Showing 24001 words to 27000 words out of 67805 words
kuka.
"Ina Umma? Ta je anguwane?"
" Ummanki bata nan Asiya. Ki shigo ciki" ta kamo hannunta zata kaita
ɗ
aki. Asiya ta tirje tace "ki gayamin inda taje"...
Asiya ta zauna a ƙofar
ɗ
akin Umma tana jiran
dawowar Abba. Ita dai ƙarya Inna Yaha ta mata da ta ce Umma ta rasu. Sharrin Inna Yaha ne kawai zata ce Umma ta rasu. Umma na nan.
Gajiya, Yunwa, ciwon jiki duk ba sune damuwar Asiya ba. Ita dai tana so ace mata Ummanta na nan da ranta, abinda ta gani a
TV ba gaskiya bane film ne.
Inna Yaha tace Musa ya je ya kirawo Abba a masallaci. A hanya suka ha
ɗ
u dan ko minti biyu bai cika da fitansa ba ya shigo biye da Abba.
"Asiya, Asiya kina lafiya? Kema 'yan sanda ne suka ku
ɓ
utar da ke?" Abba ya tambaya ya
na riƙe hannun Asiya.
Tun da la'asar da suka ji labarin an samu
ɗ
aliban nan suke sa ran su ji an samu Asiya amma shiru. Ya kira Gwamna dan ya tambayi labarin Asiya amma Gwamna bai
ɗ
auka ba.
Bayan sun
ɗ
an nitsu Abba ya fara yiwa Asiya nasiha akan mutu
wa daga ƙarshe ya sanar da ita rasuwan Ummanta.
Mutumin da take tunanin zai ƙaryata labarin da ta ji sai gashi ya sake tabbatar mata da mugun labari.
"Abba da gaske sun kashe min Umma?"
"Kul Asiya. Kul kika sake magana irin wannan, sai kace jahila"
"Abba..."
"Addu'a zaki mata ba ƙorafi ba Asiya. Addu'arki take buƙata yanzu".
Asiya ta sunkuyar da kai sai hawaye.
" na kai miki ruwan wanka Asiya. Kije kiyi wanka, sai ki zo ki ci abinci" Inna Yaha ta fa
ɗ
a lokacin data shigo falon.
Ba Asiya
ba, shi kansa Abba ya yi mamakin kalaman Inna Yaha...
Gwamna na hanyar zuwa gidan Yalla
ɓ
ai bayan ya bar Asibiti Abba ya kira shi.
"Da kanta ta dawo? Ba abinda ya sameta ko?" Gwamna ya fa
ɗ
a cike da farin ciki yama manta da sirikinsa yake magana.
Yana gama wayar yasa aka juya da shi. Da farko gidan zai wuce direct sai ya ga idan yaje haka zai ja hankalin jama'a shiyasa ya fara zuwa chan tsohon gidansa. Ya ce Dreban Gwamnati da excort su wuce chan Government house yayinda shi kuma ya shige motarsa
drebansa ya fice da shi.
Asiya ta jima a ban
ɗ
aki tana kuka kafin tayi wanka ta fito. Lokacin da ta fito an bu
ɗ
e
ɗ
akin Umma, ta tsaya bakin ƙofa tana jiran ta ga ko za ta hango Umma kwance akan sallaya ko akan gado, amma bata gani ba. Gwani da Habibu ne
a
ɗ
akin suna magana.
Gwani yace "Anty, Yaya Ubaydu yace a gaisheki"
Ba ta yi magana ba sai ta gya
ɗ
a masa kai...
Abba da Ubayd suna falo lokacin da Abba yai waya da Gwamna, jin cewa Gwamna yana hanya Ubayd ya miƙe yai wa Abba sallama. Dama yana ji
ra Asiya ta fito su gaisa ne, amma tunda mai guri ya zo sai mai tabarma ya na
ɗ
e.
9
"Ina Sumayya?" Asiya ta tambayi Ali daya shigo gaisheta.
"Yau ta koma hostel"
"Har yanzu kana yawon dare ko?"
"A'a na dena... yeeh Gwamna
yazo" ya miƙe ya fice da gudu jin ƙaran tsayuwar mota a gidansu.
Lallai yaro yaro ne. Ko sati bai cika ba da rasuwar Mahaifiyarsa, amma damuwarsa Gwamna ya zo gidansu.
Asiya ta sauke ajiyar zuciya ta zubawa abincin da aka kawo mata ido. Tuwon masara
ne da miyar kuka, da alama cikin wanda aka rage na
ɗ
umamen gobe aka
ɗ
ebo mata dan babu nama a ciki sai ƙullin balangu a leda da ke gefe. Sai kuma lipton da madara guda biyu na leda da aka ajiye a gefe.
Ta
ɗ
eba sugar ta saka a lipton
ɗ
in ta raugaya ta fa
ra kur
ɓ
a ka
ɗ
an ka
ɗ
an. Duk da yunwar dake cinta hakan bai hanata jin haushin Gwamna ba. Da zata ga fiskarsa ruwan shayin nan zata watsa masa saboda yadda ta tsani fiskarsa...
Abba yai ta zarewa su Habibu ido amma yaran suka dake suka ƙi tashi daga falo
n, suka maƙalewa Gwamna suna cewa sai yayi hoto da su.
Gwani ne mai hankalin cikinsu dan haka Abba yace "Lukman ka je ka kira min yayarka"
"Abba abinci take ci" Ali yai saurin fa
ɗ
a saboda matuƙar Gwani ya tashi suma
ɗ
in aikansu za ayi.
Abba ya ha
ɗ
e rai yace " Aliyu kayi tilawar yau ne?"
Ali yai saurin miƙewa dan yanzu idan yai ƙarya Abba zai sa shi karatun dole.
Ganin Ali da Gwani sun fita Abba ya kalli Habibu yace " kaje ka duba min lafiyar mashin"
Habibu ya miƙe yana ƙunƙuni.
Bayan y
aran sun watse Abba da Gwamna suka sake gaisawa sannan suka yiwa juna jajen abinda ya faru.
Gwamna ya nisa yace " Sumayya bata nan ne? "
"Yau ta wuce hostel"
Ganin shirun yayi yawa Asiya bata shigo ba Abba ya miƙe yace yana zuwa.
Asiya ta ƙaris
a shan shayi amma bata ta
ɓ
a tuwon ba, bata da appetite na cin komai.
Abba yai sallama ya shigo
ɗ
akin.
"Ki je ku gaisa, idan kika dawo sai ki fa
ɗ
i abinda zaki ci" babu wasa a yanayinsa hakan yasa Asiya ta miƙe ta shiga neman hijabi. Lokacin data fito
daga wanka jallabiya sabuwa Inna Yaha ta kawo mata, tana tunanin ma ba zai wuce cikin kayan Faty bane data bar wa Hindatu.
Bata san miyasa aka tattara kayan Umma ba, bata san miyasa aka ma rufe wardrobe dake
ɗ
akin ba. Sai kuma ta tuna cewa yanzu fa kaya
n Umma sun zama na gado.
"Asiya ba zaki wuce bane"
"Abba hijab nake nema"
"Ke da mijinki sai kin wani tsaya neman hijabi"
Da cikin nitsuwa take, cewa za tai "Lah! Abba da kanka" sannan tayi dariya.
Yanzu kam babu abinda ta iya cewa, sai ta
ɗ
au gyalen kayan wanda har lokacin yana cikin ledar jallabiyar, ta yafa akanta ta fita.
Lokacin data shigo waya yake yi.
"Eh nina ce su wuce gida, ina tareda Asya, an sakota...Amin"
Ya ajiye wayar gefe ya kalli Asiya da ke tsaye ta riƙe ƙugu.
Abinka da farar mace har wahala tasa ta fara dishewa. Duk da haka tayi masa kyau, baƙar jallabiya mai duwatsu blue ya amshi jikinta duk da ramar da ta yi.
"Asya" ya furta cike da shauƙi.
"Ka zo ka gani ko sun karya min ƙafa ne? Ko kuma sun datse ha
rshena?"
"Ki zauna mu yi magana Dan Allah"
hajijiya ta fara ji hakan yasa ta bi umurninsa ta zauna suna fuskantar juna.
"Ina miki ta'azziyar rasuwar Umma, Allah ya gafarta mata"
"Kanada bakin ta'aziyya dama. Ai na
ɗ
auka abinda kake so kenan"
Gwamna ya
ɗ
an zaro ido cikin rashin fahimta
"Asya bana so ki
ɓ
oye min komai. Ki fa
ɗ
amin yadda komai ya faru, ina suka kaiki? Mi suka ce miki?. Ina ganin kamar..."
"Kamar me? Har kana da bakin magana. You are a fraud Gwamna Saifuddeen, kai munafukin
e kuma Azzalumi. Har na fara tunanin tayaka Kamfen ashe kai ka riga ka shirya naka Kamfen
ɗ
in. You said it yourself ni hajar Kamfen ce, i mean nothing to you. Taya zaka sa a sace ni a ranan da mahaifiyata take kwance a gadon Asibiti. Taya zaka sa a hanani
yiwa mahaifiyata addu'a?"
Gwamna ya miƙe tsaye ya tako zuwa gabanta hakan yasa ta yi shiru sai nishi da take sama sama. Ya sa hannu biyu ya miƙar da ita tsaye. Sai da idonsu ya ha
ɗ
u kafin tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasa.
"Asya kina tunanin zan sa
a sace ki saboda Kamfen? Abinda suka fa
ɗ
a miki kenan?"
Tayi shiru ta kasa magana saboda kusancinsu da yai yawa, turarensa da take shaƙa ma kaman jawota jikinsa yake.
"Wani irin ƙiyayya kike min Asya?, miyasa akoda yaushe ba kya min zaton alkhairi sai
na sharri?. Aurenmu zai iya kasancewa ƙaddara amma ko a hakan, matar mutum matar mutum ce, no matter what. Idan zaki min adalci Asya, a iya zaman da muka yi ya kamata ki gane cewa bana wasa da iyalina, and you are my family"
"Kai kace su
ɗ
auko ni. Kai
ka tura min text kace na bisu. Akwai wanda ke da numba irin naka ne?. Ni ba yarinya bace, Excellency na san yadda 'yan siyasa suke zama a lokacin yaƙin neman za
ɓ
e. Ka yi amfani da ni ne saboda ka samu mutane"
Ya san tana cikin ra
ɗ
a
ɗ
in rashin uwa, ya sa
n abinda ya faru dole ne ya ta
ɓ
a tunaninta, amma idan da zata iya duban ƙwayan idanunsa da zata ga tsananin so a cikinsu.
Da ta san abinda yai saboda ita, da bazata ƙara tunanin zai iya cutar da ita ba.
"Ina son ki Asya" Asiya-Shahidah ta yi saurin
ɗ
a
go idanu ta kalleshi. Shima ita yake kallo hakan ya bashi daman ƙarisa maganar "Ba zan ta
ɓ
a cutar da ke ba, ba zan ta
ɓ
a amfani da ke wajen neman duniya ba. Ina fatan watarana za ki fahimci hakan"
Bai jira mi zata ce ba, bai yi ƙoƙarin goge hawayen da ya
gangaro mata ba. Bai yi ƙoƙarin ƙara wasu kalaman ba saboda babu amfanin yin hakan.
Har Gwamna ya fice daga falon Asiya tana tsaye tana rawar jiki yayinda hawaye ya cigaba da zubo mata. Ƙarshe tsayuwar ya gagareta, ta tsugunna a
ƙ
asa jikinta ya cigaba d
a rawa. Kalaman Gwamna sun ratsa kowanni lungu da saƙo na jikinta.
*"ina son ki Asya"* ya fara maimaituwa a kunnenta, hakan yasa ta toshe kunnen da hannu biyu jikinta ya cigaba da rawa...
***
Lokacin da Gwamna ya isa gida kai tsaye
ɗ
akinsa ya wuc
e ya zauna yana tunanin kalaman Asiya. Wani irin tsana ta masa ne? A iya saninsa da ita, shi bai ta
ɓ
a yi mata komai ba.
Daya fito daga ban
ɗ
aki ya ga Bilkisu zaune a bakin gado tana jiransa.
"Na
ɗ
auka gida zaka kawota ai?"
"Tana buƙatar kasancewa d
a 'yanuwanta"
"Hakane, fatan tana lafiya?"
"Ba kya ganin Baba ne ya sa aka
ɗ
auke Asiya?"
"Baba kuma!" Bilkisu ta fa
ɗ
a tana kama baki.
"Anya Baba zai iya haka?, ni gaskiya ban yarda ba" ta fa
ɗ
a ganin Gwamna bai yi magana ba.
"Junior yayi bac
ci ne?" Ya kauda maganar...
***
Lokacin da Asiya ta farka a gadon Asibiti ta ganta, kusa da ita Sumayya ce da kuma Bilkisu Kachallah.
Jiya da dare da Abba ya shiga falo ya sameta bata cikin hayyacinta. Har aka kawota Asibiti bata san inda ka
nta yake ba.
Da sassafe Gwamna ya zo ya dubata lokacin tana bacci.
"Anty Asiya ya jikin?" Sumayya ta tambaya murya ƙasa-ƙasa saboda tsoron Bilkisu Kachallah da take.
Asiya tace "Sumy zan sha ruwa"
Sumy ta miƙe ta wuce wajen ƙaramin fridge dake
ɗ
akin.
Sai da Bilkisu Kachallah ta gama waya kafin tace "sannu fa, ya jikin?"
Asiya ta kauda kai gefe.
"Ɗarling ya zo kina bacci, yace a isar masa da gaisuwa"
Asiya ta miƙe zaune tace "tunda ke da mijinki kun samu abunda kuke so, sai ku barni a
i, ku bar ni na ji da damuwata"
Bilkisu tayi murmushi tace " mijinmu dai ko ? Don't pretend cewa ba kya jin da
ɗ
in kasancewarki matar Gwamna."
"Allah ya sawwaƙa"
Bilkisu ta miƙe tace " zan wuce, Allah ya kawo sauƙi"
Daga Asibiti, Bilkisu gidansu
ta wuce saboda Hajiyarsu data kira meeting. Sai da ta isa gidan ta samu meeting
ɗ
in su uku aka kira. Ita, Saudah da kuma autarsu Halima.
Hajiya tayi musu bayani akan bata ji da
ɗ
in yadda aka watse family meeting da suka yi kwanan baya ba, an rabu ranan
ba da da
ɗ
i ba. Dama tsakanin Bilkisu da Halima babu jituwa to amma bata san miya ha
ɗ
a Bilkisun da Saudah ba, kasancewa a baya sun fi kusa da junansu.
"Hajiya yanzu har na gayyaci Halima da Saudah wajen Kamfen
ɗ
ina su ƙi zuwa"
Bilkisu ta fa
ɗ
a tana kallo
n Hajiyar.
"Ni na je Kamfen
ɗ
inki Bilkisu. Allah ya tsare" Saudah ta fa
ɗ
a tana tafa hannu
Hajiyarsu tace " Saudah wani irin magana ne wannan?"
"Hajiya taya zan amsa gayyatarta bayan abinda ta yiwa 'yata"
"Oh! Saboda shegiyar 'yarki kike fushi.
Chan ta matse miki dan ko yau na ganta a gidana sai na cire mata ƙafa"
"Hajiya kinji mi take kiran Zunnairah ko?"
"To ba 'yar shegiyar bace. You are 6 weeks pregnant lokacin da aka
ɗ
aura miki aure kuma..."
"Bilkisu! " Hajiya ta daka mata tsawa.
"Oh Lalala! Aikin ya fara warwarewa kenan" Halima ta fa
ɗ
a tana miƙe ƙafa akan kujera tareda fashewa da dariya.
Saudah ta miƙe a fusace tana fa
ɗ
in "Bilkisu kar ki manta akwai sirrinki a tafin hannuna. Zan ga da wani ido zaki kalli Yaya Saifuddeen i
dan ya san kin je an cire miki mahaifa"
"Subhanallahi!. Wai lafiyarku kuwa?. Ke Bilkisu da gaske ne abinda Saudah ta fa
ɗ
a?"
Bilkisu ta miƙe tsaye ta
ɗ
au jakarta tace " cire mahaifa ba abin kunya bane Hajiya, saboda lafiyata na cire. Amma ki jawa Saud
ah kunne idan bata
kama kanta ba, ni da kaina zan fa
ɗ
awa duniya cewa Zunnairah 'yar wani Bamaguje ne a jahar Benue"
"Yau ana drama a gidan nan" Halima ta fa
ɗ
a tana kwashewa da dariya.
"Halima!" Bilkisu ta fa
ɗ
a da ƙarfi
"Allah ya huci ranki excel
lency" Halima ta fa
ɗ
a tana ha
ɗ
a hannu biyu. Bilkisu ta fice daga falon ranta a
ɓ
ace.
Bayan fitan Bilkisu Hajiya ta kalli Saudah tana neman ƙarin bayani gameda abinda Bilkisun ta fa
ɗ
a, amma Saudah tayi shiru itama nadama ya damaimayeta.
Hajiya ta san da
batun cikin shegen da Saudah tayi, kuma ƙaryar da tayi cewa cikin na Usman ne shiyasa ta bari aka yi auren cikin gaggawa.
Ƙ
uruciya a lokacin da kake ji da ku
ɗ
i, jin da
ɗ
i da kuma 'yanci irin na turawa yana iya sakawa ka shagala da biyewa son zuciya. A w
ajen party ta ha
ɗ
u da mutumin da har yau ba za ta iya tuna sunanshi ba. Sau
ɗ
aya da suka kasance tare a yanayi na maye ta samu ciki. An riga an saka bikinta da Usman kuma shima sun ta
ɓ
a sanin juna shiyasa ta jona masa cikin.
Yanzu shekaru sun ja, amma har
yau bata dena nadamar ƙuruciyar da ta yi ba.
***
Da safe bayan fitar Bilkisu Kachallah, Hansa'u ta shiga
ɗ
akinta ta
ɗ
auko akwatin sirrin Bilkisu, ta saka password da aka aiko mata da shi nan da nan akwatin ya bu
ɗ
e. Zaro ido tayi ganin dami damin ku
ɗ
i na dollars. Sai data
ɗ
ebe ku
ɗ
in ta zuba a kan gado sannan ta ci karo da wasu takardu, takardun duk wani business da take ne. Takardan ƙarshe wanda yake cikin wata jar file shine wanda take nema.
Kwanan wata da saka hannu da duk wani bayanai gameda hark
an safarar ƙwayoyi da suke yi tsakanin ƙasar Mexico, America da kuma Columbia yana ciki.
Ta zaro wayarta ta fara
ɗ
aukan takardun a hoto, da ta gama ta maida takardun cikin akwatin tareda jera ku
ɗ
i a samansu kamar yadda ta samesu. Ta maida akwatin inda ta
ɗ
auko shi, kafin ta fice daga
ɗ
akin.
Ta riga ta samu abinda take so dan haka a yau zata bar gidan. Kayan aikinta kawai ta
ɗ
auka ta saka a jaka ta rufe da wasu tsummokara ta fito, ta yiwa masu aiki sallama akan za ta je ta dubo mahaifiyarta a ƙauye. Ita
ɗ
in ta hannun damar Bilkisu ce dan haka ba su zargi komai ba.
Tana fita daga gidan Gwamnati kai tsaye gidanta ta wuce. Tayi wanka ta chanja kaya sannan ta fito, har zata fita sai kuma ta tuna cewa ya kamata ta gayawa Asiya wacece Bilkisu Kachallah. T
a ga rahoton da aka yi da safe, inda aka nuna Bilkisu Kachallah tana matse ƙwalla a gefen gadon da aka kwantar da Asiya, tana fa
ɗ
in ba za su yafewa wanda yai wa Asiya wannan ba.
Idan ka san waye maƙiyin ka zaka iya yaƙarsa, amma maƙiyin
ɓ
oye da wuya ake
cin galaba a kansa. Saboda ba a san fiskarsa ba, ba a san ya yake ba sannan ba a san ta ina zai
ɓ
ullo ba.
Ta nemi takarda ta yi gajeren rubutu sannan ta na
ɗ
e ta saka a envelop.
Dogon hijabi ta saka a kan kayanta ta fice daga gidan, ta nemi Keke ya k
aita gidan Gwamna.
Tana shiga gidan ta tambayi masu gadi ina Yaya Bello aka ce mata ya tafi Asibiti. Ba lallai ta sake dawowa gidan ba sannan kuma tana tsoron bawa wani takardar. Sai kawai ta shige cikin gidan. Suka gaisa da Uwani tace mata an aikota ne
ta
ɗ
auki abu a sashen Asiya.
Tana shiga
ɗ
akin Asiya ta fara neman inda zata ajiye mata wasiƙar da wani ba zai gani ba, sannan Asiya zata gani da wuri. Ƙarshe ta saka wasiƙar a tsakiyar ƙur'ani data gani a kan