Showing 48001 words to 51000 words out of 95068 words
shike nan mu na
mu ido idan aka haifi aljani muna daga gege."
"Allah ma ya tsare."
cewar Gogga Bishira.
Umma karima ce da Mommy zauna anata kuskus, Umma karima ta kawo musu magani su sakawa Daddy a abinci wanda bokan ta ya bata.
sun rasa hanyar da zasu bi su saka masa
dan ba cin abincin su yake ba.
Umma karima ta gyara zama cikin yin kasa da murya ta ce
"Yanzu ya zamuyi gashi malam ya ce, mu tabbata yaci maganin nan, yana ci duk asirin da Hajiya Fatima ta masa zai karye, sannan ya sake ta tabar gidan nan, kin ga babu la
barin zuwan d'an shege cikin gidan nan, tun da ita uwar gayyar tabar gidan,
amma Hajiya Halima wani hanzari ba gudu ba, ga wani shawari mana, wata kila idan muka bi ta hanyar zamu sami kofar b'ullewa."
Mommy ta ce
"Yauwa fad'i muji Allah yasa ta b'ulle, a
yita ta kare."
Umma karima ta ce
"Na ce me zai hana a had'a Siyama aure da Abdulrahim, bayan aure da kwana biyu ta dafo abinci ta zuba maganin ciki ta kawo mishi, irin dai ace girkin amarya, amarya tayi girki ta kawo wa uban miji,
amma yanzu mu idan muka c
e zamuyi kinsan halin Alhaji ba lallai ne ma yaci ba, sai ya iya zargin wani abun ma,
amma idan ita tayi masa kuma yasan amarya ce zai iya ganin hakan a tsigar kyautatawa irin ta suruka, bazai kawo komai a ransa ba zai ci, amma me kika gani in kina gani da
wata dabarar sai a sauya, ni dai ina ga ita ce kad'ai hanya mai sauki, amma ya kika ce?."
Mommy ta d'anyi jimm sanna ta ce
"Eh to wannan hanyar da aka biyu tayi, amma kina ganin su yaran zasu amince, kinsan fa taurin kan Abdulrahim."
da sauri Umma karima
ta ce
"Haba haba Hajiya Halima kina uwar tasa bazaki iya juyasa yadda kike so ba, ai Abdulrahim yana jin maganar ki, kina bashi umurni zaiji,
nima zanje na tirsasa Siyama dolen ta ta amince dan bukatar mu yabiya,
idan ba haka ba fa wlh zamu zamo 'yan kallo
, muna ji muna gani mu da gidan 'ya'yan mu zaifi karfin zaman mu,
karshe ita da bata saka ko d'aya ba ita zata mallake gidan."
Mommy ta ce
"To shike nan inaga hakan kawai za'ayi."
Umma karima ta ce
"Yauwa shine magana Hajia Fatima tana son ganin bayan mu,
idan bamuyi da gaske ba kuwa sai ta kora mu da kafafunmu, dan malam ya tabbatar min da kalan asirin da take wa Alhaji, ya ce gurin manya manyan bokaye yake zuwa, tana yawo da sunan Alhaji da namu dan a farrakamu a kan 'ya'yan mu, gara mu tashi mu tsaya tun
kafin dare ya yi mana."
Mommy ta jinjina kai tana fad'in
"Ai kuwa ta sha karya."
Umma karima na fita Mommy ta kira shi, ta ce idan ya dawo tana niman sa.
har dare bai shigo ba takuma kiransa,
ko da yazo ta ce ya zauna tana da magana da shi.
bayan ya za
una Mommy ta ce
"Abdulrahim yakamata kayi aure fa zaman ka haka ba mata, bai kyautu ba,
ga Siyama kanwar Hajiya Karima na yaba da hankalin yarinyar, me zai hana ka aureta tun da 'yar gida ce ansan halinta, Kuraiba dai tsautsayi ce yasa na ce ka aure ta, am
ma ita wannan ai an san komai nata."
da sauri ya d'ago ya dube ta sannan ya ce
"Shi ke nan ni rayuwata a haka zata kare, ko wace kare da doki ita za'a bani na aura,
ai ni nagama aure Mommy ko da ina da burin na sake aure bazan auri wama kika ce Siyama take
ko wa? bazan aure ta ba,
idan zamata a gida ne bakwa so zantafi na baku guri."
yana kaiwa nan ya mike tsaya ya fice......!
Kuyi hakuri wlh nafi kowa son nagama littafin nan na huta wanna littafi ya katse min abubuwa da dama amma insha'allah mun kusa mu
karkare
Mommy ta bud'e baki tana kallon sa har ya fice.
a fili ta ke fad'in
"Ai dole na lallab'a ka a wannan karon dan burin mu ya cika, idan na ce zan d'aga jijiyar wuya hakar mu bazata cimma ruwa ba."
Wata mota ce ta sauke Kuraiba ta shigo gidan su,
a parlour ta tadda Hajiya Luba.
Hajiya Luba ta bita da kallon bakinciki.
ta kasara ta zube kan kujera tana fad'in
"Wai dan Allah Momma yau she ne zaki je ki sami Mommy ki bata hakuri na koma d'aki na,
wlh ni nagaji da zaman gidan nan, ko ba komai a can ina
ganin Abdulrahim naji dad'i,
haba dan Allah ni wlh nagaji ina son Abdulrahim shi d'in had'ad'd'en gaye ne,
ganin sa ma kawai yakan iya gusar da karamin kishi,
kar iddata ta cika azo kuma dole sai an sake d'aura aure."
wani uban harara uwar tata ta doka ma
sa tare da jan dogon tsaki ta ce
"Ai kin banza wai ke a hakan har kina tuanin Abdulrahim zai maida ki,
tun da kika dawo gidan nan fa kullum a kan hanyar fita kike,
kullum mai d'aukar ki daban mai dawowa da ke daban,
a hakan zaki koma ki cigaba da kasancewa
a matsayin surukar gidan AA FIYA,
ai tun da kika rushe min shirina ke ma bazaki sami abun da kike so ba,
sai ki mike kafa mucigana da zama dake a cikin gidan nan,
ke da Abdulrahim kuwa har a bada."
Kuraiba ta mike tana cewa
"To ai shi ke nan ni nasan yad
da zanyi na koma."
ta wuce d'akin ta....
A hankali cikin Feeryal ke dad'a wayo, kusan kullum tana tare da Ammie'n suna waya video call tana ganin lafiyar.
Maryam ta koma gun mijin ta can Ogun State bayan tayi wata biyu da haihuwa. yanzu ita d'aya ce tare
suke kwana da Hajja Umma, ita ke kula da ita sosai, wata nayi zata kaita gun awu a duba cikin aga lafiyar sa.
san da Major Sadam yasan da cikin yaji ba dad'i dan yasan dole yanzu sai ta hife cikin kafin ya samu damar aurenta.
ya kudara wa ransa zai jira t
a haihu amma ba zai jira har sai ta yaye ba, zai aure ta tazo da abun da ta haifa gidan sa.
san da cikin ya kai watanni 8 Daddy ya yi tattaki yazo garin Abuja.
ya ce yazo tafiya da ita yana so ta haihu a can Lagos.
Abba ya ce sam bazai tafi da itaba, a n
an zata haihu su da suka kasa iya rike ta.
da kyar Daddy ya shawo kan Abba ya aminta su tafi da ita.
karfe 8 na safiya jirginsu ya tashi zuwa Logos.
karfe goma saura suka iso Lagos, wanda tuni mota ya iso airport yana zaman jiran saukowar su.
direban Daddy
ya kwashe su suka nufi AA FIYA STREET.
Aunty na tsaye a farfajiyar side d'in ta tana zaman jiran isowarsu.
tun kafin motar ya gyara parking ta taho da sauri mai had'e da gudu ta taho jikin motar.
motar na tsayuwa ta bud'e da sauri tana fad'in
"Oyoyo 'Yamm
atan Ammie."
Feeryal da farincikin ganin Ammien ta ya lullub'e ta tafi to da sauri, zata rungume ta Aunty ta ce
"Tsaya tsaya bi a hankali."
tayi maganar tana kallon katon cikin ta.
kallonta bai isheta ba wai Feeryal d'in ta ce haka Allah buwayi.
Daddy ko D
ariya ya yi ganin yadda gaba d'aya ta tsaya kallon ta.
cikin tsigar zolaya ya ce
"To kaka Fad'imatu a kaita ciki ta huta mana."
Aunty ta yi murmushi tare da janyo hannunta suka shige ciki.. Daddy ko ya koma motar direba ya kaishi side d'in sa.
a parlour A
unty tasa ta zauna kasan carpet ta mike kafafunta, da suka d'an kumbura.
ta je dinning ta kwaso mata lafiyayyun cake data shirya mana na musamman, gami da yogurt na musamman ta dire shi a gabanta.
kana ta zauna gefen ta tana ta yi mata sannu, kallon Feerya
l baya isar ta wai 'yar ita ce da katon ciki irin wannan."
ta kuma fad'in
"Sannu kinji Feeryal Allah ya sauke ki lafiya, ga ababen kaunar ki na musamman na shirya miki."
murmushi ta yi ta ce
"Ammie yanzun fa ina cin abinci musamman tuwo sosai nake ci."
"A
i dole kici abinci Feeryal wannan ciki, dole ya saki cin abinci."
sunkuyar da kamta tayi tana kai loman cake bakin ta.
Aunty ta d'au waya ta kira Ammah ta shaida mata isowar Feeryal d'in.
kan kace me Miemie ta shigo.
ta bud'e baki da hanci tana kallon ta.
"Kai Miemie babu oyoyo."
Feeryal ta fad'a tana mata murmushi.
"Hum Feeryal ke ce haka?."
Miemie ta fad'a tana rike hab'a tare da zama kusa da ita, cike da farinciki mai had'e da mamakin ganin ciki ya bayyana sosai a jikin ta.
Ammah data shigo yamzu itama t
sayuwa kallon Feeryal d'in tayi da mamaki.
kana ta rangad'a gud'a tana fad'in
"Kaga d'an duma ko a fad'e ka ko ayi shiru zaka bayyana kanka,
anyi sake d'an zaki ya girma,
Allah sarki Feeryal sannu da kokari Allah ya kauda idon makiya."
Aunty ta yi dariya t
ana fad'in
"Kai Ammah'n Miemie irin wanan gud'a da kirari irin haka."
"Barni na fad'i da babban murya lokacin fad'ar ne yayi, kaga ikon Allah ba'ayi wa Allah dabara, shi ke tsara komai yadda yaso baya shawari da kowa."
Ammah tayi maganar tana zama da ci ga
ba da fad'in
"Amma ace cikin nan bai kai na haihuwa ba duk girmansa."
Aunty ta ce
"Ai kuwa dai kam da sauran wata d'aya nan gaba."
"To Allah ya bud'i ido lafiya."
Aunty ta amsa da "Amin ya rabbil alamina."
Tuni labari ya karad'e gidan Feeryal ta dawo da c
iki rukuku.
hankalin Umma karima ya tashi, yaran gidan kuwa sai zuwa suke kallonta 'ya'yan Umma karima suka kai mata rohoto ciki ne babba a jikin Feeryal, hankalin ta ya dad'a dugunzuma.
Ajmaal na dawo daga gurin aiki bai wuce sashin su ba ya shigo sashin
Aunty.
baki ya bud'e yana kallon Feeryal da katon ciki.
cikin ya zauna d'as ya yi mata kyau duk da girman sa,
ta kara haske sosai.
murmushi ta yi masa ta ce
"Sannu Ya Ajmaal."
ya karaso yana fad'in
"Sannu Feeryal ke ce da gaisuwa ai,
muna godiya da marab
a da zuwan babyn mu."
murmushi ta kuma tana sunkuyar da kanta kasa.
Shamsuddin da Faisal da suka biyo bayan sa, suma duk suka tsaya kallon ta.
duk ta gaishe su kanta a kasa, suna yimata barka da zuwa.
da nuna farincikin su da ganin cikin.
Aunty ta fito ta
ce
"Ku zauna mana Shamsuddin."
Ajmaal ya ce
"Dawowan mu ke nan daga gun aiki, zamu shigo anjima."
suka fita.
"Fito muje Bishira kar a ajiye abun fad'a, tun da ya amsa cikin nashi ne, ai shike nan maje mu dubota kar ace dai babu je, har ta kwana, yaro da
kalen fitina da son sa mutane wahala."
Hajiya dake tsaye tana jiran fitowar goggo Bishira tayi maganar.
goggo Bishira ta fito tana gyara mayafin ta suka nufi side d'in Aunty.
suna sallama Aunty ta tare su cike da karramawa suka zauna,
Aunty ta zamo bakin k
ujera tana gaida Hajiya.
ba yabo ba fallasa ta amsa.
suka gaisa da goggo Boshira,
Hajiya ta ce "Ina ita yarinyar take?."
Aunty ta mike ta ce "Yanzu ta shiga ciki bari a kira ta."
Goggo Bishira ta ce
"Aunty Faty in bacci take ki barta."
"Aa ba bacci take ba
, yanzunnan ta shiga."
Aunty ta shige d'aki suka fito da Feeryal.
Hajiya ta bita da ido har ta zauna kasan carpet.
Hajiya data rike baki ta ce "To haka abun yayi, to sannu ya nauyin jiki."
Feeryal ta sunkuyar da kai tana cewa "Ina kwana."
Hajiya bata amsa
ba sai kallon ta da take. tana cewa
"Da gaske dai cikin ne."
goggo Bishira ta dube ta ta ce
"Sannu Feeryal ya nauyin jikin."
kai takuma sunkuyar wa tana wasa da 'yan yatsunta.
sannan ta gaishe ta.
goggo Bishira ta amsa tana kuma tambayar ta ya nauyin jiki.
nan ma kai ta kuma sunkuyar wa.
Hajiya ta mike tana cewa
"To Allah ya bud'i ido lafiya."
goggo Bishira tayi wa Aunty sallama suka tafi.
Umma karima bata iya hakuri ba sai da tazo sashin Aunty ta gane wa idanunta zahiri.
Aunty na ganin ta tayi wani murmu
shi ta ce
"Ki karaso mana Hajiya Karima ya zaki tsaya daga bakin kofa,
ga gurin zama ki zauna."
Umma karima data dibirbirce da ganin Feeryal zaune da katon ciki a gaba.
ta juya har tana cin karo ta fita.
Aunty ta yi dariya tana girgiza kai.
Kwanan Feery
al biyar da zuwa, bata fita ko kofa daga parlour sai bedroom d'in kwanan ta.
suna zaune da Miemi suna hira, Miemie ta mike ta ce zata tafi, Feeryal ta rako ta har wajen get d'in Aunty wan da tun zuwanta bata fito nan ba.
suna tsaye a bakin get d'in ta waje
Miemie ta ce
"Feeryal wannan katon ciki yaushe ne zaki haifo shi,
ni yau sai naga cikin ya karamin girma, ko zaki haihu ne? ni nayi zaton a ranar da kika zo ma Allah haihuwa zakiyi, sai numfashi kike da kyar."
Feeryal tayi murmushi.
"Miemie ni kam zan ko
ma nagaji da tsayuwa."
"Ke ai yanzu ko abin gudu ya zo sai dai a gudu a barki."
"Kai Miemie me zai hana ni iya gudu."
ta juya tana dariya.
cak ta tsaida dariyar da take, hango shi yana tahowa da alama masallaci zai tafi, dan ana kokarin shiga sallar la'asa
r.
da sauri ta kawar da kanta ganin idanunsa a kanta,
tasa kai ta shige dad'an sauri...
Tun da Feeryal ta shiga watan haihuwan ta, bata bacci kullum ciwon baya ciwon mara,
yau kuwa ta tashi da ciwon dayafi na kullum.
hankalin Aunty ya bala'in tashi.
Dad
dy ya ce maza a wuce da ita asibiti.
asibitin Dr family'n su aka wuce da ita, dan Daddy ya ce baza'a kaita asibitin Abdulrahim ba.
yana dubata ya ce C'S za'ayi mata batare da b'ata lokaci ba aka shige da ita operation room.....!
Nan da nan aka soma shir
ya yi mata CS, in da likitan da wasu ma'aikatan sa suka soma gudanar da C'S d'in.
Aunty da Daddy suna tsaye a bakin kofar hankali tashe.
sai anbaton sunan Allah suke da nima mata sassauci daga Allah.
motarsa ne ya shigo asibitin a guje,bai tsaya wani dai-
dai parking ba ya fito da sauri.
Daddy ya bishi da kallon me ya kawo ka, fuska a d'aure.
cikin tafiya mai kamada gudu ya shige cikin operation room theater theater d'in da sauri.
yana shiga
sauran ma'aikatan suka juyo, dan ganin wanda ya shigo musu kai t
saye,
shiko likitan bai d'ago ba yana ta kan tsaga ta.
da sauri ya isa gaban wani hanga ya janyo rigar da likitoti suke sakawa idan zasuyi
operation, ya d'aura kan kayan jikinsa. kana ya zaro hand glove da facemask ya nufi gadon ya na saka hand guluf da
facemask.
da sauri ya shige gaban sauran ma'aikatan ya tsaya gefen likitan, dai-dai san da likitan yake tsaga fatar karshe.
yayi saurin kai hannunsa guda kan hannunsa ya ruko askar. yayin da
hannunsa guda ya kai fuskarsa ya ja facemask d'in kasa likitan y
a juyo ya kalleshi, sanin ko waye shi
sai ya sakar masa ya d'an ja gefe. ya gyara zaman facemask d'in, cikin kwarewa da sanin aikin sa ya idda karasawa ya zaro babyn, wanda tuni ya calla kara yana wutsil-wutsil da kafafu da hannaye.
ya lumshe ido yana bud'
e wa a kansa, kana
ya mikawa likitar bayan ya rabashi da cibiyar,
shiko likitan ya mikawa sauran ma'aikatan, suka kai shi gadon da aka tanada domin gyara jarirai.
ya gyara tsayuwarsa da kyau yana bud'a hanyar tare da kuma zaro wani d'an.
ya sauke wani ajiy
am zuciya a fili, yayin da idanunsa ke kan d'an.
bayan ya kuma mi ka musu, nan da nan ya soma d'in ke ta
in da likitan ya cigaba da taimaka masa da karb'ar kayan aikin da miko masa abun da yake bukata.
nurse biyu mata suna tsaye daga kanta suna ta janta da
hira,
jifa-jifa take amsasu cikin tsiririyar muryarta.
cikin kankanin lokaci ya gama, ya matso ta kanta idanunta a lumshe take basu amsar magar da suka matsa mata da yin sa.
hannunta ya kama ya had'e hannayen nasu kana ya sake a hankali ya juya.
a sannu t
a bud'e idanunta tabi bayan sa da kallo, bawai ko dan ta gane ko waye bane sakamakon shigar dake jikinsa irin na sauran likitotin.
ya taka gaban gadon da jariran suke, wanda tuni an kimsasu cikin kaya masu kyau da tsada wan da Aunty ta taho da shi.
ido ya
kura musu suna ta shure kafafu da kokarin tura hannu a baki.
a sannu ya mika hannayen sa ya ruko hannayen su.
ya kura musu ido sosai yana d'an jijjiga hannun nasu, fuskarsa a yalwace da annuri yana ta sakin tsiririn murmushi wa yaran.
wasu nurse mata biyu
suka karaso gurin cikin girmamawa suka ce
"Sir bari mu d'auke su iyayen patent d'in suna waje, tun d'azu suke cewa a fito musu da su, anyi musu albishir twins aka ciro."
baiyi magana ba bai kuma fasa wasan da yake da hannayen su ba.
yakai 10second kafin
ya zame hannun sa daga nasu, yad'an matsa gefe.
suka d'auke su suka fito sa su.
Daddy da Aunty har suna rige-rigen karb'ar su.
Aunty ta rungume wanda aka mika mata tana fad'in
"Alhamdulillah!."
Daddy ma haka bakinsa ya kasa rufuwa.
bayan ya yi wa nurse's
d'in tukuici da kud'i masu yawa.
Abdulrahim