Showing 42001 words to 45000 words out of 95068 words

Chapter 15 - FEERYAL BOOK3 COMPLETE

ganin iya titi ya ketare yayi not a bakin wani katon get.

ganin yana kokarin shiga gidan tayi saurin kallon shi murya a sanyaye ta ce

"

Sahab nan ba gidan bane."

kallon ta yi sannan ya kuma mai idanunsa ga hanya, ya karasa ciki ya gyara parking sannan ya bud'e ya fita.

ya zaga gefen da take ya bud'e yayi mata alama data sauka.

jiki a sanyaye ta zuro fararen kafafun ta da babu takalmi kasa.

ya juya ya samo tafiya tabi bayansa bayan ta rufe motar.

tana tafe tana waige-waige wai shin a Nigeria take ko a wani kasar dan gidan bai yi mata kamada a Nigeria take ba.

a bun da ya kuma bata mamaki yana isowa jikin kofar wanda yake na glass ne gaba d'a

ya glass d'in ya kawo haske da kaloli masu kyau, sauti kuma ya biyo baya

"You are welcome sir."

ido ta ware sosai tabbas daga jikin gilashin sautin ke tashi.

sannan ya zuge da kansa, ya sa kai ya shi tabi bayansa a hankali.

ganin ta bayyana cikin wani ham

shakin parlour taja ta tsaya.

Wani kofa ya bud'e ya shiga jim kad'an ya fito har lokacin tana tsaye.

ya tako cikin parlour'n ya zauna kan d'aya daga cikin kujeru na alfarma dake cikin parlour'n, ya d'au rimut ya kunna tv batare da ya kalli in da take ba y

a ce

"Kije kiyi sallah."

da sauri ta kalle shi ta ce

"Ni gida zan tafi."

d'agowa ya yi ya wurga mata wani kallo mai shiga jiki

"Ba zakiyi sallar ba?."

ya fad'a yana tsare ta da ido.

baki ta cuno ta tare da yin kasa da kanta.

sanna ta soma d'aga kafarta ta

nufi kofar da taga ya shiga.

tabi d'akin da kallo lallai in ba ta mance ba wannan d'akin ta bud'e ido ta ganta a ciki kafin yanzu.

a hankali ta taka ta nufi kofar da tafi yakinin nan ne bathroom ta bud'e ta shiga.

a sannu

ta tub'e kayan jikinta tayi wan

ka tare da yin al'wala ta d'auro towel da tagani a bayin, tad'anyi jim bata iya wanka ta maida kayan da ta cire.

a hankali ta bud'o kofar ta leko babu kowa da sauri ta fito.

rike da kayan tana tunanin taya zatayi sallar ba hijab kayan kuma bazata iya maya

rwa jikin ta ba.

tana saka da tunanin aka turo kofar, da sauri ta kalli kofar tana kare jikinta da gyalen ta.

ya karaso cikin d'akin ya aje laidar hannunsa bakin gado ya juya ya fita batare da yace ko mai ba.

yana fita tayi sauri ta matso ta bud'e laidar.

abaya ce a laidar sa da hijab shima a cikin laidar sa, da pant da bra.

da sauri ta saka kayan tazura hijab dai-dai lokacin da ake kwad'a Kiran sallar magriba.

ta haye sallayar da ta gani cikin d'akin, ta fuskanci ta in da sallayar ke kallo ta tada sallah.

tana idarwa ta mike da sauri ta fito parlour.

ganin baya nan ta nufi kofar sai dai ta rasa ta yadda ake bud'e kofar,

ta koma d'akin da tunanin masallaci ya tafi.

tana zaune tajiyo kiran sallar isha

bayan ta gabatar ta zauna zaman jiran shigowar sa ya bud

'e mata ta tafi.

ta gumi ta buga tana tunanin ta yadda akayi ma tazo nan.

tabbas tasan kasuwa sukaje taga wasu suna kallonta sannan suka biyo ta daga nan bata kuma iya tuna ko mai ba.

akasan ranta take fad'in

"To ina Aunty Maryam kar dai ace itama sun bita

,

to ya akayi kuma na ganni a nan tare da Sahab??."

haka ta rika tambayar kanta da kanta da bata da amsar da zata baiwa kanta.

gashi bata ga wayarta ba ba bare ta kira Maryam d'in ko Hajja Umma.

bata ankara ba taga 8 ta gota, ta mike da sauri ta isa bakin

kofa, sai jin kofar tayi a rufe.

da mamaki ta koma ta zauna bakin gado, ta kuma buga tagumi.

sai wajen takwas da rabi taji alamar ana bud'e kofar.

yana shiga ta mike da sauri.

ya karaso ya aje mata basket d'in abincin da Dr Khadija ta aiko masa da shi, san

in su biyu ne abincin yafi na inda da take aiko masa.

tun kafin yayi magana

ta shiga girgiza kai tana fad'in

"Na koshi na koshi bana jin yunwa, dan Allah Sahab gida zan tafi."

tayi maganar da sauri kamar zatayi kuka.

kallon ta yayi ta marairaice fuska hawa

ye ya cika kyakyawan idanunta.

ya juya tabi bayan sa da sauri har tana had'a wa da sassarfa.

ganin ya shige wani bedroom taja ta tsaya jim kad'an ya fito da makullin moto tabi shi da sauri.

tun kafin yace ta shiga mota ta bud'e ta shige.

sai da taga sun h

aura titi kafin tasoma jin nutsuwa.

ta rungume hannayenta ta cikin hijab dan sabo da sanyin EC dake tashi cikin motar.

idanunta akan hanya tana alla-alla su isa.

tafi mai nisa sukayi gidan Alhaji Tahir Abbas da gidan sa da rata sosai.

suna haurawa titin da

zai sada su da gidan Alhaji Tahir Abbas ta kuma jin dad'i.

suna isa dai-dai get d'in gidan yayi parking a bakin get.

da sauri ta kai hannu zata bud'e kofar taji sa a rufe,

ta juyo a d'an sanyaye ta kalle shi.

da sauri ta janye idanunta sakamakon had'uwar

da idanunsu ya yi.

'yar karamar laida mai d'auke da tambarin pharmacy a jiki ya mika mata, a hankali tasa hannu ta karb'a.

"Kullum kisha har ya kare."

ya fad'a yana janye idanunsa daga kallonta.

a hankali ta gyad'a kai ya bud'e motar da sauri ta fita.

yabi

bayanta da kallo har ta karasa get ta bubbo mai gadi ya bud'e ya leko,

ganin ita ce ya bata hanya ta shige gidan da sauri har tana had'awa da sassarfa.

sai da yaga shigarta kafin ya ja motar ya tafi.

Su Abba suna zaune suna alhenin lamarin da tuni hukuma

suka sunduma ciki.

suna ganin ta suka mike duk suka mike cike da mamaki.

Maryam ta tafi da gudu ta rungume ta na fad'in

"Feeryal ke ce ina kika shiga."

Hajja Umma ma ta rungumo ta.

Abba ko sai fad'in alhamdulillah ya ke.

ya ce "Dama hukuma sunce insha'all

ah zuwa dare za'a gano in da kike,

bari na kira wannan yaro Sadam dan yanzun nan yasake komawa, kasuwar dan yakuma bincikan lamarin, ku sake ta ta karaso zo zauna nan Feeryal hukuman suna waje ne shi ne basu shigo ba ai da sun shigo."

suka sake ta ta karo

suka zazzauna Abba ya mike yana fad'in bari yaje ya sami jami'an tsaron da suka samo ta.

ta ce "Abba ba da kowa muka zo ba fa, Sahab ne ya kawo ni."

Abba ya zauna yana dubanta ya ce

"Sahab wane ne Sahab kuma?."

da sauri Maryam ta ce

"Wai Abdulrahim kike

nufi?."

Abba ya mai da hankalin sa ga Maryam ya ce

"Wane ne shi d'in?."

"Abba Abdulrahim dai AA FIYA tsohon mijin ta."

Abba ya ce "Wane shi ne ya dawo da ke da ma shi ya d'au ke ki?."

da sauri Maryam ta ce

"Abba ni fa da take nuna min wai wasu suna kallon

, ni fa babu wan da na gani, ko da take gudun ma babu me binta ita kad'ai take gudun ta."

baki ta cuno ta ce

"Allah na gansu kuma sun bini, ni dai ban san ya akayi na ganni tare da shi ba,

amma shi ya dawo da ni."

abun da ta sani ta basu labari.

a take suk

a fahimci ciwonta ya tashi kuma taga halittun da ita kad'ai ke iya ganin su.

Hajja Umma ta ce

"Ai mun godewa Allah ma da ya takaita iya haka, Allah ya dad'a rufa asiri."

a take Abba ya sanarwa hukumar cewa an same ta.

Tun daga ranar ba'a sake barin ta ta

fita ko nan da can ba,

gudun abun da zai je ya dawo....

Lagos...



"Kuraiba ke ma lokacin barinki gidan nan ya yi."

Umma karima ta fad'a

tana wani shekewa da dariya tana kallon video da aka turo mata yanzu.

ta taka ta isa ta hakimce kan kujera tana kad

'a kafa,

"Ni ce mamallakiyar komai na Alhaji Abubakar AA FIYA, kar ki ji dad'i ki baje kafa hatta uwar mazan gidan ita kanta sai ta bar min gidan, yanzu ta kan ki zan waiwayo Kuraiba."

ta danna wani lamba ta kai wayar kunne.

"Ai kin ka yana kyau Jaguu yanz

u zakaji sakon ka, idan ka samo sauran zan turamaka tukuici mai tsoka."

ya ce "Angama Hajiya."

ta kashe wayar tana dad'a girgiza kafa...

Abuja....

Feeryal ce ta fito daga bayi da sauri tana fad'in

"Aunty Maryam ki kalli ni fa ashe da gaske ne kika ce na

rika cin abinci zan kara kiba, nakusa kai ki yau ma tuwa zanci da yawa na kara kiba."

Maryam dake zaune tana shayar da d'anta ta ce

"Kaji ta kamar wani abincin kirki ta ke ci, ke da shinkafarma bai fi kiyi cokali biyar ba kice kin koshi, sai dai in cake da

yogurt ne ke hura ki."

"Allah Aunty Maryam yanzu ina ci fa, ai kin ga banjima da cin abinci bama, yanzu zansa kaya naje na sake ci dan na fara jin yunwa."

Maryam tayi dariya tana fad'in

"Yarinya tana so tayi kiba ta dawo cin abinci."

gaban mirror ta zauna

tana murmushi tana shafa mai suna hira da Maryam, tana gamawa ta saka kaya ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta.

"Aunty Maryam."

ta kira sunan tana tana kallon ta ta cikin mirror.

Maryam ta d'ago tana duban ta, ta ce

"Ba ki gani ba Allah har tunbi nayi

, nayi kiba fa da gaske kuwa."

tayi maganar tana d'ame rigarta ta cikinta tana shafa shi.

Maryam ta girgiza kai tana mata dariya.

itama dariyar tayi.

ta zo ta d'auki Aiman tana fad'in

"Taho muje ka rakani muci tuwa, zan bawa Aunty Maryam mamaki idan naci n

a koshi nazamo katuwa kamar ta."

tayi waje Maryam ta biyo ta tana cewa

"Kamar da gaske wani cin abincin arziki zakiyi, muje naga yawan abincin."

Hajja Umma suka karasa dinning tana fad'in

"Ai zaki gani Hajja Umma zubo min tuwo cikin plt."

Hajja Umma ta yi

mata hararar wasa tana fad'in

"Ni na isa na zuba duk masu aiki sun koshi karshe na zubar, kwatan malmala zan saka miki."

"Ah to wai ita gani take wani abincin kirki take ci, kullum sai ta ce min wai ta kara jiki, har da wani wai yau har tunbi tayi dan ta

ci abinci d'azu."

Hajja Umma ta kalle ta tana zama kan kujeran dinning.

da sauri ta ce

"Ke Feeryal mike tsaye."

Hajja Umma tayi maganar tana dad'aatsowa kusa da ita.

ta mike tana cewa

"Allah Hajja Umma ke bakiga tunbin ba, ai kin san ina cin abiinci sosai.

"

"Bani d'an nan, ke Maryam karb'e shi."

Hajja Umma

ta karb'i d'an ta mikawa Maryam.

tana bin Feeryal da kallo daga sama har kasa.

da sauri ta ce

"Ke rabon da kiyi al'ada tun yaushe?."

shiru tayi tana son tuna tun yaushe ne rabon ta da yi.

Maryam ta ce

"

Ai kuwa dai kamar tun da tazo fa banga tayi ba."

Hajja Umma ta ce

"Amma Maryam baki da hankali amma kuma shine baki fad'a ba, ni ina zan sani tun da dake kuke rayuwa cikin d'aki, sai dai in kun fito mu had'u,

kullum kuna tare da ita, amma ki kasa gane sauy

i tare da ita, ni sam ban tab'a luraba in ba yau da aka kawo wanna zancen ba,

sabo da kullum babban riga abaya take fitowa da shi,

kina kallon ciki har yayi wayo a jikin yarinya ku kwana tare ku tashi tare ki kasa ganewa, duk da jikin ta d'anye ne dama ai

ko gashi nan ya kara d'anyace wa in ba ka lura ba bazaka gane ba dan jikin nata d'anye ne dama,

d'auko mayafin ki maza muje nan asibitin bayan."

Feeryal tabi jikinta da kallo tana mamakin maganar Hajja Umma.

sai da Hajja Umma ta fad'a kafin

Maryam take

ganin alamun ciki karara a jikin ta.

nan da nan Hajja Umma ta d'auketa sukayi asibiti, kwajin farko aka tabbatar mata tana da ciki, bayan anyi scanning aka tabbatar musu da wata uku da sati biyu ke nan cikin a jikinta...

ko da Abba ya sami labarin

Nan da

nan ya kira Daddy ya sanar masa.

zo kaga farinciki gun Daddy d'iyanin ya kira Abdulrahim, ya ce yazo yana niman sa.

batare da b'ata lokaci ba ya amsa kiran.

ya nimi guri ya zauna a kasan carpet.

Daddy ya dube sa da kyau sannan ya ce

"Yanzun nan na sami la

barin Feeryal tana da ciki, kimanin watanni uku da sati biyu, shi yasa na kiraka na sanar maka da wuri dan ka shaida."

shiru yayi kansa a kasa bai yi magana ba, Daddy ya ce

"Ka tashi ka je dama na shaida maka ne tun da wuri."

ya mike ya fice batare da y

a ce kala ba.......!

Babu editing sai a karanta da hakuri

Yana fita sukayi kiliya da Ajmaal zai shigo gurin Daddy.

Ajmaal ya yi masa gaisuwa na girmamawa kamar yadda ya saba, sannan ya wuce parlour'n Daddy.

a tsaye ya iske Daddy da alamar fita zaiyi,

y

a karaso yana fad'in

"Barka da warhaka Daddy."

"Yauwa Ajmaal ya aikin kun dawo?."

Ajmaal ya ce

"Eh mun dawo Daddy ai ki Alhamdulillah, dama document d'in nan ne na kawo ma ka sa hanu."

"Shi ne kabar yayan ku ya wuce ai da shi ka bawa yasa hannun kawai, ka

bisa ka kai masa ya sa hanu."

Ajmaal ya ce to, har ya kai bakin kofa Daddy ya ce

"Ajmaal kana da labarin kun sami d'a ko 'ya kuwa?."

da sauri ya juyo ya ce

"Aa Daddy haihuwa akayi ne wa ta haihu?."

"Ba haihuwa akayi ba tukun Feeryal ce ke da juna biyu, za

ku sami d'a bada jimawa ba, in Allah ya yarda."

Ajmaal da farinciki ya lullub'e shi ya wani tuma tsalle yana fad'in

"Yes! masha'allah im very happy."

Daddy ya bishi da dariya ganin ya juya da gudu ya yi waje..

Ajmaal bai tsaya ko ina ba sai sashin Mommy.

yana shiga da d'in bin farinci ya ce

"Mommy albishirinki Feeryal na da ciki."

Mommy Umma karima Siyama Sumayya Ameerah duk suna zaune cikin parlour'n.

dukkanin su zabura sukayi tare da had'a baki wajen fad'in

"Ciki!."

"Wallahi da gaske ciki take da shi."

ya yi maganar da farincikin daya gaza b'oyuwa tare da shi.

Umma karima da maganar ya nasheta yakusa kashe ta a zaune.

ta kasa iya furta komai.

sai zazzare ido take kamar tsohuwar mayya.

Mommy ko zama ta gyara

tana murtuke fuska "To sai me zaka zo kana fa

d'a min, ai dama karshen alewa kasa an turata yawon bariki kam ta ya bazatayi ciki ba."

"Mommy yawon bariki kuma? ciki kam ai na Ya Abdulrahim ne."

da sauri ta ce

"Kai kutumar ubanka, idan na sake jin maganar nan a bakin ka sai na ci maka mutunci,

au tanan

aka b'ullo taje tayi ciki za'a lankayawa Abdulrahim, shi da yake nan ita tana can wata duniyar, sabo da a b'ata masa suna to duk wanda ya fad'i maganar nan wlh bazan kyale ba."

"Allah ya baki hakuri Mommy amma ciki kam na sa ne, dan watannin cikin sun nun

a nasa ne."

Sumayya dake ta washe baki tun san da ya fad'a

ta ce "Alhamdulillah zamuyi baby, Ya Ajmaal Feeryal d'in ta zo ne?."

"Tazo gidan uban ki wa ai wlh ba a isa a yi min wanna sakar zaren ba, zancen banza fita ka bani guri, naga uban da ya isa ya ce

cikin nasa ne, dan uwar ki ke Sumayya da kike cewa zakuyi baby, d'an shegen ne abun alfahari,

tukunna ma yaushe Feeryal d'in tazamo dangin ki, ko kalen dangi kika soma, na sake jin maganar nan a bakin ku sai na ci ubanku dukan ku, shegu marasa mutunci da

rashin sanin ciwon kai."

Ajmaal kam tuni yayi waje abinsa bai ma tsaya jin abun da take kuma fad'i ba.

sai yanzu Umma karima ta sauke numfashi had'a da mulmulo wani uban ashar ta d'auna.

"Tamd'ijam! wata sabuwa wallahi karya ne!."

ta fad'i tana buga kafa a

kasa.

Mommy ta ce

"Zancen banza ne ma kawai."

Umma karima ta mike zumbur ta yi waje.

Hajiya ta rike hab'a bayan da Ajmaal ya gama fad'a mata zancen.

ta ce

"To ikon Allah yanzu ita yarinyar ciki gare ta, kuma na Abokin turawa ke nan, to ai shi ke nan Alla

h ya raba lafiya, amma wannan d'a ko ya zaizo haka zai fito irin uwarsa mutum-mutum aljani-aljani."

Ajmaal na fita Umma karima na shigowa.

ta nimi guri ta zauna tana fad'in

"Hajiya kin ji wani sabon labarin da ya fito a gidan nan kuma ko, wai Feeryal na da

ciki ana son juya lamarin ya dawo kan Abdulrahim."

Hajiya ta ce

"Yanzu wannan yaro Ajimi ya zo min da batun, na ce ko wani irin d'a za'a haifo, jinsin aljanu da mutane."

"Hajiya cikin nan fa bana Abdulrahim bane, ko kin mace yarinyar nan a cikin gidan na

n na kamata da wani kato ta sakashi cikin hijabi suna iskanci, sannan tun yaushe Abdulrahim ya sake ta, ba'a ce tana da cikin ba sai yanzu,

haba ai wannan zance hankali bama zai d'au ka ba,

duk shiri ne da son a b'atawa gida kamar wannan suna,

wlh idan aka

bari akan cikin Abdulrahim ne aka karb'i d'an shege a gidan nan, daga lokacin mutuncin gidan nan ya zube, ta ya ma yariya tana wata duniya a lankaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login