Showing 33001 words to 36000 words out of 112768 words

Chapter 12 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

Aesha daki daya, Ammar da Anas ma daki daya, kowane daki room and parlour ne se toilet.

Muhibbah ce tayi Mika tana fadin "innalillahi wa inna ilaehi raji'un Kai na gaji dayawa ina zamana aka sani biyoku da yanzu ina gida abuna" ta karasa maganan tana kwabe fuska kamar zatayi kuka.

"Toh naga dai siyayyan nan naki ne domin ki fa muka tawo mu bamuyi complain ba seke zaki ishemu, to waye be gajin ba".
Dan karamin tsaki taja "Kai wllhi Aesha kinada matsala, naga dai ban ambaci sunanki a magana na ba ko?" Ta karasa maganan da alamun tambaya.

Kafin Aesha tayi magana su suhailat ta katse ta "Wai ku bakwa zama inuwa daya baku raba hali bane, daga sauka ko hutawa bakuyi ba kun fara Jan magana" tayi maganan tana nufan akwati dubo kayan da zata zira dan fitowarta wanka kenan.

"Allah Aunty Suhailat yarinyar nan ne ta rainani kamar bani bace yayarta" ta Kai karshen maganan tana shigewa toilet.

Seda sukayi wanka sukayi sallah kana suka nufa gurin su Ummi.

Abinci sukayi order aka kawo musu parlourn dasu ummi suke sukaci bayan sun kammala suka kira aka dauke kwanukan nan suka dan taba fira kafin kowa ya koma makwancinshi saboda kowa tattare yake da gajiya.

Ko washe gari dasuka tashi breakfast kawai sukayi suka ciga da baccin su, se bayan dasukayi la'asar kafin see suka fita domin su mike kafafu sun jima a waje babu laifi se gaf magrib suka dawo masauki.
Yauma dai kamar jiya a parlourn dakin dasu Mummy suke suka yada zango har da su Anas anan sukayi dinner aka hau labarin irin al'adun dasuka gani Wanda suka Sha ban ban da al'adun Nigeria, Remote Muhibbah ta dauka ta canxa channel ta hau kallon cartoon.

"Wai ke sister bakya gajiya da kallon cartoon ne har yanzu kina nan kamar baby bakya girma se anyi magana kice kin girmeni"
"Kai Aesha kin cika sa ido, duk motsina kina nan kina kallo Kuma bakinki be iya shiru sekin tanka".

Anas yace "Kudai kamar annabi da kafiri kuke da daya yama dan uwanshi maganar arziki shikuma seya maido mai dana tsiya"
"Toh kaima ba haka kake ba da Muhibbah tama maganan arziki zaka maido mata mara dadi, zuwan Ammar ne ka dena saboda kaga dan uwa". Sun jima suna fira kafin da dai dai su tarwatse zuwa gurin kwanciya.

Tun safe suka tashi suka shirya fita kasuwa domin fara siyayyan da ya kawosu, sunayi break fast suka fita a wajen hotel din suka tari taxi zuwa Dubai outlet mall_ Al ain Dubai road.

Kayan lefe suka fara hadawa abayas, veils, shoes, bags, jewelries dasauransu kaya suke jida kamar ba gobe muhibbah na biye dasu bata dauka Kuma bata cewa a dauka ko an tambayeta choice din colour cewa take duk colourn da aka dauka yamata se Aesha ce ke daukan mata kasancewar tasan favorite colour dinta, kaya suka hada kamar za'a bude shago har seda Mummy tace a barshi haka ummi tace a barta ta zabi duk abinda take so Wanda ba su daukar mata ba tace "Aa ummi wa innan ma sun isheni haka duk abinda zan bukata kun riga kun siyamun".

zagayawa suka dingayi suna kara daukan wasu kayan seda suka tabbatar da sun hada mata kaya na uban gari kafin suka shiga diban kayan da kowa zesa ranan biki da shoes and bags, Suma su Ammar ba'a barsu a baya ba sun zaba nasu kayan, basu suka koma gida ba se magrib.

A gajiye likis suka shiga gida tunda kowa ya nufa makwancinshi be fito ba ko dinner yau kowa a masaukin shi yayi basu hadu a dakin su ummi ba.

Tun bayan tafiyan su Dubai Fu'ad ya tafi yola anyi Mai Kiran gaggawa a asibiti, se yanzu da yakira mummy bayan sun gaisa take tambayanshi gida shine yake fadamata shida Suhail sun tafi yola.
"Toh Allah yabada sa'a" "Ameen Mummy".

"Mummy ko kuna bukatan Karin kudi ne" "haba wane kudi Kuma, wa innan sun ishemu".
"Duk sanda bukatar haka ta taso dan Allah ki sanar dani".
"Wannan ma ya isa, Allah yama albarka" "Ameen". Daga haka sukayi sallama.

Tana ajiye wayan tace "Kash abin haushi seda mukayi tafiya ya Fu'ad ze tafi yola inama Muna gida yatafi mu sarara musha iska abinmu" takai karshen magana???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n tana cije yatsa.

Dakuwa Mummy ta mata "ungo nan idan yana nan bakya Shan iskan, toh Aiko kin kusa dena Shan iska gaba daya". Turo lips dinta tayi batare da tace komai ba saboda ta fahimta abinda mummy ke nufi.

Ummi tace "Kibarta ai gaskiya take fada matukar yayansu na guri be bari susha iska". Nan Aesha tashiga basu labarin kamun kunnen Daya sa su gaf zasu tawo Dubai aiko su Anas me zasuyi idan ba dariya ba.

Washe gari tun safe suka shiga taxi zuwa *Ibnu battuta mall_ sheik Zayed road*

Nan ma siyayya sukayi ba kadan ba sun siya kitchen utensils duk wani abun bukatuwa a kitchen seda suka siya basubi ta kan Muhibbah ba tunda ko sun San ko sun tambayeta cewa zatayi batada choice siyayyar su suke hankali kwance ita Kuma tana biye dasu tana Jin kamar zuciyarta zata fashe a duk sanda ta kalla kayan ta tina ba gidan ya Mukhtar za'a kaisu ba siraran hawaye ne suka fara fareti a kuncinta tayi saurin gogesu tana hadiye kukan da takeji na kokarin kufce mata se nanata innalillahi wa inna ilaehi raji'un takeyi akan labbanta. Se yamma likis suka koma masauki, tura kayan sukayi zuwa Nigeria sukuma flight dinsu ya daga se turkey.

A *hampton by Hilton cerkezkoy hotel* suka sauka Koda suka tashi dasafe basu bata lokaci ba suka fara Shirin zuwa siyayya, Mall of Istanbul suka shiga nan suka siya furnitures duk abinda ya shafi furniture seda suka dauka suka dan kara siyan wasu kayayyakin suka tura Nigeria.

Washe gari flight dinsu ya daga zuwa Nigeria.

Numfashi ta sauke ta shaki wani iska me dadi ta lumshe ido ta bude yayin da take saukowa daga matakalan jirgin, tana Janye da akwatinta can nesa da ita kadan ta hango su daddy da sassarfa ta karasa garesu tayi hugging din Abba "I'm back Abbana" "Welcome back Daughter" yafada yana rabata da jikinshi.

Juyawa ga daddy tayi Shima tabashi side hug, kanta ya shafa tareda fadin "Miss you my daughter" "Miss you too daddy na" ta karasa maganan tana murmushi.

Itama Aesha karasowa tayi tai joining dinsu. Cike da farin ciki suka shiga motocinsu suka dauki hanyan unguwan rimi low cost.

Baaba asabe ta gyara gidan tsaf ta shirya musu dining seda suka dan huta sukayi wanka kana suka nufo dining, Muhibbah da Aesha Jin gidan suke ya musu dadi saboda Fu'ad baya nan zasuyi abinda suke so kafin ya dawo.

Hidiman biki aka shigayi ba kama hannun yaro hankalin Muhibbah yakara tashi ganin kullum bikin kara matsowa yake kullum da zazzabi take kwana bata walwala se tayi kuka take samun nutsuwa koda yaushe tana daki.

Kamar kullum yauma tana kwance tarasa meke mata dadi tayi zurfi a tinaninta bataji shigowa ba seji tayi an dan bubbuga bayanta firgigif tayi ta tashi, murmushi tayi har hakoranta na bayyana "Aunty Zahra kece" Kai ta Jin jina mata itama tana murmushi tace "Nice".

"Ke kadai?"

"Nida umma ne, tana parlour".

Bata tsaya ba tayi parlour cikin sakin fuska ta karasa tanama umma sannu da zuwa, risinawa tayi ta gaisheta ta amsa cikin kulawa.

Daki ta koma suna fira da Zahra da Aesha Sega Summy sunji dadin ganinta nan ta jonasu suka cigaba da fira suna kwasar dariya.

Umma tace "Hajiya Hafsat dama wata alfarma nake nema a gurinki" .

Maido da hankalinta sosai tayi gareta "Ina jinki hajiya Sa'adatu".

Seda ta muskuta kana tace "Aron Muhibbah nake so ki bani, akwai wata me gyaran jiki da na dauko daga Maiduguri shine nake so ki bani aronta tazauna a gidan kanwata da take Nasarawa nan cikin gari".

Nannauyar ajiyar zuciya tasauke "Banki ba sedai bansan ko Mahaifanta zasu yarda ba".

Ummi dake zaune a gefe tace "Bari naje na gwada sa'a ta ko zasu yarda".
"Toh Allah yasa a dace" cewar Mummy dan tasan zeyi wuya su yarda, Aiko anyi sa'a bata dade tana lallabar suba suka amince.

Koda aka fadama Muhibbah ta hado kayanta ita da Aesha subi Umma dadi sukaji sosai harda tsalle dan sunajin lokacin da Ammar ke waya da Fu'ad yana ce mai yau ze dawo kd ko tsayawa tambayar abinda ze kaisu gidan basuyi ba.

Ba karamin gyara take samu wajen matar ba dilka take mata sannan tasa wani ice me kamshi a wuta ta turare mata jiki dashi sannan ta zuba wani ruwan turare a ruwan wankanta tasa tayi wanka dashi, tajika mata magun guna a katon cup tasata a gaba tana kuka tana Sha har seta shanye su Aesha da zahrah suna gefe suna dariya Suma ana musu dilkan sedai ba kamar nata ba wani lokacin Sumy na zuwa ta wuni ayimata dilkan ta koma gida. Kullum se ta dauko ganyan tun fafiya Kwara 7 tashafa musu man Kade a jiki takarashi jikin rushi se ya dau zafi kafin ta Mika ma Muhibbah tace ta manna a kasan ta babu yadda ta iya dole takeyin yadda hajiya hawwaye tace saboda matar babu wasa a fuskanta tana aikinta tsakani da Allah tana kuka haka take manna ganyan nan har seya wuce kafin ta kara gasa dayan ganyen har se ta manna 7 din nan zata kyaleta.

Cikin kwana 5 takara fresh tayi kyau sosae Aunty Zainab kanwar umma Bata bari tayi komai sallah kawai ke dagata itama tana bata kulawa bayan Wanda hajiya hawwaye ke bata kullum safe da yamma setayi blending din dabino da kanin fari ta zuba peak milk na ruwa ta bata tasha ko Kuma tayi blending din kankana da kanin fari da peak milk ta bata ko Kuma tayi blending din kankana da peak tabata wani lokacin Kuma ganyen zogale danye takeyin blending ta tace ta zubar da tukan ta juye ruwan zogalen a cup tazuba peak milk na ruwa ko na gari ta bata ta kwankwade su Aesha suyita rokon Aunty ta basu taki se Muhibbah tasha Aunty kecewa ta rage musu kadan ita ko Muhibbah kan dole take Sha tanayi kamar zatayi amai......


*Wae waye (Adon tafiya) Munata tafiya batareda mun wae waye baya ba batare da munji dalilin dayasa Abba ke rayuwa acikin garin yola Amma daddy ke rayuwa acikin garin kd alhali Uwa Daya uba Daya suke, sannan wane dalili yasa suka kafe kaida fata se sun hada yaransu aure bayan sun San basa son junansu hasalima babu wata jituwa a tsakaninsu*

*Wanene Alhaji Muhammad BICHI*.



[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: =???=???=???=???=???=???
_*SOYAYYAR KWANA ?AYA*_
_BY_
_*FATIMA A MUHAMMAD*_
_AMINIYAR ANGONTA_
=???=???=???=???=???=???
_*TEAM*_
_*ZAFAFAN=?%?DAWA*_
_*JARIRIYAR DAWA*_
_________________________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
________________________

*Page 29*


*Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae*
*Sunada kaya kamar haka....*
*Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....*
*Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t shirt*
*Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted*
*Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And many more......*
*Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku rikitamu da orders please we will take paracetamol >??*
*Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye

=?G?=?G?=?G?=?G?=?G?=?G? https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t



Alhaji Muhammad Shu'aib BICHI dan asalin garin Kano ne mazaunin wani karamin kauye me suna *SHERIFAWA* dake karamar hukumar *BICHI* Babban manomi ne yanada tarin dukiya shine na Daya acikin masu kudin kauyen yanada katon gida Wanda ya Kai fegi biyar inda yake kiwon shanaye da tumakai se wani bangare da aka kebe inda dakunan su yake, Matarshi Daya kwal FATIMA ansha kawo mishi mata kala daban daban da sunan an bashi kyauta idan yana so ya aura amma yaki yace zama da mace daya yafi mai kwanciyar hankali musamman da Allah yabashi mace ta gari take bin umarninshi Kuma take kokarin kula mai da dukiyarshi.

Sunada yara biyar Maza biyu mata uku, Salamatu ce babba se Haruna, Abdullahi, Bilkisu se Kuma Mariya itace karama.

Sun samu gata a wajen mahaifinsu duk cikin kauyen sun fita daban abincin gidansu ko wasu 'yan birnin basa cin irinshi Koda yaushe abokansu suna gidan safe da yamma saboda sun san iyye seta cika musu tire da abinci sunci sun koshi sannan da yamma idan baba yadawo duk seyabi kowa da tsarabarshi baya banbance tsakanin yaran makota da yaranshi.

Yasa su a makarantar gwanati dake cikin kauyen sannan ya dauko musu me lesson a gida mutanen gari nata gulman yaki aurar da yaranshi mata saboda yadda ake kawo musu harin da sunan soyayya duk da wasu kwadayin dukiyan mahaifinsu kesa su zuwa neman auren yaran, ba iya karatun zamani ba hatta na addini seda ya dauko musu malami inda yake koyar dasu a gida hade da yaran makwafta, yayi kokari sosai wajen ganin ya basu tarbiya Kuma mahaifiyar su ma ta taimaka mishi sosai wajen ganin sun gina yaran akan hanya me kyau duk kudin mahaifinsu besa su wulakanta Wanda bashida shi basa banbance kansu a cikin abokansu, ranar da babu makaranta yana tafiya da mazan gona suna taimaka mai.

Bayan mazan sun gama secondary school ya yafara koya musu kasuwanci inda ya bude musu babban shagon hatsi a cikin kauyen har ya Kai sukan bi kasuwannin kauye, Ranar lahadi da laraba suna zuwa kasuwar badume, Ranar juma'a suna zuwa kasuwar BICHI, Ranar alhamis Kuma shuwaki, Ranar litinin Sha nono se Kuma Ranar talata Dan zabuwa, Ranar asabar kadai suke hutawa kasancewar ranan babu kasuwa.

Suma matan suna gama secondary ya aurar dasu Salamatu da Mariya suna zaune nan cikin kauyen ita Kuma bilkisu aka kaita wani karamin gari Rimaye dake makwaftaka da kauyensu.

Rayuwa nata tafiya ciwo ya kama baba ga shekaru noma ya fara gagaranshi ga sha'anin kasuwa baya barin su Haruna kama mishi tun yana iya yi har ciwo yaci karfinshi ya Kai baya iya komai, kwana dayan da suke hutawa ya koma ranan zuwa gonansu ana haka Allah ya karba ran baba sunyi kuka kamar ba gobe, hatta makwabta sunyi kukan rashi kowa kyawawan dabi'un shi suke fada iyye har kwanciya tayi a asibiti itama kamar bazatayi rai ba.

Tun bayan rasuwar baba ragamar gidan ya dawo hannunsu gaba daya, iyye ta fara Sana'ar kuli kuli duk yadda suka so hanata fir taki tace zama hakan babu dadi ba yadda suka iya dole suka kyaleta, suna iya bakin kokarin su hatta 'yan uwansu mata duk da sunyi aure basa karkashin kulawarsu hakan be hana su yimusu Sha tara ta arziki su aikama ko wacce har gidanta, tun bayan rasuwar baba Haruna ya koma siyar da kaji da tumakai kasancewar dama tun baba na da Rai shi yabar ma ragamar kula da dabobin saboda yanada son kiwo, shi kuma Abdullahi yaci gaba da siyar da hatsi.

Kasuwancinsu nata bun kasa Haruna na zuwa Abuja Saida tumakai da kaji musamman lokacin sallah dakuma lokacin Christmas.

Shawarar ciga da karatu sukayi saboda ilimi shine gishirin zaman duniya, dan idan bakada ilimi ko kasuwanci kake se a cuceka, Koda suka samu iyye da maganan bata hanasu ba tayi musu addu'a da fatan nasara, ana fara registration jamb suka biya Aiko sunyi sa'a sun fito da results me kyau Nan suka fara neman Admission, A Kaduna polytechnic suka samu admission department of Business Admin.

A kasuwan kawo suka bude babban shagon hatsi, Ranan talata suci kasuwan kawo, ranan laraba suje kasuwan laraba can cikin gari, Ranan sati suje kasuwan sati dake unguwan dosa.

Kasuwancinsu be hanasu karatun su ba sun fita da kyakkyawan sakamako.

Sunji dadin rayuwa a kd saboda kasuwancinsu na tafiya musu daidai hakan yasa Koda suka kammala school basu koma kano da zama ba sedai suje ziyara ana haka Haruna yasamu matar aure acikin kauyensu Khadija anan garin ya barta tareda iyye se dai yazo yayi sati ya koma Shima Abdullahi yazo yaga gida ya koma haka suka dingayi, shekara na zagayowa Khadija ta haefo santalelen saurayi kyakkyawa murna wajen a halin ba'a magana sati na zagayowa yaci suna Fu'ad Khadija da jaririnta suna samun kulawa sosai wajen iyye.

Wata Rana Abdullahi yazo ziyara kauye washe garin daya sauka ya tafi gurin abokinshi lawal nan wani kauye *tudun wulli* dake dan gaba da kauyensu sedai yafi kauyensu girma da Kuma wayewa a hanyan dawowa ya hadu da wata budurwa hafsat daga nan suka kulla soyayya ba'a dauki lokaci ba iyaye suka shiga magana aka daura aure, itama nan gidansu ya kawota suke zaune da iyye dakuma Khadija.
Suna zaman lafiya sosai, Fu'ad Koda yaushe yana hannun hafsat ko fita zasuyi ita take goyashi, suna girmama iyye kamar mahaifiyar su tare suke aikin kuli itama ta daukesu tamkar 'ya'yanta na cikinta, shekara Daya da auren Abdullahi hafsat ta haifo Mai 'ya mace kwana Daya tayi a duniya ta koma seda shekara ta zagayo kafin ta kara haifo da namiji
ranan suna yaci suna Suhail.

Arziki ya bunkasa har ya Kai ga sun bude companynsu Haruna & Abdullahi Mill Rice.

Companyn dasuke sarrafa shinkafa susata a inji, ya cire tsakuwa ya gogeta a zuba a buhu a dinke ta koma Nigerian foreign rice sutura gari gari, sunada ma aikata sun Kai 30, sunada direbobi sun Kai 10, su kawai sa ido sukeyi akan aikin gudun ma aikatan suyi aiki mara kyau se Kuma rubuce rubuce akan in come & out come, da Kuma ware profit da loan.

Ganin ayyuka ya musu yawa basa samun dawowa gida akai akai iyye tace su gina gida su maida matansu can zasufi samun nutsuwa.
Haka ko sukayi cikin kan kanin lokaci suka gina gida dan madaidaici a unguwar sarki gidan part 3 ne kowa ne part 3 bedroom ne da kitchen se

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login