Showing 6001 words to 9000 words out of 112768 words

Chapter 3 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

da maganar fuskarshi dauke da fara'a da kaganshi kasan yana cikin farin ciki babu abinda zancema Allah se godiya abinda yasa muka taraku anan ba wani abu bane face Muna so mu sanar daku cewa mun tsaeda ranar auren Fu'ad da muhibbah domin idan akwae me wani shirin ya soma dasauri ta dago cike da mamaki tasauke idonta akan Fu'ad shima ita yake kallo da mamaki ji tayi maganar ta daki dodon kunnenta ya yimata nauyi a kirjinta duniyar tayi mata duuuum komae yatsayamata cak.............[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*


*FATIMA A MUHAMAMMAD (Aminiyar ango)*



*DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION*


Dedicated to *my lovely brother*



*Nasadaukar da ragowar pages din nan xuwa ga Abban Fateema Kuma angon Fateema har gaban gobe ana kyawun tare*



*Page 7*


"Kuka ta fashe dashi tana girgiza kae tana fadin wllhi daddy bana sonshi bazan iya aurenshi ba nashiga uku na da kallo Suka bita abin har yaso yabasu tsoro yadda take kuka tana fadin Bata sonshi"




Shiru dakin ya dauka se sautin kukan ta dake tashi Abba ne ya mike ya nufeta ya rikota ya mikar da ita tareda zaunar da ita akan kujera


"Yi shiru mana mamana kukan ya isa haka nutsu ki fadamun me yayan naki yamiki da bakya sonshi fadamun inji idan laefi yamiki da kaena zan hukuntashi a gabanki ki gani, A jiyar zuciya tasauke tana goge hawayenta tace Abba ni bana son ya Fu'ad mugu ne baya sakin fuska ko dariya seya ga dama yakeyi lokacin da ya zauna a gidan nan harda belt yake dukana ni natsa neshi ma kwata kwata gara ko almajiri ne a aura mun Kuma ma inada wanda nake so dan Allah Abba Kar ku auramun ya Fu'ad ta karashe tana kallon Fu'ad tana sakin sabon kuka, wani Abu ne ya tokare Mae zuciya wato data aureshi gara ta aure almajiri, Allah ya kyauta Nima na aureki mexanyi dake ya fada a zuciyarshi yana cije lips dinshi na kasa tareda fitar da wani iska me xafi"



Shi har ga Allah ma dariya ta bashi yace mamana kin girma amma har yanxu dae baki dena rigima ba

"Cikin bacin rae daddy yace muhibbah kifita idona a kwae abokin wasanki ne a nan idan nakaraji kin furta bakya son shi anan wllhi se jikinki ya gaya miki"


Karasawa kusa dashi tayi ta tsugunna kasan kafafunshi tana kuka tace daddy ka tausayamun Kar kace na aure ya Fu'ad wllhi bana sons....... Wani zazzafan Mari ne yasata saurin hadiye maganan, daker ta janyo numfashinta tareda fashewa da wani irin kuka me tsuma rae, kuka take kamar ranta xe fita tun ana ganin abun kamar wasa har Suka soma jin tsoro ganin yadda numfashinta ke barazanar daukewa tsabar kuka.


Allah sarki uwa

"Mummy ce ta mike jiki a sanyaye ta nufeta ta rungumota jikinta tanajin ranta babu dadi har da laefinta acikin faruwar lamarin nan batayi domin cutar da diyar ta taba tayima lamarinsu mummunar fahimta ne, lallashinta tasoma yi daker tasamu tayi shiru se ajiyar zuciya take saukewa kamar wacce tayi tseran gudu"


Shikenan mamana tunda bakya son auren nan babu Wanda ze miki dole ki nutsu kiyi karatu sosae Kar ki daga hankalinki kinga exams ne a gabanki idan kika gama exams din ki kirani a waya zandawo se muyi magana da surukin nawa kinji ko? Dasauri tadaga Mae Kae tadan yi murmushi alamun taji dadin maganarshi yace yawa mamana to tashi kije ki kwanta Kar ki makara zuwa school.


Ba musu ta mike a sanyaye tamusu sallama ta nufi bedroom dinta, suma sauran Suka mike suka nufi makwancinsu mummy ma ta mara musu baya, yayi saura daddy da Abba a parlourn




"Duban Abba daddy yayi yace haba Yaya ya zaka biyemata mufa muka haefeta ba ita ta haefemu ba dazata nemi juyamu saboda rashin kunya shi Fu'ad beyi magana ba se ita, murmushi yayi yace ba wae na biyemata bane kaga munyi ma abun mummunar fahimta a yanayinsu munyi tinanin akwae alakar soyayya Kuma danazo mummyn su itama tace ta fahimta hakan a tsakaninsu ashe duk bamu fahimce su bane shiyasa muka yanke hukunci batareda munji ta bakinsu ba, Amma yanxun ma bazamu janye ba a kyaleta tagama exams dinta karta daga hankalinta tasamu matsala idan yaso bayan ta kammala se ayi abinda yadace Dan dama ni ko ba'a fahimce wani Abu game dasuba inada burin mu hadasu aure domin Karin dankwan zumincinmu"

Se lokacin yaji sanyi yace toh shikenan ae Yaya hakanma yayi dama Kar yazamana an biye Mata ace anfasa ne Amma shawarar nan ma tayi, se a fadama iyayensu Mata su su sanar da makusanta se a soma shirye shirye, hakanma babu damuwa se da Suka gama tattaunawarsu kafin suka tafi makwanci.
[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*


*FATIMA A MUHAMAMMAD (Aminiyar ango)*



*DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION*



*Dedicated to my lovely brother*



*Nasadaukar da ragowar pages din nan xuwa ga Abban Fateema Kuma angon Fateema har gaban gobe ana kyawun tare*



*Page 8*






"Jiki a sanyaye ta isa bedroom dinta ta fada toilet tasakarma kanta ruwa tajima a toilet din kafin ta dauro alwala ta fito daure da towel, wardrobe tanufa ta dauko nighties ta shirya Riga ce me sirirrin hannu se wando iya gwiwa"


Kwanciya tayi luf akan gadon tana sauke ajiyar xuciya ta na tino abubuwan da Suka faru a parlourn daddy, da hk har bacci yayi awan gaba da ita



"Shima bangarenshi hakan ne ta kasance yana kwance idonshi a rufe amma ba bacci yakeba ya tafi tinani gabanshi babu abinda yakeyi se faduwa yana ganin fuskarta yadda ya hango tsanarshi karara a cikin kwayar idonta babu abinda yake bakanta Mae rae kamar yadda take na nata bata sonshi Kuma kalmar daga kasan zuciyarta yake firowa iya gaskiyarta take fada Amma ta wani bangaren yaji tunda sanadiyyar boren datayi anfasa auren dan koda anyi auren yasan xaman baxe musu dadi ba tunda shima baya sonta Kuma dama tun farko basa jituwa tabashi mamaki ma data yarda da soyayyar kwana dayan dasuka shirya Amma yayi mamakin yadda Abba ya janye maganar auren Nan cikin sauki da haka bacci ya daukeshi




Fitowa tayi sanye da uniform, a dining tasamu a halin gidan karasawa tayi ta risina tace "Abba Ina kwana? Lfy qlau mamana an fito Kae ta gyada tace Eh"

Daya bayan daya ta gaedasu tana zuwa kan Fu'ad ta dauke Kae taja kujera kusa da Abba ta zauna, Tea ta hada ta soma sipping dinshi a hankali kamar an Mata dole, muryar Suhael ta jiyo kamar daga sama yana cemata muhibbah ashe baki da kunya banida labari? Fu'ad din sa'an kine ki gaeda kowa amma ki kalleshi ki watsar, shi sa'an ki ne Ina tambayarki kinyi mun shiru da sauri ta girgiza kae tace aa big bro yace to gaesheshi

Kasa da Kae tayi tana Wasa da yatsunta belt dinshi ya xare ya nufeta yace gaeshar dashi nace, da sauri ta mike ta Isa gareshi tace Ina kwana Dan tasan ba karamin aekin suhael bane ya xaxxabgamata belt din ta tafi makaranta da kuka yanada saukin Kae amma baya son raeni ko kadan Kuma baya so a gabanshi yaga mutum na raena na gaba dashi to anan ne zakuyi fada dashi

Ko kallon inda take beyi ba bare tasa ran ze amsa gaba daya ranshi a bace yake ya rasa ya akayi ya bari yarinyar ta raenashi ko tamanta wayeshi ne oho, wani murmushin mugunta yayi a ranshi yace nasan mexanyi zan gyara miki zama


"Hawaye ne suka Fara bin kuncinta bakin cikinta yanxu daddy saboda Fu'ad ya juyamata baya yadena supporting dinta, wayarta ta dauka ta nufi hanyar fita tajiyo muryan Abba kiranta cak ta tsaya ya karaso kusa da ita yace yau zamu tafi baki bari munyi sallama ba ko ni ma fushin kikeyi dani, murmushi tayi a xuciyarta tanama Allah godiya yau Fu'ad xe tafi tace aa Abba ae ko zanyi fushi da kowa baxanyi da Abbana ba kawae na sha'afa ne yace toh muje na kaeki school din cikin jin dadi ta jin jina Mai Kae, hannunta ya rike Suka fice har suka isa school din suna fira yana jaddada mata cewa data gama exams dinta ta sanar dashi xexo har nan yaga sirikin nashi murmushin jin dadi kawae take yi kafin ta fito daga motar tana Mae godiya da addu'ar Allah yatsare tana daga mishi hannu har ya bace ma ganinta lumshe idonta tayi ta bude tare da sauke ajiyar zuciya kafin ta nufi cikin school din"


Karfe 12:00 Suka fito daga exam hall din ita da summayya rike da hannun juna suka nufi cafeteria suka siyo snacks kafin suka nufi main class dinsu suka zauna, kallonta summy tayi tace muhibbah Lafiya naga idonki duk sun kun bura alamar kinyi kuka, ajiyar zuciya tasauke kamar zatayi kuka tace kedae bari summy jiya saura kadan na mutum saboda bakin ciki wae ya Fu'ad za'a auramun *soyayyar kwana daya* naso tajawomun masifa nan ta kwashe duk abinda ya faru daren jiya ta Bata labari dariya ta dingamata tana tsokanarta meyasa kikace bakya son shi da munje land of beauty munsha fura da nono, hade rae tayi tace to ae ko yanxu ma zaki iya zuwa dariya tayi sosae kafin tace Allah ya huci zuciyar Amaryar Mukhtar murmushi me sauti tayi tace yauwa ko kefa yanxu naji magana, wayarta ce ta hau ringing wani kayataccen murmushi ta saki ganin sunan dake yawo akan screen din wayan *My king*


"Kara wayan tayi a kunnenta cikin sanyin murya tace Amincin Allah su tabbata ga Angon Fateema xahrah, Ameen tareda matar Mukhtar Kara fadada murmushinta tayi tace Ina fatan kana Lafiya sororo summy tayi tana kallon yadda take waya cikin nutsuwa tana sakin murmushi alamun kalaman da yake mata suna shigarta, seda tagama wayar kafin sukayi sallah Suka Dan duba 'D'/( kadan kafin suka shiga hall din"







Se karfe 5:00pm ta koma gida a gajiye likis bakinta dauke da sallama ta shiga parlourn turus tayi ganinshi zaune kan kujera suna fira da mummy, hade rae tayi takarasa shiga ciki kamar zatayi kuka............[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*


*FATIMA A MUHAMAMMAD (Aminiyar ango)*



*DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION*



*Dedicated to my lovely brother*



*Nasadaukar da ragowar pages din nan xuwa ga my yaya Abban Fateema Kuma angon Fateema har gaban gobe ana kyawun tare*




*Page 9*






Xaunawa tayi gaf da Mummy kafin tace Mummy Abba fa ya fasa tafiyan ne? Murmushi tayi saboda ta fahimce abinda yasata hada rae kamar Wanda aka aeko ma mutuwa batace Mata komae, ba munyi sallama dashi ba daxu ko fasa tafiyar yayi tayi maganar cikin xakuwa da jin amsar da mummy xata bata

"Ya tafi" tafada Kae tsaye


"Toh shi wannan fa baxe tafi bane? Tafada tana nunashi da yatsa wani kallo dayamata ne yasata saurin sauke hannunta tana kauda kanta daga kallonshi, bata ankaraba taji mummy ta bige mata baki dafa bakinta tayi da sauri hawaye na bin kuncinta"


Yaushe Kika koma haka shi sa'an kine? Wllhi xan Saba miki ki fita idona

Da gudu ta nufi bedroom dinta tafada kan bed ta fashe da kuka

Seda tayi me isanta kafin ta tashi ta shige toilet tasakarma kanta ruwa tajima a toilet din kafin ta fito ta shirya cikin bakar Abaya taji stones masu walwali kamar wuta, pray mat ta shinfida ta gabatar da sallahn magrib tana xaune tana axkar har aka kira isha'i seda tayi sallah kafin ta nade pray mat din ta xare hijjab din jikinta ta xaune gefen bed tayi ta gumi seda taji yunwa ta dameta kafin ta nufi parlourn


Suna xaune a parlour ta karasa ta gaeda daddy tana Mae Sannu da dawowa amsawa yayi sama sama saboda har yanxu ranshi a bace yake a kanta yaga idan ba haka yamata ba baxata fahimce kuskurentaba dining ta wuce ta xauna ta xuba abincin jallof din taliya ce data sha naman rago tasa fork ta soma ci Anas ne ya karaso yaja kujera kusa da ita ya xauna seda ya kalleta kamar baxe ce komae ba kafin Kuma yace wae waya tabamana ke ne naga idonki ya kumbura alaman kinyi kuka kedae kuka baya Miki wuya, rau rau tayi da Ido xatayi kuka yace sorry dear sister fadamun waya tabamun ke hawayen daya xubo Mata ta goge tace ba mummy bace ta buge min baki yanxu gaba daya saboda ya Fu'ad su daddy sun dena Sona girgixamata Kae yayi yace ba haka bane kiyi hakuri uhmmm? lallashinta yashiga yi seda yatabbatar ta hakura kafin ya nufi friedge ya dauko Mata ruwan sanyi ya xuba mata a cup ya mikamata duk abinda sukeyi mummy na kalansu girgixa Kae kawae tayi a xuciyarta tana mamakin halinsu su abin fada baya musu wuya indae xasu xauna inuwa daya se anjisu amma kuma indae daya yashiga damuwa hankalin daya baya taba kwanciya Kuma indae sukayi sirri xasu binne abinsu babu me ji

Bayan ta kammala cin abincin ta tattare dining tayi musu sallama ta wuce bedroom dinta ta shiga toilet ta dauro alwala tayi duk wani dabi'a da takeyi kafin ta kwanta tareda karanto addu'ar bacci taja blanket ta rufe har kanta bacci ya dauketa


"Bangaren Fu'ad kuwa Abba da yayi Mae maganan komawa gida yace yatafi kawae xe Kara 1 week xasu dinga su company suna ragema daddy aeki shida Suhael be hanashi ba yatafi abinshi"



Bata fito ba se 9:13am kasancewar yau Saturday babu school gaesheda mutanen gidan tayi babu Wanda ya fita suna enjoying weekend dinsu a gida ganin Bata ga mummy parlourn ba yasata nufar kitchen can ta isketa tana hada breakfast gaesheta tayi kafin ta taemakamata suka cigaba da girkin, mummy wae yaushe mama jumae xata dawo ne aekin Nan yanamiki yawa ke kadae ko xa'a samo wata house made din ne? Tayi maganar cikin sigar tambaya, Aa muhibbah bansan wacce xan dauko ba gara jummae nasan halinta tunda mun dade tare nakirata tacemun in Sha Allah nanda 2 weeks xata dawo ajiyar zuciya tayi tace Tom shikenan Allah yadawo da ita Lafiya, amsawa tayi da Ameeen


Yauwa mummy Dan Allah Ina so xanje gidan su Rufaeda anjima mamanta batada Lafiya, Tom shikenan Allah ya kaemu


Kafin 10 sungama shirya dining din ita ta tattare komae ta wanke kwanukan dasukayi breakfast din kafin ta nufi bedroom dinta wanka tayi ta fito ta tsaya gaban mirror tasoma shafa lotion simple make up tayi kafin ta nufi wardrobe ta dauko Kaya tashirya cikin riga da skirt na atamfa ta yafa mayafinta black jaka da takalminta ma black ta nufi dakin mummy


Mummy na tafi, toh ki gaeshar da su kice Ina Mata Sannu Kar ki Kae yamma, Tom Sena dawo, Adawo lafiya da Ameen ta amsa tana fita


"A compound din gidan sukayi kicibis tana kwala Kiran bala driver kamar baxatayi magana ba tace Sannu da dawowa be amsa ba se cewa yayi Ina xakije? Gidan kawata ta bashi amsa a takaece, wuce ki shiga ciki baxaki ba baki sake take kallonshi tace ya Fu'ad maman kawata ce fa batada Lafiya Kuma na tambaye mummy tace naje na gaesheta"


Baxa kiba wuce ki koma ciki ya dube driver yace yi tafiyanka yau babu inda xata se Monday shima baseka xo dawuri ba akwae Wanda xe kaeta, toh me gida abinda drivern ya fada kenan yana barin wajen, rau rau da Ido tayi xatayi kuka tace toh ae na tambaye mummy Kuma Sena je ko a napep ne tafada tana turo baki ganin Yana kokarin xare belt din jikinshi ne yasa ta kwasawa a guje tayi cikin parlourn tana kwala Kiran mummy ..........





*Aminiyar ango
'?
'?
'?*
[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*


*FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)*

*DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION*


*Dedicated to my lovely brother*


*Nasadaukar da ragowar pages din Nan xuwa ga my yaya, Angon Fateema Kuma Abban Fateema, har gaban gobe ana kyawun tare*






"Zaune suke a parlour suna taba fira rabin hankalinshi Yana kan TV yana kallon news paper"

"Abba Ina gama waec xamu je kaduna nida ummi ko? Tayi maganan cikin sigar tambaya, murmushi yayi yace Kae Khadija kullum maganan ki kenan, shagwabe fuska tayi kafin tace Abba yaushe rabon da mu hadu da muhibbah mun Kae 1 year fa ita bata son xuwa garin nan sbd ya fu'ad ya cika takura tayi maganan tana saurin rufe baki"

Murmushi ummi tayi tace ae xe dawo xaki maemaeta abinda Kika fada, dariya tasa tana girgixa Kae tace nasan yanxu tana can tana kwasar bakin cikin xaman ya fu'ad a gidan daddy har na hango yadda xata koma xaman bedroom dinta Koda yaushe ta karashe maganan tana cigaba da sakin dariyar mugunta, itama ummi dariyar take sbd tasan abinda xe faru kenan dan tasan halin fu'ad sarae musamman tsakaninshi da muhibbah da basa wani jituwa, murmusawa shima daddy yayi yana tina darun muhibbah, shiru yayi yana tinani

Dan Allah daddy kayimun alkawari xamu je da ummi idan na gama exams ta katse Shirun, Allah ya kaemu gaba dayanmu xamu tafi ihun murna tasa tana nufan bedroom dinta da gudu.

"Seda ya nunfasa kafin yace umminsu juyo da hankalinta gareshi tayi tace na'am alhaji, xuwana kaduna mun yanke hukuncin hada fu'ad da muhibbah aure! Gabanta ne ya yanke ya fadi tayi shiru takasa magana duk da ta dade tana tinanin hkn xata iya faruwa tasan halin Abba xeyi wuya ya bar fu'ad ya auro wata a waje, Lafiya kikayi shiru baki ce komae ba kakalo murmushi tayi tace naji abun ne yaxomun baxata toh umminsu banda abinki gida be koshi ba a Kae ma dawa ae gara muyi tuwo na maena xumincinmu yakara danko Kuma kinsan tsakanin fu'ad da muhibbah babu wata jituwa auren ne xesa su fahimce juna, toh Allah yasanya alkhaeri abinda ta iya fada kenan har ga Allah ba wae Bata son auren nasu bane kawae tasan akwae matsala ne kafin su jitu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login