Showing 99001 words to 102000 words out of 112768 words

Chapter 34 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

ankaraba yaji hawaye na silalowa daga idanunshi yakasa magana se girgiza kai kawai yakeyi zuciyarshi ta karye idan yace zeyi magana kuka ne ze kufce mai, bata kula ba ya zame hannunshi daga nata ya juya dasauri ya fice, dan baze iya jure tsayuwa a gabanta cikin wannan halin ba, Mota ya dauka ya fice, gudu yake kan titi kamar ze tashi sama.

Horn ya danna aka bude mai gate ya kutsa ciki, yanayin parking ya nufa ciki dasauri, wani karamin akwati da Aesha ta hada kayan baby dana maman babyn aciki ya dauko ya shige mota ya fice daga gidan. Koda ya koma asibitin kasa shiga labor room din yayi sai wata nurse yaba akwatin ta mika cikin room din shikuma ya koma office dinshi.

Waya ta daga takira wata nurse, ba jimawa se gata ta shigo labour room din

Ita ko ta kasa magana se binshi da ido da tayi har ya fice daga room din, gaba daya hawayenta sun kafe tazama kalar tausayi se jujjuya idanu take, takasa fahimtar a duniya take ko akasin haka.

Wani nishi me karfi tayi dabata san yaushe yazo mata ba, se ga kan baby ya leko. lokaci daya kuma wani azaba ya ziyarce ta tayi ihu tareda hada kafafunta tana kokarin matse kan babyn. "Madam haka zamuyi dake Kuma? zaki matse kan babynki, ki daure kin kusa saura kadan"

"Ni ki kyaleni nace miki bazan iya ba, ko dan bakisan azaban da nakeji ba, tun dazu se cewa kike na kusa amma har yanzu shiru" tafada da karfi cike da masifa.

Murmushi kawai doctor tayi bata ba maganarta muhimmanci ba ta rike kafafun

Wani nishin taji yana zuwanmata ta takura ta saki nishi me karfi tareda furta "Innalillahi wa inna ilaehi raji'un......." Cikin taimakon Allah Sega babynta ta sunbulo. Nurse din tayi sauri ta tare ta fada hannunta

Wani nannauyar ajiyar zuciya tasauke ta kwanta lamo ta rufe idanunta tana furta Alhamdulillah a kasan zuciyarta, wani sanyi takeji kamar ancire mata kaya, tanajin kukan babyn amma ko magana takasa bare ta tambaye me ta haifa.

Zama yayi ya kunna CC TV camera yana kallon abinda ke faruwa a labour room din, duk ya rude se karanta duk wata addu'a data zo bakinshi yake, zuciyarshi tayi rauni baya so kuma ya kira su ummi ya daga musu hankali. yana ganin fitowar baby ya mike da sauri yayi sujudu shukur yana mikama Allah godiya.

Ya mike ya nufo lobor room din, ya tarar nurse na goge ma babyn jiki, be tsaya nan ba ya karasa wajen Muhibbah yayi pecking dinta a kumatu. Tunda ya karaso kamshin turarenshi ya sanar da ita shine amma ko kifta idanu batayi ba bare yasa ran zata bude.

Hannayenta ya rike "Hayateee! Bude idonki yayanki ne ba doctor bace" kara runtse idanu tayi ko motsi takiyi.

Doctor fareeda ta karaso gangansu rike da allura yace, "Doctor kamar akwai sauran baby a nan ko?" Yafada yana kai hannunshi cikinta

"Uhmmm nima haka nake tinani naso naga cikin na motsi" da sauri ta tashi zaune tana shafa cikinta tashiga zare idanu, tayi kwal kwal da ido tana kokarin yin kuka.

Dariya yayi yace, "No karki kuka blood, ke kam kin cika tsoro wasa fa ake miki" se lokacin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya batasan har ta fito fili ba

Dariya doctor tayi "Madam dan gyara please" ta fada tana fasa allura (Oxytocin) ta zuka a siringe.

"Doctor badai allura ba" tafada tana ya mutsa fuska

"Kar muyi haka madam, kika iya santalo kyakkyawar baby bare wata allura, nayi tinanin daga yanzu ma kin dena kukan allura ai"

Tana kokarin tsira alluran tayi saurin rike mata hannu "Dan Allah doctor kibar alluran nan, wllhi akwai zafi" tayi maganan tana hawaye

"Kai! maman baby kina so babynki tamiki dariya kina kukan allura". Ta fada tana tsira mata alluran a cinya, tasa kuka. Juyawa tayi ta karba babyn daga hannun nurse ta mikama Fu'ad.

"Congratulations sir it's a baby girl" fadada murmushin shi yayi ya karbeta yayi pecking goshinta tare da furta

"Thank you doctor"
"You deserve more" Kai ya Jinjina ya mikamata babyn yace ta rike ze taimaka ma Muhibbah ta gyara jiki.

Akwatin ya bude ya zabo mata doguwar rigan atampha, yazo ya kamata suka karasa toilet ya mata wanka ya gyaramata jikinta tareda ziramata doguwar rigan ya kamota suka fito.

Akwatin ya janyo, ita Kuma ya tallabota ta dayan gefen suka karasa special room. "Waye ya hada kayan akwatin nan?" "Aekin Aesha ne, nace mata kaya daya naga su Aunty Asma'u na sawa, amma ita ko iya kayan baby tasa sun kai kala goma" takarashe maganan tana zama kan gadon. Kai kawai ya jinjina ya mika hannu ya karba babyn ita Kuma doctorn ta fice.

Shima hawa gadon yayi ya zauna gefenta, yasa hannunshi daya ya dago habarta yana kallon cikin kwayar idanunta tayi saurin runtse ido. Bata zata ba se ji tayi ya hade bakinsu guri daya ya shiga aikamata da deep kisses tayi loosing balance tayi baya baya ta kwanta yamata runfa, har lokacin yana rike da babyn a dayan hannunshi.

Zame bakinta daga nashi tayi tasa hannu biyu ta ture kirjinshi ta tashi zaune ta hade kanta da guiwa tana sauke numfashi. Hannu yasa ya dago kanta yana murmushi yace, "Mammi! wai fushi kike dani?" Kai ta gyada kana tace, "Bakai bane kacemun haihuwa babu wahala ashe akwai azaba harda bala'i ma" dariya me sauti yayi

"Shine laifin nawa?" Ta jinjina Kai
"Sorry a gafarceni, nayi tinanin babu wahala ne shiyasa na fada miki hak" murmushi tayi "Kuma kayimun alkawari Kai zaka zauna dani har na haihu amma kayi tafiyarka ka barni da doctor, inata shan wahala wani abun ma fa da gangan takeyimun, kaga ko gurin samun hannun nan da takeyi kar kaso kaji azaba har kwakwalwata". Pecking kumatunta yayi "A gafarceni guiwowina a kasa, nayi kokarin na kasance tare da ke amma nakasa juran ganin halin da kike ciki, Kuma na fahimta zamana kusa dake rauni yake sa miki, koda na koma office kasa hakuri nayi seda na kunna CC TV camera Ina kallon abinda ke faruwa, I'm sorry".

Murmushi tayi ta kwantar da kanta kan kafadarshi, ya doramata babyn kan jiki "bloody! Ki Kalli babyn nan dake take kama" hannu tasa ta rungume babyn tayi pecking kumatunta, Aiko tasa kuka. Kallon juna sukayi, sukasa dariya.

"Yaya kaji gulma fa, da bata tina da kukan ba seda na dauketa. Base kin fada ba ai ni tun kina ciki na gane ba sona kike ba kinata wahalar dani kinzo duniya hakan ma be miki ba na daukeki kin wani tabe baki kina kuka uhmmm"
"Kisha kuruminki gobe Aunty Suhailat zata tafi dake ta hada da Aadil na barmata". Ita ko baby kamar tanajin abinda ake cewa tayi shiru se wuwurga kafa take.

Murmushi yayi "Sannu maman baby kinga ai taji fadan Ammin ta tayi shiru" hannunta ya kama yayi pecking "Allah ya miki albarka blood, Allah ya biyaki da gidan aljannahtul firdaus Allah ya rayamana babyn mu akan sunna ya albarkaci rayuwarta mu kuma Allah yakara mana kaunar juna".

"Ameen my heart, tnx too" shiru sukayi na seconds kan tace,

"Hearty! Banga su ummi ba tun dazu nake zuba idon ganinsu amma shiru".

"Bansanar musu ba, kinsan da sunji duk zasu daga hankalinsu, yanzu Kuma dare yayi shiyasa na bari se zuwa safiya nayi surprising dinsu"

Kai ta jinjina tana murmushi "Ka kiramun mummyna please"

"Da daren nan? 3:10am fa, kiyi hakuri har zuwa asuba uhmm". Kai ta gyada batareda tayi magana ba.
"Kin mintsine babyn kuwa?" Dariya me sauti tayi tana kara shafa fuskan babyn tanajin yadda kaunarta ke mamaye zuciyarta

"Uhmmm na hakura"

"Toh ni bari nacika alkawari na, kar ki kuma fushi kice nayi alkawarin zan rankwashe baby Kuma ban cika ba" ya fada yana Kai hannunshi kamar ze rankwasheta tayi saurin kankame babyn a kirjinta ta rike hannunshi sukasa dariya a tare.

"Ai ni ta wahalar kuma na riga na yafe" kallon yadda babyn ke mutsu mutsu yayi kana ya maida idanunshi kan Muhibbah.

"Bloody babyn nan fa abinci take so"
Kafada ta make "Ta bari seda safe kasiya mata NAN" tafada tana mikamai babyn, ta zame ta kwanta. Bata jima da kwanciya ba bacci yayi gaba da ita dan jikinta duk ciwo yake mata.

A kafada ya sabata yana dan bubbuga bayanta, saida da ta koma bacci ya kwantar da ita kusa da mamanta, ya gyara ma mamanta kwanciya ya lullubesu ya tofa musu addu'a ya koma kan kujera ya kwanta.

Karfe 5:20am ya tashi yashiga toilet ya dauro alwala ya fice masallaci, dama baccin nashi rabi da rabi ne yanayi yana farkawa ya dubasu kana yakoma ya kwanta.

Koda yadawo masallaci stood ya janyo ya zauna yana kare musu kallo yana jin farin ciki mara misaltuwa na lullubeshi se sakin murmushi yake.

Wayarshi ya zaro ya shiga dialing numbern mummy, ringing biyu ta dauka "Yayansu lafiya kuwa?" "Lafiya kalau mummy, dama Muhibbah ce ta sauka" yafada yana shafa kai

"Alhamdulillah! Yaushe? Me aka samu??".

"Cikin dare, ansamu budurwa" "Masha Allah! Allah ya raya. Ina Muhibbahn?" Seda ya kalleta kafin yace, "mummy tana bacci"

"Allah sarki, toh shikenan idan ta tashi ka kirani" daga haka sukayi sallama

Seda 7 tayi kana ya kira Ummi tun kafin yayi magana tace, "Lafiya?" "Lafiya kalau, Muhibbah ta sauka" washe baki tayi cike da farin ciki tace, "yaushe? Me ta haifa?? Kuna ina yanzu???" Ta jero tambayoyin cike da kosawa da Jin amsoshin tambayoyin.

"Jiya da dadare, tasamu mace, ummi muna asibiti amma base kunzo ba yanzu zamu dawo gida"

"Alhamdulillah! Ina Muhibbahn?" "Ta shiga toilet" "Fatan dai babu wata matsala"

"Komai lafiya ummi"
"Yauwa toh nan gidan zaka kawomun ita" "in sha Allah" yana kai nan tayi hanging call din, yabi wayar da kallo jikinshi yayi sanyi Jin Kalmar ummi na karshe cewa ya Kai Muhibbah gurinta beso haka ba.

Baki ta wanke ta fito ta zauna bakin gadon "Good morning my heart" "Morning our adorable mum, ya karfin jiki?" Murmushi tayi "Dasauki our beloved father" hancinta ya dan ja "Munyi waya da mummy kina bacci" yafada yana dialing numbern mummyn. zatayi magana ya manna mata wayar a kunne.

"Hello mummy na......." Kawai ta fashe da kuka

"Muhibbah lafiya, me yafaru?" "Mummy ashe haka haihuwa take da wahala, banzata zan rayuwa ba nayi tinanin mutuwa zanyi" "Allah sarki auta na, sannu kinji"

"Dan Allah mummy ki yafemun, natuba" takarashe maganan tana sakin sabon kuka

"Toh miye na kukan Kuma, nikam bakiyimun laifin komai ba, koma kinyi mun bisa kuskure na yafe miki duniya da lahira" "Ki rokamun Abba ya yafemun" "Shima ya yafemiki, kidena kukan nan kinji" Kai ta gyada sukayi sallama.

Gefenta ya zauna yasa hannu ya share mata hawaye, yasa spoon yana dibo tea din yana kaimata baki, saida yaji yayi yadda zata iya sha ya cire spoon din yana bata da cup din har ta shanye. Hijjab ya dauko mata ya zira mata yadauki babyn ita Kuma ya rikota ta dayan side din suka fito anata mai barka yana amsawa fuskarshi dauke da fara'a. Aunty fareeda ta biyo su da akwatin.

"Toh maman baby Allah ya raya" a kunya ce tace "Ina kwana" "Lafiya kalau, ya karfin jikin?" "Alhamdulillah".

Bayan booth yasa akwatin ya budemata ta shiga ya mikamata babyn Shima ya zagaya ya shiga yaja motan suka fice daga asibitin.

Gidan ummi ya nufa, a parking lot yayi parking ya fito ya bude mata ya dauki babyn kana itama ta fito suka karasa ciki

Tasamu har Aunty Suhailat ta iso, ana fadamata haihuwan mijinta ze tafi aiki tako zaro mayafi ya sauke ta gidan ummi kan ya wuce.

Daki daban aka ware mata kafin ta iso an kara gyarashi ansa turare, Aesha ta karasa ta karba babyn bakinta yakasa rufuwa tsabar farin ciki.

Ita Kuma Suhailat taja akwatin suka nufi dakin

"Ina kwana Ummi" ta gaisheta tana sunkuyar da Kai
"Lafiya kalau Muhibbah, sannu da kokari Allah yabada lafiyar shayarwa" murmushi kawai tayi tana kallon yadda Aesha ke rike babyn ji take kamar zata fadar da ita ganin idanun ummi kawai yasa ta daure batayi mata magana ba"

"Sister wllhi babyn nan sak ke kamar an tsaga kara, ko Aunty Suhailat?" "Sosaima kamanninma bana wasa ba kamar tayi kaki" Aesha tace, "Kuma irin babyn da kike so kinganta 'yar lukuta tubarkallah"

Ita ko baby se wuwurga kafa take tana tabe baki tana kananun kuka, hakurinta ya kusa karewa.

"Wai Aesha kinaji yarinya na bukatar mamanta kin ki bada ita, ko se ta bude baki zaki fahimta yarenta" Ummi ta fada, duk akasa dariya.

Karbanta tayi ta mikama Muhibbah "Karbeta yunwa takeji, Allah ma yasa tun da kuka tashi kin bata nono" Fu'ad yace, "Ummi tun dare nayi nayi taki bata" "Innalillahi wa inna ilaehi raji'un, kisan kai zakuyi ne? Allah sarki baiwar Allah, gaskiya tanada hakuri. Toh mezakiyi da nonon da kike ajiyarshi? kwalliya zakiyi dashi ne?".

"Ummi dan Allah kiba Aunty Suhailat tabata" iya gaskiyarta take fada harda hawaye

Dariya duk sukayi, dan lamarin Muhibbah akwai ban dariya, banda Fu'ad daya hade girar sama da kasa dan ya fahimta Muhibbah da gaske take shirmen nata yayi yawa.

"Ana miki magana kina cewa Suhailat tayi feeding dinta? Kin karbeta ko kuwa?" yayi maganan rai a bace

Baki ta turo ta karbeta ta rungume

Mikewa ummi tayi tace, "Kabita a hankali bada fada zakayi ba, bari Aesha ta kawo muku zaitun da cotton wool" ta fada tana ficewa, su Suhailat suka mara mata baya.

Basu fi 2 minutes da fita ba Aesha ta miko musu zaitun din da cotton wool ta fice taja musu kofan................





*>?p? AMINIYAR ANGO >?p?*
[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*

*FATIMA A MUHAMMAD*
*AMINIYAR ANGO*


*Page 58*



Mikewa yayi ya koma gefenta ya zauna, ya Kai hannu ya zuge zip din rigarta yayi kasa da ita. Ya dauki cotton wool ya dangwali zaitun yafara goge saman nipple dinta, tayi saurin rike hannunshi tana girgiza kai

"Yaya dan Allah kabari na goge da kaina......" Ganin kallon da yakemata yasa ta saurin sakin hannunshi taja bakinta ta tsuke.

Karasa gogemata nipple din yayi, ya gyaramata babyn yasa hannunta yadda zata tallabi babyn dakyau yace, "Ki tallabeta dakyau, ki mannata sosai a kirjinki" yadda yafada tayi, ya taikamata ta seta bakin babyn yadda zata iya kama nonon. Babyn na kamawa tasaki kara tayi saurin janye bakin babyn tana fadin, "Yaya wllhi da zafi bazan iya ba, dan Allah kasiyo NAN a dinga bata kawai zefi, tunda baka son Aunty Suhailat tayi feeding dinta". Ita ko yarinya taga samu taga rashi, hakurinta ya kare, Aiko ta bude baki tasa kuka iya karfinta, bakinta har rawa yake tsabar kuka.

Cikin bacin rai yace, "Fateema! Fateema!! Fateema!!!" Daga Kai tayi ta kalleshi idanunta yafada cikin nashi ta tsaya tana kallonshi na seconds kan tayi kasa da idanunta batareda tace komai ba

"Kina so ajimu dake ko?" Saurin girgiza Kai tayi tace, "Aa".

"Kina so sena taba lafiyarki zaki fahimta abinda nake fada ko?" Yayi maganan cikin sanyin murya

Girgiza kai tayi, cikin rawar muryar dake nuna tsoronta tace, "A....aa"

"Karki ga muna gidan Ummi, yanzu sena murda ma kofar nan key na zaneki, kinsan Kuma zan iya, na fahimta har yanzu bakisan inda ke miki ciwo ba, baki gane fatar baki, kiyi feeding yarinyan nan tun muna mu biyu tun tun kafin ajimu dake" idanunta ne suka ciko da kwalla ta fara kokarin feeding babyn dan tasan ba karamin aikinshi bane idan tacikashi ya zaneta, ya gwammace daga baya yayita aikin rarrashinta.

Ganin tana kokarin saita bakin babyn yasashi taimaka mata, baby kamar jira take takama. Tayi saurin runtse ido hawayen dake makale a idanunta suka silalo ta saki kuka me sauti dama me neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki

Da mamaki yake kallonta ya Kamo hannunta, ya gimtse cikin nashi yana shafa bayan hannun ta da babban yatsanshi, yayi murmushi yace, "Wannan wace irin uwa ce haka, tana feeding babyn ta tana kuka, kina so tamiki dariya ne? Oh baby ke kam kin hadu da uwa keda ita naga me rarrashin wani".

Majinar kuka taja kan tace, "Ai ba haka mukayi da kai ba, nayima alkawarin zan haifama babyn ka, daga nan na gama aikina, amma yanzu kace ba haka ba......" ta kai karshen maganan tana karama kukanta sauti

Dariya sosai yayi, yakara matsawa ganganta kamar ze shige cikin ta ya sakala hannuwanshi daya ta bayanta daya ta gaba ya rungumeta ita da babyn tsam a kirjinshi. Bata zata ba taji saukar lips dinshi akan nata, tayi saurin wara fararen idanunta akan fuskarshi, idanunta ya sarkafe cikin nashi, su ka shiga kallon juna, hurt kisses yashiga aikamata dashi, ita ko se lumshe idanu tayi alamun sakonshi na kaiwa inda ake bukata, narke mishi tayi tana kokarin sakin baby shi kuwa se kara rungume su yake gudun ta sunbular da babyn.

Knocking kofar da akayi yasashi saurin sakinta yana kokarin daidaita nutsuwarshi, izinin shigowa yabada Aesha ta turo kofan tashigo bakinta dauke da sallama, hannunta rike da tray tazo ta ajiye kasa kusa da kafafunsu. Kallon Muhibbah dake feeding baby tana Jan majinar kuka tayi, suka hada idanu tayi dariya mara sauti gudun Fu'ad yajita ita kuma ta watsamata harara tana kwafa.

"Ummi tace ga abinci nan kici sosai bata so ki rage ko 1 spoon, kuma ki shirya yanzu zata zo ta miki wanka" ta karashe maganan tana kunshe dariyar ta

Ita ko se faman aikamata da harara take tana Jan majinar kuka.

Hannu ta kai zata Karbi babyn Fu'ad yace, "Kibarta tukunna bata koshi ba, kuje keda Suhailat ku hadomata kayanta dana baby, ki duba bedroom dinta akwai wayarta ki taho da ita" "Toh" abinda????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? tace kenan ta ta fice.

Kan kujera ta fada dariyar da take kunshewa ta kufcemata, Ummi tace, "Aesha menene haka? lafiyarki kuwa??" Seda ta tsagaita da dariyan tace, "Muhibbah ce ta bani dariya, Yaya yasata a gaba tana feeding baby tana kuka kamar wata karamar yarinya"

"Shine abin dariya?" "Allah Ummi abin ne akwai ban dariya, kinga yadda Yaya ya tsareta ne ita ko se wani turo baki take tana shasshekar kuka, ga baby ma batasan tanayi ba se shan nonon ta takeyi hankali kwance".

"Toh ke wayasan me zakiyi, ai garama Muhibbah dake" dariya tayi tace, "Haba dai Ummi nikam bazanyi shirmen Muhibbah ba, ai babyn mu ta hadu da uwa" ta Kai karshen maganan tana cigaba da dariyanta harda kwanciya.

Suhailat dake gefe tana dariya tace, "kema zaki aika, zakiyi ma abinda yafi na Muhibbah, ai duk autoci ne lamarinku se addu'a"

Saurin mikewa tayi ta dan zaro ido "Nashiga uku! Aunty Suhailat tashi muje kafin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login