Showing 18001 words to 21000 words out of 67805 words
tara da minti biyar aka yiwa Umma Sallah sannan aka wuce da ita maƙabarta. Gwamna Saifuddeen bai y
i niyyar wucewa maƙabarta ba amma yana shiga mota Alhaji Sani ya kirashi yace ya wuce maƙabarta saboda Alhaji Umaru Kwom nan zai je.
Innalillahi akan aikin ladan ma sai an saka siyasa a ciki. Haka dai aka wuce da Gwamna maƙabarta.
Asiya bata kunna
TV ba. Tsoro take ji, gani take idan ta kunna ne abinda aka fa
ɗ
a zai tabbata, amma idan bata kunna ba Ummanta za ta kasance kwance a Asibiti ba abunda ya sameta. Sai kusan ƙarfe goma da rabi saura ta samu ƙarfin gwiwar kunna TV
ɗ
in.
Kamar yarinya haka ta
zauna a gaban TV ta na
ɗ
e kafafuwanta ta riƙe fiskanta da hannayenta biyu.
Hill TV ta kunna, ta san suna ƙoƙarin fitar da labarun gaskiya ba kamar Congo News ba.
Ƙ
arfe goma da rabi suka sako maimaicin labaren safe. Labarin farko a kanun labaren shine rasu
wan mahaifiyar matar Gwamna wato Asiya Kachallah.
Haka Asiya ta baza ido tana kallon labaran. Aka nuna wajen da Alhaji Umaru Kwom yazo yana gaisawa da su Abba, aka nuna wajen da Gwamna shima ya iso, sannan aka
ɗ
an nuna wajen da ake yiwa gawar Umma sall
ah, aka nuno wajen da ake saka gawar Umma a cikin ƙabari.
Daga ƙarshe aka nuna Gwamna yana yiwa iyalen Malam Nuhu Gida
ɗ
o ta'aziyya sannan aka nuna Alhaji Umaru Kwom shima yana yiwa Gwamna da iyalinsa ta'aziyya.
Da gangan
ɗ
an jarida ya tambayeshi ko miye
dalilin daya sa ya halarci sallan sirikar Gwamna sannan har ya zo maƙabarta akayi biso da shi.
Umaru Kwom ya karkata kai yace *"watoo, ita siyasa ba gaba bace"* kafin ka ce me a duniyar yanar gizo mutane sun
ɗ
auki kalmomin Umaru Kwom suna masa kamfen d
a shi *#Siyasa ba gaba bace*
Ta ko'ina a fa
ɗ
in jihar sai maganan ƙarfin hali, jajircewa da kuma imani irin na Umaru Kwom ake. Hatta wasu masu fa
ɗ
a aji a ƙasar sai da suka yaba da Umaru Kwom.
Asiya tana ganin rahoton amma hawaye ko
ɗ
aya bai fito ba,
zuciyarta ya yi mata nauyi. Tana ji kamar kumbura zuciyar take, nan da anjima ka
ɗ
an zata fashe, idan ta fashe kuma sai itama a kaita inda aka kai Umma.
Sai dai haka ta zauna a wajen tana jiran zuciyar ta fashe amma taƙi fashewa, bata ma da alamar zata yi
komai saboda duk yadda take dokawa cikin ƙirjinta babu abinda ya faru.
Kamar wata zararriya ta tashi tsaye tana safa da marwa a
ɗ
akin tana fa
ɗ
in "sun kashe Umma, sun kashe min mahaifiya, ba abinda ta musu suka kashe min ita, bata magana ma amma basu ba
rta ba, tana fama da cancer amma basu barta ba,
ɗ
an albarka da take sa min kullum ma sun katse" ta dinga safa da marwa ƙarshe ta fa
ɗ
i ƙasa tim saboda hajijiya...
Ba a gama juyayin rasuwar sirikar Gwamna ba, special adviser na Gwamna ya fito ya bayyana
cewa an sace matar Gwamna Asiya Kachallah.
Umaru Kwom yana gidansa yana sauraren masu kawo masa gulmar yadda mutanen gari ke yabonsa aka fito da labarin da ya girgiza shi.
"An sace Asiya Kachallah?. This is a set up" ya fa
ɗ
a cike da damuwa domin ya
hango ma'anar hakan. Saifuddeen Kachallah ba zai iya amfani da iyalinsa wajen Kamfen ba amma akwai wanda zai iya...Alhaji Sani Kachallah.
Kafin dare maganar Siyasa ba gaba bace ta riki
ɗ
e ta koma *#Save Asiya Kachallah?*
Ale Faruƙ ya zo ta'aziya dan
bai samu sallar jana'iza ba. Daya zo ne kuma ya samu labarin sace Asiya da akayi. Abin ya
ɗ
aure masa kai, taya za a sace Matar Gwamna guda?.
A matsayinsa na Uba ya ji ba da
ɗ
i, ya shiga ru
ɗ
u, dan har gwada kiran numbar Asiya yai ko za a dace ta
ɗ
auka, ƙil
a wani wajen ta shiga ba a sani ba.
Bai bar cikin jaha ba sai chan yammaci, ya tafi da niyyar idan anji wani labari akan Asiya zai dawo.
Ga sauran ahalin Malam Nuhu kuma, kowa ka gani ciki kasan baya cikin kwanciyar hankali. Abba dannewa kawai yake amm
a kusan shi yafi kowa damuwa a gidan, shi daya rasa matarsa uwar 'ya'yansa uku, biyar idan ka ha
ɗ
a da wanda ya rasu kafin a haifi Ali da kuma wanda ta tafi da shi a cikinta.
Tun bayan rasuwan Hassana mahaifiyar Ubayd sai daya auri Zainabu Kurma ya samu
nitsuwa. Kai, zai iya cewa Zainabu tafi Hassana saboda zaman da yai da Hassana shekaru biyune da burbu
ɗ
i, ita kuma Zainabu shekaru goma shatara ba wata biyu.
***
"Saifuddeen...Saifuddeen...Darling. idan baka ci abinci ba taya zaka samu ƙarfin yiwa
Jahar nan aiki?"
Gwamna Saifuddeen ya
ɗ
ago rinannun idanunsa ya kalli Bilkisu. Abinci ne ƙarshen abinda zai sa a ransa yanzu.
"We can fix this amma sai ka kwantar da hankalinka. Without food, ƙwaƙwalwarka ba zata iya aikin komai ba"
"Azumi nake Bi
lkisu"
"Idan anyi Azumi ai ana shan ruwa, rabonka da abinci tun jiya fa Saifuddeen"
"Kawo min Apple"
"Apple ka
ɗ
ai za ka ci?"
"Ki ha
ɗ
o da ruwa mai sanyi"...
A
ɓ
angaren Asiya bata farfa
ɗ
o ba sai lokacin da aka kawo mata abincin dare. Suna g
aninta haka hankalinsu ya tashi suka shiga yayyafa mata ruwa har sai da suka ga ta jaa dogon numfashi kafin suka daina yayyafa ruwan.
Babu yadda ba suyi ba akan ta ci abinci amma ta ƙi, dan su tunaninsu abincin da bata ci bane tunda aka kawota ya sa ka ta
suma.
Sai da ta shammacesu sun sake jiki suna mata magana tayi wuf, ta nufi hanyar ƙofa da gudu amma bata kaiba aka sake mata bindiga a baya. Harsashin dake cikin bindigar wata allura ce dake saka mutum bacci dan haka allurar na cakarta ko sakan biyu
bai cika ba, ta fa
ɗ
i a wajen.
Bilkisu Kachallah tana zaune kusa da Gwamna tana yanka masa Apple wayarta ya shiga ƙara.
"Ki
ɗ
auka mana" Gwamna ya fa
ɗ
a ganin ta share wayar duk da kuwa ta gama yanka Apple
ɗ
in.
"Ƙila masu neman ku
ɗ
i ne"
Gwamna
bai ce komai ba ya dai cigaba da cin Apple a hankali, ba dan da
ɗ
i ba sai dan dole ne ya sa wani abu a ciki duk da ya
ɗ
au alkawarin yin Azumi har ranan da za'a ga Asiya...
"Nace ban yarda ta fita ba, idan taƙi cin abinci ruwanta ne. Idan kuka ga ta gal
abaita ku mata
ɗ
ure, ban damu da lafiyarta ba but keep her alive"
"Waye a nan?" ta fa
ɗ
a lokacin data juyo tana sauke waya daga kunnenta.
"Lah! Hajjajuna dama ina so na nemi wani alfarma ne"
Bilkisu Kachallah ta harari Hansa'u tace "shine zaki shig
omin
ɗ
aki ba sallama"
"Kwarankwatsi tun
ɗ
azu nake ta sallama a bakin ƙofa ba ki amsa ba, shine na shigo"
"Minene?" Bilkisu ta fa
ɗ
a da kakkausar murya.
Hansa'u ta tsugunna tace "An bugo wai Gyatumata bata da lafiya"
Ba zata ta
ɓ
a manta farkon zuwan
ta gidan ba. Watarana Bilkisu ta kirata
ɗ
aki, tana shigowa sai ta tsaya a tsaye. Kafin ta farga har ta kai ƙasa saboda wani maka da Bilkisun ta kai mata tana fa
ɗ
in "ina tsaye kina tsaye"
Bilkisu tayi tsaki tace "Bakin kine gyatumar ai. Mi kike so?"
"
Hajjaju ina so Dan Allah ki bani kwana biyu na je na gaisheta"
"Kwana biyu? Are you mad, wa zai kula da Junior?"
"Ranki shi da
ɗ
e akwai su Onome, su Safiya su..."
"Duk ciki waya saba da su idan ba ke ba. Ba inda zaki je, zan baki ku
ɗ
i ki aika mata,
Allah ya bada lafiya"
Hansa'u ta langwa
ɓ
a kai. Idan kaji Bilkisu tana maganar kula da Junior, zaka
ɗ
auka jariri ne. Yaro
ɗ
an shekara shida amma yadda ake nuna masa gata sai ka
ɗ
auka
ɗ
an goye ne.
"Hajjaju a taimaka ko kwana
ɗ
aya ne naje na dawo. Ban
sani ba ko jinyar mutuwa ne, ina so mu gana kafin rai yai halinsa"
"Idan mutum yai abu sai ku ce shi mugu ne. Kin san dai tunda aka fara Kamfen ba zama nake ba, sannan Junior yana buƙatar kulawa ta musamman"
"A taimaka dai, a duba Dan Allah"
"Fin
e. ki je ki dawo a goben"
"Nagode Hajjaju" ta fa
ɗ
a tana riƙe ƙafar Bilkisu. Bilkisu ta yarfe ƙafarta tareda jan tsaki ta fice daga
ɗ
akin. Tana fita Hansa'u tayi murmushi.
Washegari Hansa'u data fito daga gidan Gwamnati Keke ta nema ya kaita wani mada
idaicin gida. Tana shiga suka gaisa da matar dake kula mata da gidan sanan ta wuce ban
ɗ
aki tayi wanka.
Tana fitowa sanye da towel ta kalli kanta a madubi, shekaru sun ja amma har yanzu tana da kyau. Ba zata ta
ɓ
a manta ranan da aka kawota gidan Alhaji R
ufa'i ba, 'yar ƙauye da ita. A shekaru shashida ba abinda ta sani na uƙubar rayuwa sai data shigo gidan. Ita 'yar ƙauye ce amma a ƙauyensu ita
ɗ
in 'yar babbar mutum ce saboda Baffanta yafi kowa Shanu a ƙauyen dan haka ba cikin wahala ta fito ba.
"Aaah,
kai Masha Allah! Ashe kyakykyawar Bafulatana aka samo maka Alhaji" maganar Madam Bintu ya sake maimaituwa a ƙwaƙwalwarta.
"Wannan ai dana haihu da wuri ai sai dai nayi jika da ita, ba kishin da zan yi da ita Alhaji, ai ni 'ya ka kawo min"
Munafukin
mutum akwai shi da iya da
ɗ
in baki. Ranan da Alhaji Rufa'i ya ha
ɗ
asu yana musu nasiha Madam Bintu yadda ka san matar Aljannah haka ta dinga maganganu masu da
ɗ
i tana nunawa mijinta babu komai.
Ita
ɗ
in kamar sadaka ce aka yiwa Alhaji Rufa'i. Tana shekar
a shauku aka mata baiko da
ɗ
an uwanta Siddiƙu. Watanni uku da baikon aka fara shirye-shiryen biki. Ranan da za a
ɗ
aura aurensu Allah ya masa rasuwa. Daga nan aka ya
ɓ
a mata baƙin jini akan tana da farar ƙafa idan ba haka ba taya za ayi mutum lafiyarsa ƙalau
ace ranan aurensa ya rasu. Duk wanda aka yiwa tayi a ƙauyensu sai yace a'a yana tsoro, wasu ma har maita suka laƙa mata. A wani zuwan da Alhaji Rufa'i yai ne Baffanta ya masa maganar ko zai sama masa miji a birni dan 'yarsa tayi kwantai. Mamaki ya kama Al
haji Rufa'i lokacin da ya ji shekarun yarinyar shashida amma har ana fa
ɗ
in tayi kwantai.
Duk bayanin da Baffa Kabiru ya masa gani yai kawai jahilci ne irin na 'yan ƙauye.
Daga ƙarshe dai da Baffa Kabiru ya masa tayin Rabi'atul Badawiyya sai ya amince, a
tunaninsa ƙila za a dace ya samu haihuwa tunda matarsa Bintu shekaru ashirin da
ɗ
aya da aure amma shiru babu haihuwa.
Alhaji Rufa'i yana shekara hamsin da biyar ya auri Rabi'atul Badawiyya.
Shi ba mazaunin ƙasar bane amma saboda auren sai da ya zauna a g
ida na watanni uku ko za a dace.
Farko farkon aurensu da Madam Bintu yayi ta yawoce yawocen Asibitoci ciki da wajen ƙasa amma duk zancen
ɗ
aya ne, ba shi da matsala. Bai san dalilin dayasa ya kasa ƙara aure ba tun lokacin, duk da irin matsin lamba da ya k
e fuskanta daga 'yanuwansa. Kafin rasuwar mahaifiyarsa sai da aka aura masa mata amma zamansu bai jima ba ta gudu, tace dole sai dai ya saketa har yau bai san dalili ba kuma bai nemi sani ba.
Ƙaddarar aure ne ya shiga tsakaninsa da Badawiyya shiyasa ha
r ya ji sha'warta bayan Baffanta ya masa tayinta.
Watanni uku yai bai fita ko'ina ba yana addu'ar Allah yasa a dace. Shiru kuwa har ya tafi ƙasar Germany duba wani kamfaninsa dake chan.
Satinsa biyu a chan Likitansa ya kira shi yana masa barka domin Am
aryarsa tana
ɗ
auke da cikin sati biyar. Kaman Alhaji Rufa'i yai tsalle ya ganshi a Nigeria haka ya dinga ji, murna a gunsa ba a magana. Jirgin washegari ya booking zai dawo amma
ɓ
arayi suka shiga gidansa suka harbeshi har lahira.
Tunda Madam Bintu ta ji
bayanin Likita lokacin da ta kai Badawiyya Asibiti bayan ta suma, hankalinta yai mugun tashi. Ƙarshe ta tura ku
ɗ
i chan Germany wani Assassin ya je ya kashe Alhaji Rufa'i har gidansa.
Lokacin da aka zo maganar rabon gado haka Madam Bintu ta ƙeƙasa kasa
akan sai dai a bari Badawiyya ta haihu tukunna wai ai ba sauri suke ba. Ita ta hana 'yanuwan Badawiyya su tafi da ita tace zata kula da ita sosai.
Tayi duk abinda za tayi cikin ya zube amma bai zube ba. Ƙarshe ta haƙura zuwa lokacin da za a haifeshi t
a kashe jinjirin tace bai zo da rai ba.
Ta hana Badawiyya fita, ta dinga gana mata azaba, huron yunwa, aiki kamar jaka da tsoratarwa. Kafin ranan haihuwan gaba
ɗ
aya Badawiyya ta fice daga kamanninta, in fact, ƙwaƙwalwarta ya ta
ɓ
u.
Madam Bintu ce da w
ata tsohuwar ma'aikaciyarta mai suna Gamboji a cikin gidan, sai kuma maigadi da Dreba. Ranan da Badawiyya ta fara naƙuda Gamboji ce ta kira Madam Bintu akan ko za a kai Badawiyya Asibiti amma Madam Bintu tace fir haihuwan gida zata yi.
Gamboji tana tunan
in ita zata kar
ɓ
i haihuwan tunda ba laifi ta manyanta kuma ta ta
ɓ
a kar
ɓ
an haihuwan shekarun baya a ƙauyensu amma sai Madam Bintu tace ita zata kar
ɓ
i haihuwan wai Gamboji ta je Dreba ya kaita kasuwa ta siyo kayan jarirai saboda ba abinda aka tanada.
Gamb
oji ta fita zuciyarta na wasu-wasi.
Badawiyya na cikin ƙunci amma Madam Bintu ko ka
ɗ
an bata tausaya mata ba, lokacin da kan yaron ya fara fitowa haka ta dinga turashi ciki da ƙarfi dan kar ya fito, so take ya mutu a ciki kar ma ya fito duniya. Badawiyya
tun tana kuka har wahala yasa tayi dogon suma.
Ganin kan yaron ya koma ta ƙarfi sai ta fara duba alamun numfashi a tattare da Badawiyya amma bata gani ba.
"Sa'a biyu kenan, shegiyar itama ta koma"
Madam Bintu ta yarfe gumi ta fice daga
ɗ
akin tana jir
an dawowar Gamboji.
Da Gamboji ta dawo kuwa samun Madam Bintu tayi a falo tana kuka.
"Madam miya faru?"
"Badawiyya ta mutu Gamboji"
Gamboji ta wuce
ɗ
akin da gudu tana salati.
"Madam ya aka yi? Lafiya na tafi na barta fa"
Ba ta iya yin mus
u ba lokacin da Madam Bintu ta ce tayiwa Badawiyya wanka ta mata sutura kafin ta dawo, idan ta dawo zata kira mutane ta fa
ɗ
a musu cewa Badawiyya ta rasu wajen haihuwa, sannan babu mahalukin da zai san ita ce ta kar
ɓ
i haihuwan Badawiyya.
Tana da 'ya'ya b
iyu a ƙauye, kowacce da iyalinta. Madam Bintu tayi alƙawarin kashe mata 'ya'ya da jikoki idan ta bu
ɗ
e bakinta ta fa
ɗ
i abinda ya faru.
Fitar Madam Bintu daga gidan, Gamboji ta kasa zaune ta kasa tsaye, jikinta sai ƙyarma yake. Ba wai bata ta
ɓ
a yiwa gawa
wanka bane amma wannan gawar daban ce. Ta sani Madam Bintu ce ta kashe Badawiyya.
Sanda ta fara yiwa Badawiyya wanka ne kuma baiwar Allah ta farfa
ɗ
o, da ke Allah yayi da sauran numfashinta a duniya.
Gamboji ta tsorata ta fice daga gidan da gudu tana ih
u. Maigadi ne ya kamota ya fara tambayar lafiya. Da ƙyar Gamboji ta iya yi masa bayanin komai. Maigadi ya shawo kanta da ƙyar suka koma cikin gidan. Sai da
Maigadi ya shiga ya tabbatar Badawiyya da ranta kafin ya fito ya sanar da Gamboji da ke zaune a falo
tana rawan jiki.
Bayan ta shiga ta tabbatar Badawiyya ba mutuwa tayi ba sannan suka shiga shawaran ya za ayi, idan suka bari Madam Bintu ta dawo to ba makawa sun ka
ɗ
e sannan Badawiyyar ba zata tsira ba tunda sun ga manufar Madam Bintu akanta.
Ƙ
arshe Mai
gadi ya kawo wata shawara. Dake mai
ɗ
akinsa itama a gidan take sai kawai suka nemo taxi suka saka Badawiyya a ciki Kande matar Maigadi ta wuce da ita Asibitin Dr Mustafah wanda ya kasance likitan Alhaji Rufa'i kuma aboki gareshi.
Da Madam Bintu ta dawo
Gamboji ta fa
ɗ
a mata cewa 'yanuwan Badawiyya ne suka zo suka
ɗ
auketa wai zasu binneta a chan ƙauyensu.
Tunda Malaminta ya fa
ɗ
a mata babu mai sake
ɗ
ago maganar gado ta sawa kanta salama ko ma ya akayi da gawar Badawiyya bai dameta ba.
Ba dan an kaita wa
jen Dr Mustafah da wuri ba da mutuwa za ta yi na gaskiya saboda jini da taketa zubarwa.
Hansa'u ta shafa cikinta. Shekaru sun ja amma ba zata manta cewa akwai
ɗ
an daya ta
ɓ
a zama a ciki ba, ba zata manta cewa saboda Madam Bintu Likitoci sun tabbatar mata
ba zata sake haihuwa ba.
Bilkisu Kachallah
ɗ
aya take da Madam Bintu, shiyasa zata iya sawa a sace matar mijinta har ma tayi iƙirarin bata damu da lafiyarta ba.
Koma minene ta kusa ƙarisa aikinta tunda taga inda Bilkisu Kachallah take ajiye mahimman ta
kardunta. Da zaran ta samu Engineer
ɗ
insu ya gano