Showing 57001 words to 60000 words out of 95068 words

Chapter 20 - FEERYAL BOOK3 COMPLETE

yau kar mu sak

e damuwa tun da dama nasu ne."

Aunty ta matse ido da karfi tana son had'iye kukan da ya taso mata.

da sauri ta mika mata cup d'in ta mike ta fice ta shige d'akin ta, dan bata son yin kukan agaban ta.

bin bayan Aunty tayi da kallo har ta fice.

a hankali ta

kai cup d'in bakin ta ta kurb'i yea d'in.

Aunty tayi kuka sosai kafin ta fito bayan ta wanke fuskarta ta share kamar batayi ba.

tana fitowa Abdulramin ya shigo d'auke da sallama mara sauti a bakin sa.

Aunty ta amsa ya karaso ciki ya gaisheta batare da ya h

ad'a ido da ita ba.

Aunty ta amsa gaisuwar tasa gami da d'an yin murmushi ta ce

"Tana ciki."

ta juya ta koma d'akin ta.

a sannu ya tako ya tura kofar, da sauri ta d'ago zaton ta Aunty ce.

ganin shine ta sauke idanunta kasa.

ido ya kura mata tare da soma ta

kowa cikin d'akin, ya iso bakin gadon.

tana jin yadda idanunsa yake kafe a kanta.

sinkayo muryarsa tayi

"Ina mai baki hakuri na rasa 'ya'yan ki da kikayi."

ta jiyo maganar sa daga in da yake tsaye a kanta.

da sauri ta d'ago ta kalle sa sai kuma ta cuno lip

s tare da sauke idanunta kasa ta ce

"Ya'yan ku dai ai dama naku ne, ba haka kuka zab'ar musu ba, ni babu ruwana."

tayi maganar tana dad'a cuno baki cikin yanayin ta mai sanyi da fita da yanayin shagwab'a.

cike da jin haushin yadda Mommy'n sa tasa Ammie'n t

a tashiga damuwa take ta kuka akan yaran.

ta juya kai ta d'aya gefen tana mai dad'a cuno baki gaba.

bataji takun tafiyarsa ba sai karar bud'e kofa taji, ta juyo ta hangi bayan sa yana fita daga d'akin.

kai ta kuma juyawa tana mai dad'a b'ata fuska da gaske

wai haushi take ji dan ansa Ammie'n ta kuka..

"Feeryal."

taji an fad'a ta juyo da sauri jin muryar Chuchu da Chulu.

yunkurin mikewa tayi da sauri, suka rike gefe da gefen kafad'un ta suna cewa

"Yi a hankali Feeryal."

ta zauna suka zauna a gefen ta suna

fad'in

"Ki gafarce mu san da abunnan ya faru bama kusa, munyi bakincikin da muka gaza taimakon 'ya'yan ki har suka salwanta, muna niman afuwarki ki gafarce mu."

hannaye bibbiyu suke rokonta.

ganin yadda suma suka nuna damuwa sosai ta ce "Ni fa yanzu na dai

na damuwa tun da dama nasu ne, ko ma me sukayi da su oho ni ban damu ba."

Chuchu da Chulu sun dad'e a gurun ta kafin suka tafi...



Zaune yake a office d'insa, idanunsa a lumshe ya jingina bayan sa jikin kujera yana d'an jujjuyawa.

Dr Imran ne ya shigo y

a karaso yana yi masa kallon tausayawa,

tabbas uwansa ta kasance mai son kai,

ko bai fad'i damuwar sa ba bayau ya saba zama da shi ba,

duk da halayen sa masu wuyar gane wa ne, amma tabbas ya lura da shiga kunci tare da shi tun ranar da uwassa tayi sananiyy

ar mutuwar 'ya'yan sa.

table d'in gaban sa ya bubbuga, a hankali ya bud'e lumsassun idanuwan sa.

Dr Imran ya ce

"AA akwai C'S da kasa time 1 30 an shirya ko mai saura 20 seconds yanzu."

mikewa yayi tare da d'aukar makullin motar ya nufi kofa yana cewa

"Kay

iwa Dr John magana bazan yi C'S ba."

Dr Imran yabi bayan sa da kallo har ya fice.

ire-iren wad'an nan halayen nasa duk wan da yake tare da shi yakan sha wuya wajen gano inda lamuran sa suka dosa, baka b'a gane albiblarsa.

Ya shige mota ya bar asibitin.

ko

da ya koma gida wanka yayi ya sauko parlour, da gajeren wando kad'ai babu riga a jikinsa.

ya kure gudun AC yana zama kan kujera.

system nasa dake kan table d'in gaban kujerar daya zauna, ya kunna,

sosai ya mai da hankalin sa ga system d'in.

yana dada ware

idanunsa cikin system d'in, yayin da damatsan hannunsa suke bud'awa.

sai kuma ya mike zumbur ya nufi stairs, cikin zafin nama ya yake had'a stairs bibbiyu ya shige bedroom dakika uku yafito yana gyara zaman riga da wandon jikinsa.

ya sauko ya d'au makilli

n mota yayi waje da sauri.

ganin yadda ya figi motar da sauri cikin azama mai ganin side d'in ya wangale masa get.

ganin yadda ya dumfaro babban get da gudu security suka bud'e masa get ya fice kamar zai tashi sama.

sosai yake sharara gudu kamar ba'a ciki

n gari yake tafiyar ba a wajen gari yake.

mintuna kalinan suka kawo shi asibitin da akayiwa Feeryal C'S.

bai ko dai-dai ta parking ba ya duro a motar da bai tsaya rufe kofar motar ba.

wata doguwar igiya mai karfi yana rike a hannunsa.

da karfi ya naushi ko

far office d'in Dr ya bud'e yasa kai ya shige ciki.

da sauri Dr ya mike yana fad'in

"Lafiya Dr AA FIYA! zaka shigo ta irin wannan yanayin?."

hannunsa yakai kan belt d'in kugunsa yana gyara zamansa, yashiga d'aga kafarsa yana takowa cikin office d'in tamkar

na mijikin zaki!.

Dr ya mike zumbur yana kuma fad'in

"Ya zaka shigo min kai tsaye irin haka, kamar baka san aikin ka ba."

a gabansa ya tsaya yana binsa da wani irin kallon da ya kusa sashi ya saki fitsari a wando, murya a gautsatse ya ce

"Ina file d'in da

ke d'auke da rcd d'in bazata iya haihuwa ba dole sai an mata C'S!?."

da sauri Dr ya ce

"Ya zaka zo kana challenge d'ina, I'm Dr ka sani yadda kake likita haka nima likita ne,

so baka da hurumin shigo min kana yi min irin wannan tambayar kamar ka mai da

ni bansan aiki na ba,

kasan na fika a shekaru tun kafin ka zamo likita nake aikin likitanci,

so ba bu wani abun da zaka nuna min, in zaman duniyar ce nariga ka sanin ta,

haka ma hai kin."

wani irin wawan mari ya d'auke shi da shi, da sai da bakin sa ya fas

hi jini ya fita daga gefen bakin,

ya shako makokwaronsa

cikin kakkausar murya ya ce

"Waya saka!."

numfashi na sama-sama idanunsa suka firfito da kyar ya iya fad'in.

"Ka sake ni zan gaya maka."

gara shi ya yi da jikin bango da karfi sai da kansa yayi jini,

kana ya saki wuyan nasa yana kuma d'auke shi da marin daya fi na farko.

a gigice ya ke fad'in

"Babu wan da ya sani, ba zata iya haihuwa ba ne dole sai an mata C'S."

igiyar daya shigo da shi ya janyo yana ware shi,

yayin da suffarsa ya dad'a rikid'ewa ya c

anza izuwa na ban tsoro.

da sauri likitan yashiga ja da baya fitsari ya kwace masa, murya na gargada ya ke fad'en

"Ka dakata na gaya maka da gaske babu wan da ya sani."

wani irin naushi ya kai masa ya zube kasa ya d'ad'd'aure shi da igiyar ya ciccib'o shi

ya yi waje da shi, ya bud'e bayan bot ya jefa shi ciki, ya shige motar da mugun gudu yabar asibitin.

A wani b'ari na gidan gona ya shiga da shi,

wani katon d'aki ne mai d'auke da na'urori ya yi masa kyakkyawan d'auri jikin kujerar karfe.

bayan ya masa duk

a bugun girma, ya farfasa masa jiki ya yi masa jina jina sannan

ya kunna shocking jikin kujerar."

ya soma jijjiga gami da ihun azaba.

sai da ya tabbatar da shocking ya shige sa sannan ya kashe.

numfashin azaba yake saukewa,

yana fad'in

"Zan gaya maka kad

a ka kashe ni, matar baban ka ce ta sani."

ya kunnan na'uwar d'auka gani kai tsaye yayi connecting da satellite

d'in in house nasu AA FIYA STREET.

gaba d'aya TV gidan ya d'auke duk wanda yake zaune gaban TV gyara zama ya kuma yana kallon TV da mamaki gan

in sa a wani guri shi da Family Dr su,

dayake d'aure jini na fita aduk in da yamasa rauni.

Bappa Salihu Daddy Dad Abbieh Ajmaal Shamsuddin Faisal.

duk suna parlour'n Daddy.

in da kowa ya mai da hankalin kan TV.

dai-dai in da Abdulrahim yake d'auke sa da m

ari ya shako wuyansa.

likitan ya tuntsire da dariya jini na sauka a bakin sa,

"Idan ka kashe ni a ina zaka sami sauran labarin, akanta ita da ban ma aikata mata komai ba, ina daf da aikatawan ka shigo."

Aunty na d'aki ita da Feeryal kiran Ammah ya shigo w

ayarta.

tana d'agawa Ammah ta ce

"Ammien Feeryal kina gaban TV kuwa?."

Aunty ta ce "Aa Ammah'n Miemie me ya faru."

da sauri ta ce

"Kunna TV ki gani ko ni kad'ai nake gani."

da sauri Aunty ta d'au rimut ta kunna TV d'akin Feeryal.

tayi arba da abun da kowa

yake gani a cikin gidan.

Sumayya ta shigo bedroom d'in Mommy da gudu tana fad'in

"Mommy Mommy kunna TV ki gani."

Sumayya ta d'au rimut ta kunna TV.

Hajiya ta gyara zama tana fad'in

"Bishira Kulu wa nake gani ne nan kamar abokin turawa,

shirin fim ya koma k

o kisan kai shima ya soma."

Hajiya tayi d'ip da maganar jin yana fad'in

"To bari na aika ka lahira tun da can kake son zuwa."

ya mika hannu zai kunna shocking d'in da sauri likitan ya ce

"Aa a'a zan gaya maka Hajiya Karima ce ta sani na ciro mata mahaifan

ta tare da 'ya'yan a cikin mahaifan,

kafin kuma na cire kazo, hahahaha ka girgiza ne to ai bakaji komai ba, dan wannan ba shine karo na farko ba,

mamarka da amaryar baban ka yanzu haka babu mahaifa a jikin su........!

Mommyn twins ce

"Dukansu tasa na c

ire mata mahaifar su,

lokacin da baban ka ya auri Hajiya Fatima da wata uku ta sami ciki, ta kwanta tana laulayin cikin, ni ya kirani nazo naja jinin ta, dan naje nayi gwaji dan an d'auka malaria ce, bayan na je na gwada naga ciki take da shi,

na dawo gida

n ku domin na yiwa Alhaji albishir da cikin nata,

Hajiya Karima ta tare ni kafin na isa sashin Hajiya Fatima,

ban kawo komai ba nafara yi mata albishir da cikin amaryarta.

a take ta yi min tayin kud'i masu soka kan tana son na ciro mata mahaifar da cikin k

e ciki na kawo mata,

kuma zatasa a gina min sabon asibiti.

yawan kud'in da kwad'ayin sabon asibitin yasa banyi tantama wajen aminta ba, dan ba kud'in wasa tace zata bani ba, a take na canza result d'in na sanar wa Alhaji akwai wani ciwon da nagani cikin j

inin ta, ina so a kawota asibiti dan a bincika da kyau.

a ranar Alhaji ya d'auke ta ya kai ta asibitin nayi scanning naga twins ne a cikin nata na tsawon 2mon.

na samarwa Hajiya karima tace fad'uwa yazo dai-dai da zama dama mahaifa mai d'auke da twins take

so, ta kuma karamin kud'i a kan wanda tace zata bani,

a take na sanarwa Alhaji akwai wani ciwo a cikin ta wanda idan har ba'a yi gaggawan cirewa ba zata iya rasa ranta.

nan take ya sa hannu ya ce a cire mata.

a ranar ba'a kwana ba nayi mata

operation nac

iro mahaifar mai d'auke da cikin 'yan biyu, na bawa Hajiya Karima nan take ta tura min kud'in da tace zata bani,

a cikin watan tasa aka fara gina min sabon asibiti.

na gina sabuwar rayuwa nasoma fantamawa da kud'in da ta bani ga sabuwar ginanniyar asibitin

a."

Yaja numfashi yana fad'in

"Zan sha ruwa ka bani ruwa na sha."

wani gigitaccen mari ya d'auke sa da shi, zuciyarsa na tafarfasa, ya shiga naushin bakinsa sai da ya zubda masa hakoram gaba.

Daddy ya yi wani irin mikewa hannu na rawa yake nuna Dr ta ciki

n TV yana fad'in

"Dama a ranar mahaifan Fad'imatu ka cire da 'ya'ya na aciki, kayi min karyar cewa ciwo ne a cikin ta!?."

Bappa Salihu ya roko Daddy ya zaunar da shi yana cewa,

"Zauna Abubakar Allah baya zalunci sannan karya bata d'aurewa raminta kurarriy

a ce."

Abbie da Dad Ajmaal Shamsuddin Faisal, duk sun cika da d'inbin mamakin daya sasu bud'e baki suna kallon abun da ke faruwa kamar a shirin film.

a b'angaren Hajiya kuwa wani uban salati ta sake tana fad'in

"Laaaha'ilaaha'illaaa, amma Karima anyi sheg

iyar bakar makira, a she dama Fatima ba juya ba ce ta sani kullum da kalar gorin da nake mata kan ta kasa haihuwa, ashe-ashe ita ce tayi sanadin rashin haihuwar nata,

amma dai Allah ya d'ebe miki albarka Karima."

goggo Bishira da kulu sai tafa hannu suke.

"Allah ya toni asirinki Hajiya Karima, Yaya Abubakar ya haifo zaki mai share masa hawaye,

munafuka algunguma, ka kashe shi Abdulrahim sannan kazo ka had'a da ita."

cewar goggo Bishira tana gyara zaman ta idanunta akan TV.

Ammah ta fito da sauri ta nufi sa

shin Aunty Miemie na biye da ita.

tayi mamakin ganin Aunty zaune tana kallon TV tana sakin murmushi, Feeryal na gefe tana sharar kwalla.

Ammah ta karaso ciki jiki a asanyaye.

Aunty ta d'ago ta kalle ta tana murmushi ta ce

"Ammah'n Miemie ashe dai ni ba juy

a ba ce."

Ammah ta zauna jiki ba kwari ta na cewa

"Hajiya Karima idan batayi wasa ba bazata sami rahamar Allah ba."

Ihun azaba ya yi yana fad'in

"Ka taimaka ka bani ruwa na sha zan gaya maka sauran."

gorar ruwa ya d'auka da sauri ya bud'e baki dan ba ha

nun karb'a duk a d'aure hannayen suke.

ya tsiyaya masa ruwan cikin baki ya kama sha kot-kot, baiyi fin kurb'a uku ba, ya sheka masa sauran a fuska kana yayi wurgi da gorar.

Dr ya ja numfashi yana latse ruwan dake bin bakin sa sannan ya cigaba da fad'in

"

Bayan wani lokaci a ranar da mamarka zata haifi Ameerah, tare da ita akaje asibiti bayan tayi min tayin kud'i mai tsoka ta waya, ganin yawan kud'in yasani amincewa suna kawo ta asibitin ita da baban ku da kakarku, nayi rubutu na ce C'S za'a mata, kamar yad

da Hajiya Karima ta bukata, bayan da kanta ma zata iya haihuwa na ce dole sai an mata C'S,

kamar yadda Hajiya Karima ta shirya.

babu b'ata lokaci mahaifin ka ya sa hannu aka shiga da ita.

bayan na ciro Ameerah sannan na cire mahaifar na damkawa Hajiya Kari

ma, ta biyani kud'in da tayi min tayinsa.

ganin yawan kud'in yasa naji dad'i, har na kara ginin asibiti na da kud'in,

a cikin 'yan shekarun nan ma ta kuma nima na tana niman mahaifa yazo a sa'an zanyi wa wata C'S na cire na kai mata ta biyani.

shi ne da ak

a kai matarka haihuwa ta ce na cire mahaifar da yaran a ciki gaba d'aya,

kuma ai kazo kafin na cire ka sani dai ba ni na kashe maka yara ba mamarka ce ta kashesu,

kar ka kashe ni kayi hakuri dan Allah kar ka kashe ni."

d'ip TV ya d'auke ya dawo tashar da k

owa ke kallo..

Mommy da ta mike tsaye jikinta na tsuma, tun san da Sumayya ta kunna mata TV har yanzu da TV ya d'auke.

wani irin suya gami da girgiza zuciyarta yake, lallai mutum a bin tsoro ne, wacce ta yarda da ita tabata dukkan yarda, ashe ita ce makas

hin ta.

lallai hausawa sunyi gaskiya makashin ka na tare da kai.

nannauyar numfashi Mommy ta sauke a fili ta furta

"Lallai Hajiya Karima kin jima kina zurma ni a rami, ban ankara ba har sai da kika ruftamin kasa a ka."

Wani irin zufa ne yake sassafowa Umm

a Karima, ta cire d'ankwalin kanta tana fifita.

"Bazan kyale ka ba Abdulrahim tun da ka tono asirin da ya dad'e a bisne."

Bilkisu Rahma Nabila duk suka juyo ga mahaifiyar tasu, ya yin da jikinsu ya yi matukar sanyi, gami da matukar jin mamakin abun da mama

r tasu ta aikata.

Siyama ko hannu ta nad'e duk da tasan Aunty'n nata ma'abociyar ta'ammali da bokaye ne, amma batayi zaton abun nata yakai nan ba.

Bilkisu ta ce

"Umma me yasa zakiyi haka."

duk sauran 'yan'uwan nata ma kalar tambayar da sukayiwa uwar tasu k

e nan.

Saddiqa data shigo da sauri ta ce

"Umma kowa a gidan nan ya kalli abun da ya faru, Umma ya zakiyi haka."

Nabila ta d'aura hannu a kai tana fad'in

"Mun shiga uku mu da gidan uban mu za'a rika mana gori da hantara, wanna tsintacciya Feeryal d'in shike

nan ta sami abun mana gori itama,

shike nan muda gidan mu zata rika yimana kallon banza."

Rahama ta ce

"Wacce irin magana ce wannan Nabila ai abun da Umma ta aikata, shine abu mafi muni ba kallon da Feeryal ko mutane zasuyi mana ba,

idan Feeryal tayi mana

kallon banza batayi laifi ba, dan mun aikata mata fiye da yadda zata mana."

Nabila ta yamutsa fuska tana fad'in

"Ko ma me Umma tayi wlh ni da gidan ubana bata isa tayi min kallon banza banci ubanta ba."

Bilkisu ta ce "Ki rufa mana baki Nabila, abun da Umm

a ta aikata abun kunya ne agare mu,

Umma baki kyauta ba."

Bilkisu bata rufa baki ba

Umma Karima ta juya ta shige d'aki tana fad'in

"Dole naje gurin boka yanzu yarufa min bakin kowa."

ta shiga tana kokarin d'aukar mayafinta

taji wani irin karar durowar abu

da saida ilahirin side d'in ya girgiza, tamkar sama zai rusho ya afko kasa.

girgiza mai matukara ban tsoro da firgitarwa.

kafin ta dawo hayyacin ta daga sananin firgitan data shiga taji anyi sama da ita an buga da kasa.

wasu halittu masu ban tsoro suka bay

yana wa ganin ta,

ya yin da

muryoyin su masu matukar bantsoro da firgitarwa suka karad'e jinta tamkar dodon kunnen ta zasu zazzago kasa.

idan kaji ana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login