Showing 39001 words to 42000 words out of 95068 words

Chapter 14 - FEERYAL BOOK3 COMPLETE

kafarta,

tana

waigen su tsoro tashin hankali su suka bayyana a gareta.

tamkar hankalin ta zai bar jikin ta sabar tashin hankilin da take ciki.

Maryam da ta biyo ta tana kiran sunanta hankali tashi, Maryam ta saka ihu ganin tasa kai zata sallaka titi, batare da tsayuwa

duba titin ko jiran ababen hawa su wuce ba.

karan ababen hawa kake ji suna taka burgi.

jama'a sai d'aura hannu suke a kai suna salati.

wani irin burki wata moyar da tayi daf da ita tayi,

duk da haka sai da gaban motar ya tureta ta zube kasa.

da sauri ta

mike a zabure ganin sun dumfaro titin, ta karasa sallake titin da gudu a kid'ime ta yi bayan wata mota dake pake gefen titi.

tab'oye jikin ta na kakkarwa.

tarika rab'ewa jikin motar tana tafiya da gefe da gefe.

yana zaune cikin motar gaban wani shago yana

jiran Dr Imran daya shiga shopping cikin shagon.

tun ihu da salatin mutane ya maida hankalin sa kan titin, sai dai sam bai lura ya gane ko wace ce ba, sai yanzu da yake kallon ta ta cijin

glass d'in motar.

kamar gilmawar walkiya suka ketaro titin

wani igigitaccen kara ta sake ganin sun bayyana a gaban ta.

da karfi cikin zafin nama ya bud'e motar,

dai-dai sanda tayi baya luuu zata zube kasa ya yi saurin rukota ya janyo ta jikinsa.

da karfi, hannu ta shiga nunawa tana fad'in

"Gasu nan sun biyo ni, ba

na son ganin su ina jin tsoron su!."

hannunta ya sake jikin ta ya sake gaba d'aya,

idanunta ya rufe.

da sauri ya d'ago yana duban in da take nuna masa, bai ga kowa ba.

da sauri ya ciccib'e ta ganin hankalin mutane yafa dawowa kansu.

ya bud'e mota ya shinfi

d'a ta a sit d'in baya, kana ya dawo mazaunin direba da karfi ya figi motar.

Dr Imran daya fito da kaya niki niki a hannunsa ya bud'e baki yana kallon yadda ya figi motar.

A bakin wani katafaren had'ed'd'en gida yayi hon,

aka wangale mata get.

yasa kai y

a shige ciki, a farfajiyar gidan ya yi parking, ya bud'e ya fito da sauri kana ya bud'e gefen da take ya ciccib'o ta ya yi ciki da sauri da ita.

kai tsaye bedroom ya wuce da ita ya shinfid'a ta a kan gado.

kugu ya rike yana kallon fuskarta da idanunta suke

a lumshe.

numfashi ya fesar kana ya juya har yakai kofa zai fita, yaji ta yi wani irin gurnani.

da sauri ya juyo, tayi wani irin mikewa ta fincike d'ankwalin kanta ta yamutsa gashin ta dayake a tsefe ta kuma yamutsa shi tare da girgiza kan.

ta duru a gado

n tana kokarin rufawa a guje.

da karfi ya tako ya dawo da baya, ya damko hannunta.

ihu ta kuma yi ta fizge hannunta ta d'aga kafa zata kuma sa gudu.

ya kuma damko ta ya d'au ke ta da wani irin gigitaccen mari da sai da ta kife kasa.

har sai da gefen bakin

ta ya fidda jini.

Ta d'ago tana wani irin kecewa da dariya, da wani irin murya mai fidda amon sautin muryoyi daban daban har kala uku.

"Hahahahaha yau ba makawa sai mun tafi da ita, tun da muka samo ta."

ta mike yayi saurin rigata isa jikin kofar,

ya ruf

e tare da murza key ya zare key'n ya jefa cikin aljuhun wandon sa.

da wata irin murya take fad'in

"Tun da muka samo ta dole zamu tafi da ita, shekaru masu tarin yawa muke jiran zuwan wannan rana,

tun ranar da muka sami tabbacin zuwanta duniya muka d'aura d

'amarar samo ta,

mun zaga duniyar nan muna niman ta,

an baza mu ta ko ina dan nemo ta, tun da muka samo ta dole mu tafi da ita, mu karb'o kambun karramawa, dan mu mukayi nasarar samo ta,

muna da hanyoyin fita da yawa basai ta kofar can ba."

ta yi wani mike

wa da karfi cikin b'acin rai ya sa mata kafa ta zube kasa.

wani irin ihu gami da hargagi tayi, ta d'ago tana binsa da wani irin kallo da kwayar idanunta suka sauya isuwa wani kala na ban tsoro.

mari ya d'auke ta da shi cikin fusatacciyar murya ya ce

"D'auk

e idanun ku a kai na!."

kururuwa ta sayi tare da birgima a kasa tamkar wacce aka zubawa ruwan zafi a jiki.

tana fad'in

"Kai bil'adama karka sake dukan mu da wannan hanun naka,

mai kamada garwashi, idan ba haka ba zamuga bayan ka."

bata rufa baki ba yakuma

d'auketa da mari,

ihu ta kuma tana birgima da maganganu barkatai da muryoyi daban-daban.

ayoyin alkur'ani ya soma karantawa yana tufa mata, tuni jikin ta ya d'auki rawa tana.

tana fad'in

"Ka dai na kona mu ka daina kona mu, bazamu fita a jikinta ba har sai

mun kaita ga sarkin bakaken aljanu,

bazamuyi asarar shekara da shekaru muna neman ta mu same ta yanzu mu kasa tafiya da ita baaaa, ka dai na kona muuuuu!

bazamu janye baaaaa sai mun tafi da itaaaaa!."

ta zabura zata mike ya shako wuyanta tare da taka kafa

funta da nashi kafan.

sannan yaci gaba da tofa mata ayoyin Alkur'ani.

wan da tuni jikin ta ya shiga kakkarwa, tana kokarin janye hannunsa a wuyanta ta kasa.

nan da nan zufa ya shiga tsastsafo mata.

ko wani hudan gashi na jikin ta, fita yake da zufa hatta d

aga cikin gashin kanta kuwa zufa ne ke gangarowa zuwa fuskarta.

Da kyar ta iya bud'e baki cikin muryar jin azaba suke fad'in

"Zamu fita zamu tafi ka dakata kada ka kashe mu, mun rantse maka zamu kauce a jikin ta."

a fusace ya ce

"Fita zukuyi duka a jikin

ta ba kaucewa ba! idan kuka sake muka kara karo da ku to na rantse muku da girman zatin Allah sai na kashe ku! kada ku sake tunanin dawowa jikin ta, idan kuka kuma sai na kashe kuuuu!!."

yayi maganar cikin karaji sosai mai firgita kunnuwan duk mai saurara.

kai take gyad'awa ba kakkautawa tana fad'in

"Mun rantse munyi alkawari duk randa muka kara dawowa ka kashe mu, sakar mana manumfasa zamu tafi, zamu fita a jikin ta bazamu sake dawowa ba mun d'au alkawari, hannunka akwai garwashi ka sake mu zaka kashe mu,

zamu fita zamu fita."

ya sake mata wuya yana binta da mugun kallo, da karfi ta saki tawayen atishawa sau uku a jere jikinta ya sake ta sulale kasa.

Ya mike tsaye yana jan dogon tsaki, ya gyara zaman rigarsa.

ya sunkuya ya d'ago ta cak ya nufi cikin bathro

om da ita.

cikin bathtub ya direta,

a sannu yashiga zare kayan jikinta,

ya tub'e ta tsaf batare da ya cire bra da pant d'in jikin ta ba.

yana tallafe da ita, yana daga wajen bathtub d'in.

kana ya soma tara ruwan d'umi cikin bathtub d'in.

nannauyan numfash

i ta sauke jin d'umin ruwan na rasa ta, ta juya kai ta dad'a manna kanta jikin hannunsa kamar jaririya a hannun uwanta.

a hankali take sauke numfashi.

ido ya kurawa fuskarta bacci tayi a hannunsa.

d'aya hannun nasa ya saka cikin ruwan ya d'iba ya wanke mat

a fuska yayi hakan har sau uku.

kana a hankali yakai hannunsa zuwa bayan ta, ya b'alle mab'allin bra'n jikinta ya zare shi yana kauda kai da ganin ta.

sannan ya cirota ya had'eta da kirjinsa ido ya rumtse jin zuciyar sa ya buga.

a sannu ya ware idon akan t

a, da sauri ya d'auke kai daga kallonta.

ya zaro towel ya nad'eta da shi,

yafice a bayin da d'an sauri ya karasa bakin gado ya kwantar da ita.

ya janyo blanket ya rufeta yasa hannu ta cikin bargon ya zaro pant d'in jikinta, da yake a jike.

ya ajiye shi na

n bakin gadon kana ya juya ya nufi kofa ya zaro key cikin aljuhun sa ya bud'e kofar ya fita.

A b'angaren Maryam ko da ta ketaro titin bata ganta ba.

tashi waige-waige tana tambayar mutanen gurin.

tanayi musu kwatancen ta, wasu suka ce mata sunga san da wa

ni ya d'auke ta ya sa a mota.

kuka maryam ta fashe da shi tana fad'in ta shiga uku.

ta koma in da motar su yake cikin kuka take fad'a wa direban su abunda ke faruwa.

direban ma yashiga tashin hankali.

ta shiga motar ta ce suyi sauri su tafi gida su sanar.

suna isa gida Maryam ta shigo da kukan ta.

hankali tashe Hajja Umma take tambayar ta meke faruwa ina Feeryal.

cikin muryar kuka take sanar mata abun da ya faru.

Hajja Umma tayi salati tana kwad'awa Abba kira.

Abba ya sauko hankali tashe, jin abunda ke faru

wa hankalin sa yayi bala'in tashi.

nan da nan yayi report, wa jami'an da kes d'in ta na wancan karon yake hannun su.

nan da nan aka baza jami'ai da tuanin mutanen mai tawargar d'aukar amarya ne,

suka d'auke ta.

dan har yanzu yana tsare ana ta kan kama mut

anen sa...

Sai wajen kare 4 na yamma ta farka daga nannauyan baccin da take.

a hankali ta mike tana ma mammatse ido jin jikin ta ya bala'in mata tsami.

mika tayi gami da salati tana jin kamar an mata duka duk jikinta yayi laushi.

a hankali ta ware idanunt

a a cikin d'akin, da mamaki take dad'a ware idanunta, ganin d'akin ya sauya mata.

hannu ta kai ta mussuke idanunta, takuma ware shi da kyau cikin d'aki.

sai kuma da sauri ta janye bargon dake rufe a jikinta,

ta kai duban ta jikinta tana mamakin ganin ta ba

bu kaya sai towel shima towel d'in ba'a d'aure yake ajikin nata ba.

da sauri ta ja towel d'in ta d'aura a kirjin ta,

da sauri ta zamo bakin gadon ta sako kafafunta kasa, tana kokarin mikewa tsaye.

ta hango pant d'in ta a gefe.

mamaki yakuma kamata.

kafafun

ta ta ta aje kasa tana kokarin mikewa ba shiri ta koma ta zauna tana fad'in

"Wash."

jin yadda kafar tayi tsami tana yi mata zafi sosai.

kallon kafar tayi taga kafar tayi ja.

a hankali takai hannu ta shafo wuyanta da take jikin sa kamar ba nata ba.

karar bu

d'e kofar da taji ne yasata d'agowa da sauri.

wani irin zabura tayi da ganin shi. kwakwalwarta ya tsaya ya daina aiki, me yakawo ta nan, ko shine zatace me yakawo shi.

to ma wai a ina take ne?.

ganin ya na takowa cikin d'akin gaba d'aya ta kid'ime tashiga

ja da baya ta haye sakiyar gadon.

tana nuna shi da hanu murya na rawa take fad'in

"Ina ne nan me yakawo ni nan? kar ka matso ni."

ganin yana kuma nufo ta ta zamo ta d'aya gefen ta duro a gadon,

ta yarfe hannu tana fad'in

"Wayyo kafata."

ta d'aga kafar da k

yar ta nufi kofa.

ganin kokarin fita take ya daka mata tsawa.

"Ke kar ki sake ki fita a haka."

bata tsaya ba ta mika hannu zata bud'e kofar,

ya yi taku biyu zuwa uku ya damko hannunta ya dawo da ita ciki.

kuka ta saka tana fad'in

"Ni dai tafiya zanyi wayy

o Ammie na."

gaba d'aya ta birkice tana son kwatar hannunta da ko kyakkyawar motsi hannun baiyi ba a cikin nasa.

ido ya zuba mata kamar mai son karantar wani abu.

da sauri ya d'aga ta cak ya direta kan gado,

sai kuma da sauri ya kai hannu ya ja towel d'in

jikinta kasa nonuwanta suka bayyana.

wani irin b'ari jikinta yakara,

ta saki kara wani irin masifaffen tsoro yakuma lullub'e ta.

kai tashiga juyawa tana fad'in

"Sahaaab kar kayi min dan Allah."

da sauri ya kuma rirriketa yana cewa

"Tsaya mugani."

yayi mag

anar idanun sa a kan ababen kirjinta......!

Ya kurawa nonuwan ta ido dai-dai kan nipples d'in,

sai kuma da d'an sauri ya kai hannu ya cafko d'aya yana dad'a kurawa nipple d'in ido.

zabura tayi jin yadda ya cafko breast nata, ta ja numfashi mai cike da

mashahuriyar tsoro cak numfashin ya tsaya.

kallon sa ya maida kan fuskarta kana ya saki nonon nata ya kai yatsarsa hancinta, ido ya d'an waro jin bata numfashi.

ya mike yana mamakin yadda take babu wuyan tsoro yasakata suma.

ya sauko a gadon yaje ya d'au k

o kayan ta daya cire mata, d'azu yanzu a bushe suke,

ya saka mata underwear da doguwar rigar ban da bra da pant.

ya sunkuce ta yayi waje da ita, yana kallon fuskarta da idanunta ke a lumshe.

cikin mota ya sakata gidan baya ya dawo mazaunen direba ya ja mot

ar mai gadi ya bud'e masa ya fita.

yana fita daga gidan titi ya ketare ya isa bakin get d'in

AA FIYA HOSPITAL, asibitin sa da ke cikin garin Abuja.

wan da yake kusa da gidan sa titi ce ta rabasu.

duk weekend yana Abuja ranar juma'a yake zuwa da yamma yaga

patients asabar da lahadi, ranar Monday kuma yabi jirgi ya koma Lagos da safe.

cikin hanzari security'n dake bakin get d'in asibitin suka wangale masa get, yasako hancin motar duk suka rusuna suna miko masa gaisuwa.

ya gyara pakin a farfajiyar asibitin,

yafito da sauri ya bud'e gefen da take ya cirota ya rungumo ta a jikin sa da sauri yayi cikin asibitin da ita.

yana shiga hankalin jama'a da ma'aikatan dake cikin asibitin yadawo kansa.

da sauri wata Nurse ta turo welcher, in da wasu Nurse's maza uku suka

nufo sa suka mika hannu zasu karb'e ta.

hannu ya d'aga musu tare da furta

"It's okay."

ya sakai da sauri ya shige office d'insa.

a kan gadon dake cikin office d'in ya shinfid'a ta, kana cikin hanzari ya shiga bata taimakon gaggawa ya d'aura mata drip mai

d'auke da allurai cikin sa.

cikin hanzari ya kunna na'uwar Scanning.

ya matso ya ja rigarta sama yana kallon shafaffen cikin ta fari tass.

a sannu ya d'aura scanner kasan mararta.

yayin da ya maida idanunsa kan computer, yana d'an yawo da shi kasan marar

ta.

ido ya waro sosai kan computer yana mai dad'a d'an danna scanner a marar nata.

da sauri ya kalli fuskarta kana ya maida dubansa ga computer, yana sauke ajiyan zuciya a fili.

knocking akayi batare da ya janye idanunsa daga kallon na'urar ba ya ce

"Who i

s at the door?."

daga bakin kofar akace

"Im Dr Khadija Barau Can I come in?."

tsayuwarsa ya gyara ya dad'a jan underwear jikin ta ya rufe cinyoyin ta zuwa gwuiwarta,

sannan ya ce

"Yes, come in."

ta turo kofar da sallama ta shigo, babbar mace ce da shekaru

n ta zai iya kaiwa 40 tana sanye da medical glass.

ita d'in d'aya daga cikin likitotin da suke aiki da shi ne, Dr Khadija Barau tana da zama da iyalanta a nan cikin garin Abuja,

a matsayin kani ta d'auke shi tana bashi kulawa irin na yaya da kani,

a duk sa

n da yake Abuja d'awainiyar abincin sa a wuyanta ya ke sanin baya cin abincin masu aiki.

kullum direban ta yana hanyar kawo masa abincin safe da rana da dare, a gidan sa dake nan.

Ta karaso ciki tana fad'in

"Doctor naga shigowarka lokacin ina duba wani m

ara lafiya ne, ba dai bigeta kayi da mota ba, subhanallah buguwar a ciki ke nan, Allah yasa babu wata matsala sosai? ."

ya ce

"No, she is my wife."

zaman gilashin idanunta ta gyara da kyau, kana ta kalli Feeryal dake kwance sannan ta maida idanunta kan co

mputer ta waro ido tana cewa

"Wow! I congratulate you."

kai ya jinjina yana kokarin numfashin ta ya dawo.

Dr Khadija ta masa ta gurin kafafunta ta saka tafin hannunta tana gogo tafin kafanta.

ta ce

"Doctor, hurry up and get her breath back, don't take t

oo long."

bata rufa baki ba ta ja numfashi, ta zabura tana kokarin mikewa.

Dr Khadija ta bita da murmushi tana fad'in

"Sannu kinji."

ido ta kura mata ta lumshe idanunta ta bud'e su a kanta.

firgigit tayi ta mike zaune tana kokarin durowa a gadon.

tayi sa

urin ce mata

"Bi a hankali, a kwai drip a hannunki."

da sauri ta kalli hannun nata kana ta kalle shi.

Dr Khadija ta ce

"Dr Allah ya sawaka bari naje akwai patients a layi."

ta fita tana mata Allah ya sawaka.

tana ganin fitarta ta kuma yunkurin sauka, hann

un ta da ruwa ke shiga ya rike.

kuma yunkurin sauka tayi ya ce

"Ki jira ya karasa shiga."

kallon ruwan tayi saura kiris, ta kalle shi tana kwab'e fuska zatayi kuka.

cikin muryar da ke kunshe da son yin kuka ta ce

"Ni gida zan tafi."

tayi maganar tana koka

rin kwatar hannunta ta kasa.

ido ya zuba mata hawaye ya fara gangara fuskarta.

bai sake ta ba yana rike da hannun nata bai kuma yi magana ba.

yana kallon yadda hawaye ke bin fuskarta.

yana tsaye rike da hannun nata har ruwan ya karasa shiga,

ya cire mata.

ai ko da sauri ta dire a gadon tana yarfe hannu.

key ya d'auka ya bud'e d'ya kofar wan da kofar fita ce ta baya.

alama ya yi mata ta zo ta wuce.

a hankali ta tako ta wuce yabi bayanta.

ke b'abb'en hanya ce wan da shi kad'ai yake bi, idan zai shigo asibitin

ko zai fita, a kwai motar hawan sa a d'an ma dai-dai cin parking lot a gurin.

motar ya bud'e ya shiga san nan yayi mata alama da ta shigo.

jikinta na d'ari-d'ari ta shiga yaja motar mai gadin dake bakin get d'in wannan hanyar ya bud'e suka fita.

tana ta r

aba ido wai ya akayi ne ta ke ta ganin ta a wurare daban-daban, wan da ba ita take kawo kanta ba.

tunanin ta ne ya tsaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login