Showing 63001 words to 66000 words out of 112768 words

Chapter 22 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

sukayi jajir ji yake zuciyarshi namishi mugun zafi.

Mikewa yayi ze bar gurin tasaki kuka tareda mikewa da sauri a dan tsorace ta riko hannayenshi "Yaya a idanunka ina iya hango tsantsar bacin rai da tarin damuwa nasan kuma duk nice silar faruwan hakan, nasani banyi ma adalci ba amma nayima alkawarin gyarawa kar ka kwanta kana fushi dani kar kabarni na kwana cikin fushin ubangiji karkashin ka nake kanada iko da ni da duk wani abu da ya shafeni, kanada ikon yanke mun ko wane irin hukunci wllhi a shirye nake na karba hannu bibbiyu ni din mallakin kace se yadda kaso kayi dani nasani na cutar da kai nayima laifi sannan daga karshe kai Abba ya daurama laifi kuma bakayi yunkurin fadar laifin da nayima ba, yaya dan Allah ka mareni idan har marina zesa kaji sanyi a zuciyarka amma kar ka cigaba da fushi dani" kuka take sosai kamar zata shide, bata tsanmaci zeyi magana ba se tsinkayan muryarshi tayi

"Muje ki kwanta". Be kuma maganaba yaja hannunta suka haura sama, a kofar dakinta ya saki hannunta "Seda safe" seda taja majinar kuka kafin tace "Allah yatashemu lafiya".

Bece komai ba ya shige dakinshi ya kullo ta jima tana kallon kofar dakin kan ta shiga nata taje toilet tayi alwala tazo ta kwanta tana faman sauke ajiyar zuciya ajere ajere.

Da safe kusan tare suka fito "ina kwana" "kintashi lafiya?" "Alhamdulillah & you" "normal" ya fada yana dagemata gira daya.

Dukar da kai kasa tayi ta karasa dining tayi serving dinshi.

Shiru babu wanda yayi magana har suka kammala breakfast din ficewa yayi daga parlourn tabi bayanshi karo sukayi da mairo suka gaisa kan ta karasa ta shiga motan yaja suka fice daga gidan

Har suka isa bakin gate babu Wanda yace uffan se sautin karatu kawai dake tashi.

Kudi ya ciro ya ajiyemata kan cinya ta dan kalleshi taga ita yake kallo ta kai hannu ta dauka "thank you". Ta fada tana ficewa.

Jan motan yayi yabar arean.

Hakanan take Jin mood din yamata dadi har tashiga school din tana murmushi a lokaci daya kuma tana mamakin hali irin na Fu'ad idan ya hade rai zaka rantse be San wani abu dariya ba daka kalleshi se ka tsorata bata son suke hada ido dan duk lokacin daxa su hada idanu se gabanta ya fadi. Amma yau kamar bashiba duk da ba dariya yake ba amma fuskarshi ba'a hade kamar ko yaushe ba har tantama take akan gaske shi din ne yau ya sake mata kodai mafarki take.

Sun jima sosai a class dan se 4 suka fito cafeteria suka nufa su hudu Aesha, Muhibbah, Umaina da Kuma Ramlat seda suka siyo snacks da drink kana suka dawo suka zauna sunaci suna fira can Ramlat ta dan kalli Aesha "Wai ni in tambayeki gidanku ba daya bane da Fateema?"

Dan kallanta tayi kamar bazatayi magana ba "gida daya muke mana me kika gani?" "Aa babu komai kawai dai naga ba tare kuke zuwa bane" "kawai duk Wanda ya riga shiryawa ne Abba ke saukeshi a school wanda Kuma be shirya da wuri ba driver ke kawoshi shiyasa kikaga bama zuwa a tare".

Umaina tace "Kiji Ramlat da wata magana gidansu daya mana last week naje gidansu ai karki so kiga kirkin Ummi".

"Toh daga tambaya shine nayi laifi, ai matambayi be bata ba gashi yanzu an fahimtar dani sosai ba, Allah sarki Aesha ki gaisharmun da Ummin" "zataji, mungode"

Ita dai Muhibbah tana gefe bata ce musu kala ba.

"Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuh" saurin daga kai sukayi suka kalla inda sukaji sallaman ganin malam mukhtasir tsaye yasa su danyin murmushi suka shiga gaishe shi ya amsa hankalinshi na kan Muhibbah

Ita ko tayi kasa da kanta tana operating phone dinta ko dagowa ta kalleshi batayi ba bare yasa ran zata tankashi.

Ta gefen da take zaune ya dan matsa "Barka da rana hajiya" dan dagowa tayi ta kalleshi "Barka dai Ina wuni" "lafiya kalau, Fateema kwana biyu?" "Se alkhaeri".

"Kin buya kwata kwata bamu hadu ba fatan dai kina lafiya" "Kasan lafiya ita ke buya" ta fada a takaice.
Kai ya Jinjina "Ina alkawari na?" Dan Jim tayi kamar me tinani kan can tace "oh Allah sarki se yanzu na tina, gashi wayan Ummin ma ya dan samu matsala ya baci". ta Kai karshe tana mika ma Umaina wayan hannunta

"Umaina rike wayanki na kirata yaki shiga shine kawai na turama message ta watsapp"

"Kuma kinyi dubara dan maybe ba network ne inda take tunda bata kashe wayanta amma tunda message din ya tafi zata yi reply"

"Toh Allah yasa tayi reply dawuri, kinga idan kika tafi bazan San amsar data dawomun dashi ba ga wayan ummi ya lalace bare ki kira ki fadamun duk abinda tace"

"In Sha Allah ma kafin mu tafi zakiga tayi miki reply kinsanta 24 hours tana online"

"Haka ne Kam".

Ganin tsayuwar baze yi mai ba "Se idan Allah ya kaimu gobe" abinda ya fada kenan yabar gurin jiki a sabule.

Yana tafiya suka tafa da Umaina suna shekewa da dariya "Kai Umaina ya akayi kika gane abinda nake nufi dawuri haka?" Dariya tayi "Ai tunda naga kin mikomun wayanki Kuma naji kina cewa wayan Ummi ya lalace na dau haske" "kyale dan anaci zemayi ya bari ne ayi mutum ba zuciya bani wayata mu tafi".

Ramlat ta dubesu "Wasu mazan fa akwai nacin jaraba base an fito an ce ba'a sonka ba a alamu zaka gane".

"Hmmmm kedai bari kawai Ramlat zan seta mishi hanya daga yanzu yaga ina tankashi ne baze jazamun bala'i ba in ke daukarwa kaina zunubi". Aesha tayi saurin taran numfashinta "Wallahi sister nima abinda nake tinani kenan kar ubangiji ya kamaki kuma wllhi ina tsoron ranan da ya Fu'ad ze sani mun Kade bake kadai abin ze shafa ba harda ni ke hatta su Ramlat bazasu tsira ba sedai idan basa gurin amma wllhi se yamana bugun sakwaran lagos" duk dariya sukasa harda rike ciki Muhibbah ko kawai hasaso irin shakar da ze mata take se ta gwanmacin marin da yamata akan mukhtar sau dari kan ukuban daze mata idan tasake yaji labarin nan.

"Toh shi haka ya Fu'ad din yake da zafi, baya so ku kula kowa"

"Bazaki gane yaran bane, shi baya so muke kula samari barkatai yace har yanzu mu yara ne bamu isa aure ba".

Da sauri Umaina ta tari numfashin ta
"Amma dai duk da haka Aesha ki kalla yadda fateema kema sauban wulakanci har gara malam mukhtasir yasa mu arzikin magana amma shi kam bawan Allahn nan ko muryarta be taba jiba har saki tayi kika cemai wai tanada aure se jiya ya tareni yake tambayata dagaske ne kinada aure, dole namai karya nace eh nima bansan kinada aure ba seda naje gidanki saboda dai ya hakura ya dau dangana ko zuciyarshi zata samu salama babu kyau irin abin nan baki ga yadda jikin bawan Allahn nan yayi sanyi ba nan nabarshi tsaye gwanin tausayi, wai kina cewa ubangiji ze kamaki kiji wata magana naga fa".

Dogon tsaki taja "toh kema naga macece ki aure su mana, shikuma sauban yake kowa dama ya tambayeki kin kara tabbatar mishk inada aure amma dazu da safe dana shigo school ya biyoni har bakin department dinmu yanamun magana naki kulashi ya gaji ya juya tsabar be san abinda yakeyi ba"
"Maida wukar kawata abun bana fada bane gani nayi bashida wani aibi Kuma bacewa nayi ki kulashi ba se yaje yasamu ya Fu'ad din idan yayi bincike akanshi yaga yayi shikenan, amma tunda bakya son maganan in Sha Allah bazan kara ba".

Daganan suka ajiye zancen suka dauko wani firan.

Bakinta dauke da sallama tashiga parlourn a zaune tasamu mairo tana kallon MBC Bollywood da fara'arta ta zauna kusa da ita "Sannu da gida Aunty mairo, ko kefa ba gashi kin samu abin debe kewa ba amma seki zauna shiru" "Yauwa hajiya sannu da dawowa, ya makarantan" "Makaranta ba dadi ba damar bari".

Dariya tayi tana mikewa, kitchen taje ta kawomata abinci da ruwa tajanyo center table din dake parlourn ta ajiye a kai.

"Kai ai da kin bari na tashi na zubo da kaina sannu da kokari nagode"

Ganin sun gama film din ta kai hannu ta dauki Remote ta canza channel din MBC 3 "Yi hakuri Aunty bari na dan Kalli cartoon dan ni bana gane kallon film sama da cartoon"

Murmushi tayi "Bari na tafi" "Se ana fira kice zaki wuce" "Yamma tayi kuma yanzu zakiga mijinki yadawo"

Dariya tayi sosai "Oh kice Yaya kike gudu bakya so ku hadu" murmusawa tayi sukayi sallama.

Seda tagama cin abincin kan ta haura dakin ta ta ajiye jaka da hijjab din ta ta nufa kitchen ta hada dinner ta shirya dining ta je tayi wanka ta dawo parlourn ta hakimce ta cigaba da kallon cartoon dinta hankali kwance.

Da sallama iya kan lips dinshi ya shigo kamshin turarenshi ya sanar da ita dawowan shi.

Mikewa tayi ta karasa ganganshi a dan tsorace take amma ta daure "Sannu da dawowa" "Yauwa" ya fada yana Kallon ta itama shi take kallo kawai ta tsinci kanta da sakin murmushi.

Shima murmushin gefen baki ya mata seta lumshe ido gani take kamar a film. Karbar ban brief case din hannunshi tayi suka fara takawa a tare har dakinshi ganin yafara kokarin cire kayan jikinshi ta ajiye brief case din ta fito ta rufo mai kofa.

Wanka yayi ya zira jallabiya sauri sauri ya fice ya nufa masallaci.

Itama dakinta ta haura tayi sallah seda tayi isha'i ta fito tana zama yana shigowa.

Seda yagama dinner ya koma parlour ya fara aiki a wayanshi a kujeran dake facing dinshi ta zauna ta dauki wayan ta ta fara chatting da Aesha tana kwatanta mata ukubar da ya Fu'ad ze musu idan yasan malam mukhtasir na kula ta.

"Sister kinga nidai shawarar da zan baki kifara sanarma Yaya da kanki tun kafin ya gane da kanshi" "Waa rufamun asiri so kike gobe da safe a zo a dauki gawata sedai idan ke zaki fada mai kinga a gaban Ummi baze miki komai ba" "Sannu muguwa ke dakike matarshi kina jin tsoro se niii, ai wllhi ko gaban Abba ne sedai idan ban mai laifi ba dukana yakeyi".

"Keeeee hadomun coffee" seda safe tama Aesha ta ajiye wayan ta shiga kitchen.

Bata jima ba ta dawo rike da cup waya ta hangi yanayi dan zaro ido tayi Jin sautin kuka na tashi daga cikin wayan, indai kunnenta ba karya yake fadamata ba muryar mace takeji tana kuka "Dan Allah doctor ka saurareni sonka na neman kaini lahira, wllhi ni ko baka sona indai zaka aureni zan zauna dakai a haka" "Ba kisan inada aure bane?".

"Kar kadamu ni wllhi ko mata 3 gareka zanzo ata hudu" duk da tayi mamakin Jin yanada aure bata taba Jin labarin aurenshi ba ko a social media bata tinanin ko nurses din dake aiki a asibitinshi sun san yayi aure, wata zuciyarta Kuma na kokwanto akan auren kodai kawai ya fada ne.

Jin yayi shiru tace "Dan Allah yaushe zaka shigo ka gaida Ammi kullum ina bata labarinka" ganin Muhibbah tsaye tana kallonshi ya saki murmushin gefen baki "Ki ajiyemun address dinki zuwa gobe idan Allah ya kaemu zan shigo".

"Thank you" "It's my pleasure" yana kai nan ya yanke wayan.

Bata ankara ba taji glass cup din hannunta ya kufce ya fadi kasa seji kake tuusss ya fashe, dasauri ta matsa baya a tsorace ganin kallon dayake mata takun da zatayi se ji tayi ta taka fasashen glass din ta ko saki razananniyar karaaaaa tayi baya zata fadi yakarasa da hanzari ya tarota ta fado jikinshi yasa hannu ya rungumeta a kirjinshi........



*>?p? Aminiyar ango >?p?*
[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*

*FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)*

*Page 44*




Tana ajiye wayan tayi wani uban tsalle ta rungume Rumaisa "Sister yau rana daya Dr Fu'ad ya saurareni, shekara nawa ina binshi babu irin rokon da banyi mai ba ko sau daya yazo inda nake amma yaki gashi yau shi yake cewa na turami address dina nakasa yarda mafarki ne ko gaske" takarasa maganan tana fadawa gadon cike da farin ciki

"Dama Aunty zee bana fadamiki ba don't give up, addu'a babu abinda ta bari gashi yanzu kin fara ganin haske"

"Wllhi nayarda Allah maji rokon bayinsa ne, haka nake faman tsayuwan dare akan bawan Allahn nan amma sena mishi 20 missed calls beyi picking ba sena jera 1 month ina Kiran wayanshi befi yayi picking sau daya ba, har asibiti nakan je a hanani shiga office dinshi se an sanar mai da nice wani lokacin yace kar abarni shiga wani lokacin Kuma yace nashiga amma Kona shiga daga amsa gaisuwata baya kara cewa uffan har nagama surutuna na karaci zamana na tashi, addu'ar nake amma kullum jiya I yau har na soma gajiya ashe ubangiji na sane dani"

"Sedai abinda yaso ya kashemun guiwa wai yanada aure, Kuma ni bantaba Jin labarin aurenshi ba ko a social media ban taba ganin ya dora ba" takarashe maganan kamar zata saki kuka.

"Dama haka Allah ke lamarinshi addu'a bata fadi kasa banza wani lokacin Allah yana jinkirtamana kafin ya amsa wani lokacin Kuma da munyi a take ze amsa mana wani lokacin ma se ya hanamu abinda muke roka ya canzamana da mafi alkhaeri, Toh Aunty zee ma banda abinki menene dan yanada mata kedai ba burinki ki mallakeshi ba gashi kuma kin fara dauko hanyan samun matsuguni a zuciyarshi ki maida hankali wajen ganin yazama mallakin ki, bare ma nafi tinanin kawai yafada ne yaji abinda zakice amma bashida wata matar".

"Rumaisa kenan bakisan yadda nake kaunar gayen nan bane, ina mugun kishin shi fiye da tinaninki ni kaina ina mamakin kaina, fatana dai Allah yasa abinda ya fadamun ba gaskiya bane"

"Kema Aunty ki bar maganan wata matarshi kiyi focusing akan yadda zaki sace zuciyarshi koda yana da matar kisan yadda za'ayi yaji kece on top azuciyarshi, kawo kunnenki kiji"

Kasa kasa tayi mata magana, hannu tabata suka tafa "Kai kanwata kanki naja, Gobe akwai cire wanka"

"Toh idan Abba ya ganshi fa ya zakiyi?"
"Ni ai zanso ma suyi 4 eyes da Abba ayita ta kare"

"Kai Aunty zeeee ke Kam bakida dama" tafawa sukayi suna kwashewa da dariya.

***************

Runtse idanunta tayi tana jira kawai tajita a kasa, Jin tafada kirjinshi yasa ta saurin bude idanu karaf suka fada cikin kwayan idanunshi, kallonshi tayi na seconds kan ta kawar da kanta zuciyarta na tsalle a tsorace tace "I'm sorry wllhi bansaniba ne cup din ya fadi ya fashe, Allah yasama ruwan zafin be zubanma a jiki ba"

Murmushi ya danyi

"Duk kishin ne haka matar Yaya?" Dasauri ta juyo ta kalleshi gabanta na faduwa Jin yakira ta da matar Yaya, kar dai dama yanajin sunan da su Aesha ke kiranta dashi.

"Kishi Kuma mezanyi ma kishi?"
"Ga kishi nan ya bayyana karara a kwayar idanunki, budurwata kike kishi?"

Kuka me sauti ta saki tana kokarin raba jikinta danashi, kara kamkameta yayi yadda bazata iya kwacewa ba

"Wayyo Allah mummy na kafata zata cire na shiga ukuna innalillahi wa inna ilaehi raji'un......"
Kuka take sosai kamar wacce aka cire ma kafar gaba daya.

Dariya taso bashi ya waske shidai yasan wannan kukan ba iya na jin zafin ciwo bane.

Kacho Kam ya dagata ya nufa bedroom dinshi da ita, a bakin bed ya ajiyeta ya juya ya fice

Fasashen glass din ya tattare ya zuba a dust bin ya goge jinin gurin kana ya dauki first aid box ya haura dakinshi.

Har lokacin kuka take ya karasa ganganta yasa guiwowinshi a kasa ya Kamo kafan ya dora akan cinyarshi yafara yimata dressing Jin ya dangwali spirit a jikin cotton yafara gogemata ciwon takwallara kara tanayin baya baya ta kwanta kan gadon

Rike kafar yayi Kam tana kuka amma yaki sakinta har seda ya gama yimata dressing din.

A hankali ya sauke kafara kasa "Raguwa kawai" ya fada yana daukar box din ya fice.

Kitchen ya maida box din ya dawo, gefenta ya kwanta yasa hannu ya dan ja hancinta "Wai duk wannan kishin na miye daga Jin ina waya da matar da zan aura kika rude kika saki cup ya fashe gashi har kinjima kanki ciwo" saurin bude idanunta da suke a lumshe tayi Jin yace tana kishi, Rai a bace tafara magana "Toh ni meze sa nayi kishi, ina ruwana da budurwarka" iya gaskiyarta take fadan ita ba kishin da takeyi akan mema zatayi kishin shi.

Janyota jikinshi yayi ya rungumeta tsam ya Kai bakinshi saitin kunnenta "Nidai nafada miki ki rage wannan kishin naki dan soon zan kawo miki abokiyar zama, stress namiki yawa ga school ga girki ga kula dani ai seki rame kisa Ummin ki tace bana kula dake yadda yakamata, kinga idan na kawo miki abokiyar zama zaki dinga hutawa na kwana biyu, ko ya kika ce" ya Kai karshen maganan yana dage mata gira daya.

Kokarin mikewa ta fara yakara matseta sosai a jikinshi.

"Ina zaki haka kike Shirin mikewa?"

"Ni kasakeni na tafi daki bacci nakeji"
Tafada kwalar dake kwance a idanunta na silalowa.

"Nan a daji kike?"
"Ni dakina nake so ka maidani"
"Uhmmm uhmmm nikuma a dakina nake so ki kwana" yayi maganan yana kwaikwayonta.

Kuka ta shiga rera mai ya birkitata tadawo tana kallan ceiling yamata runfa da faffadan kirjinshi, tsoranta ne ya ninku zuciyarta na tsittsinkewa tashiga girgiza mai kai ta bude baki zata fara rokonshi ya hade bakinsu a zafafe ya fara kissing dinta yana yawo da hannunshi a jikinta ya mutsa gashin kanta yashigayi ita ko se kokarin kwacewa take.

Dayan hannunshi yasa yarike kugunta ya fara shafa daga wuyanta zuwa hannayenta lumshe idonta tayi hawaye na gangarowa Jin canjin feeling ajikinta yasa tasa hannayenta ta rungumeshi.

Seda ya kashe mata jiki kan ya mirgina ya kwanta gefenta tareda janyota yayi tighting dinta a Kan kirjinshi yana maida numfashi a hankali basu motsa daga gurin ba har bacci yayi awan gaba dasu.

Shi ya fara farkawa ya kai hannu ya janyo wayarshi yaga 5:00am a hankali ya janyeta daga jikinshi ya kwantar da ita kan pillow ya nufa toilet yayi wanka tare da dauro alwala ya fito ya shinfida pray mat ya zauna yayi karatun alqur'an na 15 minutes kan ya mike yayi raka'atanil fajr.

Kusa da ita ya karasa ya duka ya hura mata iska a fuska a hankali ta fara bude ido

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login