Showing 87001 words to 90000 words out of 112768 words

Chapter 30 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

a hankali yake cin abincin se yajishi duk a ta kure dan yasa ba yamata masauki akan cinyarshi suci abincin a tare yana zolayanta tana dariya

Kallonshi tayi ta dage mai gira daya ganin yana tsakuran abincin kamar anmishi dole, kasa kasa yace "Feed me please" ya fada yana bude baki

Dan zaro ido tayi ta mai alama dasu mummy ya make kafada irin he don't care din nan

Abincinta ta cigaba da ci hankali kwance, kafarshi yasa ya dan taka nata ta saki kara mara sauti "Ash kai hearty so kake ka karya ni kaje ka auro wata ko" tayi maganan a shagwabe

Mikewa Mummy tayi ta shige dakinta yana ganin haka ya riko hannun ta ya mikar da ita ya janyota yamata masauki kan jikinshi "oya feed me! Kinga ma mummy tabamu guri mu shana" dariya tayi "Wannan abubuwan da kakeyi ba dole su koreta ba" ta fada tana kai mai abincin baki, Shima Suhail tashi yayi yabar musu parlourn

Soyayyarsu suka sha kan ya fice ita kuma ta nufi dakin mummy

***********

Tana zaune bedroom dinta tana karatun novel din da Muhibbah ta turamata *Haihuwa da hanji* wayanta ta dau kara tsaki taja dan Bata son abinda ze katse mata karatun ta har ya kusa tsinkewa kan tayi picking ta kara a kunnenta

"Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuh"

"Wa alaekumussalamu warahmatullah wabarakatuh"

"Barka da dare Aishatul humaira"

"Barka dai, dawa nake magana please?"

"Mukhtar" ya fada a takaice

"Mukhtar! Mukhtar!!" Ta maimaita a saman lips dinta tana kokarin tino me irin sunan.

"Gaskiya malam ban gane kaba"

"Haba dai Mai babban suna kidai kara zurfafa tinani"

Shiru ta danyi badai mukhtar din Muhibbah ba? se Kuma ta girgiza kai aa kam bashi bane shi me zesa ya kirata kuma ma ai beda numbernta

"Ya Mukhy!"

"Yeah kin canka" yafada yana murmushi

"Fatan dai lafiya?" "Lafiya kalau se alkhaeri"

Seda yayi gyaran murya kan yace

"Ina fatan zaki amshi kokon barana ki bani dama mu gina rayuwa mai cike da so da kauna" waro ido tayi ta mike a zabure har bakinta na rawa wajen furta "What? Ka gane da wanda kake magana??"

"Tabbas na gane mana"
Kai ta girgiza "Aa inaga wrong number ne, bani Aeshan kake so ka kira ba"

Murmushi me sauti yayi

"Ke Aeshan kam cousin sistern Muhibbah my wife to be Mrs Mukhtar in Sha Allah"

Shiru tayi tama kasa magana
"Ina fata zaki bani dama mu karashe rayuwar mu a tare my Angel"

Gaba daya ta kidime maganganunshi sun zo mata a bazata "Okay zanyi tinani" kalmomin da tayi kokari ta hadasu daker kenan

"Seda safe sweet dreams dear se najiki" batace komai ba tayi hanging call din ta koma ta zauna tana dafe goshinta se yanzu ta tina Muhibbah ta Karbi wayanta jiya ashe abinda take shiryawa kenan, rai a bace tashiga dialing numbern Muhibbahn.

***********

Suna gama dinner suka koma parlour gaba Daya a halin gidan Muhibbah se zuba zance take suna dariya hatta Anas yayi missing abokiyar fadarshi amma duk da haka yau din ma seda suka taba rikicin

"Fu'ad ya kake ganin nutsuwar yarinyan da Suhail ke nema" cewar daddy

"Gaskiya daddy yarinyan batada matsala daga gidan tarbiya ta fito iyayenta nada dattaku"

"Ah Masha Allah abinda muke son ji kenan muma ba tsayawa bata lokaci zamuyi ba Abbanku da abokinshi idan suka samu lokaci se suje ayi magana kawai a tsaida lokaci"

Wayanta ne ya dau kara ganin sunan Aesha na yawo kan screen din wayan yasa ta mike tana murmushi ta nufi dakinta, bakin gado ta zauna "Hello 'yar kanwata"

"Me kike Shirin yi haka muhibbah? Kinsan abinda kika aikata kuwa? kina tinanin zan iya soyayya da wanda kika so shi tamkar ki mutu ne? bare har a kai ga maganar aure? gara tun wuri ki janye kudurinki ki Kuma bashi hakuri kar ya kuma kirana wllhi da nasan abinda kike shiryawa kenan da ban baki wayata ba" ta Kai karshen maganan tana nishi kamar wacce tayi tseran gudu

Murmushi me sauti tayi "Kai Aesha wllhi Allah yashiryeki" tafada tana dariya sosai

Kara kula tayi "Wato ga banza na magana ko"

"Calm down my lovely sister kinsan inda ya mukhy nada wani aibi da bazan taba miki sha'awarshi ba kinsan bazan baki abinda ze cutar dake ba, sannan maganan na so shi ai wannan yazama past tense, ina yanzu ina tare da mijina toh me kuma ya rage tsakanina da ya Mukhtar daya wuce mutumci dan Allah ki ajiye wannan maganan a gefe" seda ta numfasa kan taciga ba da magana

"Ya Mukhtar yanada duk wani qualities irin na namijin da duk macen da ta sameshi ta gama dace a rayuwarta, ilimi, nasaba, kamala, nutsuwa, kyau babu Wanda bashida shi acikin abubuwan nan da na lissafa duk da be kama Koda kafar hearty ba" tafada tana dariya, itama Aesha seda ta murmusa

"Dan Allah ki karbeshi hannu bibbiyu bazaki taba nadama ba kiyarda dani please"

Ajiyar zuciya ta sauke "Okay zanyi tinani tnx"

"Kyaji dashi dai seda safe ki gaida Ummi" tana Kai nan ta kashe wayan.

Koda ta dawo parlourn tasamu kowa ya shige dakinshi dan haka itama ta juya ta koma daki tasa kayan bacci tayi kwanciyarta tanajin kewan mijinta pillow ta janyo ta rungume tana murmushi dan tasan Shima yanzu haka yana can rungume da pillow

Wayarta ce ta dau kara ta janyo wayar tareda yin dariya mara sauti ta kara wayan a kunnenta

"Hearty! Bakayi bacci ba?"

"Uhmmmm kema me kikeyi baki kwanta ba?"
"Laa na kwanta fa tun dazu"

"Toh me ya hanaki bacci?"
"Yanzu zanyi"

"Bakiyi kewata ba ma ko"
"Nayi mana irin sosai din nan fa" ta fada a shagwabe

"Toh kizo ki sameni yanzu ina jiranki"

Zaro ido tayi "Kai gidan mummy fa muke" "na sani kizo maza ina jiranki"

Turo baki tayi "Toh ya Suhail fa"

"Shima yasan yanzu da dah ba daya bane yasan ina da mata shiyasa ma ya barmun dakin ni kadai"

"Aa nikam idan su mummy suka ganni fa to ina zan ce musu zanje"
"Gurin mijinki, nabaki 5 minutes idan baki zo ba wllhi wllhi ni zan zo da kaina ai kinji abinda nafada ko?" "Uhmmm" abinda tace kenan ta ajiye wayan

Mikewa tayi ta dauki hijjab dinta har kasa tasa ta fice dan tasan ba karamin aikinshi bane yazo har dakinta yadda ya fada.

Tana tafiya tana waige kamar mara gaskiya ta bi ta kofar kitchen ta isa bangaren su da sauri ta karasa shiga dakin kamar an korota har tana bugan kirjinshi dan shima har ya mike yana shirin zuwa ya sameta

"Ji yadda duk kika firgice kina zaro ido kamar wacce aka Koro" turo baki tayi ta karasa ta zauna gefen bed
Karasawa yayi
ya zare hijjab din jikinta yayi wurgi dashi ya dagata cilak ya kwantar da ita tsakiyar gadon ya mata runfa "Wai fushi kike" "Dan Allah Yaya ka bari kar muyi abin kunya gidan mutan..." Be bari ta karasa ba ya hade bakinsu yajima yana bata hurt kisses kan ya zare bakinshi ya kai saitin kunnenta "Waye yace miki gidan mutane muke? Nan dinma ai gidan mu ne kuma babu wanda besan mu ma'aurata bane, su mummy da dare nan babu abinda ze kawo su part din nan" Yana maganan yana yawo da hannunshi a jikinta

Duk ya kashe mata jiki dole yasa ta biye mai suka sha bidirin su seda suka samu nutsuwa kan ya dauketa suka shiga toilet sukayi wanka suka kwanta rungume da juna tanata rigimar yabarta ta tafi dakinta yaki a haka
har bacci ya dauke su.

Koda yatashi da asuba toilet ya shiga yayi alwala har ze tasheta ya fasa dan yasan rigima zata tsiro kan yabari ta kwana tare dashi a gidan daddy

A hankali ta bude idanu Jin har an sallame sallah a masallaci yasa ta diro daga gadon da sauri ta dauki hijjab dinta ta zira ta fice daga dakin cikin sanda ta biyo ta kofar kitchen seda ta leka parlourn taga babu kowa kan ta karasa dakin ta da sassarfa.

Gidan Aunty Asma'u sukayi ma tsinke ta tura kofar parlourn bakinta dauke da sallama su yusrah da Abdulrahman da Muhsin suka rugo da gudu suka rungumeta suna mata Oyoyo kan suka karasa suka rungume Fu'ad ya daga su daya bayan daya yana direwa guri suka samu suka zauna, Jin hayaniyar yaran yasa ta nufo parlourn da sauri ganin su Muhibbah yasa ta fadada murmushin ta cike da farin ciki ta kara so ta zauna

"Yaya wannan bazata haka saukar yaushe?" "Babu ruwana laifin rigimamiyar yarinyan nan ce Mummy zata kiraki ta hanata"
Shagwabe fuska tayi "Nicema rigimamiyan?"
Gira ya dage mata batareda yayi magana ba, ita dai Asma'u se murmushi take dan bakaramin birgeta sukayi ba kamar basu ne suke kin junan su ba a kasan ranta ta furta Alhamdulillah

"Aunty hadamu yake so yayi amma ni surprising dinki nake so nayi ne shiyasa nace kar mummy ta fada miki, Kuma fa jiya ne muka zo"

"Ah ai kam kunyi surprising din nawa" ta fada tana mikewa abin tabawa ta cika musu gabansu dashi kan ta Kai zaune

"Yaya ka biye ma yarinyan nan kuka tawo ni na dauka seta haihu ai ita da garin nan"

Shidai bece komai ba yana jinsu sedai ya danyi murmushi

"Kai Aunty wane irin haihuwa tun yanzu school fa nake gaskiya ba yanzu ba tukunna"

"Eyyeeee mu duk da muka haihu muna karatun me yasa me mu? Ai yayan najinki gaki gashi nan"

"Kudai fara Shirin zuwa sunan Aunty Suhailat" "Toh Allah ya sauketa lafiya"

Sun dan jima suna fira kan ta kirata suka shiga daki ta cikamata leda da magunguna ta kara fadamata wasu sirrikan hade da nasihohi a kunyace ta karba tamata godiya kan sukayi sallama Fu'ad ya ajiyemata kudi tanata godiya kan suka fice

Gidan su summy suka biya tanata mata tsiyan taki kiransu suje suna yola bata jima sosai ba saboda Fu'ad na jiranta waje se summy ce tace zata zo gobe sukara gaisawa

Gidan su Rufaida ya kaita nan ma tsiyan take mata kamar sun hada baki da summy bata jima ba ta wuce har gidan umman mukhtar ya kaita taji dadin ganinta sosai sun sha fira da zahrah kan ta musu sallama ta ajiye ma umma tsarabarta ta wuce umma nata godiya

ShopRite suka nufa sukayi siyayya kan suka siya ice cream suka zauna suka sha sukayi hotuna. Se yamma likis suka shiga gida.

Daker ya bari su kayi kwana 5 da kuka ta baro gidan babu rokon da batayi mai ya tafi yabar ta ba yace inaa idan ta bata mai rai ma se tayi 2 years bata dawo garin ba.

Har airport su daddy suka rakata sunata rarrashinta daddy na mata albishir din may be ma su dawo yola da zama, ita dai rai a bace sukayi sallama daddy ya cikata da gift mummy ma ba abarta a baya ba

Driver suka samu na jiransu airport ya karba kayansu ya zuba a booth kan suka shiga yaja motan

"Bloody!" "Ni kadenamun magana" dariya sosai yayi "Wai fushi kike da Yayanki?"

"Haka nan ka dauko mutum daga gidan su amma kaita iko dashi kamar siya na kayi, yana da ga cikin abinda yasa fa tun farko na tsani auren ka saboda bana so nayi nisa da iyayena" da iyaka gaskiyarta take maganan

Hannunta yakama ya gimtse cikin nashi yana murmushi "My love auren nawa kika tsana"

Baki ta dan tura "Ai dah ne" tafada tana kauda kai gefe

Chakulkuli yashiga yimata tana dariya yanata janta da wasa har ta mance ma tana fushi dashi.

Bangaren Aesha da Mukhtar ma sun sa santa tsakanin su sunata Shan kauna ba kama hannun yaro.

Driver na parking ta sauka ta nufa ciki
Murda handle din kofar tayi ta shiga kamshin dadi ya bige hancinta amma da mamakinta se taji kamshin na yamutsa mata ciki bata zauna parlourn ba ta shige dakinta tana kokarin shiga toilet ya turo kofan yashigo ya dauketa tana dariya suka nufa toilet seda suka bata lokaci kan suka fito dakinshi ya koma ya shirya ya fice masallaci ita Kuma ta karasa shiryawa doguwar riga iya guiwa tasa kan ta zira hijjab tayi sallah seda tayi isha'i ta nade pray mat ta sauko down stairs tana kokarin zama taji ana danna door bell ta karasa ta bude taga me gadi tsaye rike da basket karba tayi tana murmushi a zuciyarta tace "Allah sarki ummi na Allah ya biya"

Kulolin ta fiddo ta shirya kan dining taja kujera ta zauna zamanta ba jimawa ya shigo bakinshi dauke da sallama ta amsa kan ya karaso dining din ya zauna tare da mikar da ita ya dawo da ita kan kafafunshi ya janyo food flask din yana budewa kamshin abincin ya daki hancinta ta dauke numfashinta na seconds tare da binne kanta a kirjinshi tanaji cikinta na yamutsawa

"Hayatee! Lafiya kuwa" "Lafiya kalau"
"Anya kuwa kwana biyu naganki wani sukuku ko wani abu na damunki ne"

"Aa Yaya Lafiya ta kalau kawai kwana biyu zazzabin dare nake fama dashi da safiya kuma tayi se in nemeshi in rasa"

"Sorry shine baki fadamun ba" "Ai ba sosai bane" "Uhmmm duk da haka dai kinga da nasan maganin da zan baki"

"Yaya yunwa" lakace hancinta yayi "Toh da Ummi bata aiko mana abinci ba fa dase kinjira andafa" "bakaji ba kace da amma yanzu tunda an kawo case closed" ta fada tana dariya

Serving dinsu yayi ita dai daurewa kawai take dan kamshin abincin ba karamin hawa mata kai yake yi ba

A baki ya soma bata tana karba chokali uku tayi ta fara kokarin mikewa ya riketa "Ina zaki? Kina bukatar wani abu ne?" Ta bude baki zatayi magana amai ya kufce mata tashiga kwarara mai a jiki............




*Gobe Monday >???=???=?"?*



*>?p? Aminiyar ango >?p?**>?p? Aminiyar ango >?p?**Toh bance gobe zanyi update ba gaskiya se wani iko dg Allah dan se yamma zan dawo gida*
[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*

*FATIMA A MUHAMMAD AMINIYAR ANGO*

*Page 53*


*Dedicated to masoyinah, Abdulraheem (yaron umma), wannan page din naka ne, Allah yakarama lafiya me dorewa =?O? =?O? =?O?*


Kokarin mikewa take ya riketa, ta kalleshi ya dagamata kai. tako cigaba da kwarara amanta, seda ta amayar da duk wani abu da taci tun na safe har zuwa na rana kan ta kwanto kan kirjinshi tana maida numfashi.

"Bloody! Kingama?".
Kai ta jinjina ya mike da ita a jikinshi ya haura sama. Dakinshi ya nufa ya direta a toilet ya cire mata kaya yasata cikin kwamin wankan shima ya zare kayan jikinshi yashiga yamata wankan kan Shima yayi. A towel yana dota ya kwantar da ita kan bed. ya nufa wardrobe ya dauko jallabiya yasa itama ya dauko mata jallabiyarshi Ash colour ya karaso ya zauna bakin bed din tareda rungumota jikinshi yasa mata jallabiyan. Hannunta yarike cikin nashi kan yace "Heebbah!"

"Uhmmm".

"Meke miki ciwo?"
"Babu" tafada tana yatsina fuska.

"Toh me yakawo aman?" Yafada yana kallon kwayar idanunta.

"Nima bansaniba. Tunda naji kamshin abincin kawai naji cikina yana yamutsawa".

"Eyyyaaa sorry my Angel. Yanzu me kike so?" "Cake".

"Cake Kuma bloody?" Kai kawai ta Jinjina, yace "okay" ya kwantar da ita ya fice.

Tattare dining din yayi ya gyara gurin. Ya hada coffee ya dora kan tray kan ya bude fridge ya dauko cup cake ya dora gefen tray din ya nufa dakinshi. A kan bed ya ajiye tray din ya haura ya dagota yamata masauki akan cinyarshi yashiga bata cake din. Ko daya bata cinye ba tace ta koshi. Lallabata yaitayi har yasamu tacinye daya. Akan kafafunshi ya kwantar da kanta yana shafa gashin ta a hankali yana sipping coffee din har yagama kan ya mike ya maida tray din kitchen. Ya dawo ya kwanta ya janyota jikinshi ya matseta a kirjinshi yana shafa bayanta a hankali.

"Hayatee! Yanzu me kikeji ajikin ki?"

"Bacci nakeji" tayi maganan a shagwabe.

Bece mata komai ba se matseta daya karayi a kirjinshi kamar za'a kwace mai ita, a haka bacci ya dauketa. Shikuma ya tsuramata idanu yana kare mata kallo har bacci yayi gaba dashi.

wajen 5 na asuba cikin baccinshi yaji nishinta. A hankali ya bude idanunshi ya sauke su a kanta, bacci takeyi amma se nishin zazzabi take ga jikinta yayi zafi rau kamar wuta. Cikin kidima ya sauka daga gadon ya dauko allura iya kan paracetamol da atimeter yaja a siringe. ya haura gadon ya janyota jikinshi yana shafa fuskanta hade da huramata iskan bakinshi.

A hankali ta fara bude ido har ta sauke shi cikin nashi. Yasakar mata murmushi batareda yayi magana ba, ya juyata yamata alluran. da mamakinshi batayi korafi ba yadda tasaba idan zemata allura se ranshi ya baci kana take tsayawa amma yau ko tari batayi ba. Seda ya rungumeta kan yaga hawaye na silalowa daga idanunta. Yasa hannu yana share mata, Hade da bubbuga bayanta. yana nan zaune manne da ita har ta koma bacci kan ya kwantar da ita yaja blanket ya rufeta shikuma ya sauka ya nufi toilet. Alwala ya dauro ko masallaci be iya fita ba ya shinfida pray mat yayi sallah yadawo ya zauna gefenta.

Se 8 yaje kitchen yasama musu breakfast, Koda ya dawo dakin yasamu har tayo wanka tazo ta tada sallah.

Shima wankan yaje yayi kan ya fito har ta fice daga dakin. Shiryawa yayi cikin white shirt da bakin jeans, ya feshe jikinshi da turare ya nufi dakinta.

Shirye take cikin doguwar rigan material tasa hula ta dan jata baya kwantacen gashinta ya bayyana, suna hada ido yasakar mata murmushi itama murmushin tayi kana tace "Good morning my heart".

"Morning Angel of my life" yafada yana karasawa ya riko hannunta.

"Ya Jikin ki?".
"Na war ware" "uhmm nima sheda ne, dan gashinan kinsha kyau abinki" yayi maganan yana pecking goshinta.

Murmushi tayi tana rufe fuska.

"Dagaske fa kinyi kyau"
Yafada yana kureta da ido ganin yadda takara haske har tana kashe ido.

Murmushi ta danyi kan tace, "Dan saurayi! Ya akayi ne? Karka hadiye ni mana" tayi maganan da zolaya.

Murmushi me sauti yayi "Wankan naki ne ya tafi dani". Dariya tayi har hakwaranta na bayyana, tace, "Kai kam baka rabo da zolaya".

Kamo ta yayi ya tsayar da ita gaban mirror, ya manne bayanta da kirjinshi
"ke kyakkyawa ce ajin farko, ki Kalli kanki da kyau a madubin nan zaki tabbatar da abinda nake fada miki. Ko dawisu bazata nunamiki ado ba, duk wata mace idan baki ne take amsa sunanta mace amma dakin doso dole su ja da baya".

Juyowa tayi ta rungumeshi tana dariya tace, "Hearty muje please yunwa nakeji" tafada tana shafa cikinta da takeji kamar an yashemata 'yan hanji.

Lakace hancinta yayi, "Ba dole kiji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login