Showing 54001 words to 57000 words out of 112768 words

Chapter 19 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

daki ya daga waya yakira malam mukhtasir ya nemi alfar mar yasama ma kanwanshi admission, nan ya turamai kudi yace yamata duk abinda yadace.

Gidan Abba yabiya Ummi yasamu zaune cikin kujeru "Sannu da hutawa ummi" "Yauwa ya aiki?" "Alhamdulillah"
"Ya jikin Muhibbah?, karta ke aiki sosai fa girkinma tabar ma mairo takeyi kawai" "Dasauki ummi tama war ware, Kuma kinsan ba son abincin masu aiki nake ba dan dai girki kawai ai babu wani gajiya"

"Toh ciwo be Kori komai bane banda abinka, ai larura ne, Kuma naga kana cin girkin mairo" "Eh ummi gara girkin mairon ina daurewa inci amma bisa larura" Baki tasake tana kallonshi daga haka bata sake cewa komai ba, Dan dama ba fira take dashi ba zatayi dariya da kowa amma bandashi yanzuma yasan saboda Muhibbah ne tayi mai Wannan dogon maganan tun abin na damunshi har ya saba, Shima idan kaji ya sake yanata fira toh shida mummy ne dan jinta yake kamar ita ta tsugunna ta haifeshi.

Suna zaune daga shi har ummin kamar kurame ya shige cikin kujera idonshi a rufe kamar me bacci, mekewa yayi yamata sallama tace ya jirata kitchen tashiga ta dauki food flask ta zuba danbun shinkafa ta dauki basket tasa food flask din ciki ta fito ta mika mai tace ya kaima Muhibbah, godiya yamata ya fice.

Yau taji dadin zaman gidan sun sha fira da mairo se yamma driver yazo daukanta sukayi sallama tanaji kamar karta tafi.

Burner ta dauko tana karama dakin turare taji ana danna door bell, dan dama kulle kofan take seta dai daici lokacin dawowanshi take budewa saboda kar yaita knocking batajiba tana daki.

Ajiye burner tayi taje ta bude a cikin idanunshi idonta ya fada nan suka shiga kallon juna.........


*Aminiyar ango >?p?>?p?>?p?*


*Aminiyar ango >?p?>?p?>?p?*


*Aminiyar ango >?p?>?p?>?p?*



[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*

*FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)*

*DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION*

*Page 39*

https://chat.whatsapp.com/K2nZjsqqivQ4PcFd1p65a8



"S...san...nu da dawowa" tafada a dan rarrabe bakinta na rawa "Yauwa" abinda yace kenan yana shigowa parlourn.

Dakinshi ya nufa ya cire kayanshi ya shige toilet, ya jima ciki kana ya fito ya tsaya gaban mirror yana tsane gashin kanshi, shafe jikinshi yayi da mayuka masu kamshi ya feshe ilahirin jikinshi da turarenshi na mufaddal, Jallabiya ya zira ya nufa masallaci Jin an fara kiraye kirayen sallahn magriba.

Cikin shigan doguwar rigan leshi dinkin bubu ta fito se zuba kamshi take.
Plate ta dauka ta zuba danbun da mummy ta aiko mata dashi ta zuba juice din banana data hada a cup ta nufa parlour ta janyo center table ta dora plate din danbun a kai ta zauna kan kujera tashiga ci.

Se bayan isha'i ya shigo parlourn da sallama iya kan lips dinshi, dan kallon inda take yayi na seconds ya dauke kai ya nufa dining ya zauna.

Mikewa tayi ta karasa dining din ta dauki plate ta zuba mishi abincin ta ajiye a gabanshi ta juya ta koma taci gaba da cin abincin ta, be ko dago ya kalleta ba seda tabar gurin ya ajiye wayan yashiga cin abincin shi hankali kwance.

Sosai taci danbun dan ba karamin dadi yamata ba yaji zogale da hanta ga yaji a gefe.

Be wani ci abincin ba saboda shinkafa ce Kuma baya son abinci me nauyi da dadare.

Ganin ya haura sama ta mike tashiga tattare dining din, dawowa tayi kan 3 seater ta kwanta tana chatting a group din su na old student tana sakin murmushi "Muhibbah me kikeyi online yanzu? Ina kika baro habibin naki" Cewar Summy.

"Kai matsalata dake yarinyan nan sa ido, ina ruwanki mijin ki ko Mijin Zahara?"
"Eyyeeee yarinya an girma mijinki ne, keee ni muje private akwai labari".

"Hello maman baby" sakon data ajiyemata kenan ta pc.
"Aa kakan baby, nidae bani nasha" "Aesha kemun albishir kin kusa haifo mana baby" yadda zataji dadin masifan ta danna voice note "Abinda yafi baby nakusa haifo muku, duk me son babyn tayi aure mana ta haifo zaku dameni da wani zancen ciki, mutum ba daman yayi ciwo indai yanada aure se a dameshi da wani ciki zamu hadu da Aeshan ai hala ku kukamun cikin".

Bata san ya shigo parlourn ba seda ya kai hannu gefen kujerar da take ya dauki remote, saurin tura voice din tayi tana mikewa zaune.

Kan kujera ya zauna be ko kalleta ba Kuma sarai yaji maganganun da take gayama summy.

Mikewa tayi a dan tsorace tace "Seda safe" Da hannu ya nunamata gefen da yake zaune, kallonshi tayi dan bata fahimce abinda yake nufi ba
Hannu yasa ya dauka ya mika mata da sauri ta karba ko tsayawa tambayar namiye batayi ba, seda ta rufo kofar ta sannan tasauke nannauyar ajiyar zuciya dan duk a tinanin ta ta zauna gefenshi yake nufi, harta fara tinanin kwasawa da gudu murmushi tayi tana zama bakin gado.

Admission letter tafara cin karo dashi bude ido tayi da kyau taga sunanta ne a jiki radau, mikewa tayi tayi tsalle ta fada kan gado tana furta "Alhamdulillah".

Wayanta ta dauka ta danna numbern Aesha Ringing biyu ta daga "Hello maman baby" dogon tsaki taja "Matsalata dake kenan wasa" "Eyyyeee Aunty babba" "dama mun kwana biyu bamu raba hali ba, ni ba abinda na kira kenan muyi ba, karki bata mun rai ina cikin farin ciki" "Ah ni dama tunda naga kiranki cikin daren nan nasan akwai labari" "kedai bari ina cikin alkhaeri dumu dumu, Nima Yaya yasama mun Admission a (AUN) Kuma course dinmu daya dake "Masha Allah, ai ina jima nafiki farin ciki sister kice yanzu Koda yaushe Muna tare, dazu Abba kecemun on Monday zamu fara lectures" Wani juyi tayi akan gado "Karshen zaman kadaici ya kare kullum mutum na gida yanzu naga mutane su ganni" dariya Aesha tayi "Nidai bari na barki kije ki kulamun da yayana seda safe" tsaki tayi ta katse wayan.

Kamar an tsunguleta ta mike ta bude wardrobe ledojin da zarah ta ajiye mata tun ranan da aka kawota ta fiddo zama tayi gefen bed tashiga bude ledan Turaren wuta ta ciro har kala 5 a wasu kwalabe masu girma ajiyewa tayi ta zaro humra Suma har kala biyar tana bude humran dakin ya dau kamshi murmushi tayi ta dan girgiza kai "Allah sarki umma" ko ba'a fada ba tasan wa innan ne sakon umman.

Jiki a sanyaye ta janyo dayan ledan ta bude, hannu ta Kai ta ciro wani red box budeshi tayi ta zaro wata hadaddiyar sarka da dan kunne, rungume sarkan tayi a kirjinta wasu zafafan hawaye suka shiga kwararo mata hannu ta Kai ta dauke su, ta zaro wani katon frame an rubuta *ALLAHU* ajiki se Kuma wani frame Shima yana da dan girma irin Wanda zaka iya sa hoto ajiki ne se Kuma wani agogo kasanshi hoton dawisu ne guda biyu sun hada bakunan su.

Tsamm ta mike ta dauko wata 'yar jaka da aka hadomata kananun abubuwan ta ciki, bude kayan tashiga yi sarkar daya bata ranan graduation dinta ta dauko ta hada data hannun ta ta Kai bakinta tayi kissing dinsu ta saki murmushi hade da hawaye hatta abin hannun daya bata duk suna nan maida kayan tayi cikin jakan ta rufe ta maidata mazaunin ta, Wayan daya bata ne a hannunta dan tun ranan da yabata ta cire sim dinta ta maida ciki ta cigaba da amfani da ita, kiss ta manna ma wayan kukan da take rikewa ya kufcemata seda tayi me isarta ta kunna suratul bakara ta ajiye wayan Saman bed side drower tayi azkar ta kwanta zuciyarta cike da tinanin ya mukhy dan a hankali rayuwar su na baya ke dawomata ta dade tana juyi kafin bacci ya kwasheta.

Se karfe 10am ta ziro kafafunta kasa tana addu'ar tashi daga bacci, toilet ta nufa ta dan jima ta fito.

Kitchen tashiga sharp sharp ta fara kokarin hada breakfast dan yunwa takeji.

Potatoes ta fere ta yayyankashi ta barbada flour aciki sannan ta soya ta dauko stick ta tsitsira a jiki.

Fridge ta bude ta dauko nama ta yayankashi kanana kanana ta tafasa, ta dauko pan ta zuba oil da kayan miya ta kawo seasoning ta zuba ta kawo naman ta zuba ta juya ta rufe after 5 minutes ta kashe gas din, dining din ta shirya kana ta nufi dakin.

Wanka tayi ta shirya ta shafe jikinta da humran da umma ta Aiko mata dashi ta dauki ledan sauran humran da turaren wutan ta fito

Tana fitowa Shima yana fitowa karaf idanunsu ya sarke dana juna gabanta ne ya fadi tayi saurin janye idanunta daga nashi a darare tace "In...Ina kwana" "lafiya kalau" ya fada yana taka staircase din, seda ta tabbatar ya isa dining kana itama ta sauko, ajiye ledan hannunta tayi ta karasa dining din tayi serving dinshi kana ta dawo parlourn.

A show glass ta jera kwalaban turaren wutan ta dauko wani kwalba ta dura humra ta maida ta rufe ta dauki sauran humran ta maida daki, tana kokarin zama taji ana danna door bell, da fara'a ta nufa kofan dan tasan mairo ce, ai ko ta cinka dai dai tana budewa suka sakarma juna murmushi, hanya ta bata ta shigo suka shiga gaisawa, seda takarasa ta gaisheshi ya amsa da kalma daya kana tashiga aikinta. Dining din ta koma tafara breakfast dinta seda ta kammala ta dauki na mairo ta mikamata dakin data zaba, parlour ta koma ta danna Kiran umma, mukhtar na zaune gefenta suna dan fira ringing daya ta dauka "Ina kwana umma" "Lafiya kalau diyar kirki, ya gidan?" "Lafiya kalau umma" "ina fatan komai kalau" "Wllhi lafiya kalau umma "A yita hakuri kinji, shi aure dan hakuri ne" murmushi tayi kana tace "Naga sako na gode Allah yasaka da alkhaeri Allah yakara girma, Shima ya mu....." Da sauri ta hadiye maganan tana toshe bakinta "Babu komai Muhibbah Allah yabada zaman lafiya" murmushin yake tayi batare da tace komai ba sallama sukayi ta ajiye wayan.

Duniyar tinani ya tafi yana dan taba saitin zuciyarshi ji yayi kirjinshi na suya umma ta fahimta sauyi a tattare dashi "Mukhtar lafiya? Me kake tinani?" Kai ya girgiza "Babu komai umma bari na dan kwanta kinsan weekend kawai muke samu mu dan huta" yana Kai nan ya bar gurin
Da kallo tabishi tana sauke ajiyar zuciya tama rasa me zatace tayi tinanin zuwa yanzu ya manta da batun Muhibbah.

Mairo kin zama tayi tunda tagama aikinta tayi breakfast tace wucewa zatayi tunda yau Saturday Fu'ad na gida, dole Muhibbah tasa driver ya maidata gida.

Da rana sega Ammar taji dadinshi sosai iso tayi mai har parlourn ta cike Mai gabanshi da kayan ciye ciye, seda yaci abincin rana ta dauko mai babban frame din da agogo ya buga mata, har Fu'ad ya dawo daga masallacin a zuhur gaisawa kawai sukayi ya musu sallama ya fita.

Da daddare bayan ta hado Mai coffee shi da Shan shi yazaman mai kamar ibada, ta dan zauna kan kujera ta mai godiyan ganin admission letter Kai kawai ya jinjina bece komai ba ta mike ta tafi ta kwanta.

Da wuri ta tashi ta hada breakfast ta shirya "Aunty mairo yau zan fara zuwa school kishiga kitchen ki dauki break fast, dan Allah kiyi mana abincin rana kafin na dawo" "Toh shikenan Allah yabada sa'a me za'a dafa?" "No koma menene babu matsala" ta Kai karshen maganan tana ficewa dan tasan ba tsayawa jiranta zeyi ba gaban motar ta bude ta shiga yaja motar yafice daga gidan. A bakin gate din school ya ajiyeta yamata kwatancen office din malam mukhtasir sannan ya mikamata kudi tamai godiya ta shige ciki.

Office din malam mukhtasir ta fara zuwa tayi knocking yabada izinin shigowa bakinta dauke da sallama ta shiga gaisheshi tayi cikin girmamawa, amsawa yayi yana dan murmushi, file din ta Mika mishi yana karanta sunan ya dago ya dan kalleta "kece wacce doctor Fu'ad yace nanema ma admission?" Kai ta gyada.

Fadada murmushin shi yayi "Allah sarki yacemun kanwarshi ce, hakane ko?" Jim tayi can Kuma ta gyada kai tana dan murmushi
"Ki dage da karatu, duk abinda ya shige miki duhu baki fahimce shi Dan gane da school din nan ba ki zo office ki sameni" Kai kawai ta Jin jina ta mai godiya tabi hanyar Daya mata kwatancen inda ze sadata da department dinsu.

A class tasamu Aesha basu jima ba lecturer yashigo yashiga fasa musu physics.

Karfe 12 suka fito daga class suka zauna kan kujerun dake school din suna jiran karasowar driver.

Wani kyakkyawan saurayi ne yakara so inda suke "Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuh" "Wa alaekumussalamu warahmatullah wabarakatuh" Aesha ta amsa. Muhibbah ko tunda ta mai Kallo daya ta dauke Kai, kyakkyawa ne dan da ganinshi zakasan daga gidan manyan mutane ya fito sanye yake da Jan t shirt da bakin jeans gashin kanshi baki sidik se sheki yake idanunshi sanye da glass.

My name is sauban Muhammad Auwal & You? Ya fada yana kallon inda Muhibbah ke zaune.
Dogon tsaki taja ta mike ta riko hannun Aisha suka barshi nan tsaye
Da sassarfa ya bisu har kofar gate "Dan Allah baiwar Allah ki taimaka ki fadamun Koda iya sunanki ne please" Aesha ce tayi karfin halin yin magana "Malam me kake so? Matar aure ce" murmushin rainin wayau yayi "Wannan ce keda aure? Haba dai ki gyara kalamanki" can kuma ya dan tabe baki ya dage kafada "dama ko wace mace ai matar aure ce tun da ko ba dade koba jima indai da rai da lafiya zatayi aura" "To ina nufin matar wani ce" ta dan fada a zafafe dan ranta ya soma baci. Ita ko Muhibbah ko ci kanku bata ce ba ta jingina jikin wata mota ta harde hannayenta a kirji.
"Wanene wanin bayan niii?" Kallon bakada hankali ta mishi taja tsaki taja bakinta tayi shiru dan ta lura tacigaba da biye Mai ranta ne kawai ze baci.

Ganin sun shiga mota driver yaja sun wuce ne yasa ya dan shafa sumarshi a zuciyarshi yace "yanzu aka fara game din, nayi alkawari sena siye zuciyarta yarinya dani kike wasa bakisan sauban bane" komawa ciki yayi yashiga motanshi yana mamakin yau shine mace take shareshi a school din nan shida 'yan mata ke binshi da sunan soyayya Amma ko kallon arziki basa samu a gurinshi.

Dubanta Aesha tayi kana tace "Sister yafara saukeki a gida se ya juya ya saukeni kawai" "No ya kaimu gidan Ummi gaba daya, ina so na gaisheta" Kai ta Jin jina batareda tace komai ba.

Bakinsu dauke da sallama ganin Fu'ad zaune kan kujera yasa Muhibbah daskarewa bakin kofan parlourn, Ummi tace "Aa shigo mana Muhibbah ya kika tsaya anan" tanaj ummi namata magana kallon tuhumar dake aikamata yasa ko motsi ta kasayi takasa gaba takasa baya bata taba tinanin ze zo gidan ummi a wannan lokacin ba kuma basuyi dashi zata zo gidan ummi ba cemata yayi idan sun tashi ta kira driver ya maidata gida.

Ganin ya mike yasa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? hawayen dake makale a idanunta samun nasarar zubowa..........



*Aminiyar ango >?p?>?p?>?p?*
[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*

*FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)*

*DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION*

*Page 40*

https://chat.whatsapp.com/K2nZjsqqivQ4PcFd1p65a8


"Ummi bari na koma asibiti akwae patient din da aka kawo emergency, ana bukatata urgently"

"Toh Allah ya bada sa'a"
Sallama yamata ya fice.

A hankali ta karaso cikin parlourn ta risina ta gaida ummi ta amsa cikin kulawa tana tambayarta jiki ta amsa da dasauki.

Aesha ce ta kwashe da dariya harda dafa ciki "Kai Muhibbah wannan tsoro haka karki bada mu mana" hawayen fuskanta ta share tana aikamata harara.

"Gidanku ke waya kaiki tsoron"
"Toh ai ummi gara ni, itafa matarshi ce amma ki dubi yadda ta tsure ita ba wani abu yace mata ba".
"Kyaleta Muhibbah itama idan taga yayanku rudewa take kamar tasaki fitsari" "Toh ai yayan ne idan yana zare ido dole ka tsorata" Aesha tace "Babu ruwana zaku hadu dashi ai" labarin shi sukeyi suna dariya harda rike ciki ummi se biye musu take.

"Sister muje muyi sallah se muzo muci abinci" "kije kiyi ina jiranki" Ummi ce ta dan kalleta batareda tace komai ba a ranta take raya kodai hasashenta ba gaskiya bane? Duk da wasu ko sunada ciki sukanyi period.

Seda Aesha tayi sallah ta fito kana suka nufi dining sukayi lunching.

Firan school suka shigayi can Aesha tace "Ummi yau muka hadu da wani mahaukaci a school" "Mahaukaci Kuma toh shi ko ya akayi ya shigo cikin school din, securities din bakin gate basu hanashi ba" "Ba mahaukacin gaske bane nice nasa mai mahaukacin" "Kinci gidanku ya mutum me hankali zaki dinga kiranshi da mahaukaci?".

"Toh idan banda hauka ya za ace mai mutum nada aure yace dama ko wace mace matar aure ce kinga ai babu hankali a lamarin nan".
Nan ta kwashe labarin yadda sukayi da sauban taba ummi.

Salati ummi tayi kana tace "Kubi a hankali fa se kunyi taka tsantsan, kema Aesha karki Kuma yi mishi magana idan ya gaji ze kyaleku, karku yarda ku biye mai kundai San halin yayanku duk randa yaji wannan labarin kun Kade koni bazan iya kwatarku hannunshi ba".

"Ni ummi ko maganama banyi mai ba shida Aesha ne sukayi magana" "Yauwa karki sake ki kulashi kinji ko?" Kai ta jinjina, aka shiga wata firan.

Agogon dake manne a bangon parlourn ta kalla 15 minutes after 5 dawo da kallonta ga ummi tayi "Ummi zan tafi" "Bari ki tafin muku da dinner, Aesha kira driver ya kaita" laraba ce ta shiryo kulolin a basket takawo mata.

Godiya tama ummi sukayi sallama har tsakar gidan Aesha ta rakota ita ko se korafi take mata dan me zata fadama ummi labarin sauban haka suka rabu.

Bakinta dauke da sallama tashigo parlourn bataga kowa ba basket din hannunta ta ajiye ta nufa dakin mairo a zaune ta sameta murmushi ta sakarmata itama murmushin takeyi "Sannu da gida Aunty mairo" "Yauwa hajiya, ya makaranta?"
"Lafiya kalau, gidan ummi na biya shiyasa na jima ban dawo ba, yanzu ma ke driver ke jira".

"Hijjab dinta ta zira tamata sallama ta wuce"

Tana kokarin shiga bedroom dinta yana fitowa daga dakinshi, Karan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login