Showing 27001 words to 30000 words out of 67805 words
wardrobe na gefen gado tana addu'ar Allah y
a sa Asiyar da ta ajiyewa ce kawai za ta gani.
Daga gidan Gwamna kai tsaye office
ɗ
insu ta wuce. Ofishin Oga ta shiga fiskarta
ɗ
auke da murmushi, ko da hukumomin Nigeria ba su kama Bilkisu Kachallah ba akwai hukumomi na ƙasar waje da za su shigo cikin l
amarin, kuma za su iya sawa a hukunta Bilkisu Kachallah da Madam Bintu Chadi.
Oga na ganinta hankalinsa ya tashi suna gaisawa zata fara magana yace "Badawiyya ba ki duba wayarki bane?"
Wayarta yana silent a koda yaushe saboda aikinta shiyasa ba ta ji ƙ
aran shigowar saƙonsa ba.
Ta
ɗ
auko wayar a jaka ta karanta saƙon da ya turo mata kusan minti goma da suka wuce.
*Badawiy ki bar gidan Gwamna, an aika wasu suje su kama ki. Ki
ɓ
uya a inda kika san ba za a sameki ba*
Badawiyya ta
ɗ
ago kai cikin rashin
fahimta. Oga ya miƙa mata wayarsa yana
ɗ
aura yatsa
ɗ
aya akan bakinsa alamar tayi shiru. Ta kar
ɓ
i wayar ta karanta abinda ya rubuta.
* ki bar nan, ance a arresting
ɗ
inki. Idan kika yi gardama an bada umurnin a halbe ki*
Badawiyya ta
ɗ
ago ido da sau
ri cikin ka
ɗ
uwa. Mi tayi? Tana yiwa Gwamnatin Nigeria aiki sama da shekaru takwas kenan.
Oga ya mata nuni data ƙarisa karantawa.
*ance ke
ɗ
in 'yar ta'adda ce da kika shiga aikin nan dan ki samu bayanan sirri. Ance kina shirin tada Bomb a gidan Gwamna.
Na gaya miki dama Bilkisu Kachallah tanada protection daga sama*
Badawiyya ta shiga maimaita Innalillahi... a ranta. Ta miƙe da sauri ta fice daga office
ɗ
in Oga.
Tana kaiwa bakin ƙofar da zai fitar da ita daga building
ɗ
in aka
ɗ
aura bindiga a ƙeyart
a aka ce " Agent Rabi'atul Badawiyya Kabir, you are under arrest"...
10
Bilkisu Kachallah na isa gida kai tsaye
ɗ
akinta ta nufa ta je ta
ɗ
auko akwatin sirrinta. An gaya mata duk abinda ya faru kuma da izininta aka rufe Agent Badawiyya a kurku
ku. Bilkisu ta fito da damin ku
ɗ
a
ɗ
enta ta gansu yadda ta barsu sai kuma ta duba takardunta duka sun cika. An riga an kar
ɓ
e wayar Agent Badawiyya dan haka bata da wata matsala.
Tabbas ta ji zafin yadda aka yi tayi sake irin haka, bata jan mutane jikinta a
mma kuma Hansa'u ta daban ce. She carried her disguise so perfectly, ta yadda tsawon wannan lokaci bata ta
ɓ
a zarginta ba. Ta jinjinawa Agent Badawiyya saboda a rayuwarta tana son mata masu jajircewa akan aikin da suka sa a gaba. A tsarinta, mace is very po
werful...
***
Bayan Azahar
ɗ
akin Asiya ya cika da 'yan dubiya. Motoci uku suka biyo bayan ta Ale Faruƙ cike da 'yan gidansu. Fulani da Tabawa ne suka zo a manyan mata, a maza kuma Ale da Baffa Malam. Sauran kuma yayyu da ƙannenta ne da kuma jikok
in gidansu.
Ran Asiya a
ɓ
ace yake tun tafiyar Bilkisu Kachallah saboda Sumayya ta fa
ɗ
a mata cewa wasu 'yan jarida sun zo sun yi hira da Bilkisu lokacin da take bacci.
Bata da lafiya ma ba za a ƙyaleta ba. Ta sake tabbatarwa kanta cewa ita
ɗ
in bata da w
ani matsayi a rayuwar Gwamna da Bilkisu Kachallah.
Sai dai zuwan 'yan gidansu ya washe duk wani baƙin ciki da ka
ɗ
aici da take ciki. Ta yi kewansu sosai.
Kaka Tabawa da ta fara
ɓ
aran-
ɓ
arama a
ɗ
akin haka Asiya ta
ɓ
igire da dariya har da ƙwallah. Yau ne
rana na farko da tayi dariya tun rasuwan Umma.
Tabawa ta dage wai sai ta ga Gwamna kafin ta tafi hakan ya sa Asiya ta tsuke fiska.
Tabawa ta shiga tsokalarta wai kota
ɓ
ata rai ba za ta janye batunta ba, ai Gwamna mijinsu ne duka.
Ba su bar Asibitin
ba sai yamma liƙis, sun so kwana amma Baffa Malam ya hana.
Da dare Bayan Isha Ubayd ya zo dubiya. Ganinsa da Asiya tayi ya tuno mata da wasiyyar Umma. Shikenan ta rasa Ubayd har abada kenan?
Shima Ubayd
ɗ
in a daddafe ya gaisheta ya fita, tsoron kasanc
ewa da ita yake saboda abubuwan da zuciyarsa ke ayyana masa. Asiya Shahidah ce first love
ɗ
insa, kuma har yanzu daya amince zai auri Salma bai ji ko ka
ɗ
an wani abu ya ragu na soyayyar da yake mata ba, sai dai kawai zai cigaba da
danne zuciyarsa har lokacin
da Allah zai yaye masa soyayyarta gaba
ɗ
aya, duk da kuwa hakan ba lallai ya faru nan kusa ba.
CY ne ya zo na ƙarshe kafin Asiya ta yi bacci. Ya zo da yamma ya samu ƙofar
ɗ
akin cike da mutane sai ya juya bai ƙariso ba.
Yana sane cewa zuwansa dubiyan za
i iya zama wani abu amma bai damu ba saboda zuciyarsa ba za ta ta
ɓ
a samun sukuni ba har sai ya ganta. Tunda aka nunota kwance akan gadon Asibiti ya ji tsananin tausayinta ya kamashi. Ita
ɗ
in wata
ɓ
angare na zuciyarsa ne da ba zai iya yakicewa ba.
"CY th
e CY, mi ka kawo min ne?"
CY ya miƙa mata
ɗ
an ƙaramin box
ɗ
in daya shigo da shi. Asiya ta kar
ɓ
i box
ɗ
in hannunta ya shafi hannun CY. Duk da hannun na roba ne hakan bai hana CY jin wani abu ya ratsa jikinsa ba.
Asiya ta bu
ɗ
e box
ɗ
in cike da farinciki.
"Chocolate?. Shine ka kawo guda
ɗ
aya, marowaci kawai" ta cire chocolate
ɗ
in ta
ɓ
are ta fara ci
"Allah ya shiryeka CY, harda wani yin karama ka saka a box kamar abin kirki"
CY yai murmushi itama Asiyar murmushi tayi sannan ta cigaba da cin chocola
te
ɗ
in.
Sallamar Abba ya saka CY da Asiya
ɗ
agowa suka dubi Abba da yake bin Asiya da wani irin kallo.
CY ya gaishe shi sannan yai wa Asiya sallama ya tafi. Su biyu ne a
ɗ
akin saboda shigowar CY
ɗ
akin yayi dai-dai da ficewar Sumayya data je kiran nu
rse da zata zo ta cirewa Asiya ruwan da aka
ɗ
aura mata saboda ya kusa ƙarewa.
Abba yace "Asiya!" sai yai shiru saboda Sumayya data shigo tareda wata nurse.
Bayan an cire ruwan Abba yai musu sallama ya tafi.
Asiya ta san akwai magana a bakin Abba k
uma koma minene abu ne da ba zai mata da
ɗ
i ba saboda yanayin fiskarsa tunda ya shigo babu walwala a tattare da shi.
Ƙ
arfe sha
ɗ
aya da rabi na dare Sumayya na kwance a kan ƙaramin katifa a ƙasa tasa earpiece a kunne tana kallo aka ƙwanƙwasa ƙofar
ɗ
akin. B
a ta ji da farko ba sai a na uku ta miƙe ta kunna wutan
ɗ
akin sannan ta je ta bu
ɗ
e ƙofa, ganin Gwamna tsaye a bakin ƙofa tayi saurin matsawa gefe tana fa
ɗ
in "sannu da zuwa"
"Ya mai jiki?" ya tambaya lokacin daya shigo
ɗ
akin.
Ta amsa "da sauƙi ance ma
gobe za a sallameta".
"Ta yi bacci ne?"
"Tun
ɗ
azu" Sumayya ta fa
ɗ
a tana komawa gefe.
Gwamna ya matsa kusa da gadon Asiya ya zuba mata manyan idanunsa. Bacci take hankalinta kwance dan har hulan kanta ya zame gefe.
Murmushi Gwamna yai ganin wani
baƙi-baƙin abu a gefen bakin Asiya. Hannu ya kai zai goge mata, Asiya ta
ɗ
an juya gefe ta kwantar da fiskarta akan hannunta.
Maimakon ya sa hannu a wajen sai ya sa hannu a kanta ya fara shafa lallausan gashinta, ya warware bun
ɗ
in da tayi saboda ya ga tsa
yin gashin. Ya kai hancinsa yana shinshinar gashin wanda ke ƙanshin coconut da jasmine oil.
Ya kai bakinsa ya sumbaci gashinta, goshinta da kuma saman hancinta. Ya kai harshensa ya lashe baƙin abinda ya gani wanda yake tunanin ragowar abinda ta ci ne. Ɗa
n zaƙin daya ratsa harshensa ya tabbatar masa da chocolate ne. Ya kissing lips
ɗ
inta a hankali sannan ya miƙe sai ya ji tace "i love you Asya, mtsww... munafuki, what did he think of himself mtsww ... Sumy kina jina ko?..." ta yi maganar tana nuna yatsa, s
ai kuma ta juya
ɗ
aya gefen ta cigaba da bacci.
Gwamna yai murmushi, Junior da Nana ne masu magana cikin bacci. Bai san manya ma suna iya magana cikin bacci ba sai yanzu. Ya ji da
ɗ
i daya fahimci abinda ke ranta shine sirrin daya bayyana mata jiya.
Yai
wa Sumayya sai da safe sannan ya fita. Bayan tafiyarsa Sumayya ta fito da dariyar da take ta gimtsewa tuntuni...
Washegari da safe Sumayya ta shiga tsokanar Asiya akan jiya Gwamna yazo ta fa
ɗ
a masa tana son shi cikin bacci.
"Sumy bana son maganar
banza"
"Inada shaidah fa Anty"
"Maƙaryaciya"
Sumayya ta fito da wayarta ta nuna mata hoton da ta yi musu jiya dai dai lokacin da Gwamna ya kissing goshinta da kuma lips
ɗ
inta. Asiya ta zaro ido tana fa
ɗ
in "na shiga uku. Sumy hoton nan gaskiya ne k
uwa?"
Sumayya ta ha
ɗ
e rai tace " ke da bakinki kika ce masa i love you, please kiss me. Shi kuwa yai kissing
ɗ
inki"
"Zan ci ƙaniyarki Sumayya"
"Ni ƙarshe dana ga kin kanainayeshi ma bar muku
ɗ
akin na yi"
Asiya ta yi saurin
ɗ
aura yatsarta a baki
tana tantamar maganar Sumayya.
Ta sani tana da magagin bacci musamman lokacin da take yarinya, dan har cewa ake tana ta
ɗ
i har ma tayi fa
ɗ
a cikin baccinta. Amma anya za ta iya fa
ɗ
in abinda Sumayya tace ta fa
ɗ
a? Wani dalilin ne zai sa ma ta fa
ɗ
i
haka? "Ka
i Nooo!" Ta furta a fili tana goge bakinta da bayan hannunta da babu canula. Sumayya ta fashe da dariya.
Duk yadda ta nace akan Sumayya ta fa
ɗ
a mata gaskiyar abinda ta fa
ɗ
a cikin bacci ƙi tayi, sai maimaita mata maganarta na farko ta ke yi. Hakan ya sa
wani
ɓ
angare na zuciyarta ya fara yarda da maganar yayinda
ɗ
aya
ɓ
angaren yake ƙaryata haka. Ko a mafarki Allah ya sawwaƙa ta cewa Saifuddeen I love you balle har ta roƙe shi ya kissing
ɗ
inta.
Ƙ
arfe shabiyu na rana aka sallameta. Ba su san ya akayi 'yan
jarida suka san da sallamar ba. Suna fitowa daga cikin Asibitin 'yan jarida suka musu chaa suna neman ƙarin bayanin sace ta da aka yi da kuma jinyarta, ko kidnappers
ɗ
in sun mata wani abu?, sannan su wa ta ke zargi da wannan aikin?.
Idan ba ta yi magana
ba matsala ne, idan tayi ma matsala ne, dan ko mi ta fa
ɗ
a ma sai an fassara shi zuwa wani abun daban. Shirun dai shi yafi dacewa tayi.
Yaya Bello da Habibu ne suka sata a tsakiyarsu suka ratsa 'yan jarida suka wuce da ita har wajen mota...
***
Asiya ba ta samu zama da Abba ba sai dare bayan sallar Isha.
"Ya jikin naki?"
"Da sauƙi Abba"
"Alhamdulillah"
Shiru ne ya biyo bayan abinda ya fa
ɗ
a. Sai chan kuma ya
ɗ
ago maganar rabon gadon Umma da za ayi.
Miyasa da wurwuri haka? Miyasa kayan U
mma zai kasance na magada? "Mutuwa" zuciyar Asiya ya bata amsa.
"Ban ji da
ɗ
in yadda na sameki da wannan yaron ba. Asiya ki riƙe aurenki da daraja dan Allah"
"Abba gaisheni fa ya zo yi"
"Shine kike mishi tarban da ba kya yiwa mijin ki?"
Asiya
ta
ɗ
ago da sauri ta kalli Abba cike da rashin fahimta.
"Ban san mi kuka tattauna ba amma na wuce naji kina
ɗ
agawa mijinki murya. Kina ganin hakan ya dace Shahidah?"
"Allah ya gafarta wa Ummanki, har na koma ga Allah addu'a zan dinga yi mata, saboda
ita
ɗ
in macen da ta dace da a kira da suna mar'atul saliha ce.
Mahaifinki da ya zo ta'aziyya a nan ya zauna yana zubda hawaye yana bayyana mini kyawawan halayenta a iya zaman da suka yi. A lokacin tanada ƙarancin shekaru ma kenan.
Asiya ba ki
ɗ
auki aure
nki da mahimmanci ba, ba ki
ɗ
auki mijinki da daraja ba. Idan har saboda mun raba ki da Ubaydullah ne kika yi watsi da aurenki to ki sani abinda kike ba abinda zai haifar miki sai baƙin ciki. Ban ji da
ɗ
i ba Asiya. Shikenan ba zaki saki ranki ki rungumi aure
nki a matsayin ibada ba"
"Abba shine bai
ɗ
aukeni da daraja ba. He's using me for his campaign"
"Sai me?"
"Abba!"
"Sai me idan yayi amfani dake wajen kamfen
ɗ
insa, ba mijin ki bane?"
Asiya ta saka hannu ta fara goge hawayenta. Ita kam akan
Gwamna Abba kamar baya sonta.
Sauran nasihar Abba ma dai Asiya ba ji tayi ba, dan rabi kuka rabi saƙe-saƙe ta ke yi a zuciyarta.
A rana ta uku da dawowarta sai ga Mahirah da Junior sun zo gaisheta. Lokacin da take Asibiti Hajia Umma da wasu 'yan tsir
aru cikin 'yan uwan Gwamna sun zo sun gaisheta.
Sai yau ne Asiya ta zauna da Mahirah saboda duk zaman da tayi a gidan Gwamna Mahira tana Kachallah house. Yarinyar kam ba laifi akwai hankali ba kamar Nana ba. Maganarta sanyi, kominta a sanyaye.
Ta yi
tunanin Bilkisu Kachallah ce ta turosu amma ga mamakinta sai Mahira tace mata Gwamna ne ya ce su zo su gaisheta.
Junior ya sake jiki da su Ali da Gwani suka tafi da shi yawo.
"Ya jikin Nana?" Asiya ta tambaya ganin shirun yayi yawa dan Mahira bata d
a yawar magana kamar 'yar uwarta.
"Da sauƙi"
"Har yanzu ba a dawo da ita gida ba?"
"Sun ce sai ta cika wata shida a wajen"
"Amma kuna zuwa dubata ko?"
"E muna zuwa duk weekend"
Asiya tana ƙoƙarin updating wayarta saboda lokacin da aka
bata wayar kafin a sakota sun share kusan komai na kan wayar.
"Anty Shahidah dan Allah ki kula da Daddy, wallahi bashida lafiya"
Asiya ta kalleta da mamaki.
Kanta a ƙasa ta cigaba da bayani "tunda aka
ɗ
auke ki bashida lafiya. Akwai ranan da ya zo
gaishe da Dadda da zai tafi sai kawai gani muka yi ya fa
ɗ
i. Ya cewa Dadda kar ta fa
ɗ
awa kowa, kuma har yanzu ya ƙi yaje a duba shi. He was busy, Mommy ma kuma kamfen ne a gabanta yanzu"
"Miyasa kike gaya min wannan?"
"Because...because you are a go
od person"
Asiya ta kauda kanta kamar bata damu da abinda Mahira ta fa
ɗ
a ba.
Sai yamma kafin suka tafi, lokacin da aka dawo da Junior yayi futu-futu da shi wai ball ya buga. Da ke yaron kullum a takure yake, yanzu da ya zaga anguwa yai wasa da sa'ann
insa da kuma wanda suka girmeshi sai ya langwa
ɓ
e jikin Ali yace ba zai tafi ba. Da ƙyar Asiya ta lallashe shi akan za a kawo shi gobe.
Bayan tafiyar su Mahira, Asiya ta shiga tattauna maganar da Mahira ta mata, da ma maganar Abba daya tsaya mata a rai t
un jiya.
Ta kasa yarda cewa Gwamna ba shi da hannu a saceta da aka yi saboda alamu sun nuna shi munafukine. Amma yanzu kuma maganar Mahirah ya sa ta fara tantama da abinda ta sawa ranta.
A wani gefe kuma kalaman Gwamna na ranan suna kashe mata jiki, s
una tunku
ɗ
e duk wani haushinsa da take ji.
'Ina son ki Asya' duk lokacin da ta tuno wa
ɗ
annan kalamomi sai ta dinga ji tsikar jikinta na tashi. Sannan ƙwaƙwalwarta na ƙoƙarin gano mata a wani siga za ta fayyace kalaman. Shin Gwamna yana sonta a matsayin
matarsa ne, ko kuma a matsayin wacce ya kamu da soyayyarta?...
Kwananta biyar a gida ta warware kamar ba ita ba. Ranan ne kuma aka raba musu gadon Umma wanda Abba ko tsinke bai
ɗ
auka ba, dan cewa yai ya yafe nashi kason.
Washegari Abba yace ta tattar
a ta koma gidanta. Tun maganar da Abba ya mata take shakkarsa dan haka da yai maganar ko musu ba ta yi ba ta kira Yaya Bello tace ya zo ya
ɗ
aukesu bayan sallar magariba.
Abin mamaki gidan Gwamna ta
ɗ
auka za su wuce sai ta ga yayi hanyar gidan Gwamnati.
"Yaya Bello ka kaini gidansa bana son hayaniyar wanchan gidan"
"Mai girma ne yace nan gidan za a kawoki"
Tayi shiru ba dan ranta ya so ba, sai dan tana ƙoƙarin bin nasihar Abba. Shine da ikon sakata a duk inda ya ga dama, tunda sunan matarsa take a
msawa.
"Mommy where is Hancha'u?" Junior yayi wa Bilkisu tambayar nan yafi a irga. Yanzun ma Safiyya ce ke zuba masa abinci shiyasa ya tambaya saboda tunowa da yai da ita.
"Na gayama kar ka sake tambayar Hansa'u a gidan nan. She's gone"
"Mommy w
hy?"
"Ni kam ko yarinyar nan mayya ce, kullum minti
ɗ
aya biyu sai ka tambayi Hansa'u. Eat your food ko kuma na hanaka zuwa Kachallah house gobe"
"gidansu Ali zan je gobe"
"Waye kuma Ali?"
"Alin gidansu Asiya. Oops Anty Asiya"
Dai dai lokac
in Asiya