Showing 45001 words to 48000 words out of 112768 words

Chapter 16 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

kamar tsuntsuwar da ta kubuto daga keji dan tun shekaran jiya da aka kawota ko compound din gidanta bata leko ba Kuma tun jiya dasu Aesha suka tafi babu Wanda takara gani se drivern da Ummi ta Aiko ya kawo break fast Shima me gadi ne ya karbo basket din, se Kuma Fu'ad Wanda da dawowanshi gidan da rashin shi duk daya tunda yana bedroom dinshi itama tana na???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ta Koda rana ita kadai a gidan kamar mayya idan tasoma Jin tsoro ta koma bedroom dinta ta kudundune a kan bed ta kunna kira'ar sheik Ahmad sulaiman a wayanta ta ajiye kan bed side drower. Yana yin parking ta balle murfin motan tayi cikin gidan da sauri tana murna................



*Aminiyar ango >?p?>?p?>?p?*
[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: =???=???=???=???=???=???
_*SOYAYYAR KWANA ?AYA*_
_BY_
_*FATIMA A MUHAMMAD*_
_AMINIYAR ANGONTA_
=???=???=???=???=???=???
_*TEAM*_
_*ZAFAFAN=?%?DAWA*_
_*JARIRIYAR DAWA*_
_________________________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
________________________

*Page 34*


*Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae*
*Sunada kaya kamar haka....*
*Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....*
*Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t shirt*
*Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted*
*Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And many more......*
*Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku rikitamu da orders please we will take paracetamol >??*
*Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye

=?G?=?G?=?G?=?G?=?G?=?G? https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t


Bakinta dauke da sallama tashiga parlourn, ganin bataga kowa ba ta nufa dakin Aesha a kwance ta sameta tana faman sheka dariya, har Muhibbahn ta matso kusanta bataji zuwanta ba

Hannu ta Kai ta zare wayan, a firgice ta dago ta Kalle Muhibbah suka sakarma juna murmushi "Laa sister yaushe kika shigo?" "Uhmmm ina Zakiji shigowa ta kina waya da abin kauna" "Ni nace miki da saurayina nake waya?".

"Oho koma dai waye idan tayi wari ma ji" ta Kai karshen maganan tana mika mata wayan.
"Bazama tayi warin ba"
Wayan ta kara a kunne sukayi sallama kana tayi hanging call din.
"School mate dina ne, senior na ne a school bakisan Yakub bane ko lokacin Muna school mutane dayawa na tinanin akwai alakar soyayya tsakaninmu kuma babu wata alakar data wuce ta friends tsakanina dashi".
Murmushi tayi tana girgiza Kai "Bazan tabbatar ba nima, lokaci ne ze tabbatarmun da gaskiyar abinda ke tsakaninku, amma Allah ya taimakeki kar a rabaki da abinda ki kafi kauna" tayi maganan tana rau rau da ido kamar zatayi kuka. Ajiyar zuciya tayi dan tasan inda ta dosa "kowa da kaddararshi Muhibbah duk yadda rayuwa ta zoma bawa toh ya bida ita a haka yayima Allah godiya"

Ka Kalo murmushi tayi tariko hannun ta "Muje kar Ummi tayi fushi da diyarta, banje bedroom din taba nayo nan".

A parlour suka tarar da a halin gidan guri tasamu ta zauna tace "Ummi ina wuni" tafada cikin sanyin jiki tana yin kasa da Kai, ji tayi tana masifar Jin kunyan ummin. "Lafiya kalau Muhibbah, ya bakon guri". Yatsun hannunta ta shiga wasa dasu batare da tace komai ba.

Dariya Ummi tayi "Aa wai yau ni Muhibbah ke Jin kunya" gyalenta ta janyo ta rufe fuska takasa cewa uffan.
Aesha tace "Ummi so take kice kinyi sa'ar sirika, alhalin munsan komai". Dukan wasa ta kaimata tana harararta.

Dakuwa Ummi tamata "Toh da banyi sa'ar sirikar bane, rabu da ita Muhibbah tasan ke ba irin ta bace mara Jin magana" gwalo tama Aesha tana dariya kasa kasa.
Shikam Fu'ad bazakace yana parlourn ba hankalinshi na kan wayarshi yana Jin abinda sukeyi amma ko dago Kai ya Kalla idan suke beyi ba bare ya nuna yaji abinda suke cewa.
"Aunty Asma'u yaushe zaki koma gida?". "Yau naso na tafi Aunty Maiminatu ta dinga Jana da fira ta hanani tafiya kinga ita dazun nan tayi tafiyanta gidanta, Suhailat ma mijinta yazo ya dauketa sun barni ni kadai, Amma gobe da wuri zan tafi in Sha Allah" "Eyyyaaa big brother fa ko shima ya tafi ne?". Aesha tace "Ya Suhail ai tun jiya ya tafi daddy nata kiranshi aiki yamai yawa". "Allah sarki Mummy na Aunty Asma'u goben ki biyo mu tafi please" Saurin dagowa yayi ya kalleta kawai idanun su ya sarke dana juna hawayen dake kwance a idanunta suka silalo, wani siririn tsaki yaja ya mai da kanshi ga abinda yakeyi.

Dariya sukayi gaba dayansu Aunty Asma'u tace "Sannu Muhibbah toh se kin dawo" Ummi tace "Ashe dai keda Aesha duk tafiyarku guda wajen shirme, Amma gaki ga mijin naki a gefe idan ya yarda toh se kin dawo" ta karashe maganan da zolaya.
Aesha tace "Ummi kyaleta zanma rakata air port idan kinje wata nawa zakiyi ki dawo" tayi maganan tana dariyar mugunta.
Harara ta watsamata tana Shirin yin magana Abba ya kutso kanshi parlourn bakinshi dauke da sallama duk suka amsa ya nemi guri ya zauna suka shiga mai sannu da zuwa.

Se yanzu Fu'ad ya dago yama Abba sannu da zuwa tare da gaisheshi ya amsa cikin kulawa.

"Abba ina wuni" "lafiya kalau maamana, ya bakunta?" Kasa tayi da kanta gaba daya se taji kamar ta nitse a kasa kunyan Abban yakamata.

Ummi tace "Alhaji munfa zama sirikan Muhibbah yanzu kunyarmu take ji"
Na lura da haka tunda har na shigo Muhibbah Bata zo da gudu ta tarbeni ba, Zo nan ki zauna kusa dani maamana ni ba sirikin ki bane Abbanki ne ni har yanzu, kin ji ko?". "Kai kawai ta gyada tana zama gefenshi inda ya nuna mata, Allah yasani gaba daya kunyarshi shida Ummi takeji gani take kamar zasuyi tinanin ko wani abu yashiga tsakaninta da ya Fu'ad alhalin Kuma ko maganan minti daya be hadasu ba.

Tashi Abba yayi ya nufa dakinshi seda ya watsa ruwa ya shirya kana suka tafi masallaci da Fu'ad da Ammaar basu dawo gidan ba seda akayi isha'i.
Duk mutanen gidan dining suka hallara domin yin dinner, ita dai Muhibbah cakulan abincin kawai take har yanzu bata dawomata kamar baya ba kawai addu'a take Allah yasanya yamata zuciyarta "Aunty Muhibbah ya bakyacin abincin" Taji muryar Ammar na mata magana.Dan zaro ido tayi "Kai ya Ammar wane irin Aunty" tafada tana rufe fuska.
"Ehmana kefa yanzu duk family nan kece babba girma ya kamaki tunda kina auren babban Yaya".
Hada ido yayi da Fu'ad ya watsa mishi wata uwar harara dinke bakinshi yayi be kara cewa komai ba.

Abba yace "Idan kun gama dinner a sameni a parlour" yafada yana mikewa.

Mutanen gidan gaba daya sun hallara parlourn Abba Fu'ad da Muhibbah zaune gaban Abba da Ummi, Abba yafara nasiha "Fu'ad ga Maamana nan a matsayi na daban a gurinka kai ne babba Kuma Kaine namiji ka kasance me adalci ga iyalanka kayi kokarin sauke hakkinsu ka kyautata musu Allah seya kara budama, ban yarda da duka ba idan wani laifi tama daya gagara ku sulhunta a tsakaninku toh kasanar dani amma idan naji labarin duka zanbatama rai fiye da tinaninka" seda yaja fasali kan yace "Fatima" Saurin dago kanta tayi ta kalleshi da jajayen idanunta da suka rine tsabar kuka Jin ya kira sunanta Kai tsaye tasan maganar daze mata me Muhimmanci ce dan ko Muhibbah baya kiranta dashi bare Fateema "Na'am Abba" ta amsa da dasashirya muryarta data dishe tsabar kuka "Gaki ga yayanki matsayin mata da miji kiyi mishi biyayya kiyi kokari ki sauke duk wani hakki da Allah ya doramiki kisani aljannar ki na karkashin kafan mijinki dan haka ki bishi, idan har yayi miki laifi kisanar dani zanyi kokarin ganin komai ya dai daita, Allah ya muku albarka yabaku zaman lafiya Allah yasa muyi alfahari da ku".

Ummi ce ta juyo garesu "Muhibbah zan fara da cewa kiyi hakuri domin shi zaman aure dan hakuri ne har yau har gobe muma iyayenku hakuri muke matukar kikasa hakuri a zaman aurenki toh zaki zauna lafiya da mijinki amma akasin haka Koda yaushe za'a dinga Jin kanku, karki kasance me yawan Kai kara domin mu da kuke kawomana kara zamu gaji sannan Kuma zaku manta da wani abu ya hadaku amma mu munanan rike dashi, kizama me kula da dukiyar miji banda almubazaranci kidinga tattala kayan miji, kizama me biyayya ga mijinki indai kika dauki halayen mahaifiyar ki mijinki baze taba kuka dake be, domin mummynku mace ce me hakuri da kauda Kai da tsananin biyayya, ki zauna lafiya a gidanki Allah ya albarkaci aurenku yabaku zuri'a dayyiba".
Hannu Muhibbah takama ta damka a hannun Fu'ad, wani shork sukaji a tare suka dago idanunsu ya sarke dana juna kasa tayi da kanta tana shasshekar kuka, Ummi tace "Ga Amanar Muhibbah a yanzu bata da Wanda yafika kusanci da ita, banda duka matsayinta na yanzu ya banbanta dana baya, ka kula da hakkin matarka kar inji kar in gani Allah yamuku albarka yama aurenku albarka yabaku zuri'a dayyiba".
Gaba daya kowa jikinshi yayi sanyi sautin kukan Muhibbah kawai ke tashi

"Fu'ad ku tashi ku tafi dare yayi" Jin jina Kai yayi ya mike rike da hannunta yana musu godiya kafin yamusu seda safe.

Seda yazo shiga motan ya sake hannunta ya zagaya yashiga itama tabi dayan bangaren tashiga ya yaja motar yafice daga gidan. Babu abinda ke tashi a motan se sautin kukanta, waigowa yayi ya dan kalleta tayi saurin rage sautin kukanta, Jin kukan na hawa mai kai ya gangara gefen titi yayi parking ya juyo yatsareta da birkitattun idanunshi masu tsoratata "Will you shut up! Kinyimun shiru ko sena saukeki anan" hannu tasa ta toshe bakinta dan tasan ba karamin aikinshi bane yabarta nan din tunda ya furta gashi sunyi nisa da gidan Abba.

Dogon tsaki yaja ya koma kan titi ya ja motar suka dau hanyan gida........[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: =???=???=???=???=???=???
_*SOYAYYAR KWANA ?AYA*_
_BY_
_*FATIMA A MUHAMMAD*_
_AMINIYAR ANGONTA_
=???=???=???=???=???=???
_*TEAM*_
_*ZAFAFAN=?%?DAWA*_
_*JARIRIYAR DAWA*_
_________________________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
________________________

*Page 35*


*Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae*
*Sunada kaya kamar haka....*
*Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....*
*Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t shirt*
*Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted*
*Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And many more......*
*Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku rikitamu da orders please we will take paracetamol >??*
*Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye

=?G?=?G?=?G?=?G?=?G?=?G? https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t



Suna isa gida kowa yayi dakinshi, towel ta daura tashiga toilet wanka tayi ta fito ta shirya cikin kayan bacci ta haye bed, wayanta ta janyo tashiga watsapp suka hau chatting da Aesha seda taji idonta tsabar bacci kafin tama Aesha seda safe ta kashe datan ta kwanta batafi 5 minutes ba bacci me nauyi yayi awon gaba da ita.

Yana shiga dakinshi wanka yayi ya zauna a gefen bed ya janyo karamin center table dake dakin ya daura system dinshi a Kai yafara aiki seda yaga yaci karfin aikin kana ya kashe system din ya kwanta.

10 minutes after 7 ta tashi kafafunta ta ziro kasa tasa takalmi tashiga toilet ta wanke fuska ta nufa kitchen, dube dube tashiga yi a kitchen din komai a jere gwanin sha'awa takai hannu ta bude freezer taganshi cike da kayan bukatun girki kamar dama tun can akwai mutane a gidan duk abinda take bukata akwaishi cikin freezern

Kaza ta dauko ta wanke tasa a tukunya ta daura akan gas ta zuba garlic, citta, cloves, seasoning and spicy ta rufe tukunyan ta koma upstairs ta fara gyara dakinta seda ta gyarashi tsaf kana ta sauko daga stairs ta gyara parlourn kasan ta fesa room freshener ta kunna turarukan wuta parlourn ya dauki kamshin dadi.

Koda ta koma kitchen din tasamu har kazar ta nuna ta kashe gas din ta sauke tukunyan, bowl ta dauko ta cire naman daga roman ta zuba man gyada a pan ta Dora a gas tafara soya Kazan, seda tagama suyan, tayi grating kayan Miya sannan ta dora karamin tukunya a gas ta zuba man gyada, sannan ta zuba kayan miyan ta kawo spicy da seasoning ta zuba ta yanka albasa me dan yawa ta zuba ciki ta kawo soyayyen Kazan ta zuba ta dauko roman ta zuba kadan ta juya kana takawo murfi ta rufe pot din 5 minutes ta bashi sannan ta kashe gas din.

Irish potatoe ta dibo ta fere ta yayyankashi a tsa tsaye ta fasa kwai a bowl ta shiga tsomashi cikin kwai tana soyawa, ta zuba a wata hadaddiyar food flask ta shirya dining din, ta nufa dakinta.

Wanka tayi ta shirya cikin atampha dinkin borno style straight skirt se riga iya guiwa taji stones ta feshe jikinta da turare ta nufo parlourn se zuba kamshi take.

A dining ta sameshi a zaune yana danna wayanshi, lallaima mutumin nan ni kake zaman jiran na zuba ma abinci to da ban girka ba fa tayi maganar a cikin ranta, wata zuciya tace mata da bakiyi ba ai da se kisan abinda zaki fada mai ya hanaki yin breakfast din.

Karasawa dining din tayi daf dashi ta tsaya tace "Ina kwana" "Lafiya" ya amsa da kalma daya batare da ya dago ya kalleta ba

Plate ta dauka ta shiga zuba mishi soyayyan potatoe da chicken pepper soup ta ajiye a gabanshi ta dauko wani plate din tayi serving kanta taja kujera tazauna tashiga cin abincin takasan ido yake kallon yadda take cin abincin a natse cikin sanyin jiki, yana Kai abincin baki ya dan dago Kai ya kalleta suka hada ido ji tayi gabanta ya yanke ya fadi ta rasa dalilin dayasa duk lokacin da zasu hada ido se gabanta ya fadi

Dauke idonshi yayi daga kallonta ya dan ja siririn tsaki ya cigaba da cin abincin shi, yana gamawa ya mike ya fice daga parlourn batareda yace mata uffan ba

Mikewa tayi ta tsaya jikin window parlourn seda taga yaja motarshi ya fice kana ta girgiza Kai, yaushe za'a hada wannan me fadin ran da Mukhtar ina bazasu taba haduwa ba ma, tattare kayan tayi ta Kai kitchen ta wanke kayan da aka bata ta maida ko wanne mazauninshi.

Handle din kofan ta kama se tazo zata murda seta fasa babu abinda kirjinta yake se bugawa gani take idan tashiga dakin zata ganshi a ciki ko Kuma yazo ya ritsata a ciki, shahada tayi ta murda handle din kofar ta shiga kamshin turarenshi na mufaddal ne ya daki hancinta ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, dakin tsaf tsaf Shima babba ne girman su kusan daya dana ta furnitures din dakin white colour hatta curtains din dakin white, bed sheet ta canza mai ta gyara dakin duk da ba wani dirty yayi ba ta dauko burner ta jona tasa turare ta fesa room freshener kana ta kullo dakin ta fito

Bed dinta ta fada tashiga chatting Aesha ke bata labarin tasamu admission a (AUN) Apti American university.
"Nifa?" "Toh gaskiya banji Abba ma yayi maganan school dinki ba.

Saurin mikewa tayi daga kwanciyar da take, Jin maganan ta watsapp baze mata ba yasa tashiga dialing numbern Aesha, Ringing biyu ta dauka "Hello! Matar Yaya" "kina nufin Abba ko maganan school din nawa bayayi?" "Eh gaskiya banji yayi maganan school dinki ba nadaiji yana cewa ya Fu'ad ze neman miki school din da yake so" Bata barima ta kai karshen maganan ba ta kashe wayan

Numbern Abba ta shiga dialing be dagaba seda ya tsinke kafin ya biyo call din tana dauka tasa mai kuka, hankalinshi ne ya tashi "Maamana lafiya?, me ke damunki?, yayanki ne ya miki wani abu? Ko dukanki yayi?". Ya jero mata tambayan a kidime

"Abba Aesha tace "ansama mata admission" amma wai banda ni" ta Kai karshen maganan tana shasshekar kuka
"Toh miye abin kuka anan, kema za'a sama miki in Sha Allah, Amma kiyima yayanki magana seya nema miki a school din da ya mishi" "Abba nafi son school din da Aesha tasamu" "Kima yayanki magana idan hakan ya mishi shikenan" yana Kai nan ya kashe wayan, yasan ko yasama mata admission a (AUN) ba lallai Fu'ad ya barta taje school din ba ze iya cewa gara yasama mata school a nan jimeta.

Kuka taciga da yi Allah yasani bazata iya ma fu'ad magana ba tsoro takeji gashi bata da numbernshi bare kota text message ne ta tura
mai sako, seda taji kiran sallah kana ta mike ta shiga toilet ta dauro alwala ta zo ta gabatar da sallahn azuhur.

Qur'an ta dauko ta karanta ta dan kwanta tayi bacci seda tayi la'asar kana ta sauko kasa, karfe biyar tashiga kitchen tafara Shirin dora dinner.

Kasancewar tasan baya cin abinci me nauyi da dadare yasa ta shiga shirya soyayyiyar taliya

Nikakken naman kaza ta dauko bowl ta zuba aciki kawo spices da kayan Miya ta zuba tayi mixing dinsu tazo tayi moulding dinshi tasa a oven kafin ya gasu ta dauko tukunya ta daura a gas ta zuba ruwa takawo gishiri da man gyada ta zuba ta rufe seda ruwan ya tafasa kana ta zuba taliya ta barshi ya tafasa for 8 minutes sannan ta juyeshi a basket.

Pot ta maida kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login