Showing 21001 words to 24000 words out of 112768 words

Chapter 8 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

tanata musu godiya suka wuce.


Ita inda suka fita tanan suka lallaba suka shiga, Allah yataimakesu babu wanda yagansu.

Hijab dinsu suka cire suna kokarin nufar parlour muhibbah ta riko Aisha tace "sedai Daya ya fara fita daga baya se dayan fita". Aisha tace "toh sedai ke ki fara fita" "nayarda".

Parlourn ta nufo tana Mika tana mutsutsuke fuska tayi wata hamma tana fadin "Alhamdulillahil laxi ahyana ba'ada ma amatanah wa ilaehin nushur".

Ummi tace "Aa muhibbah dama kuna ciki" "Eh ummi Muna ciki Muna kallo kawai bacci ya daukemu ashe har yamma yafara yi" "Toh ina Aishan" "har yanxu bata tashiba ummi". Umi tace "jeki ki taso ta kuci abinci baccin ya isa haka" "toh ummi".

Tana shiga dakin tafada kan bed tana dariya taba Aisha labarin wayan data masu ummi basu gane sun fita daga gidan ba.

Dining suka dawo sukayi lunching dinsu.

Kitchen suka shiga suka fara girke girke, Aisha nayin na gida ita Kuma muhibbah nayin na kaiwa asibiti.

Aunty suhaila ce tashigo ta samesu tace "me ake dafa mana"?. "Tuwon shinkafa da miyan agushi" cewar Aisha.

Ta bude dayan pot din taji kamshi ya duke hancinta tace "wannan Kuma girkin fa" suka Kalli juna ita da Aisha, muhibbah tayi saurin cewa "namu ne mu bazamu ci tuwo ba gaskiya" toh kun huta mu ai zamuce tafada tana barin kitchen din.

Favorite food din mukhtar ta dafa ta dauki hadadden flask ta zuba aciki ta hada juice din banana ta zuba a hadadden mug ta jera food flask da mug din a basket tasa spoons da cups ta kwance gyalen riganta dake daure a kanta ta yafa ta fita taba driver tafada mai sunan hospital din da abinda ze ce idan yaje, kafin ta juya ta koma ciki.

Kama ma Aisha aikin tayi suka jera abincin a dining suka shirya gurin tsaf.

Wanka sukayi sukayi sallahn magrib basu fito ba seda sukayi Isha'i.

Parlourn daddy suka nufa suka gaishe dasu kafin suka dawo dining din sukaci abinci.

A parlour suka baje anata fira tana ma yusrah wasa ita Kam se wangale baki take tana dariya tana so muhibbah ta dauke ta amma taki daukarta.

Suhaila tace "Kai muhibbah ki dauketa mana" tace "Aa ki rike 'yarki rawa take so nikuma bazanyi ba".

"Toh ai ke kika koyamata rawan" dariya tayi tace "toh nikuma yazu bana Jin yin rawan, kiba mummy ko ummi suyi mata". Ummi tace "Aa da dare nan sedae mummy din" ai kamar tasan me ake fada tasa kuka mummy tace "Suhaila tashi ki goyata kozatayi bacci".

Maida hankalinta tayi kan wayarta tana chatting da mukhtar se murmushi take, itama Aisha chatting dinta take suka bar su mummy suna firar su.

Kamar daga sama sukaji muryan Fu'ad ya kira sunan su "Aisha! Muhibbah!" Har suna hada baki wajen cewa "Na'am" yace "follow me"

Zaro ido sukayi suna dafa kirji, yana gama fadar haka ya juya yabar gurin.

Ummi tace "ko bakuji kiranku ake ba" mummy tace "ai da Gani basuda gaskiya yanzu haka wani laifin sukayi tunda kika ga haka" "kuje ku karba hukuncin ku zaku hadu da ya fu'ad" cewar suhaila tana dariya.

Sum sum suka tashi tare da barin wayoyinsu suka wuce, suna isa gabanshi sukayi kneeling down

Wani kallo ya watsa musu Wanda yasa 'yan hanjinsu kadawa yace "ina kukaje dazu" ai take gabansu yayi mugun bugawa suka hawa rawar Baki, suna mamakin yadda yaga fitar su daga gidan.

Aisha tace "munje mall ne" muhibbah ma tayi saurin karbe zancen gudun kar Aisha ta kwafsa tasan halin shirmenta tsoro ze iya sa asirinsu ya tonu "dama munje mall ne shine muka biya gidan su summy kawata muka gaisheta batada lafiya".

Harara ya watsa musu yace "wa kuka tambaya?" Sukayi shiru kana can muhibbah tayi karfin halin cewa "babu kowa, kayi hakuri" dan Allah Yaya kayi hakuri wllhi bazamu kara ba" cewar Aisha tana matsar kwallan tausayin kansu.

"No ban hanaku ba kucigaba gobe ma ku kara" suka shiga girgiza Kai suna bazasu karaba. yace su kama kunne, sun Kai 20 minutes a haka se zufa suke suna kuka tun hawaye na zuba har idonsu ya kafe, amma ko kulasu beyi ba bare su sa ran ze hakura sema zama dayayi yana operating phone dinshi..........



*Sister ta ta haehu tasamu baby girl kusama babyn albarka*


*Ku lallaba da wannan please*





*Aminiyar ango >?p? >?p? >?p?*
[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: =???=???=???=???=???=???
_*SOYAYYAR KWANA ?AYA*_
_BY_
_*FATIMA A MUHAMMAD*_
_AMINIYAR ANGONTA_
=???=???=???=???=???=???
_*TEAM*_
_*ZAFAFAN=?%?DAWA*_
_*JARIRIYAR DAWA*_
_________________________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
________________________

*Page 22*




"Go on your knees" ya fada batareda ya ko Kalle su ba, dama kamar jira suke suka zube kan guiwowinsu suna matsar kwalla.

A hankali ya mike ya tako gabansu, suka yi saurin kankame jikin su suna jira suji saukar duka, kawunan su ya gwara babu zato se ji kake kuuuum, kuka suka sake tsabar azaba ya dora dan yatsarshi a kan lips dinshi yace "shiiiiii! Ku hadiyeshi bana son Jin ko tarinku anan, ba kun raina mutane ba kanku na rawa ko, zan gyara muku zama".

Hannu suka sa suka toshe baki suna kokarin hadiye kukan.

"Get out" yafada cikin tsawa.

Da gudu suka kwasa har suna bige juna wajen rige rigen fita, babu kowa a parlour se wayoyinsu suka dauka suka karasa bedroom da gudu kamar ance gashinan a bayan su, a kan bed suka zube suna fitar da numfashin wahala ko motsin kirki sun kasa, daker muhibbah ta fisgo maganan tace "wllhi na kosa ya Fu'ad ya bar garin nan kije kita amsar ukubanki ke kadai ayi mutum babu imani".
"Allah nima bazan bar garin nan ba ai nazo kenan shiyasa na tattaro duk wasu takardun school dina nima nan zan cigaba da school" ta karasa maganan tana haki kamar wacce tayi tseran gudu.

Basu San lokacin da baccin wahala ya daukesu ba, makara sukayi basu tashi farkawa ba se 6am, dasauri muhibbah ta ziro kafanta da niyyan shiga toilet ta dauro alwala base kafa tace takani mu gani ba, hawaye ne suka shiga ambaliya a fuskarta se da rarrafe ta shiga toilet din tazo tayi sallahn a zaune. Rarrafawa ta karayi ta haye gadon ta tashi Aisha itama kasa mikewa tayi seda rarrafe tayo alwala.

Wajen 9am Aisha tabasu shawarar suyi wanka su gasa kafar ko haka ko akayi bayan sunyi wanka sun fito suka dauki man zafi suka shafa, cikin iKon Allah ko sukaji dama dama daker suka isa parlourn Koda sukayi break fast ma dawowa bedroom sukayi suka cigaba da baccin wahala.

Su ummi na zaune a parlour sukaji ana danna door bell, Fu'ad ya kalla Ammaar dake zaune suna game da Anas, sum sum ya tashi yaje ya bude kofar, Bala driver ya gani tsaye suka gaisa ya mika mai basket din hannunshi da wata white paper yace wai gashi a ba hajiya karama, bece komai ba ya karba ya koma cikin parlourn yaba mummy ya fada mata abinda drivern yace.

Da mamaki take kallon basket din tace "oh ni hafsatu wa kuma muhibbah ta aikama abinci". Suhail yace "Anas jeka ka kira Muhibbah".

Tsayawa tayi tsakiyar parlourn tana mutsutsukan idanu.

Mummy ta dubeta tace "wakika ai kama abinci". Se lokacin ta ware idonta da kyau ta kalla basket din ta waske tace "Laaa mummy mantawa nayi ban fada miki ba, wani class mate dina ne bashida lafiya shine fa na aika driver ya Kai mai abinci" ta karasa maganan tana saurin daukan basket din saboda hango white paper din da tayi a ciki, a kitchen ta tsaya ta war ware papern taga an rubuta "ThANk YOU SO MUCH DEAR, LUVS YOU HAYATEEE". Wani murmushi ne ya kufcemata a kan lips dinta tace "LUVS YOU TOO LIFE CYCLE" tafada tana kashe ido daya tanajin kamar tana gabanshi. Snacks ta zuba ta fito parlourn ta zauna kusa da ummi tafara cin snacks din tace "Allah ummi yaron akwai kirki kinga lokacin Muna school bakiga kirkin daya kemun ba shiyasa nace bari na aika mishi da abincin nasan zeji Dadi" ummi tace "gaskiya kin kyauta, kin rike alkawari". "Kinsan wasu fa ummi da an rabu daga school shikenan sun manta irin zaman da kukayi dasu a class kota waya basa kiran mutum, shiyasa anjima nake so Aisha ta rakani inje na gaishe shi" wani kallo Fu'ad yamata ta dauke Kai daga kallonshi tana tabe Baki a zuciya tace "dan iyayi kawai, kamar bashi bane lokacin da mukayi soyayyar kwana daya yake mun magana cikin tattausan murya ba, amma yanzu se wani cin magani yake".

Mummy tace "Aa base kunje ba kimai sannu ta waya". Marairai ce fuska tayi "please ummi ki roki mummy ta barmu baze ji dadi ba idan banje ba". "Kar ku tafi ku kadai ku kira driver ya kaiku, kar ku dade" cewar ummi.

Tsallen murna tayi ta dauko gyalenta ta mikama Aisha nata suna???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? hada ido da Fu'ad ta kashe mai ido taja hannun Aisha suka fice.

Girgiza Kai yayi a zuciyarshi yace "lallai yarinyar nan".

Ko da sukaje asibitin an tabbatar musu da an sallame shi babu jimawa

Mota suka koma taba driver umarnin juyawa malali low cost "hajiya wane area a malalin?". Se lokacin ta tinama batasan gidan ba ita dai tasan a malali low cost suke, kin kiranshi tayi se Aunty Zahra ta kira tayi mata kwatance.

A bakin gate din gidan yayi parking suka sauka suka fara knocking, me gadi ya bude "lafiya?" Kallon mamaki tabishi dashi kafin tace "kamarya lafiya? Kaga alamun rashin lafiya a tattare damu ne dazaka wani ce lafiya, toh idanma ba lafiya ba gurinka zamu zo ka bamu magani ne, kajimun mutum fa". Yace "ni ba haka nake nufi ba, ina nufin me yakawo ku? Gurin wa kuka zo? Kuma ansan da zuwanku?".

Wani kallon uku saura kwata ta watsamishi "toh miye hurumin ka da me ya kawoni, ina ruwanka da gurin wa nazo kasan dai bazan zo gurin dan rainin sense irinka ba ko?, dan haka malam matsamun in wuce". "Babu yadda za'ayi ki shiga gidanan batareda an bani umarnin nabarki ba". Wani kallon bakada hankali ta mishi "toh malam kabi a hankali kar karasa aikin ka, nice future wife din young Alhaji". Aisha tace "kinga sister mu kira ya mukhtar din kawai yazo ya mai magana".

"Tafdi ashe ba sunana Zahra ba, wllhi babu wanda zan kira kuma sena shiga gidan nan besan halina bane".

Turo kofar tayi tariko hannun Aisha suka shigo ciki, ya biyosu yana masifa tayi banza dashi, Jin hayaniya kadan kadan yasa Aunty hauwa da mukhtar lekowa compound din.

Da mamaki yake kallonta ya akayi Kuma tasan gidansu.

"Yauwa ya mukhy kajama wannan mutumin kunne ya kiyayeni tun be rasa aikinshi ba, ya tsare ni da tambayoyi wai gurin wa nazo toh kafada mishi nice future wife din young Alhaji yabi a hankali tom". Ta karasa maganan tana girgiza kugu kamar me shirin dambe.

Shi dariya ma ta bashi ya fuske gudun yayi dariyar yanzu ta hau fushi, kallon me gadin yayi sum sum sum ya wuce ya koma wajen aikinshi tun kafin taja a sallameshi a aiki.

Juyowa gareta yayi "muje ciki". Baki ta turo ta rike hannun Aisha suka bi bayanshi, itama Aunty hauwa da tun dazu take kallon iKon Allah tabi bayan su.

A kasa suka zauna tare da ajiye ledojin fruits din dasuka siyo, suka shiga gaeshe da umma amsawa tayi cikin kulawa tace "yau kune a gidan namu". suka jinjina Kai, muhibbah na dan murmushi takasa dago ido ta Kalle umma wai ita kunya.

Ummi tace "kutashi ku zauna sama, matsayin mahaifiya nake a gareku Kuma 'ya'yana ne kamar mukhtar". Bakaramin dadi furucin umma yama muhibbah ba hakan yasa babu musu suka zauna akan kujera.


Abinci Zahra takawo musu da drink ta ajiye tana fadin "sannu da zuwa sirikar mu". A kunya ce taja mayafinta ta rufe fuska kana tace "ina wuni Aunty Zahra". "Lafiya kalau muhibbah, yasu mummy?". "Lafiya kalau" ta amsa a takaice.

Aunty hauwa tace "haba ni abun ya dauremun kai tashigo me gadi ya biyota yana sababin meyasa zata shigo batare da an bashi umarnin shigowarta ba, naji tana itace future wife din young Alhaji, Ashe sirikar muce". Ta karasa maganan tana dariya, Suma su umma sukasa dariya "Ai da gaskiyarta idan ba haka ta Mai ba baze bari tashigo ba, amma banda abinki ai ko mukhtar din seki kira yaje ya shigo dake" Cewar umma.

Kasa tayi da Kai tace "ai umma mutumin ne se a hankali yasan dai hakanan bazamu zo gidan mutane batare da sun sanmu ba shiyasa na gwada mishi niba kanwan lasa bace". Ta karasa maganan tana kwafa.

Aiko su Aunty hauwa me zasuyi idan ba dariya ba itama kanta umma seda ta dara, kawai hakanan taji yarinyar ta kwantamata a rai batada tsoro Kuma batada boye boye free take maganan iya gaskiyarta.

Mikewa yayi yace "keba bakin ki baya shiru gaban sirikar taki kike zuba ko". "Eh babu ruwanka ai gaban ummana ne ka rabu dani " "kyaleshi ke kam ummanki ce batashiba" cewar umma. Kafada ya dage ya haura sama ya barsu nan.

Aunty hauwa tace "kuci abinci mana ko a dining zakuci". "Eh Aunty dining zefi" cewar muhibbah.

Dining din aka Kai musu abincin suka saki jiki sukaci suka koshi kana suka dawo parlour aka cigaba da fira kamar dama tasansu tun tuni gara Aunty Zahra dama sun saba suna chatting sosae duk da basu taba haduwa face to face ba sedae pic din juna sukayi sharing.


Zaune suke gaba daya a halin banda muhibbah da Aisha da basa nan.

Abba ya dube Fu'ad "ina sadakin diyata?". Ba musu ya dauki envelope ya mikamai. Bude envelope din yayi yashiga irgasu bugun Abuja sababbi fil dubu dari biyar cirr kana yace "Masha Allah"

Mikama daddy yayi, yayi saurin girgiza Kai yace "aa Yaya ka ajiye a gurinka ayi abinda ya dace dasu". "Babu abinda za'ayi mata da sadaki ko a musulumci hakkinta ne a mallaka mata amma yanzu batayi hankalin da xa'a bata su a hannu ba sedai mu bari tadawo a tambayeta abinda take so se a siyamata a ajiye har zuwa lokacin daza'a damka mata. Kowa yayi na'am da maganan da Abba yayi.

Har bakin gate suka rakota har da umma har sun kusa fita taja ta tsaya "yauwa umma ki fadama wannan mutumin karya sakemun abinda yayi mun yau idan ba haka ba ze iya rasa aikinshi" tafada tana nuna me gadi dake zaune yana faman zare ido.

Dariya sukayi sosai umma ta kalla me gadin tace "malam tanimu a kiyaye duk lokacin dakaga wannan kabarta tashigo diyata ce gidansu ne nan kajini?".

"Eh hajiya a gafarceni in Sha Allah bazan sake ba yau dinma rashin sanine".

"Toh Allah yabada ikon kiyayewa".

Umma tace "diyata kin dage dai sekin tafi tun yanzu". "Ai umma tunda yanzu nasan gidan zan kara dawowa zanzo namiki wuni in Sha Allah". "Allah ya yarda diyata". "Ameen umma".

Humra tabata na 'yan Maiduguri me kamshi sosai, godiya tama umma kana tayi musu sallama tafita tana daga musu hannu. Hakanan sukaji suna kaunarta har Aunty hauwa.

A kofar gate din suka tsaya tace "ya mukhtar ya jikin naka?". "Se yanzu kika tina dani? Keda kika zo dubiya kika buge da labari ko". "Allah sarki ya mukhy umma ce akwai kirki har Aunty ma tanada kirki, naga Kuma kama". "Uhmmm yayata ce kinga ko dole muyi kama". "Laaa ai bansaniba bari naje na kara gaisheta sosai". Dariya yasa kana yace "Banda gaisuwar da kika mata duk be isa ba" "toh ai bansan Aunty bace da na gaisheta dakyau". "Kinganki! ki bari zan fadamata kina kara gaisheta". "Yauwa thank you".

"Ya mukhtar kadai ki fadamun yadda kukayi da Abba". Murmushi ya kakalo "nama Abba alkawari bazan fada miki ba shida kanshi ze fadamiki, zaki labari me Dadi". Murmushin farin ciki tayi tace ya jirata ta koma mota ta dauko wani box me kyau tadawo, bude box din tayi taciro wani hadadden zobe ta Mika mai ya karba yasaka yace "Wow, thank you my D" murmushi tayi ta dauko agogo ta Mikamishi ya karba ya daura a tsintsiyar hannunshi "thank you my zahraaaa". "You deserve more dear".

Shima hannu yasa cikin aljihu ya ciro hadadden zobe me dauke da harafin F&M ajiki tana zira zoben a dan yatsanta ta saki murmushi "thank you husband to be, LUV YOU". "LUVS YOU TOO".
Sallama tayi mai tashiga mota "Ai dakin kara 10 minutes da cema driver zanyi mu tafi ya mukhtar din ya kawoki, tunda ku idan kuka fara soyayya bakwa gajiya" "Eh bama gajiyan banson sa ido". Bata kulata ba se umarnin tafiya da tabama driver, dama jiran umarni yake ya danna hancin motar suka bar unguwar.

Da sallama suka shigo parlourn ganin babu kowa yasa muhibbah cema Aisha bari taje ta ajiye humran da umma tabata kar a tuhumeta inda ta sameta seda ta ajiye kana suka karasa shiga parlourn daddyn da tasan tunda bataji motsin kowa ba maybe ana meeting a parlourn daddyn.


Da sallama suka shiga suka samu guri suka zauna suna musu sannu da gida, duk amsawa sukayi cikin kulawa.

Abba yace "yauwa maamana matsa kusa" karasawa tayi ta zauna kasa kusa da kafafunshi.

"Karba wannan" ya mikamata envelope din, ta karba tana kallonshi alamun tana jiran Karin bayani.

"Sadakin kine naira dubu dari biyar" dasauri ta dago ta kalleshi se Kuma ta kalla daddy takara juyawa ta kalla sauran mutanen dake zaune a parlourn tana jira taji Wanda zemata Karin bayani, Ko dama mukhtar yabada sadakinta ne Abba ya hanashi yafada mata saboda yayi surprising dinta. Maganar Abba ne ya katse mata tinaninta.

"Muhibbah wannan sadakin ki ne, inaso ki fada abinda za'a siya miki dasu kudinki ne halak malak" sunkuyar da Kai tayi tace "Aa Abba banida wani zabi duk abinda kuka yanke yayi". "Allah yamiki albarka, zan cika na siyamiki gida dashi". "Nagode Abba, Allah yakara arziki" "Ameen maamana".

"Yauwa Fu'ad kabama su mummynku kudi se suje Dubai su hado lefe". Daddy yace " Yaya hidimar tayi mai yawa bari ni zan basu se su hado lefen". "Dan yabada sadaki dubu dari biyar shine aiki da kudinshi za'a hado lefen zefi ganin darajarta ba wai ya sameta a sama ba". A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login