Showing 6001 words to 9000 words out of 67805 words
ido alamar marar gaskiya.
"Mr Silas yanzu dai kana nufin akwai script
ɗ
in Lami Ninja a ƙasa"
"Na ra
ntse da jinin Yesu yana nan. Lokacin da aka ce mu je mu tattare scripts na shekarar 2000 mu ƙona na san saboda case
ɗ
in Gwamna ne shiyasa na cire nata na
ɓ
oye"
"Kenan akwai script na course
ɗ
in da ake magana akai?"
"Duka scripts na first and second
semester nata na sace"
"Ina suke?"
"Oga Clement you know nah. 5M to my account zakuga script"
Yaya Bello da ba wai ya gama gane maganarsa bane yace " amma kasha giyar wake, akan takarda za a baka miliyan biyar"
"Oga Clement, idan ba za ku iya b
ayarwa ba zan kai wa wa
ɗ
anda zasu biya"
"Za mu tura maka daga nan zuwa dare"
"Haba baƙin Inyamuri..."
CY ya sa hannunsa na ƙarfe ya dafa kafa
ɗ
ar Yaya Bello yace " takardun sun fi ku
ɗ
in mahimmanci, ka barshi"
Bayan Mr Silas ya bada account numba
rsa sannan ya bar wajen, yana tafiya yana waige-waige.
"Dan kawai dukkanku ba kwa Sallah shine zaku cuci ƙanwata. Kwaranƙwasi babu wanda zai bashi miliyan biyar koda Gwamna ne da kansa kuwa. A barni na buge shege wallahi sai ya fitar da takardun nan"
C Y yai dariya duk da maganar Yaya Bello ya
ɓ
ata masa rai. Da ya san matsayin Asiya a zuciyarsa da babu abinda zai sa ya ce wai zai cuceta ku
ɗ
i. Duk da ya rasata har Abada, duk da ta kasance Mallakin wani hakan ba zai hanashi taimaka mata ba, koda kuwa za
i rasa rayuwarsa ne.
Lokacin da Asiya ta gayawa CY cewa ta zo makaranta ance an riga an ƙona scripts
ɗ
in shekarar, shine ya jarraba tasa basirar. Maimakon ita da
taje wajen manyan department shi ya bi ta wajen wanda suke ƙasa ne, mutanen da sune ke san
in duk wani shige da fice na department
ɗ
in.
Bai sha wahalar gano cewa Mr Silas shine ya fito ya dinga ihu ya tara mutane lokacin da ya shiga office
ɗ
in Prof SS Kachallah ya ganshi suna kokawa da Lami Ninja ba. Yanzu da suka yi magana da shi ya sake tabb
atar da cewa akwai hannun Mr Silas a abinda ya faru tun shekaru shabiyar da suka wuce, idan ba haka ba taya zai san mahimmancin scripts
ɗ
in Lami Ninja har ya
ɓ
oye su kafin a ƙona.
Sai da suka shiga mota CY yace da Yaya Bello idan yana son dukan Mr Silas
to ya shirya zuwa dare, Yaya Bello yace yanzu na ji magana.
CY ya
ɓ
oyewa Asiya komai ne saboda baya son sa mata rai a zo ba a samu komai ba, gara kawai sai komai ya tabbata kafin ya sanar da ita.
***
Yau lauyoyin Gwamna dana Lami Ninja zasu gan
a. Close case za'ayi, dan haka daga Lauyoyi, Alƙali sai shaidun mai ƙara da wanda ake ƙara.
Tunda Asiya ta tashi da Asuba bata koma bacci ba, tana gama Azkar ta wuce main kitchen inda ake dafa abincin iyalen gidan, ta ta
ɓ
a duba wajen sau
ɗ
aya amma wanna
n karan ba wai ta je dan ta leƙa bane, ta je dan tayi girki ne. Chief cook
ɗ
in namiji ne dan haka ta sallameshi akan ita za tayi abun kari. Daga ita sai Hansa'u da Sumayya da ta biyota suka fara shirya komai. A wajen Hansa'u ta samu bayanin yadda ake tafiy
ar da girki a gidan. Ba koyaushe Gwamna ke karyawa ba kafin ya fita, musamman ma ranakun Litinin da Alhamis da yake yin Azumi. Sunada menu da suke bi sai dai idan Bilkisu ta bada specific na abinda za a mata.
Bayan sun gama komai aka jera abincin a dini
ng room inda suke ha
ɗ
uwa su ci abinci.
Ƙ
arfe bakwai da rabi ta buga ƙofar
ɗ
akin Gwamna jin ba a amsa ba yasa ta kutsa kai cikin
ɗ
akin. Yana tsaye gaban madubi yana taje gemunsa. Ta madubi suka ha
ɗ
a ido amma yai kaman bai ganta ba ya cigaba da abinda yak
e.
"Ina kwana" ta yi maganar tana kallon ƙasa dan tun da ta ga idonsa ta madubi zuciyarta ya shiga taka rawa a cikin ƙirjinta.
"An shirya maka abin kari, Junior yana jiranka"
"Ba aikin ki ba kenan"
"Na sani amma ina so na yi"
"Bana buƙata"
"Dan Allah ka yi haƙuri, na san abinda aka rubuta a jaridar Climax zai dameka amma..."
"Ba yau jaridar Climax ta fara rubutu akan abinda zai dameni ba"
Ta yi shiru ganin ya juyo yana fiskantarta.
"Matsa min"
"Na'am" ta fa
ɗ
a cikin rashin f
ahimta.
Ta gefenta ya bi zai wuce ta riƙo hannunsa. "Allah ya bada nasara"
Cikin zuciyarsa ya furta Amin ya cire hannunsa cikin nata ya fita.
"Anya damuwa bai fara ta
ɓ
a min kwanya ba kuwa?" Asiya ta tambaya bayan fitan Gwamna. Ba ta san dalilin ri
ƙ
e hannunsa da tayi ba, bata ma san dalilin da ya sa take son faranta masa ba yanzu.
Ta
ɗ
auka ba zai tsaya karyawa ba amma sai ta ga ya zauna Hansa'u tana shirin serving
ɗ
insa. Asiya ta yi saurin ƙarisawa wajen ta ce "Hansa'u jeki kawai"
Hansa'u ta a
jiye serving spoon
ɗ
in ta bar wajen. Gwamna yana riƙe da jarida yana dubawa amma hankalinsa na kansu.
Bayan ta gama zuba mishi soyayyen dankali da miyar hanta sannan ta ajiye masa toasted bread da shayi a gefe. Zama ta yi gefen Junior da yake cin noodle
s da ƙwai ta shafa kansa sannan ta
ɗ
au plate ta fara serving kanta.
Krit krit krit krit ƙaran takalmin Bilkisu ya sanar da shigowanta dinning
ɗ
in. Ta kalli Asiya sannan ta zauna gefen Gwamna tana fa
ɗ
in "ina kuma Hansa'un ta shiga yau"
"Hansa'u, Hans
a'u"
"Hancha'u where are you?" Junior ya taya Bilkisu kira
Hansa'u ta fito da gudu kamar dama a ankare take. Asiya ta tsaya kallon mamaki wai ga abinci a gaban Bilkisu amma sai mai aiki ta fito daga wata duniya ta zo ta zuba mata a plate.
"Miyasa a
ka yanka dankalin manya?"
Hansa'u ta fara sosa kai tana inda inda.
"Wuce ki bani waje"
Bayan tafiyar Hansa'u ta kai lomar abinci sai ta tsaya, kaman za ta ce wani abu akan abincin sai kuma ta fasa.
"Barrister Waziri is the best, Darling kar ka ji
komai, we'll win this case" ta riƙo hannunsa tana murzawa.
"Daddy yaushe Nana da Mayrah za su dawo" Junior ya katse kallon-kallon da ake tsakanin Bilkisu da ke riƙe da hannun Gwamna da kuma Asiya da ta kasa sauke idonta daga kallon Bilkisu zuwa hannun
ta da ke kan na Gwamna.
"Daddy zan je wajen Dadda nima"
"Ba inda zaka je, suma su Nanan sun kusa dawowa gida"
Gwamna bai ƙare cin abincin ba ya miƙe ya ce ya tafi. Bayan tafiyarsa Bilkisu tace "gurin shiga kike nema a wajen Darling" ta ƙyalƙyale d
a dariya sannan ta cigaba "idan aikin girki kika zo yi, zaki iya komawa Quaters
ɗ
in mai'aikata saboda nan yafi dacewa da ke, "
"Indai kullum zai dinga cin girkina zan so komawa Quarters
ɗ
in"
Bilkisu ta sake bushewa da dariya wannan karan har sai da
ta ƙware...
***
Zaman da akayi bai haifar da
ɗ
a mai ido ba saboda Lauyoyin Gwamna ba su iya bada ƙwararren shaida da zai ƙaryata iƙirarin Lami Ninja ba, haka aka sake
ɗ
aga zaman zuwa wata sati.
Gwamna yana duba wasu takardu COS ya shigo ya sanar
da shi zaman da aka yi bai yi wani tasiri a case
ɗ
in da aka yi ba kuma House gobe za su kada ƙuri'a ko a fara trial ko kar a fara .
Gwamna yai kaman bai ji shi ba ta hanyar sako zancen wani project da yake so ya fara.
A chan gidan Mr Silas ana jimam
in rashin ganinsa sa da ba ayi ba tun daren jiya.
A
ɓ
angaren mutanen Umaru Kwom ma sun shiga ru
ɗ
u saboda suna tunanin za su sameshi daren jiya akan za a kira shi shaida a kotu sai suka tarar baya nan, kuma ba a san inda ya shiga ba. An riga an biya shi Mi
liyan biyu saboda aikin da zai yi. Sai gashi kuma ya sa
ɓ
a alƙawari.
Gwamna daga office Rehab center ya wuce inda aka kai Nana. Ita Zunnairah ƙasar waje mahaifiyarta ta kaita.
Sai yanzu da Nana ta shiga withdrawal stage ya ganta cikin yanayi na ha
uka ya ji hankalinsa ya tashi fiye da ma lokacin da ya gano tana shaye-shaye.
Zuciyarsa a cunkushe ya dawo gida bayan ya mata addu'ar samun lafiya.
Yana shiga falonsa ya tarar da Asiya tana zaman jiransa.
"Mi kike nema?"
"Ina so Dan Allah ka bani d
ama naje Lagos"
"Kin saba yin abinda kike so"
"Ka yi haƙuri" ta fa
ɗ
a tana kallon ƙasa saboda ba za ta iya dubansa ba, tana buƙatar zuwa Lagos ko akwai abinda za ta iya samowa akan Lami Ninja.
"Akwai abinci a dining ko na kawo nan?" Ta fa
ɗ
a lokacin
da take shirin shigewa. Bai amsa ba ya wuce ya barta tsaye.
Bisa mamakinta tana cin abinci da junior ya zo ya zauna ta serving nashi. Har suka gama ci Bilkisu bata
ɓ
ullo ba, kamar ma bata gidan.
Lokacin da ta shiga
ɗ
aki ta fara ha
ɗ
a kayanta Sumayya ta
tambayeta ina kuma za ta je, tace mata Lagos.
"Anty Asiya kinada gajen haƙuri Allah. Yanzu ana cikin matsala za kiyi tafiya, idan wani abu ya sameki fa"
"Ba ruwanki da ni, ba zan iya zama komai ya lalace ba"
*"Kinada taurin kai Asiya, Ba kya jin
shawara a rayuwarki, babban matsalarki kenan"* ta tuno kalaman Ubayd.
Ta zauna bakin gado riƙe da gyale a hannunta. Sumayya tayi gaskiya, Fou'ad yace zai nemeta idan ya samu evidence, C Y yace mata ta kwantar da hankalinta akwai abinda ya samu amma sai
ya tabbatar da komai zai gaya mata. Miyasa ba za ta iya jira ba?
4
Wani ƙyamusasshen mutum ne zaune a kan Buzu yana muimui da baki alamar yana magana da Ruhanai ko Aljanu.
Ya kai kusan minti biyar yana buga ƙasa, yai rubutu akan ƙasar da k
e kan wani faifai ya share, ya sake wani rubutun nan ma ya share.
Bayan ya gama bincikensa sai ya
ɗ
ago ya kalli mutumin dake gabansa yace "Akwai wata mace a jikinsa, tana da ƙarfi sosai, tauraronta yana da haske. Matuƙar tana tare da shi sai dai bai nem
i abu ba amma yana nema, ya samu. Ita
ɗ
in irin matan nan ne da aka haliccesu da baiwa, duk wanda suka ra
ɓ
a sai rayuwarsa ta chanja, irinsu da za su auri faƙiri da bashi da anini, to da sannu sai ya samu wadata"
"Malam wace macece kenan? Matarsa ce ko
'yarsa, ko kuma wa? Sannan kana nufin Umaru Kwom ba zai samu nasara ba?"
Mutumin ya ƙyalƙyale da wata irin dariya marar da
ɗ
in ji, idan ka saurari dariyar da kyau ka
ɗ
auka tsuntsuwa ce ke kuka.
Bayan ya gama dariyar sai kuma ya ha
ɗ
e rai kamar bai ta
ɓ
a d
ariya ba.
"Kai! Ubangiji ka
ɗ
ai ke da sanin Gaibu. Wacece ita? kamanninta, ina take? Banida amsar su. Abunda aka fa
ɗ
a mini shine, ita
ɗ
in kariya ce a gareshi kuma zai
ɗ
aukaka fiye da tsammani matuƙar tana tare da shi. Kabar batun tsige shi, an hasko mini
shi akan kujerar mulki"
Mutumin da aka fa
ɗ
awa maganar ya shiga ru
ɗ
u yana neman agaji ko akwai abinda za a iya yi. Malam Nawaso ya fatattake shi daga wajen, yana fa
ɗ
in
shi aikinsa yana da iyaka, kuma ya riga ya fa
ɗ
a masa abinda ya zo tambaya.
Tunda y
a bar wajen Malam Nawaso, ya shiga jujjuya maganar a ransa, yana neman ta yadda zai fa
ɗ
i maganar ba tareda ya
ɓ
atawa Umaru Kwom rai ba.
Lokacin da ya isa gidan Umaru Kwom, kasancewar akwai kusanci tsakaninsu bai tsaya wata-wata ba aka masa iso a falon Alh
aji Umaru Kwom.
A ƙasan carpet ya zauna yana jiran fitowar Maigidansa. Minti bakwai sai ga Alhaji Umaru Kwom ya fito sanye da farar riga 'yar shara da wando. Tun kafin ya zauna mutumin ya shiga yi masa kirari yana fa
ɗ
in sai ka yi Gwamnan Jahar Congo.
Umaru Kwom ya zauna akan kujera ya
ɗ
aura ƙafa
ɗ
aya akan
ɗ
aya yace "Bature kai ne da dare haka. Fatan ka taho min da labari mai da
ɗ
i"
Bature ya ha
ɗ
iyi yawu maƙwot sannan ya fara washe baki yana zuba bayanin da ya tsara kafin tahowarsa.
"Ai Excellenc
y, Malam Nawaso ya kai inda mutane suke maganarsa. Yace akwai nasara a tafiyarka, sai dai kuma..."
"Ka fa
ɗ
i koma minene, ba yau muka fara jin labarai marasa da
ɗ
i ba "
Bature ya ka
ɗ
a baki ya cigaba da bayani " ya fa
ɗ
amin cewa
ɗ
aya daga cikin matans
a tana da asiri mai ƙarfi a tattare da ita, ba zata ta
ɓ
a bari Saifuddeen Kachallah ya fa
ɗ
i a za
ɓ
e ba. Yace ba za a tsige Saifuddeen Kachallah ba, sannan idan lokacin za
ɓ
e ya zo za ta yi komai wajen ganin mijinta ya ƙara hawa kujera"
Jiki na rawa Umaru K
wom yace " akwai mafita? wani mafita ya bayar? sannan waccece a cikin matan nasa?"
Bature ya gyara zamansa, ganin haƙarsa ta soma cimma ruwa.
"Ai wato Malam Nawaso bai bayyana wacece a cikin matan ba, amma inaga ba zai wuce Bilkisu Kachallah ba dan mat
ar nan da ka ganta ka ga hatsabibiya"
Ya karya murya ya cigaba " Malam ya buƙaci wasu abubuwa da za ayi amfani da su wajen yaƙar wannan Asirin. Yace akwai sadakar da zai sa ayiwa Aljanu kaman miliyan goma, saboda su dinga yi maka addu'a har ranan za
ɓ
e"
"Nawa yake buƙata?"
"Ranka shi da
ɗ
e ya buƙaci ku
ɗ
i dayawa fa" Bature yai maganar yana sosa kai.
"Na ce nawa ne?"
"Miliyan goma cash"
"Shine ku
ɗ
i dayawa. Zan sa a ha
ɗ
a maka shi gobe da safe sai ka kai masa. Ka tabbatar yayi duk abinda ya dac
e"
Bayan tafiyar Bature. Umaru Kwom ya zauna yana nazarin waccece a cikin matan Saifuddeen. Wani zuciyar na riya masa cewa Bilkisu Kachallah ce, amma kuma Asiya ma akwai alamar tambaya akanta. Yana da labarin ita
ɗ
in jikar wani babban malami ne maiƙusum
bi. Malaman zaure kuma akwai su da sirrika, ƙila kafin Kakanta ya rasu ya bata wasu laƙanin ƙarfi. Bai manta yadda take masa magana babu tsoro bare wani
ɗ
ar ba jiya data kira shi. Koma minene dai wannan za
ɓ
en sai ya lashe, ko ta yanene...
***
"Baba
, mi kake yi akan wannan zancen?. Monday fa House za su voting, kuma kasan saboda wannan abun wa
ɗ
ansu sun fara maganar kar a bari Saifuddeen ya tsaya takara. Primary election is this Saturday amma saboda wannan abin an sake kaishi wata sati. I can't stand
this"
Bilkisu ta fa
ɗ
a cike da damuwa a ranta, abu
ɗ
aya da zata iya yi ta warware wannan maganar kuma zai iya jawo a banka
ɗ
o nata sirrukan, shima kuma scandal ne da zai kawo wa Saifuddeen matsala a kujerarsa.
"Kin san dai ba zan zuba ido a tsige Sai
fu ba ko, dan haka ki kwantar da hankalinki"
"Baba there's no time"
" na yi waya da shugaban ƙasa, sannan mun zauna da party chairman na ƙasa, sun tabbatar mini House zata dismissing trial
ɗ
in. Matsalar da zamu fiskanta shine, dole kotu ta wanke Saif
u kafin za
ɓ
e idan ba hakaba, zamu bar gi
ɓ
i mai fa
ɗ
i da Umaru Kwom zai yi amfani da shi wajen Kamfen"
"Indai aka warware maganar impeachment shikenan, sauran mai sauƙi ne"
Da haka ta
ɗ
au kofin shayi ta kai bakinta ta kur
ɓ
i ka
ɗ
an, zafin daya ratsa hars
henta ko ka
ɗ
an bai kai zafin da take ji a zuciyarta ba, saboda fargabar barin kujerar first lady of the state.
Zumar da ke ƙunshe cikin kujerar Mulki tanada wuyar sha'ani, saboda zaƙi da da
ɗ
inta. Da ka
ɗ
an
ɗ
ana, ko da
ɗ
an ka
ɗ
an ne, to sai kayi da gaske k
afin ka iya rabuwa da shi.
Alhaji Sani da 'yarsa dukkansu sun
ɗ
an
ɗ
ani zumar Mulki kuma sun san zaƙinta, ba abinda suka rasa na ku
ɗ
i da dukiya amma Mulki...suna son wannan Mulki ya kasance na su, har zuwa lokacin da aka
ɗ
iba.
Yayinda ake cikin wannan
kuma, an sako Mr Silas ya dawo gida.
Mr Silas ya sha bugu a hannun Yaya Bello kafin ya fa
ɗ
i gaskiyar lamarin abinda ya faru shekaru shabiyar da suka wuce.
Lami Ninja ce ta biyashi ku
ɗ
i akan ya bar mata ƙofar ofishin Prof Kachallah a bu
ɗ
e. Sannan shine y
a tsaya stand by akan idan Saifuddeen ya fito ya saka masa ihu, ya tara masa mutane. Domin idan ya amince da buƙatarta ita zata fara fitowa daga office
ɗ
in ba shi ba.
A ranan da Lami