Showing 1 words to 3000 words out of 71408 words
*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA
Bismillahir Rahmanir Rahim
Book one
*Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya bani iko da kuma damar fara rubuta wannan labari. Ina addu'ar Allah ya sa yadda na fara lafiya na ƙare shi la
fiya. Amin*
*wannan labari zai zo daga kashi na
ɗ
aya zuwa kashi na uku Insha Allah. Na
ɗ
aya zai zo a kyauta yayinda kashi na biyu da na uku zai zo na ku
ɗ
i a farashin 400*
*wannan labari ƙirƙirarre ne, idan yayi kamaceceniya ta wani fanni da rayuwar w
ani, wata ko wassu to bisa kuskure ne, ba ayi dan cin zarafin kowa ba*
01
(CONGO STATE is a fictional state in Nigeria. Jahar Congo ƙirƙirrerren Jaha ce a Nigeria)
*MAFARI*
Da ƙyar kyakykyawar matashiyar budurwa da ke riƙe da hann
un Mahaifiyarta ke jan numfashi da dogon hancinta da ya zauna
ɗ
as a tsakiyar fiskarta wanda ya ƙara ƙawata ma ta fiskar sosai. Iskar asibitin wanda ke gauraye da warin magunguna, allurai, jini, fitsari da sauran su shi ya ke yiwa mutum iso a duk lokacin d
a ya kusancin farfajiyar asibitin. Ansan Asibitoci da wari amma wannan warin na sa ya fita daban. Ko dan Asibitin ta gwamnati ne, oho. Rabonta da zuwa General Hospital Congo tun wani ciwo da Abba yai kusan shekaru biyar da su ka wuce.
Ba su jima da zama
a wajen reception ba wata mata mai
ɗ
auke da jaririya ta fito daga office
ɗ
in Likita ta ce " wai Zainabu Inusa ta shiga"
Budurwar nan ta kama hannun mahaifiyarta su ka shige ofishin Likitan.
Lokacin da su ka shigo Likitan yana ta cike-cike a file
ɗ
in su. Ba tareda ya
ɗ
ago ba ya ce "Malama Zainabu mi ya ke damunki?"
"Ciwon ciki"
Da sauri Likitan ya
ɗ
ago fiskarsa saboda yadda muryar budurwar ya shige shi, bama wannan ba, a file
ɗ
insu an rubuta Zainabu Inusa matar aure ce mai shekaru talatin da
takwas wannan budurwa kuwa da ƙyar idan ta haura shekaru ashirin da
ɗ
aya.
Lokacin da ya ha
ɗ
a ido da budurwar sai da numfashin sa ya tsaya na
ɗ
an wasu sakanni. Muryar da fiskar ba baƙon sa ba ne amma wannan ne karo na farko da ya ke ganin ta gaba da gaba.
"Mu ne wanda Dr Ubaydullah Gida
ɗ
o ya turo" ta fa
ɗ
a da siririyan muryarta me ratsa zuciyar mazaje.
"Masha Allah! ke ce ƙanwar mu kenan. ya jikin Umma?"
Sai da ta yi murmushi kafin ta amsa mi shi da cewa jikin Umma da sauƙi.
Duban Umma Dr Hassan
yai ya ce "Umma tun yaushe kika fara jin ciwon cikin?"
Ido kawai Umman ta bishi da shi har ya gama maganar sannan ta maida dubanta ga 'yarta wacce ta fara ma ta bayani da yaren kurame. Dr Hassan ya sake baki yana kallon ikon Allah, sai yanzu ya gane dalil
inta na iya sign language na kurame dan watarana a wani rahoto da ta na
ɗ
a ta yi amfani da shi wajen yiwa wani kurma tambayoyi. Abin ya burge mutane da dama amma yanzu da ya ke ganinta tana yiwa mahaifiyarta tafintan (interpreting) duk abinda ya ke fa
ɗ
a sai
tausayinta ya kama shi. Bayan ya gama sauraron bayanen ta ya ma ta tambayoyi sai ya rubuta mu su takardar scanning ya ce su je su yi su kawo ma sa ya gani.
Ba su suka bar Asibitin ba tun takwas saura minti biyar da su ka shigo har sai ƙarfe sha
ɗ
aya d
a minti biyu.
Lokacin da su ka fito daga Asibitin Keke daban-daban su ka hau saboda sauri da budurwar ke yi dan ta je wajen aiki yayinda Ummanta ta wuce gida.
Da gudu-gudu sauri-sauri ta shigo cikin ma'aikatar ta su, kai tsaye studio na biyu ta wu
ce domin yau ne za ta fara gabatar da sabon shiri da za a fara a tashar su. Ƙarfe sha
ɗ
aya da rabi saura minti hu
ɗ
u ta gani lokacin da ta duba agogon hannun ta. Ta ja dogon numfashi kafin ta bu
ɗ
e studio ta shiga.
Zaro ido waje ta yi ganin wanda ke zaune
akan kujera tareda baƙon su na mako.
Gefen C Y ta tsaya wanda ke ta faman saita Camera dan fara
ɗ
aukan shirin.
"C Y mi yake faruwa? ya na ga Iklimah a nan"
"Sorry Sweery, Oga ya chanja ki"
"Amma..."
"We are going live in one, two, three
" C Y ya fa
ɗ
a yana
ɗ
agawa Iklimah hannu.
Iklimah ta yi wani fari da ido ta fara bayani kamar haka: ma su kallon mu kuna tareda gidan Talibijin na HILL TV, inda a dai-dai wannan lokaci mu ke gabatar mu ku da sabon shiri mai suna BAƘON MU wanda ni Iklimah
Jibril zan gabatar. To a yau dai mun taho mu ku da babban baƙo. Jajirtaccen Ɗan kasuwa wanda duniya ta ke damawa da shi. Baƙon na mu dai shine Alhaji Isa Madara...
Juyawa ta yi cike da
ɓ
acin rai ta bar cikin studio
ɗ
in. Wannan wani irin walaƙanci ne
Oga ya ma ta haka.
Kai tsaye ta wuce sama inda office
ɗ
in Ogan su ya ke.
Gaisawa ta yi da Sakatariyar sa wata mata wacce za ta iya kaiwa shekaru Arba'in zuwa Arba'in da biyar.
"Madam Deborah Oga na nan?"
"Yana ciki" ta amsa tana cigaba da la
tsa na'urar computer da ke gaban ta.
Wucewa ta yi ciki zuciyar ta cike da jin haushin Ogan na su.
Office ne da ya fi kowanne girma a cikin kamfanin. Mamallakin office
ɗ
in na zaune kan kujera yana duba wa su takardu.
A
ɗ
an ƙaramin katako da aka ajiye a
tsakiyar table da ke gaban sa an rubuta *MD Adamu Riba
ɗ
o*
"Ina kwana Sir"
"Lafiya"
"Sir na ga Iklimah ta kar
ɓ
i shirin BAƘON MU"
"Eh" ya fa
ɗ
a ba tareda ya
ɗ
ago ya kalleta ba.
"Sir amma ni aka ba wa shirin nan, ranan Jummu'a kai da kan ka ka
jaddada mini cewa ni zan fara shirin nan, ni na tsara tambayoyi, ni ne na kira Alhaji Isa Madara..."
"Kin zo da wuri?" Yai tambayar yana
ɗ
ago ma ta ƙananun idanun sa.
"Sir inada uzuri, na yiwa C Y text tun da sassafe, kuma na zo kafin lokaci ya ci
ka"
"So?"
"Sir wannan ba adalci ba ne, kuma..."
"Fita" ya fa
ɗ
a da
ɗ
an ƙarfi.
Ranta a
ɓ
ace ta fice daga office
ɗ
in da sauri. MD ya bi bayan ta da kallo yana ƙara yabawa da wannan halitta ta Asiya.
Kai tsaye office
ɗ
in su ta wuce wanda su takw
as ke amfani da shi. Mutum biyu ta tarar a wajen ta gaishe su kafin ta wuce kan madaidaicin desk
ɗ
inta ta zauna, ta ajiye jaka da wayoyin ta sannan ta kifa kan ta a kan desk
ɗ
in.
Idan mutum ya ce yana son ka ka ƙi shi shikenan sai ya zama abin damuwa.
Tunda ta fara aiki a wannan waje MD ke takura ma ta.
"Da wani ƙaton tumbinsa a wajen" ta furta a fili tareda jan dogon tsaki...
Yinin ranan gaba
ɗ
aya a hasale ta ke saboda abinda MD ya ma ta. Ita gani ta ke ma da gangan yai hakan, dama tun asali Ikl
imar ya ke so ta yi shirin ba ita ba. Dama ƙwalele ya ke son yi ma ta...
Kusan ƙarfe biyu na rana su ka fita
ɗ
auko rahoto chan wani ƙauye. Fa
ɗ
a ne ya
ɓ
arke tsakanin manyan ƙabilu guda biyu da su ke wajen.
Sun samu sun tattara bayanai sannan sun yi hira
da mutane da dama a ƙauyen kasancewa an
ɗ
aura labarin ne life. Fa
ɗ
a ne da ya faro daga ƙona gona guda
ɗ
aya sai abin ya zamo rikicin ƙabilanci akayita ƙone-ƙone.
*"bayan Gwamnatin Jahar Congo ta turo jami'an tsaro zuwa wannan ƙauye, ƙura ta fara lafawa
, yayinda iyayen da aka yi awun gaba da 'ya'yan su su ke cikin Alhini. Na tambayi wani jami'in tsaro wanda ya tabbatar mini da zaran sun gama bincike sun tabbatar babu hannun yaran nan guda biyar a sakawa gonar Malam Bala wuta za su sako su wa iyayen su. M
una fata dai wannan abin da ya faru zai tsaya a iya haka domin zaman lafiya ya fi zama
ɗ
an Sarki. Ta ku ASIYA-SHAHIDA FARUQ BABA, tashar Hill TV"* ta ƙarasa maganar tana murmushinta mai shiga rai.
Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da C Y ya ce cut. Ba yau
ta fara kawo rahoto ba amma yau tunda ta fara ta ke jin ƙirjinta na mata nauyi. Ko dan ranta a
ɓ
ace ya ke oho. Ta
ɗ
an
ɗ
aura hannunta a ƙirji tana jin yadda ya ke bugawa da ƙarfi. Ikon Allah! Ko ranan da ta fara tsayuwa gaban camera ta kawo rahoto shekara
ɗ
aya da ya wuce bata ji irin wannan tsoron ba. Lokacin da ta ke kallon camera ta sani tana fiskantar duniya ne, amma yau ji ta ke kamar mutum
ɗ
aya ta ke fuskanta, kamar wannan mutumin da ke kallonta koma wanene idonsa yana ma ta nauyi, ya saka ma ta tsoro,
ya kassara duk wani ƙwarin gwiwa da ta ke da shi.
Za ka fahimci halin da ta shiga ne kawai idan har ka tuna yadda ka ke ji idan wani mutum da ka ke tsananin jin kunya ya zuba maka ido. Kana jin idon sa na yawo a ko'ina na jikin ka har hakan ya saka ma k
a kasala har ma ka kasa iya aiwatar da komai, idan ma kana wani abu to ka dinga kuskure kenan.
To ko dai Ubayd yana kallon news
ɗ
in nan ne? Ta tambayi kanta.
"You Ok?" C Y ya fargar da ita daga tunanin da ta ke yi
Ta gya
ɗ
a ma sa kai tana murmushi.
"Ko dai saboda abinda MD ya miki ne? Yau gaba
ɗ
aya kin yi wani iri. Babu wani spark lokacin da ki ke camera"
Yana maganar yana lanƙwasa doguwar tripod da aka
ɗ
aura camera a kai.
"Ban san mi ya ke damuna ba, its like kamar mutumin da na ke jin kunya
yana kallon program
ɗ
in nan. I'm feeling his eyes all over me"
"Ba ma her ba, his eyes. Lallai Aseey, ko kin yi sabon crush ne" C Y ya fa
ɗ
a yana dariya.
Ba yau Ubayd ya fara ganin report
ɗ
inta ba. Infact akwai ranan da ya ke wajen ma ta ke ba da r
ahoto a gaban camera
ɗ
in kuma bata ta
ɓ
a jin irin haka ba. Idan ba Ubayd ba waye? Certainly not Umma da Abba saboda su kam tun ma kafin ta fara aikin sun kasance confidante
ɗ
inta. Ta iya tuna
ranan da aka ƙara mata matsayi ta zama field reporter sai da ta k
ira suka boosting confidence
ɗ
inta kafin ta fara aikin.
Idan ba Ubayd ba idan ba Abba da Umma ba, to WAYE? Ta fa
ɗ
a tana kallon motar su da su C Y ke faman saka kayan aikin su ciki...
***
GOVERNMENT OFFICE, CONGO STATE,
dif...dif
...dif... ƙarar da yatsar sa ke bayarwa kenan lokacin da ya ke buga table
ɗ
in gabansa da yatsarsa manuniya. Tunda aka fara rahoton ya ke kallo bai
ɗ
auke idon sa ba sai da mai ba da rahoton ta fa
ɗ
i sunan ta sannan aka
ɗ
auke wajen zuwa announcer da ya ke cha
n studio yana ƙara commenting akan abinda ya faru a ƙauyen.
Ya bibiyi labarin ne saboda shine abu na farko mai mahimmanci da ya aiwatar a wannan shekara wanda har an kusa cin rabi cikin ta.
Mutane dayawa kallon hoto su ke ma sa. It has being a challeng
e lokacin da aka kira shi da gaggawa aka sanar da shi fa
ɗ
an daya taso a ƙauyen Kayal
ɗ
in. Gwamna baya ƙasar dan haka shine ya ke da damar ba da umurni a aiwatar da duk abinda ya dace gameda matsalar.
Tuni ya rattaba hannu a takarda wajen tura jami'an tsa
ro ƙauyen domin daidaiton lamurra a wajen. Ya ji da
ɗ
i da reporter
ɗ
in ta yabawa Gwamna duk da dai shi da yai aikin ba Gwamna ba ne, da alama ko dai ta manta cewa Gwamna baya gari ko kuma dai ta furta Gwamna ne a matsayinsa na wakilin Gwamna
ɗ
in.
Gidan Ta
labijin na HILL TV ba ta Gwamnati ba ce shiyasa ya damu da ganin rahoton daga tashar maimakon CONGO NEWS wacce ta ke gidan Talabijin na
gwamnati ba lallai a ya
ɓ
awa Gwamnati baƙin fenti ba idan har ba su yi abinda ya dace ba sai ma ayi ƙoƙarin kare su.
B
ai ida wannan tunanin ba wayar sa ta hau ringing. Mr Governor ya gani
ɓ
aro-
ɓ
aro a screen
ɗ
in. Da sallama ya amsa wayar cikin muryarsa mai sanyi.
Daga
ɓ
angaren Gwamna kuwa ko amsa sallamar bai yi ba ya ce ma sa maganan Albashi da zai sa hannu akai ya bari
sai ya dawo tukunna.
Deputy Governor ya ce "Mr Governor nan da kwana shida fa kenan "
"To mutuwa za su yi kafin kwana shidan?"
Bai ce mishi komai ba har ya gama magana ya kashe kiran.
Yayi tunanin ya kira ne domin yai ma sa magana akan fa
ɗ
an da
aka yi a ƙauyen Kayal may be ma ya yaba ma sa akan ƙoƙarin da yai wajen daƙile fa
ɗ
an da wuri amma shi damuwar shi kada ya saka hannu a bawa mutane Albashinsu har sai ya dawo. Yau Albashin ya shigo daga gwamnatin tarayya, kwanan wata ya kama ashirin da bakw
ai idan aka ƙara kwana shida zai zama uku ga wani watan kenan, mutane za su ji jiki.
Minene amfaninsa idan har a matsayinsa na mataimakin Gwamna ba zai iya aiwatar da komai na cigaban al'umma ba idan Gwamna baya nan. Ya tabbata kenan shi hoto ne.
*
**
Lokacin da Asiya su ka koma office har anfara kiraye-kirayen sallar Maghriba. Tana shiga office
ɗ
in su aka sanar da ita saƙon MD da ya ke nemanta. A gajiye ta wuce office
ɗ
insa, ta sani ƙorafi ne zai yi ba komai ba. Tunda a wajensa kullum ba ta i
ya aiki ba.
"Miye matsalar ki ne Asiya?. Today's report was full of crap, sati biyu Gwamna baya gari amma kina ta fa
ɗ
in Mai girma Gwamna ya turo jami'ai, Mai girma Gwamna ya damu da talakawansa. Give credit to whom credit belongs. Kina ganin da Gwamna
Saminu Bacci ne zai tura jami'an tsaro cikin ƙanƙanin lokaci haka? I'm dissappointed in you"
Ita kwata-kwata ta manta da cewa Gwamna baya ƙasar to ko yana nan ai Deputy Governor hoto ne. Ba abinda ta ta
ɓ
a jin ance yayi sai shegen yin ado kaman mace. Ind
ai SSK ne ko mace sai albarka wajen iya ado.
Chief Editor na su da ke zaune a office
ɗ
in ya kalli Asiya ya ce " miya faru na ga rahoton ki na yau ba wani armashi, ba ki da lafiya ne?"
"no Sir, Ummata ce ba lafiya" Asiya ta fa
ɗ
a ranta a
ɓ
ace.
"Al
lah ya bata lafiya"
Ta amsa ma sa da Amin. Da hannu ya ma ta nuni da ta fita daga office
ɗ
in. Bayan ta fita Chief Editor ya kalli MD ya ce " mutumina ka mata a hankali. The girl is good ba wanda ya fi ƙarfin kuskure"
"Idan har bama nunawa jama'a good
ness na Mataimakin Gwamna kullum kallon hoto za a dinga ma sa. Wallahi da shine Gwamna da jahar nan ta fi haka cigaba cikin shekaru ukun nan. S S Kachallah mutum ne da ya san darajan
ɗ
an Adam, he's a man of vision and mission"
"Ni zan gaya maka halin Pr
of Kachallah tunda ya koyar dani lokacin ina Masters ..." daga nan su ka buge da hiran mataimakin Gwamnan.
Asiya na fita daga office
ɗ
in MD ƙasa ta koma wajen office
ɗ
in su ta
ɗ
au jakarta ta fito. Wani mahaukacin yunwa ke cinta ga gajiya a haka tafito
daga farfajiyar gidan Talabijin
ɗ
in. Da Ubayd na gari da shi za ta kira ya zo ya
ɗ
auketa amma yanzu sai dai ta nemi abin hawa. Tana tsaye C Y ya fito da tsohuwar baƙar roba-roba
ɗ
in sa.
"Ke kalar mota ce da na miki lift zuwa gida" ga fa
ɗ
a yana dariya.
"Ƙaniyarka C Y, kana nufin tafiya za ka yi ka barni kenan"
Ɗ
an dawowa yai da baya ta hau mashin
ɗ
in sannan ya ja suka tafi. Suna tafiyan suna ta
ɗ
i saboda Clement Yohanna (C Y) akwai surutu shima kamar Asiyar shiyasa ma tasu ta zo
ɗ
aya.
A ƙofar gida
n su ya sauketa yana fa
ɗ
in ta gaida ma sa da Umma.
Da sallama ta shiga gidan na su, Inna Yaha na faman