Showing 51001 words to 54000 words out of 67805 words

Chapter 18 - MATAR GWAMNA BOOK2 COMPLETE

waƙa na yabo da jinjina ga mijina Gwamna Saifuddeen. I want it to be a surprise, so ki tura min reply ta email

ɗ

ina mai suna seeyashahidah@gmail.com*

Ba kalmar data

ɗ

au hankalinsa sai kalmar MIJIN

A data rubuta. Kenan... sai kawai yai murmushi.

***

"Ina ga wa

ɗ

annan su zasu kasance candidate namu. Ku duba ku gani"

Yalla

ɓ

ai ya miƙawa Mr Paul wasu takardu. Mr Paul ya kar

ɓ

a ya rarraba takardun dan kowa ya gani. Bayan sun gama gani suka yi n

a'am da list

ɗ

in sai mutum biyu da Alhaji Sani Kachallah yai ƙorafi akansu amma ganin cewa shi ka

ɗ

ai yai ƙorafin sai kawai aka buga stamp akan cewa list

ɗ

in za a ba wa Gwamna Saifuddeen.

Da yammacin ranan kuwa Bilkisu ta samu Yalla

ɓ

ai ta tambayeshi muta

nen da aka saka a list. Yana miƙa mata list

ɗ

in ta kar

ɓ

a ta kekketa shi ko karantawa ba ta yi ba.

Yalla

ɓ

ai ya zaro ido da mamaki amma ya kasa cewa komai.

"Zan duba mutanen da suka dace, ko suna cikin list

ɗ

inku ko basa cikin su wanda na za

ɓ

a za a sa

ka"

Yalla

ɓ

ai ya gya

ɗ

a kai.

Tana isa gida ta samu Asiya na zanawa Nana lalle.

"Mommy ki ga hannuna yayi kyau"

"Wani irin

ɓ

ata guri ne wannan? Za a iya yin baƙi a kowanni lokaci amma kun zauna anan kuna

ɓ

ata waje"

Asiya ta kalli Bilkisu sai ku

ma ta sunkuyar da kanta ta cigaba da sakawa Nana lalle a ƙafa. Tun jiya da Nana ta ga lalle a hannunta ta dinga damunta akan tana so ta mata irinsa. Bata ga aibun zamansu a nan ba, ba falon da ake kar

ɓ

an baƙi bane, zamansu a wajen ma saboda Queen Bee data

zo ne Nana ta fito wai a mata lalle shine kawai suka fara a wajen.

Bilkisu ta tauna le

ɓ

enta na ƙasa tana ƙoƙarin shanye rashin mutuncin Asiya. The mighty Bilkisu Kachallah tana tsaye amma ta yi kaman bata ganta ba.

Wannan iyayi da Asiya ta ke ya isheta

. Yau yau zata sa Saifuddeen ya mayar da ita gidansa, idan aka rantsar da shi kuma guguwar za

ɓ

e ya lafa sai ta sa ayi waje da ita. Ta riga ta gama amfani, ba abinda zamanta zai ƙara musu yanzu.

Ta wuce fuuu ba tare da ta sake cewa komai ba.

Da dare da

suka kwanta Bilkisu ta riƙo hannun Gwamna Saifuddeen, lokacin da hannunsu ya ha

ɗ

u zoben hannunta yai wani ƙyalli na sakan da bai wuce

ɗ

aya ba.

"Darling, ina so ka maida Asiya gidanka"

"Asiya?"

"Yes" ta fa

ɗ

a tana shafa ƙirjinsa.

Yana son tambay

ar dalili amma kuma ya kasa.

Ganin yayi shiru sai ta cigaba

"Ina so ka hanata fita hidima kowanni iri. Kuma bana so ka bata haƙƙin matarka"

Ta yiwa Yalla

ɓ

ai haka kuma ya ci shi, dan haka shirun Gwamna akan zancenta bai zo da mamaki ba. Dan ma ta ƙ

ara tabbatarda ƙarfinta sai tace

"Ina so kace mata ta bar gidan nan a daren yau"

Gwamna Saifuddeen ya kalleta a firgice amma kuma hakan bai hanashi miƙewa ba, ko takalmi bai sa ba ya fice daga

ɗ

akin ya nufi

ɗ

akin Asiya.

"Excellency ka bari gobe sai

na tattara na koma chan

ɗ

in tunda baka son zamana a nan" Asiya ta fa

ɗ

a bayan Gwamna ya tasheta daga bacci ya mata maganar barin gida.

"Ba za

ɓ

i nake baki ba, umurni ne"

"Allah ya baka haƙuri" Asiya ta fa

ɗ

a a tunzure dan taga abin nasa ma rainin hanka

li ne. Taya zai zo ƙarfe goman dare yace ta tattara ta koma

ɗ

aya gidan.

Babu wanda ta kira cikin masu aikin gidan, da kanta ta shiga ha

ɗ

a kayanta. Tana yi zuciyarta na ƙuna, yadda take jefa kayan cikin akwati ka

ɗ

ai zai tabbatar maka

ɓ

acin ran da take ci

ki. A cikin zuciyarta tayi alƙawarin ba zata sake zama a wannan gidan ba, na ƙarshe kenan da zata zo, idan ya ga dama chan gidansa ma zai iya

ɗ

auketa ya kaita duk inda ya ga dama.

Ƙ

arfe shabiyu da rabi saura na dare Asiya ta shiga

ɓ

angarenta na gidan Sa

ifuddeen. Wajen yayi shiru kuma da

ɗ

an ƙura dan da alama an kwana biyu ba a gyara ba.

Haushi da ke cinta ya

ɗ

auke duk wani bacci da take ji. Ta cire hijabi ta shiga gyara

ɗ

akinta, data gama ta koma falo shima ta fara gyarawa. A ƙalla ta yi kusan awa uku k

afin ta gama komai ta zo ta yi wanka sannan ta fa

ɗ

a gado sai baccin gajiya. Bata tashi bama sai ƙarfe bakwai na safe. Ta miƙe da sauri tana hailala sannan ta shige ban

ɗ

aki ta

ɗ

auro Alwala, data idar da sallah sai ga kiran Hajiya Umma.

Walima ce aka shir

ya a Kachallah House saboda taya Saifuddeen murnan cin za

ɓ

e. Ƙarfe hu

ɗ

u na yamma za ayi walimar iya matan family.

Dake maganar walimar cikin kwana biyu aka tsarata shiyasa ba a gaya mata ba sai yau

ɗ

in.

Asiya ta amsa da zata je, ba dan tana son zuwan ba

sai dan kawai bata son musawa Hajiya Umma dan tana ganin girmanta.

Ta fi minti goma tana kallon numbar Gwamna ta kasa kira. Yadda suka rabu jiya ke dawo mata, miye matsalarsa da zamanta a gidan Gwamnati, minene dalilinsa na fitar da ita a gidan cikin da

re? Ganin Shai

ɗ

an ya fara tunzura mata zuciya sai kawai ta dinga Istigafari a zuciyarta, ƙarshe ta tura masa text akan zata je Kachallah House. Bata samu reply

ɗ

insa ba sai kusan ƙarfe biyu na rana, har ta fitar da rai ma akan zai reply sai kuma ta ga suna

nsa lokacin da text ya shigo wayarta tana biga game.

*ban amince ba*

Ga saƙon gajeriya amma abinda ta haifar a zuciyar Asiya yayi girma matuƙa.

Saƙonsa ya ƙara tabbatar mata akwai wani abu a ƙasa. Ko lokacin da suke zaman shiru ma bai ta

ɓ

a hanata fit

a ba balle yanzu kuma da ya kasance akwai fahimta mai ƙarfi tsakaninsu.

Duk yadda ta yi ƙoƙarin hana kanta shiga damuwa saboda saƙonsa sai da hakan ta faru. Ta kasa zaune ta kasa tsaye. Mi yake faruwa? shine abinda take tambayar kanta. Rashin samun amsa

r yasa tayi ƙarfin gwiwa ta danna masa kira.

Kira har sau biyu amma bai

ɗ

auka ba. Ta riƙe wayar a hannu kamar abin sadaka, ta tisawa fiskar wayar ido. Tun tana jiran ganin haske har ta karaya da shigowar kiransa.

Ganin ƙarfe hu

ɗ

u saura sai ta kira Ha

jiya Umma tace mata ba zata samu zuwa ba ƙaninta ba lafiya ta je gidansu.

Har dare bata sake jin

ɗ

uriyar Gwamna ba. She was totally confused. Kwana biyu suna tare lafiya-lafiya amma cikin yini

ɗ

aya komai ya chanja mata. Bata gane wannan chanji ba, bata ku

ma san mi ya kawo wannan chanjin ba.

Ta gama tunanin duniyan nan amma duk abinda ta kamo sai ta ga bai kai dalilin da zai sa Gwamna ya mata haka ba...

***

19

Asiya tana kishingi

ɗ

e akan kujera hannunta riƙe da littafin Jojo Moyes mai s

una Me Before You, a zahiri karatu take amma ranta baya ga labarin, kewar mutumin da yanzu ganinsa a TV yafi ganinsa a zahiri take. Ba za ta iya tantance irin damuwa da take ciki akan shi ba. Yana cin abinci? Yana bacci? sau nawa yake murmushi a rana, har

yanzu yana tusa da Asuba? Mi yake a kwanakin da ba na uwargidansa ba.

"Ranki shi da

ɗ

e, Ranki shi da

ɗ

e" Asiya tayi firgigit ta kalli Uwani da ke risine a gabanta.

"Uwani lafiya?" Asiya ta fa

ɗ

a tana saukar da ƙafafuwanta ƙasa.

"Yanzu aka kira daga g

ate wai wata yarinya tana iƙirarin ita ƙanwarki ce"

"Ƙanwata?. Yaya Bello baya nan ne?"

"Ina ga, dan Badamasi yace yarinyar duk tsoratar da ita da akayi taƙi tafiya sai rantse rantse take wai ƙanwar Sumayya ce"

"Mi tace sunanta?"

"Jummala Ale

Faruƙ"

Asiya ta yi shiru tana tuno waye cikin ƙannenta ake kira da Jummala. Babu wacce ta fa

ɗ

o mata a rai amma sai ta cewa Uwani a shigo da yarinyar.

Da Sumayya na nan ma da ita zata tura ta dubo waye tunda babu wacce bata sani ba cikin 'ya'yan Ale, t

o bata nan ta tafi makaranta.

Asiya ta jingine kai tana ƙoƙarin saita tunaninta wanda har yanzu tafiya yake ga mutumin da ƙarfi da yaji ya mata kane-kane a cikin zuciya.

Yarinyar da Uwani ta shigo da ita falon Asiya tun daga babban falo taketa ihu da

shirirtar ƙauyenci irin ta 'yan ƙauye.

Tana sanye da riga da zani na Atampa da suka yanƙwane saboda rashin guga da kuma zaman cikin babban mota. Hijabinta yellow shar dashi har wani wawal wawal yake a ido. Ta rungume jan jakar Ghana-must-go wadda tsabar

tsofewa ya fara zare zare, ba wasu kayan azo a gani bane hakan yasa ta cukwuikwuye jakar a ƙirjinta kaman za a ƙwace mata.

"Adda Shahidah" hakan data fa

ɗ

a ya bayyana haƙwaranta da suka dafe da datti har da wani green green ta saman haƙoran wanda yai kam

a da da

ɗ

a

ɗɗ

en kuka ne daya samu gindin zama a wajen.

"Adda Shahidah Jummala ce, aaf! Jummai, Jumman Delu"

Kafin ta gama lissafinta Asiya ta riga taga kamannin 'yan gidansu a jikin yarinyar, datti ne ya maida ta haka amma idan ta sha wanka zata iya fi

n Asiya ma farar fata.

Akwai wata Delu mai Daddawa da Ale ya aura kusan shekaru shabiyar da suka wuce alokacin Asiya ba zata wuce shekara tara zuwa goma ba amma akwai abinda zata iya tunawa game da Delu. Ƙazantar matar ya kai na misƙala zarratin, ga sana

'ar Daddawa da take babu tsafta. Sai ya zamana koyaushe gidan yana nan gum, idan baka

ɗ

auke kai bama ba zaka iya cikakken minti shabiyar a gidan ba koda kuwa kana sashen Ale ne wanda yake

ɗ

an nesa da nasu

ɓ

angaren.

Kwashe kwashen Ale ba irin macen da ba

su gani ba a gidan. Delu ga ƙazanta ga kuma masifa. Sau uku tana aure tana fitowa kuma dukkansu babu rabo ciki, sai dai shigarta gidan Ale da watanni uku rabo ya ratsa tsakaninsu. Ta zauna ta haifi Aisha wacce suke kira Jummai saboda sunan mahaifiyar Delu

ce. Jummai na da watanni biyar auren Delu ya mutu, sai data tafi ne ma suka san cewa saki na uku kenan aka yi dan haka babu kome. Jummai bata tashi a gidan Ale ba amma takan zo lokaci zuwa lokaci musamman a lokutan Sallah ko kuma idan tayi fa

ɗ

a da Delu.

Abinda Asiya zata iya tunawa akan Jummai shine kusan shekaru uku da suka wuce taje hutu gida ta samu yarinyar ta zo gida. Fulani na mata magana tana mata tsiwa hakan yasa Asiya ta zo ta

ɗ

auketa da mari. Yarinya sai ta kwanta ƙasa tana shure shure wai Alj

anunta sun tashi. Asiya ta sa aka

ɗ

auko mata bulala ta shiga zane Jummai ta ko ina, da ta ji wuya ta miƙe garau wai sun tafi.

"Waya kawo ki?" Asiya ta fa

ɗ

a bayan ta ƙarewa Jummai kallo.

"motar Ubale na biyo"

"Mi kika zo yi? Waya nuna miki nan? An

san da zuwanki a gida?"

"Kwarankwatsi ko kin koreni ba zan tafi ba. Nima ina son zama 'yar birni irin Sumayye. Ha'an ai ba Sumayye bace kawai ƙanwar matar Gamna"

"Bakin ki ne Gamna ai. Ba zaki jawo min masifar Delu ba, gobe zaki koma gidanku"

"De

lu ta rasu, a gidan Ale nake yanzu"

Jikin Asiya sai yai sanyi. Ba zata iya tuna yaushe rabon da ta saka Delu a idonta ba tun bayan barinta gidansu. Ance ta sake aure a wani ƙauye bayan ta rabu da Ale iyaka abinda Asiya ta sani kenan.

"Yaushe Delu ta

rasu?"

"Cikin Azumin bara"

Asiya tayi mata ta'aziyya sannan tace Uwani ta kai Jummai

ɗ

akin Sumayya tayi wanka ta chanja kaya.

Bayan tafiyarsu Asiya ta kira Ale dan ta tambayeshi ko yasan da zuwan Jummai.

Dama ta addabi 'yan gidan da fitina shiyas

a babu wanda ma ya lura ta gudu daga gida idan ba yanzu da Asiyar ke magana ba.

Ale dai ya nuna Asiya ta bar Jummai a wajenta tayi kwana biyu ko zata nitsu.

"Baba idan na kar

ɓ

i Jummai gaba sauran 'yan uwanta ma zasu iya cewa zasu bar gida"

"Kiyi haƙ

uri ta zauna a wajenki kafin na sama mata miji"

Bata da ƙarfin yin ƙorafi dan haka ta ce masa zata fa

ɗ

awa Gwamna, idan ya amince shikenan.

Bayan wayarta da Ale sai ta gwada kiran numbar Gwamna ko wannan karan zai

ɗ

auka, amma kamar koyaushe har wayar

ta gama ringing ba a

ɗ

auka ba. Bata tsaya

ɓ

atawa kanta lokaci ba sai kawai ta tura masa text akan ƙanwarta Jummai ta zo zata zauna da su. Ba a jima ba kuwa ya mata reply da cewa babu matsala.

Lokacin da Sumayya ta dawo ta ga Jummai a

ɗ

akinta ihu ne ka

wai bata kurma ba musamman data ga kayanta ajikin Jumman sannan ga yagaggiyar Ghana-must-go akan gadonta. Jummai ta sake tunzurata da cewa "nima na zo cin arziƙi, ai dukkanmu ƙannen matar Gamna ne"

Asiya na kitchen tana ha

ɗ

a abincin dare Sumayya ta shig

o fiskarta a ha

ɗ

e kamar zata yi kuka.

"Anty Asiya, wai Jummai ta zo zama damu kenan?"

Ko kallon inda ta tsaya Asiya bata yi ba tace "kema ba kina zama dani ba"

"Anty, Jummai fa na da Aljanu, Wallahi zuwan da nayi hutu kusan kullum sai ta tada isko

ki"

"Idan sun tashi akwai ayoyin ruqya zan karanta mata su"

Sumayya ta ƙara taƙune fiskarta tana hura hanci.

"Ki duba cikin kayan da ta zo da shi idan babu na arziƙi ki bawa Uwani taje ta ƙona su. Ki bata kaya guda biyu, zuwa gobe ko jibi zan mat

a siyayya. Kin san daga inda ta fito dan haka ki koya mata brush da duk abinda ya dace"

"Ni kam..."

"Zaki wuce ki bani waje ko sai na make ki a wajen"

Sumayya ta fice tana ƙunƙuni.

Asiya ta yi tsaki. Halayen da Sumayya ta tsiro da su yana bata

mamaki, tamkar shigarta Jami'a ya chanja mata tarbiyya.

Da yamma lis Queen Bee ta kawo wa Asiya ziyara. Kallo

ɗ

aya ta mata ta shiga ƙorafin ko lafiya?. Asiya ta kauda tambayar da cewa yanayin sanyin garin ne ya sa mata zazza

ɓ

i.

Bayan sun gama lissafi

n ku

ɗ

i da kuma wasu chanje-chanje da suke son yiwa shagon Queen Bee ta kawo shawaran chanja sunan shagon daga Halaal salon zuwa sunan Asiya Kachallah. Asiya ta

ɓ

ata rai tace " sunana Asiya Faruƙ ki daina jingina min Kachallah domin bada shi za a tasheni ba

ranan gobe. I'll always be Asiya Faruƙ Baba, aurena bai chanja komai ba"

"Na sani Bestie, wai kinga dai tunda kika samu wannan matsayi shagonmu ya ƙara samun

ɗ

aukaka. Kuma a matsayinmu na 'yan boko dan kin amsa sunan Kachallah ai ba komai bane"

Kama

r dama jira take tayi wannan magana Asiya ta fusata "zai iya saki na any moment from now, idan hakan ta faru zaku maida sunan shagon Asiya Faruƙ ne? Bamu bu

ɗ

e shagon saboda zan zama matar Gwamna ba. Da matsayina ko babu our business is doing fine, kuma da

yardar Allah zamu cigaba da samun alkhairi a cikin sana'ar mu. Bama buƙatar chanja sunan shago, bama buƙatar sunan Kachallah kafin mu samu

ɗ

aukaka. Allah ke

ɗ

aukaka mutum ba..."

"Shahidah?" Queen Bee ta kira a

ɗ

an tsorace saboda tsananin

ɓ

acin ran data

gani a tattare da Asiya ga kuma kukan da ya ci ƙarfinta har ta kasa ƙarisa kalamanta.

"Mi yake faruwa? Kina da matsala da Gwamna ne?" Tayi tambayar tana rungumo Asiya jikinta.

"Ya dena kula ni Bahijjah, ya dena shiga harkata, tunda yace na dawo wan

nan gidan sau

ɗ

aya na saka shi a ido, bai iya min magana sai dai yai text. Ban san matsayina a gidan nan ba, ban san mi yake nufi dani ba"

Queen Bee ta shiga bata haƙuri har ta samu ta nitsu ta dena kuka. Tana shirin bata shawara. Jummai ta fito da gudu

tana ihu.

"Lafiya?" Asiya ta daka mata tsawa.

Jummai ta miƙa mata hannunta na hagu tana fa

ɗ

in "Sumayya ta ƙona min hannu"

Asiya da Queen Bee suka zaro ido cike da mamaki dan ba ƙaramin ƙonewa yatsunta hu

ɗ

u suka yi ba.

"Mi ta saka miki a hannu?"

"Wani abu ne kamar almakashi tace min wai yana miƙar da yatsun mutum shine tace na gwada na gani"

"Shahidah ina jin flat iron ne" Queen Bee ta fa

ɗ

a tana ƙara duba hannun Jummai.

"Idan ban sa Yaya Bello ya min maganin Sumayya a gidan nan ba zata s

a min hawan jini"

Queen Bee ne ta shiga ƙwalawa Sumayya kira yayinda Asiya ta wuce da Jummala

ɗ

aki dan ta mata first aid.

A tsorace Sumayya ta fito dan bata

ɗ

auka wautan Jummai ya kai harta manna flat

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login