarin a ranar na zurfafa bincike har na gano a k
asar Lebanon aka haifo ta,
washegari aka tura dakarun bakaken aljanu domin su je su d'auko ta,
ni na rigasu tafi.
tun da aka gano na gudu a fadar aka tura dakaru nima na,
akayi ta jefa kifiyar tauraru tana sukana,
mutuwa ce kad'ai banyi ba amma nasha wuya
sosai kafin na isa ga in da take,
dan naci alwashin sai na kub'utar da ita daga zalincin su, sannan na kaita ta taimaki shugaban mu.
na sauka a gidan su na d'auke ta tare da sarkar masarautar mahaifiyarta domin na tabbata komin daren dad'ewa zata had'u da
danginta,
ta sanadin lu'ulu'un masarautar su,
na had'a da hoton ta na sakata a kwando na tafi da ita.
ina fita na bayyana a babban tekun Bahar Rum.
na tafi ta sama har na shigo kasar nan na sako ta a dai-dai tsakiyar tekun Matip,
in da yake d'aure a karka
shin tekun, ta isa kasan tekun taje ta ceto shugaban mu,
shugaba bai barta ta halaka ba a lokacin data ceto shi, aka fito da ita sararin duniya."
Sanda Waziri Kutup ya kawo nan
Abdulrahim cikin b'acin rai ya damki wuyar ta yana fad'in
"Da kun sa ta mutu
fa! ina ruwan ta da lamarin ku ita tana mutum ku kuna aljanu, kuje ku magance lamarin ku mana!."
Waziri Kurup ya yi dariya ya ce
"Haba Garkuwa d'an sassauta rukon,
da mun barta ai da dakarun sarkin bakaken Aljanu sunje sun kasheta,
a cikin ruwan da muka b
arta tana yawo ai ba ita kad'ai bace a rike a hannun yaran mu take,
bazasu bari komai ya same ta ba, duk da muna da tabbacin zata fuskanci kalubale a duniyar nan,
dan munsan sarkin bakaken Aljanu bazai kyale ba,
bamu barta ita kad'ai ba kullum a cikin bata
tsaro muke,
ko kuda bamu yadda ya sauka a kanta dan cutar da ita ba,
kwasam binciken mu ya gano mana kai, ta hanyar jefa taurarun bincike,
muka gano wasu tarukan baiwa a tare da kai,
da tabbacin kaine Garkuwar ta
har lokacin da ka bayyana a gareta, haki
ka kai Garkuwa ne a gareta tsaron ka a kanta yafi namu, domin kai d'in Garkuwa ne,
kana da wasu sirrukan da kai kanka baka san kana da shi ba, kai d'in daban ne acikin mutane."
Fuska ya murtuke ya ce
"Babu ruwan ku da wannan ku kauce ku bamu guri, kar ka
sake mu kara gamuwa."
"A gafarce mu Garkuwa."
tana fad'in haka ta sauke wasu tagwayen atishawa jikin ta ya sake.
parkour'n ya kacame da hayaniya.
acan fadar Sarki Al'Ayzaan kuwa da suke biye da wayar suna ganin komai ta cikin waya,
Uncle Aliyu ya sanar mus
u abunda ya faru da harshen larafci,
suma suka cika da al'ajabi.......!
Rasheedat S Director
Mommyn Twins ceğ¤ğ»
Kowa yacika da d'in bin al'ajabi.
Allah ke nan buwayi gagara misali, su Hajiya jiki ya dad'a sanyi hakika sarki ya tabbata ga Allah.
s
u Ameerah kowa sai ido wacce ake ta wa gori a baya ita ba kowa ba, sai gashi tayi musu fintinkau.
jinin larabawa jinin sarauta uwa da uba hamshakan masu kud'i.
Mommy ko sai sunkiyar da kai kunya ya dad'a lullub'e ta.
kowa ya watse da al'ajabin abun.
Tuni
labari ya isarwa su Abban Abuja da Hajja Umma, Feeryal 'yar Uncle Aliyu ce, farincikin su bazai fad'uba.
ashe jinin su ce ita shiyasa suke jin ta a cikin ransu.
labari ya zaga dangin su gaba d'aya, sukayi murna sukayi farinciki mara misaltuwa.
a ranar Unc
le Aliyu ya koma Abuja wanda ya so tafiya da Feeryal a ranar Abuja sabo da su wuce Lebanon ya kaita wa dangin mahaifiyarta kamar yadda suka bukata.
Daddy ya ce ya bari ta shirya tukun ana gobe zai koma zataje Abujan ta same shi sai su wuce.
Ana gobe zata
je Abuja, da daddare tana zaune tana kara bra cikin a kwatin ta, da Aunty ta ce ta kara kan wanda ta saka mata su ciki, dan Aunty'n ce da kanta ta shirya mata kayan.
Abdulrahin ya shigo ya tako bakin gadon.
yana isowa ya ture akwatin gefe ya zauna ya jany
o ta jikinsa,
ya saka hannu ya zagaye ta tare da sauke mata kiss a gefen wuya kana ya d'ago yana kallon cikin idon ta.
"Kina shiri waya baki damar tafiya?."
ya yi maganar idanunsa cikin nata.
kasa tayi da idanunta tana turo lips d'in ta gaba,
ta kuma sinka
yo muryarsa
"Idan kikayi wasa babu inda zakije."
fuska ta kwab'e ta ce
"Daddy ne fa ya ce naje."
"Shi ke nan baza'a tambaye ni ba sai ayi ta yanke hukunci, to bazakije ba."
da sauri ta d'ago ta kuma kwab'e fuska kamar zatayi kuka, tana kallon cikin idanun
sa kamar yadda shima yake mata.
a hankali ya matso da fuskarsa daf da nata ya d'aura lips d'in sa kan nata, ya cafke ya d'an tsotsa, lumshe idanunta tayi tare da kawar da fuskarta,
ta kifa fuskar nata a kirjinsa tana matso kwalla.
a hankali ya ciro kanta y
ana kallon kwayar idanunta da suke tsiyayar da kwalla,
a ransa yake mamakin saurin kuka irin nata.
a sannu ya kuma had'e bakin su yashiga tsotsar bakin ta.
ya yin da ya tura hannunsa cikin rigar baccin jikinta yana matso ababen kirjinta.
sai kuma ya zaro
bakin sa da sauri ya zare rigar a jikinta,
tana kokarin janyewa tuni
ya kwantar da ita ya bi jikinta, ya shiga tsotsar ta.
da zafi zafi yake shanye ababen kirjinta, ya d'ago ya na kokarin zare wandon jikin ta, da sauri ta rike hannunsa jiki a mace dan ya s
aukar mata da kasala,
ta ce "Sahab kar ka cire."
huci ya furzar tuno a in da suke, ya mike ya sauko a gadon yana rumtse idanunsa ya fice a d'akin.
a bakin kofar d'akin sukayi kicib'us da Aunty da ke kokarin shiga d'akin, Aunty tayi baya da sauri, bata san
yana ciki ba dan bataga shigarsa ba.
ya sunkuyar da kai yana gaisheta, kana
yasa kai ya shige yana kawar da kansa dan a fili ake hango yanayin da yake ciki.
Aunty ta juya ta koma d'akin ta bata kuma shigowa d'akin Feeryal ba sai washegari.
da safe Daddy y
a kaita airport da kasan.
Feeryal ta isa Abuja da wuri.
a cike ta sami gidan da 'yan'uwa har da wanda bata tab'a sanin su ba.
Maryam ma ta zo daga Ogun da d'anta.
kamar yau suka fara sanin ta, wani sabon kauna da soyayya suka rika nuna mata.
musamman Hajj
a Umma da Abba.
kwana d'aya tayi a Abuja washegari, jirginsu ya d'aga ita da Uncle Aliyu zuwa Lebanon,
tana like da mahaifin ta a jirgi ga sit d'in shi ga nata,
duk da a baya bata tab'a jin maraicin uwa da uba ba,
dan
Daddy da Aunty sun maye mata gurbin s
u,
amma