Showing 57001 words to 60000 words out of 112768 words

Chapter 20 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

kula kofarshi yasa ta juyo karaf idanunsu ya sarke dana juna, gabanta ne ya fadi tayi saurin janye idanunta a dan tsorace tace "Sannu da dawowa" be ko kalleta ba ya wuce ya barta tsaye.

Ajiyar zuciya ta sauke ta murda handle din kofar ta shige.

Se datayi wanka sannan ta nufo parlourn sanye da kananan kaya karamar riga me hannun vest da pencil wando Legis, kulolin ta shiga jerawa kan dining kitchen ta koma ta dauko cups da plates ta zuba abincin tashiga ci har ta gama be shigo gidan ba.

Tana Shirin mikewa kamshin turarenshi ya daki hancinta hakan ya sanar da ita shigowarshi kujera yaja ya zauna ido ta dan tsuramai can tace "sannu da dawowa" "Yauwa" abinda ya iya cewa kenan.

Serving dinshi tayi ta tura mai gabanshi ta barshi gurin, bayanta yabi da Kallo har ta haura sama.

Break fast kawai ta hada taci tana Shirin fitowa ya sauko serving dinshi tayi a hankali tace "Ina kwana" "kintashi lafiya?" A dan mamakance tace "lafiya kalau" tafada tana juyawa da niyyan barin gurin kamar daga sama taji yace "Wait for me outside" juyawa tayi ta wuce batareda tace mai komai ba.

Drivern gidan Abba ne ya kawo mairo ta tambayeshi Aesha yace ya kaita school.

Gaisawa sukayi da mairo ta fada mata break fast dinta na kitchen godiya ta mata ta shige ciki.

Tana tsaye se faman tsaki take kasa kasa tarasa me yakeyi har yanzu be fito ba da ya bari da yanzu driver ya sauketa.

Tafi minti 10 tsaye kana ya fito motarshi ya shiga ta zagaya ta bude gaban motan ta shiga me gadi ya wangale mai gate yana gaisheshi hannu kawai ya daga mai yaja motar yafice daga gidan.

Shiru motar ya dauka babu wanda yayi magana kamar saukar aradu taji muryarshi yace "Wa kika tambaya kikaje gidan Ummi?" Duk da bada karfi yayi magana ba Kuma bada fada ba amma seda gabanta ya yanke ya fadi, shiru tayi tarasa me zatace "Ba dake nake magana ba?" "Babu kowa" tafada a sanyaye.
Be Kuma cemata komai ba har suka isa school din.

A bakin gate ya sauketa "Allah yatsare" "tnx" abinda yace kenan yaja motar yabar arean.

Murmushi tayi ta shiga ciki, da sauban suka fara cin karo saurin hade girar sama da kasa tayi "Barka da safiya beauty" Shida banza duk daya a gurinta dan ko waigawa batayi ta kalleshi ba.

Har department dinsu ya bita kana ya juya ya nufa class.

Malam mukhtasir taci karo dashi a bakin department din su "Ina kwana" "lafiya kalau kanwarmu, yaya kike?" "Lafiya kalau" ta fada tana wucewa "Dan tsaya mana please Saurin me kikeyi haka?" Tsayawa kawai tayi tana kallonshi "Idan babu matsala ko zaki samun numbern ki?" da mamaki take kallonshi anya yanada hankali kuwa abokin ya Fu'ad ne fa, can kuma tace Koda yake ba laifinshi bane laifin ya Fu'ad ne da yace mai kanwarshi ce ni.

"Dan Allah kayi hakuri yaya baya barinmu rike waya ko Assignment zamuyi sedai muje cafe ko Kuma ya bamu nashi muyi" "Hakan ma yayi wannan tarbiyya ne me kyau, toh Kona mama ne ki bani akwai maganar da nake so muyi ne" "Allah sarki gashi ko ban haddace numbern Ummi na ba, amma zuwa gobe idan ban manta ba zan rubuto a paper" bata jira amsarshi ba ta wuce class.

Kusa da Aesha ta zauna ranta a jagule "lafiya kuwa matar Yaya?" "Lafiya kalau, me kika gani?" "Naga kin shigo rai a bace ne" "Babu komai ke Kam, amma dan Allah kidena kirana da matar yayan nan a class kar mutane su kama".

Karfe 10 suka fito daga class suna zaune da wata Kawarsu dasukayi
A kunne Aesha ke rada mata "Wai yau meke damunki ne? badai yayana bane ya batamiki rae?, ko Kuma babynmu ne ke wahalar mana dake, yake samana ke bacin rai kinsan masu ciki akwai saurin fushi".

Tsungulinta tayi a cinya tako saki kara mara sauti Muhibbah tayi dariya "Kadan namiki karki kiyayeni da wannan maganan kiga yadda zamuyi dake".

"Assalamualaikum"
Kusan a tare suka dago su duka ukun, akan sauban suka sauke idanunsu, dauke kai tayi, Umaina tace "Wa alaekumussalamu warahmatullah".

"Dan Allah idan babu matsala ina son magana dake, Kona minti daya ne" dogon tsaki ta buga twsssss "Just 1 minute please" ya fada yana hada hannayenshi biyu alamar roko.

Umaina ce tace "Karki ce nayi miki shisshigi tunda ya hadaki da Allah ki saurareshi ko Yaya" harara ta watsamata tareda daga mata hannu, Jan bakinta tayi tai shiru batakara cewa uffan ba.

"Ko sunanki ki daure ki fadamun ki tausayamun tun jiya da na dora idanuna a kanki naji cewa a raina in Sha Allah nayi mata" a hassale ta mike ta bar gurin fuuuuu, Aesha tabi bayanta, Umaina ta bisu da kallo.

Dawo da hankalinshi wajen Umaina yayi "Dan Allah ki shawomun kanta please" Kai ta Jin jina "okay I will try my best" "Nagode zuwa gobe zan dawo in Sha Allah".
Jinjina Kai tayi itama ta mike tabi bayan su.
Shiru yayi yana tinani dagaske dai ba matar aure bace tunda da matar aure ce da kawarta nan ta kara fadamishi.

"Haba Fateema miye haka? Wulakanci babu kyau Koda bakya son shi at least ko hakuri kika bashi zeji dadi".

"Dan Allah Umaina ki kyaleni naga kema macece zaki iya karbar soyayyar shi idan ya miki, jiya ba'a yi mai magana bane yaki sauraren mutane" "Sister calm down ki rabu dashi ze gaji ya kyaleki, Umaina wannan mutumin da kike gani dan rainin sense ne jiya babu abinda bamu ce mai ba yaki ji kema ki fita batunshi kawai".

Ajiyar zuciya tasauke "Toh ai bansaniba, ai shikenan".

Koda suka tashi sun fito sun fara takawa zuwa inda drivern su yayi parking sukaga wata mota ta tsaya gabansu glass din motan ya sauke "ku shigo na kaiku gida" cewar malam mukhtasir
"Mun gode ga driver can na jiranmu" tana Kai nan ta wuce.

Tana gani aka sauke Aesha kamar ta bita, juyawa yayi itama ya sauketa gida.

A parlour tasamu mairo "Sannu da dawowa hajiya" "Yauwa Aunty mairo, ya zaman shiru?"
"Alhamdulillah"

"Nace miki kisaki jikinki, kin zauna shiru ko tv base ki kunna ba ya dan debe miki kewa" ta fada tana karasawa ta kunna tv din.
Ita dai murmushi kawai tayi.

Seda tayi wanka kana ta dawo dining tayi lunching, fira suka shigayi ita da mairo wajen 5 mairo tace "Ina so zan tafi" "Kai Aunty mairo tun yanzu?" "Yamma tayi hajiya" "Toh shikenan Allah yatashemu lfy" har tsakar gidan ta rakota tasa driver ya kaita kana ta juyo ta dawo parlourn.

Abinci mara nauyi ta dafa taje tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigan material me santsi tasa hula rabin kwantacen gashinta a waje ta shafe jikinta da humra.

Serving dinshi tayi itama ta zauna tana cin nata a hankali

Ta kasan ido yake kallon ta sosai yaci abinci kana ya tashi ya koma parlour, harta fara taka staircase taji yace "Hado mun coffee" dan turo karamin bakin ta tayi ta koma kitchen ta hado mai

Center table ya nunamata ta ajiye a Kai ta wuce.

Brush tayi ta canza kayan jikinta zuwa na bacci ta haye gadon bata jima ba bacci ya kwasheta dan ba karamin bacci takeji ba.

Ya jima zaune yana aiki ta wayanshi yanayi yana sipping coffee dinshi seda ya kammala ya mike ya nufi dakinshi, toilet ya nufa yayi brush ya dawo ya feshe jikinshi da turare ya fito daga dakinshi.

Hannunshi ya daura kan handle din kofar yana murdawa yajita bude a hankali ya kutsa kanshi ciki, a hankali ya karasa kan bed din ya haura rungumota jikinshi yayi, ita ko har wani gyara kwanciya take a kirjin shi tana cusa Kai tana shakar kamshin shi cikin bacci.

Wani shock yaji ajikinshi saboda yadda take narke mai a jiki.

Shin Shinar wuyanta yake yana ya mutsa gashin kanta yashiga yawo da hannunshi a jikinta hannunshi ta rike a hankali ta bude idanunta dakin duhu bata ganin komai "Waye ne?" "Ki nutsu wa kike tinanin ze shigo dakin ki a daren nan".
Kara wara idonta tayi ashe ba mafarki takeyi ba se yanzu taji kamshin turarenshi

Zame hannunshi yayi daga nata ya cigaba da yawo dashi a jikinta.

Kuka tasa "Dan Allah Yaya ka kyaleni bacci nakeji" "cigaba da baccin ki ni ban hanaki ba" Jin bashida niyyan denawa tasaki kuka me sauti "shiiii yimun shiru wani abu namiki kikemun kuka" yayi maganan yanayin kasa da hannunshi.

Cikin kuka tace "Dan Allah Yaya kabarni" "Ni ba wani abu zan miki ba sadakina na zo mora".

"Wayyo Allah mummy na, Allah zan biyaka sadakin ka zan dawo ma da kudinka ka kyaleni" saura kadan dariya ta kufce mishi ya fiske.

"Dama ana dawo da sadaki ne banida labari?, fadamun inda kikaji an tabayin haka" yana maganan yana yin kara kasa da hannunshi.

Ban karewa tayi tana ihu "Wallahi Yaya banida tsarki, period nakeyi"

"Toh bari na duba da kaina na gani" ya fada yana zare rigar baccin jikinta.........


[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*

*FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)*

*DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION*

*Page 41*

https://chat.whatsapp.com/K2nZjsqqivQ4PcFd1p65a8



Ganin tana neman sume mishi yasashi sakinta yana fadin matsoraciya kawai. dasauri ta janyo blanket ta lullube har kanta.

Ficewa yayi daga dakin yajanyo mata kofar ya rufe ya nufi bedroom dinshi toilet ya fada ya sakarma kanshi ruwa ya dan jima a toilet din yafito daure da towel kayan bacci ya zira ya haye gado ya kwanta lumshe ido yayi yanajin kamar har yanzu tana kwance a kirjinshi.

Kuka taciga da rerawa har bacci ya kwasheta bata dena sauke ajiyar zuciya ba

Da ciwon Kai ta tashi saboda kukan da tayi daren jiya a daddafe ta hada breakfast tayo wanka tayi Shirin school

A dining ta sameshi a sanyaye tace "Ina kwana" "lafiya kalau" ya fada ba tareda ya ko Kalli inda take ba

Serving dinshi tayi ta tura mai gabanshi kana ta hada tea tana sipping tanajin kanta kamar ze cire, ido ya dan tsuramata na seconds ya dauke kai ya cigaba da cin abincin shi.

Can ya mike ya nufa kitchen har lokacin bata shanye tea din ba hannunshi rike da first aid box ya fito, dago kanta tayi suka hada ido sun kai minti 1 suna kallon juna kana ta danyi kasa da kai

A kan dining ya ajiye box din ya bude ya dauki paracetamol ya mikamata, bata fuska tayi "Nifa lafiyata kalau" wani mugun kallon da yake mata yasa tayi saurin karba ta balli biyu ta watsa a baki ta kora da tea tana yamutsa fuska.Ganin ya ciro allura yana kokarin fasa paracetamol ya zuka a siringe din tayi saurin mikewa tana zare ido kamar tayi karya, tsayawa yayi yana kallonta tafara girgiza Kai "Dan Allah kabarni wllhi lafiyata kalau kaina kawai ke ciwo zanji sauki" kafada ya dage ya dauki box din ya maida. Ya dawo ya zauna ya ciga da cin abincin shi hankali kwance

Dakinta ta haura ta dauko jaka tazo ta tsaya dan nesa dashi "zan tafi, karfe 8 mukeda lectures"
Kai kawai ya jinjina.

"Kuma yau lecture daya garemu dan Allah zan biya gidan ummi" tayi maganan tana marai raice fuska amma gabanta faduwa yakeyi a tsorace take.

Shiru yayi ba tareda yace mata komai ba. "Dan Allah inje???" Ta kare maganan da sigar tambaya. Daga mata Kai yayi alamun eh, da fara'arta tace "Tnx" ta fice.

Sauri sauri tashiga school din tanayi tana duba agogon dake daure a damtsen hannunta 5 minutes to 8 takoyi sa'a lecturer be karaso ba General mathematics MTH 101 suke dashi
2 hours suka kwashe a class.

Su uku suka fito daga class Aesha da Umaina se zuba suke ita kam maganan su ya dameta amma batace musu komai ba suka cigaba da tafiyansu.

Kallon Muhibbah ta danyi cikin kulawa tace
"Lafiya?" Yatsine fuska tayi "Kaina kemun ciwo, amma nasha magani" "Eyyyaaa sorry, Allah yabaki lafiya"
"Ameen tnx"

"Aesha dazu naga mutumin Fateema Allah yasa be gannin ba" cewar Umaina.

Dariya Aesha tayi "Dan anace ba, yanzu ke ze nacemaw...." Bata karasa magana ba ta hangoshi ya yo inda suke.
"Amincin Allah yatabbata ga sarauniyar kyawawa"
Tsaki tajaa tanajin kamar ta kwada mishi mari.

Umaina ya Kalla "Ya ake ciki?" "Indai zan baka shawara toh kayi hakuri shine zancen gaskiya dan ba samun zuciyarta zakayi ba". tana fadan haka tabi bayan su da sassarfa.

Bayan su yabi da Kallo yama rasa mezeyi wata zuciya na cewa ya hakura wata zuciya Kuma na zugashi akan karya gaza yayi iya iyawarshi wajen ganin ya mallaketa.

Sun danyi gaba ta hango malam mukhtasir yana washe mata baki kara hade rai tayi kamar an aikomata da mutuwa da sassarfa ya taddosu duk su biyun saurin gaishe shi su kayi ya amsa yana tambayarsu karatu.

Can kasan makoshi tace "Ina kwana" "lafiya kalau, ya karatu ana kokari ko?" ya fada yana kara washe baki.
" Alhamdulillah" ta fada a takaice.

Ganin tana kokarin wucewa yayi saurin cewa "Ina alkawari na?"

Ya mutsa fuska tayi "Ya Salam kaga ko na sha'afa kayimun afuwa zuwa next week idan Allah ya kaimu" tana kai nan ta wuceshi fuuuuu.

Kallo yabita dashi har suka bace ma ganinshi.

Gidan Ummi suka nufa gaba dayansu har Umaina a parlour suka yada zango a 3 seater ta baje tun tana Jin firar su har bacci ya kwasheta.

A parlourn Ummi ta samesu Umaina ta risina ta gaisheta cikin girmamawa ta da kulawa tana tambayarta mutanen gida

"Aa ya akayi ta kwanta nan batashiga ciki ba?" "Wllhi Ummi nata tashin ta taki tashi" karasawa tayi taba goshinta taji babu dumi.

Bacci sosai tayi dan dama ita indai tana period wuni take bacci bata gajiya. Bata farka ba se 2 ta iya sa'a tana tashi taji ciwon kan ya sauka
Baccin datayi yakara sa Ummi tabbatar da zarginta.

Dakin Aesha taje ta wanke baki da fuska tazo sukayi lunching se 3 Umaina ta tafi ummi ta cika mata leda da abubuwa tanata godiya har compound suka rakota sukasa driver ya maidata gida.

Se 5 tama Ummi sallama Aesha ta rakota compound din gidan sukayi sallama.

Tana shiga gidan jaka kawai ta ajiye ta shiga kitchen seda ta musu dinner ta haura sama dakinshi ta shiga ta gyara ta canza bed sheet tasa turare ta janyo kofar ta fito ta koma dakinta.

Wanka tayi ta shirya cikin doguwar rigan abaya ta zauna bakin gado ta janyo wayarta gabanta na faduwa tafara dialing numbern Mukhtar har tagama ringing ta tsinke beyi picking ba seda tayi 3 missed calls ana hudun yayi picking.

Cikin rawar murya tace "H..he...llo ya Mukhtar" shiru ya danyi kan yace "kina lafiya?" "Lafiya kalau, fatan kaima kana lafiya" ta kai karshen maganan hawayen idanunta na tsiyaya.

"Ina lafiya, akwai wata matsala ne?" "Aa, dama nace bari na kiraka ne mu gaisa na Kuma yimaka godiya naga sako" "Masha Allah, se anjima".

"Ya mukhy" shiru yayi bece komai ba

"Yanzu da gaske mun rabu?" Saurin tarar numfashinta yayi "Dan Allah Muhibbah kar ki dawo da hannun agogo baya abinda ya wuce ya wuce ki dauki haka matsayin kaddarar rayuwarmu" be jira Jin abinda zata fada ba ya yanke wayan.

Babu zato ba tsammani taji an zare wayan daga hannunta dasauri ta dago kanta suka hada ido mugun kallon dake watsamata yasa tasha jinin jikinta.

Bakinta ne yafara rawa tana kokarin yin magana kafin ta bude baki taji saukar lafiyayyen Mari a kuncinta a zabure ta mike tareda sakin kara tana ja da baya.

Binta yake har suka kai karshen bango.

Kankame jikinta tayi tana bashi hakuri "Dan Allah Yaya kayi hakuri bazan sake ba nayi kuskure".

Wani yawu me zafi ya hadiye idanunshi sun kada sunyi jajir wani abu me daci ya tokare mai kawon zuciya jikinshi har rawa yakeyi hannu yasa ya fisgota ya kuma kwada mata lafiyayyun maruka har 3 kana ya tureta ta fadi.

Kuka me sauti ta saki "Kiyimun shiru, wllhi ko tari kika Kuma yi sena shakeki kin mutu kowa ya huta, gardi kike kiramin acikin gida na" ya Kai karshen maganan cikin dacin rai yana nunata da yatsa Da sauri ta rike kafafunshi "wllhi Yaya tunda aka kawoni gidan nan ban taba waya dashi ba se yau natuba bazan kara ba nayi nadama" kallon da yake aikamata yasata saurin sakinshi "Bance ko tari kar ki kuma yi ba? Yaushe nafara wasa dake?" Kai kawai take girgiza wa tasa hannu ta toshe baki gudin kar tari ya kufcemata ya shaketa ta margaya kamar yadda ya fada.

"Ki Kuma magana kiga idan ban buga kanki a bangon nan ba ya tawarwatse, nadama Kuma bakiyi ba tukunna". Yana kai nan yafice yana wuci.

Durkushewa kan guiwowinta tayi tasaki kuka me sauti tana fadin tashiga uku. Tsoro ne ya kamata tasan baze barta haka ba gashi ya kwace wayanta bare takira Abba yakawo mata dauki can dubara yazo mata ta mike daker ta zira hijjab ta dauki kudi cikin sanda ta sauka daga stairs din.

Sauri sauri ta karasa ficewa daga parlourn ko driver bata nema ba ta fice daga gidan me gadi yabita da kallon mamaki Anya kuwa lafiya madam ta fito hankali tashe cikin dare, maida gate din yayi ya rufe ya koma ya zauna.

Napep ta tara tashige a bakin gate din gidan ya ajiyeta ta mika mai kudi tana ji yana ta tsaya ta karba chanjinta daker ta iya cemai ya rike tabarmishi chanjin, bubbuga gate din takeyi da karfi tana waige da sauri me gadi yazo ya bude dan dajin wannan bugun bana lafiya bane a hankali ya dan leka ganin Muhibbah yasa yayi saurin bude mata tashigo da kallo yabita a ranshi yana tambaya to wannan ko lafiya?.

A sukwane ta shiga parlourn ta fada jikin Abba tana kuka, dago ta yayi dasauri "Mamana lafiya? Meke faruwa?" "Abba na shiga uka Yaya" "menene ya samu yayan?" Hankali tashe a halin gidan suka kara so gurin Muhibbah suna tambayar lafiya amma se kuka take "Meyasamu Yayan naki?, bashida lafiya ne? Ko mutuwa yayi?" Ummi ta jero mata tambayan a kidime cikin kosawa da Jin amsanta.

"Yaya kasheni zeyi nashiga uku na wllhi nasan baze kyaleni ba, na kade Abba ummi kuyimun rai dan ku boye ni innalillahi wa inna ilaehi raji'un".

Dago fuskanta yayi yaga shedar yatsun Fu'ad kwance.

"Mamana shine yayi miki wannan dukan? Me kika mishi?" Ita dai takasa magana se su boyeta kawai take maimaitawa.

Ran Abba bace ya dauko wayanshi yashiga dialing numbern Fu'ad.

Be fito daga asibiti ba se gaf magrib a masallacin unguwar su yatsaya yayi sallahn

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login