Showing 15001 words to 18000 words out of 112768 words

Chapter 6 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

A MUHAMMAD (Aminiyar ango)*


*DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION*

*Page 17*


*Aisha*

Zaune suke a parlour sunata fira, "tace ya Ammaar na kosa Saturday tazo mu tafi kd". "Hmmm! ai dole ki kosa saboda ku hadu da muhibbah ku ishe mutane da rashin Ji ko?".

"Aa ya Ammaar kasan mun dade bamu hadu bane, munyi missing din juna, Kuma ina so muje naga graduation dinsu".
"Toh Allah ya kaemu, Nima nadade ban hadu da Anas ba over 5 years" "tace ai ya Ammaar bancin Muna video call muma da yanzu mun manta kamaninka". "yace nima ai da nashigo gidan nayi tinanin bakuwa ce, seda mummy tacemun autanta ce kafin na gane yafada Yana dariya" "itama dariyar tayi"

Juyawa wajen Abba tayi kafin "tace Abba har yanzu ba'a kai ma tailor dinkina dana muhibbah ba Wanda zamusa ranan graduation dinta"

Aisha keda muhibbah rigimar ku iri daya "nakira tailor din yace gobe ze kawomiki na graduation dinki se kibashi sauran kayan"

Ummi ce tayi murmushi "tace ba dole rigimar su tazama daya ba tunda sun fito daga a hali daya" dukansu sukayi dariya

"Ai danma bamu taso guri daya b... Karar wayanta ya katseta, dauka tayi ta kara wayan a kunnenta tace 'yar halak yanzu muke maganarki dasu ya Ammaar". "tace no wonder shiyasa naji gabana nata faduwa ina tauna harshe Ashe gulmata kikeyi."

"Harara ta watsamata kamar tana ganinta tace gulmanki ke awa?"

"Dariya tayi tace matsayina na Auntyn ki mana"
"Tafdi wllhi Allah ya kiyaye kizama Aunty na, kwata kwata da wata nawa kika girme ni".

"Tabe Baki tayi kamar tana gabanta, oho dai koma da second ne dai na girmeki dole kicemun Aunty".

"Kefa se a hankali mubar wannan maganan cewar Aisha"

"Abba yacemun Saturday kuna nan zuwa"
"In Sha Allah Saturday zakiganmu harda Aunty suhaila ma dasu ummi"

"Can't wait to see you dear, Allah yakawomun ku lafiya, Nima naso nabiyo flight yau natawo graduation dinki se mu tawo tare Kona huta da takuran ya Fu'ad amma daddy yace aa".

"Dariya ta kwashe dashi tace dama nace muhibbah na can cikin ukuban ya fu'ad, aini kwana nan na huta ji na nake kamar tsuntsuwar da tasamu ta kufce daga keji."
"Uhmm! kedai bari ina cikin yanayi, shiyasa har nakosa kudiro garin nan ko zan huta."
Da haka suka cigaba da firan su sannan tace "ki gaisharmun da ummi."
"Zataji, good night"

Abba!ummi!ya Ammaar "good night, ta fada tana daga musu hannu".
"Shima Ammar sallama ya musu ya wuce".

"Ajiyar zuciya me nauyi tasauke tace nidai Alhaji daza'aji ta tawa da kun hakura da hadin nan da kuke Shirin yi, har ga Allah bawai bana son hadin bane itama muhibbah diyata ce dukansu ina kaunar su, kawai ina tinanin abinda ze je yadawo ne duba da yadda suke takun Saka hankalina be natsu da lam..." "Ya isa ya katseta, bana son nakarajin bakinki kan abinda ya shafi auren nan idan ba haka ba zakiyi mamakina babu abinda ze faru se alkhaeri"
"Kayi hakuri ban fada da wata munafa ba, Allah ya tabbatar mana da alkhaeri."

"Ameen! Ya fada a fusace ya wuce yabarta nan zaune"
"Bayanshi tabi da kallo tasauke ajiyar zuciya, tana addu'ar Allah yazaba abinda yafi alkhaeri idan Kuma babu alkhaeri Allah ya lalata al'amarin cikin sauki"........





*Aminiyar ango >?p?>?p?>?p?*
[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*

*FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)*


*DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION*

*Page 18*






Kwanci tashi babu wuya gurin Allah

Zaune take a parlour tana faman chatting tana sakin murmushi da alama firan ya dauke hankalinta, wucewa ya zoyi aiko ya take kafanta "wayyo Allah mummy na nashiga uku" "Harara ya watsamata ya bige kafan ya wuce yabarta nan tana matsar kwalla"
Seda taga yabar gurin kafin tace "Allah ya isa ban yafe ba" bata zata ba taji rankwashi "wa kike ma Allah ya isa".

A guje ta nufi dakin mummy tana zare ido

"Lafiya kika shigo babu sallama kike ta zare ido kamar kinyi karya?".
Numfashi tasauke kafin tace "babu komai fa mummy, dama kitchen zanshiga na hadama su Abba dinner kafin su sauka shine nace bari na leko banji motsin kiba".

Kallonta tayi badan ta yarda ba tace "naji! Muje nima ganinan zuwa in kama miki".

Tom kawae tace ta juya ta shiga kitchen

Haduwa sukayi da mummy da me aikinsu suka yi girkin a dafa wannan a dafa wancan muhibbah tace be isaba seda akayi abinci kala 5 da drinks kala 3 sun Kai 5 hours kafin suka kammala, muhibbah ce ta shirya dining din kafin me aikin ta gyara kitchen din tsaf aka zuba mata abincin a food flask ta tafi dashi.

Wanka tafito ta tsaya gaban mirror ta taje gashin kanta ta kama da ribom ta dan shafa powder tasa kwalli se lipstick, wardrobe ta bude ta dauko black abaya ta zira tayi rolling gyalenta ta feshe jikinta da turare ta dauko black flat shoe dinta tasa ta nufo parlourn.

"Daddy mu tafi please su Abba sun kusa sauka" tafada tana duba agogon dake manne a parlourn

Ki bari yayyinki su fito su muke jira, ba tace komai ba Kuma bata zauna ba seda suka kara kusan 10 minutes kafin suka fito

*Fu'ad*
Akanta ya sauke idonshi yana karemata kallo, tana dago idonta karaf suka sarkafe dana juna, juyamai ido tayi "ya tabe baki yana dauke Kai" "itama dauke Kai tayi daga kallonshi tabi bayan mummy suka fita".

Saukar flight dinsu babu jimawa suka karaso airport din.

*Muhibbah*

Da gudu ta karasa tayi hugging din Ammar tareda fadin "oyoyo ya Ammaar, I really miss you".
"Miss you too muhibbah" ya fada yana rabata da jikinshi

"Ke Kam muhibbah bazaki taba girma ba, Baki san kin girma bane kike hugging din Ammar" cewar mummy.

Dan turo baki tayi ta karasa zatayi hugging Abba yayi saurin riko hannunta yace "maamana kinfa girma".
"Nidai Abba ban wani girma ba fa" tayi maganar a dan shagwabe, duk gurin sukasa dariya.

Hugging din Aisha tayi tace "you are welcome dear, Miss you"
"Miss you too sisto"

Driver ne yazo ya dauki kayansu yasa a booth

Abba da daddy suka shiga mota Daya, Mummy, Ummi, suhaila suka shiga dayan motan, Muhibbah, Aisha, Ammaar suka shiga mota Daya, Anas, Fu'ad da Suhail suka shiga dayan motan suka dauki hanyan unguwar rimi low-cost.

Mazan basu shiga ciki ba suka nufi masallaci saboda kiraye kirayen sallahn magrib da akeyi.

Su Kuma matan driver yakarasa dasu gida Suma babu Wanda ya zauna suka nufi sama dakunan da suke sauka idan suka zo kd, muhibbah da Aisha suka haura da kayansu da driver yashigo dashi.

Seda suka idar da isha'i kafin suka sauko kasa, basu Kai ga zama ba mazan suka karaso, za'a soma gaesuwa ne mummy tace "Aa gaisuwar nan bazata kare ba a bari aci abinci tukunna" haka ko akayi suna zaune a dining gabaya Daya a halin kowa cike yake da farin cikin ganin 'yan uwa.

Muhibbah ce ta soma saving dinsu Daya bayan Daya kowa seta tambayeshi abincin da yake so da drink din daze Sha tana zuwa kan fu'ad ta kafeshi da ido taki magana Shima bece komai ba da ido tayi mai alaman me zeta samishi, kadan ya rage beyi dariya ba saboda yadda tayi da idon amma ya fiske, yayi kamar besan da itaba.
Kuma babu Wanda ya nuna yasan me sukeyi, ganin ya kyaleta se danna wayanshi yakeyi ya sata cewa "me zan zuba ma?" Seda ya dauki mintina kamar baze yi magana ba se Kuma ya dago yace "komai ma" ya maida kanshi kan wayarshi.
Sanin baya son cin abinci me nauyi musamman da dadare yasa ta zuba Mai jallof din spaghetti ta tura Mai, ta bude baki daker kamar anyi mata dole tace "drink fa?"

"Any one" yafada a takaice, kunun Aya ta zuba Mai takara tura Mai

Parlourn daddy ta Kai musu nasu abincin, kafin tadawo tasoma cin nata suna dan taba fira da Aisha.

Parlour suka koma aka shiga gaesawa daganan aka hau firan yaushe gamo, Aisha ta dauko dinkin su ita da muhibbah Wanda za susa gobe tashiga nuna mata aikam ta hau tsallen murna saboda yadda dinkin ya tsaru.

Se 10 suka tafi bedroom, Aisha Kuma tabi muhibbah bedroom dinta suka kwanta

Da wuri suka tashi, sauri sauri muhibbah ta shirya cikin riga da wando, a bayan rigan an rubuta sunan school dinsu (KA'AB BN MALIK) class of 2025, sama sama tayi break fast din ta dauki after dress ta daura tasa baby hijjab ta tafi.

Seda taje school din suka kara shiryawa da kyau sukasa graduation gown dinsu

Tanata waige waige gurin graduation se can ta hango a halin nata reras a zaune take sanyin dadi ya rufeta, tanajin a kaunar dangin nata har cikin Kashi da jijiya.

Sunayensu aka fara kira daya bayan daya ana basu gift

Ana Kiran the must obidient student in the school kamar daga sama taji ance *FATIMA A MUHAMMAD (BICHI)*
Gabanta ne ya yanke ya fadi tashiga zare ido take, summy tace "kije mana kefa ake kira" cikin sanyin jiki ta iso filin gurin Abba ya karaso ya rike gefe itama ta rike dayan gefen akayi musu hoto, kamar jira take a dauka ai Ko tafada jikin Abba tasa kuka, rarrashinta yashigayi mutane na kallon shagwaba suna mamakin miye abin kuka wasu Kuma suna dariya sunaji ta birgesu, daker tayi shiru ta koma gurinta ta zauna.

The must brilliant student in SSS 3 *FATIMA A MUHAMMAD (BICHI)* tun kan ta fita hawayen farin ciki suka balle mata daddy yafito ya rike gefen gift din itama ta rike gefe aka daukesu hoto, har tadawo ta zauna Bata bar hawaye ba, summy se sharemata su take wasu na gan garowa.

Best student in physics *FATIMA A MUHAMMAD (BICHI)*

Ai sandarewa tayi a zaune tama kasa tashi seda teachern physics dinsu Dan ladi Dan juma dake ba bahaushe bane ya riko hannunta ya karaso da ita, Abba yace Suhail yaje ya amsarmata daddy yace aa Fu'ad yaje tunda shine gaba da Suhail, hakanan ya karaso ba don yaso ba, ita Kuma se juye juye take tacika fam da haushi bataga mukhtar ba karaf suka hada ido ya dagamata hannu, tako washe baki tana dariya aka daukesu wannan karon award ne aka bata.

Seda aka tashi suka dinga selfie ita da family dinta sunyi gaba dayansu sannan suka koma yi da ita idan wannan yashiga anyi musu wannanma yashiga fu'ad ko daker yatsaya aka musu tako kwanto jikinshi akayi musu hoton ana dauka ya tureta ta tabe baki a ranta tace "kaji dashi dai"

Aisha taja bayan classes din a can suka samu mukhtar tsaye ai Kam aka shiga daukarsu hotuna.
Daga Mai hannu tayi tace "bye dear zamu tafi ina jiranka anjima a gida after asr". "Okay I will be there in Sha Allah"

Gida yacika babu laifi family sun hadu su Aunty Asma'u dasu Aunty hafsat duk sun zo anata fira ana Raha.

Wanka tashiga ganin har 3pm gashi sunyi da mukhtar by 4 zezo

Me kwalliya aka kira tayi musu itada Aisha sun hadu sosai sunyi kyau ha??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????r sun gaji da kyau

Parlourn ta nufo sanye da less me bala'in tsada maroon colour straight gown yaji bead work ta yafa gyalenta me nett maroon ga sarkarta se sheki take kamar ta gold, Aisha na biye da ita sanye da irin kayanta, ai Kam tana isowa parlourn ya dauki guda Aunty Asma'u tace "kunga Amaryar next week kin ganki kuwa kamar yau ne ranan" murmushi tayi dan bata fahimce komai tace "Ah Aunty kice yau shalele idan ya ganni seya rude" murmushin tausayinta tayi tace "uhmmm! ba lallaima ya iya ganeki ba" murmushi tayi tace "Nagode"

Hannun Aisha ta rike suka karasa compound din.

Can ta hango shi jingine jikin motarshi, cikin tafiyarta me daukar hankalinshi take takawa har ta isa gabanshi, iska ta hura mishi a ido tace "Hey" shikam tun fitowanta ya kafe ta da ido yakasa ko motsi ya daskare a tsaye yaushe numfashi ya ja ya sauke ajiyar zuciya yace "baby kin ganki kuwa, you look so cute, and adorable, kinyi kyau" fuska ta rufe tace " kaima kayi kyau irin sosai din nan fa" sukasa dariya dukansu har Aisha.

Karaf idanunsu suka hade dana juna gabanta yayi mummunar faduwa tsoro yakamata amma ta fuske tacigaba da murmushin yake, Ai suna hada ido da Aisha tace "innalillahi wa inna ilaehi raji'un, muhibbah kinsani a musiba daga rakiya nima nasan nashiga cikin ukuba"............





*Wanda be SO kutambayeshi dame yake more rayuwaaaa*

*Yau yakamata atamfamun nayi page me Dan tsayi nayi kokari atafamun Kuma ayimun comments indai anji Dadi=???=???*

[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*

*FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)*


*DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION*

*Page 19*

Jikin Aisha ne ya dauki kerma, kirjinta se bugun sakwaran Lagos yake ta sadakar kawai jira take taji saukar duka, itama muhibbah tsareshi tayi da ido ganin ya nufo inda suke tsaye tana jira taga iKon Allah koran mukhtar din zeyi ko kuwa dukansu zeyi a gaban mukhtar.

Karasowa yayi ya mikama mukhtar hannu sukayi musabaha yace "Barka da yamma" "barkaka dai".

Murmushin karfin hali muhibbah tayi kafin tace "baby ga big bro". "Oh shine ya Suhail din?".
Girgiza Kai tayi tace "Aa wannan shine babban yayanmu gaba daya ya Fu'ad sunanshi daga yolah" juyowa tayi tana kallon Fu'ad tace "ya Fu'ad ga ya mukhtar" ta fada tana sakin murmushi.

Cije lips dinshi na kasa yayi ya furzar da wata iska me zafi daga bakinshi, lallai muhibbah wuyarta ta isa yanka ko darr batajiba ta tsaya tana introducing dinshi ga wani a gabanshi, batareda taji ko shakkanshi ba hmmm! Yasauke ajiyar zuciya.

Mukhtar yakara bashi hannu suka gaisa sosai, Fu'ad ya tafi yabarsu nan a tsaye.
Ai Aisha tuni tashige ciki gudun taji an kwadamata Mari.

Seda fu'ad ya wuce kafin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, dan duk abinda takeyi a tsorace take duk da tana da goyon bayan Abba tunda shi yace ta turomai mukhtar din su tattauna.

"Uhmmmm! Wae ni banma tambayeka ba wayama kwatancen gidan nan". Girgiza Kai yayi yace "zuciyata mana" dariya tayi sosai tace "uhmmm! Aa fa banyarda ba Kai dai fada gaskiya ga goma". Murmushi yayi har hakoranshi suka bayyana kafin yace "namiki karya kenan" "wace niii na isaaa?" Tafada tana zaro ido.

Seda suka gama shirmensu tace "muje ko" babu musu tayi gaba yabi bayanta har parlourn baki, Fu'ad na kallansu aiko suna hada ido dashi ta sakarmai murmushi tana kanne mai ido Daya. Murmushin gefen baki yayi ya girgiza Kai alaman zaki sani.

Gurin zama ta nuna Mai ya samu guri a Daya daga cikin kujerun parlourn yazauna, takawo Mai ruwa da abinci amma fir yaki ci yace ya koshi dole ta hakura tace "toh bari na kawoma snacks" snacks ta kawo mai da drink Shima daker ya dan tsakura.

"Yanzu fa saura watanni kadan kizama mallakina ko my Zahra". Hannu tasa ta rufe fuska wai ita kunya tace "in Sha Allah ya mukhy". Sun dade suna fira kafin yace mata yana zuwa, aiko yana fita ta dauki wayarshi daya ajiye kan kujera tadanyi danne danne ta maidata idan tadauketa kana ta Koma tazauna, tana nan zaune yadawo hannunshi rike da wata 'yar karamar bag me bala'in kyau.

Yace "close your eyes" rufe idon tayi gam, ya ciro wani box dan dai dai anyi decoration dinshi, bude box din yayi kafin yace open your eyes.

A hankali take bude idon har ta budeshi gaba Daya ai ko idanunta suka sauka akan wata hadadiyar sarkar gold dake cikin box din, hannunta har rawa yake ta ciro sarkar tana kare mata kallo, sarkar tasha ado se walkiya take.
Hannu ta Kai taciro dan kunne ta kara a kunnenta suka saki murmushi gaba dayansu, takara Kai hannu taciro abin hannu tako zira tana jujjuya hannunta yace "wow kinga yadda kika has Kashi you look so beautiful". "Lallaima shalele bama shi ya haskani ba ni na haskashi ko?". "Ai bashida kyawun daze haskaki sedai ke ki haskashi" "dariya kawai tayi tanajin kaunarshi nakara mamaye zuciyarta dama gangan jikinta baki daya ba tace Mai komai ba idan da sabo tasaba da Jin abinda yafi hakama a bakin ya mukhy.

Wani box yakara cirowa ya mika mata tana budewa taga sabuwar waya dal i phone 13 pro, tsallan murna tayi tace "Thank you Hayateee" shiiii ya Dora yatsanshi a lips dinshi yace "it's my pleasure, you deserve more". "I luv you with all my heart Hayateee". "Luvs you too my one". "Fadin irin son da nake miki ma bata lokaci ne, Baki yayi kadan wajen zayyana miki irin tarin kaunar da nake miki habeebtee".

Gyaran murya Abba yayi, tayi saurin mikewa tana kasa da Kai tace "sannu da fitowa Abba". "Yauwa maamana". Fakan idon Abba tayi ta dubi mukhtar tayi tamai alama da hannu se sunyi waya, ta fice tayi cikin babban parlour inda take jiyo hayaniyar mutane.

Shi kanshi Abba yadda yagansu seda yaji jikinshi yayi sanyi.

Bata tsaya a parlourn ba sannu kawai tamusu tayi bedroom Aisha tabita. "Muhibbah kinga yadda jikina yake rawa kuwa gaba daya nayi tinanin kashin mu ya bushe a hannun ya Fu'ad, nayi mamaki da naga be mana komai ba".
Dariya tayi sosai tace "Matsoraciya kawai toh ai Abba ne yasa nakirashi Nima da wani ganganci zesa in kirashi, nacema Abba ya Fu'ad dukana zeyi idan yaganshi yace kar nadamu baze mun komai ba, ina kyautata zaton Abba ya Mai magana, Amma ai da yanzu jikinmu ya dau dumi". Ta karashe maganan tana sakin dariya, itama Aisha dariyar tasa.

Kasa ya zamo ya gaishar da Abba cikin girmamawa, amsawa yayi cikin kulawa kafin yace yatashi yakoma kan kujerar, daker ya koma ya zauna.
Abba ya dubeshi cikin kulawa yafara magana

"Wai ke muhibbah yanzu aure zakiyi? School dinfa?". Harara ta watsamata tace "toh uwata shakeni in fada miki kike jeromun tambayoyi". "Dan Allah mu bar batun wasa ki amsamun". "Hmmm! Aisha kenan, kinfi kowa sani a tsarina babu batun aure yanzu, bantaba tinanin soyayya zata iya canzamun tinani cikin sauki haka ba har na amince zanyi aure ba tareda nagama school dina ba, Amma ina son mukhtar fiye da yadda nake son kaina babu abinda bazan iya yi saboda Shiba, duk abinda ya tambayeni zanyi Mai shi indai be sabama shari'a ba".

"Eyyeeee muhibbah gaskiya kin fada da yawa, irin wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login