Showing 90001 words to 93000 words out of 112768 words

Chapter 31 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

yunwa ba, jiyafa da yunwa kika kwana blood". Yana kai nan yayi sama da ita ya fice.

Kan rough center carpet din dake parlourn ya ajiyeta ya nufi kitchen ya dauko tray, yadawo dining yashirya breakfast din kan tray din ya nufo parlourn.

Zama yayi ya dauki plate yayi serving dinsu tareda janyota jikinshi yamata masauki akan kafafunshi. Abincin yashiga bata tanaci, shima yana ci, babu laifi kam taci sosai.

Kan kujera ya dorata ya tattare kayan ya kai kitchen, gefenta ya zauna ya kwanto da kanta kan cinyar shi yashiga shafa gashin ta.

"Bloody! Ya kike Jin jikin ki yanzu?" "Naji sauki".
"Zazzabin fa?" Yayi maganan yana kallon kwayar idanunta yana so yatabbatar da abinda yake zargi.

"Dama na fadama dadare ne zazzabin ke rufeni amma da safiya tayi seka nemeshi ka rasa" tayi maganan tana kai hannunta tana shafo sajenshi zuwa gemun shi.

"Jeki ki dauko hijjab mu tafi asibiti" make kafada tayi tace, "Yaya kabarshi kawai base munje ba nasan malaria ce ma, bakina gaba daya babu taste.

Hancinta yaja "toh doctor Fatee". Dariya tayi tana kokarin yin magana taji amai na taso mata, ta mike da gudu ta shiga wani daki a down stairs, tafada toilet tashiga Kwara amai.

Da hanzari ya mara mata baya ya riketa har tagama aman, ya wanke mata baki da fuska kan ya dubeta, "Sorry dear, ki jirani Ina zuwa". Kai kawai ta gyada, ya fice.

Be jima ba yadawo toilet din ya mikamata PT, tsayawa tayi tana kallonshi dan batasan amfaninshi ba.

"Yimun fitsari akai". Ba musu ta tsugunna tayi fitsarin, tayi tsarki ta mike yana tsaye yana kallonta.

Mikamishi tayi yasa hannu ya karba, befi 30 seconds ba yaga 2 lines sun fito rada rada jajir, ya dan zaro idanu yayi murmushi har fararen hakoranshi na bayyana.

"Yaya meyafaru? Me kagani a fitsarin nawa? Malaria ce ko? Dama nafadamaka ba wani abu bane malaria ce, lokacin ina KD na taba irin ciwon kullum da dare zazzabi kamar zan mutu, amma gari na wayewa ze sauka kamar aljani sedai mummy take kwana dani Kuma doctor yace ba wani abu bane malaria ne". Murmushi mara sauti yayi, bece mata komai ba ya dauko Dettol ya wanke musu hannuwa, ya daukota suka dawo parlour.

Ajiyeta yayi tanata maida numfashi tanajin Jiri na dibanta. Hijjab yaje ya daukomata ya ziramata suka fice rike da hannunta, ya bude mata mota ta shiga ya zagaya ya shiga mazaunin driver yaja motan suka fice daga gidan.

Cikin asibitin yayi parking ya fito, ya bude mata ya rikota tareda mannota da jikinshi suka nufo ciki anata miko gaisuwa sedai ya gyada musu Kai.

Lab ya nufa da ita, yasamu doctor fareeda na zaman jiran su dan tun kan su tawo ya kirata. Gaisheshi tayi ya amsa cikin kulawa dan babu wacce yake kulawa tun daga kan doctors din har zuwa nurses kamar ita, saboda tasan aikinta kuma tasu tazo daya kowa shakkar yi mai magana yake, ita kadai ke iya fuskantarshi su tattauna kan abinda taga ya dace a gyara kuma ya saurareta.

Zama yayi yamata masauki kan kafafunshi, ta karaso taja kujera tazauna kusa da su ta riko hannun Muhibbah.

Ina kwana doctor "Lafiya kalau madam, ya jiki?" "Alhamdulillah".

"Fatan dai kin dena tsoron allura?" tayi maganan tana murmushi dan sarai ta gane itace wacce tasama drip kwanaki. wajen yin allura suka dinga drama, kwanaki kuma taji anata cewa matar boss ce gashi kam ta tabbatar tunda gata kan cinyar shi dare dare, duk da dah tayi tinanin ko kanwarshi ce saboda kaman data ga suna yi.

Murmushi tayi, shi Kuma hankalinshi na kan waya yana duba abu.

Jin tsinin allurar a fatan ta tun bata shige ba tayi saurin janye hannunta tana hawaye.

"Madam haka zamuyi dake?, doctor inaga seka dan rike mun hannun ta" tayi maganan cikin kulawa.

Wayarshi ya ajiye a gefe, ya rike hannunta ta binne kanta a kirjinshi tana kuka har aka gama diban jinin.

Mikewa yayi ya rike hannunta yace "Doctor ina jiran results din office" "in Sha Allah sir". Office dinshi suka nufa ya kwantar da ita kan kujera.

"Yaya! na baro wayata gida nasan Aesha zata zo yimun sannu da dawowa ka kirata please karta je bana nan.

Bece komai ba ya zaro wayan yashiga dialing numbern Aeshan.

"Assalamualaikum! Ina kwana Yaya" tafada a hankali dan ji take kamar yana gabanta.

"Kina ina yanzu?"
"Ina gida yanzu dai zan tafi gurin Muhibbah".

"Okay ki biyo asibiti ku tafi tare" yana kai nan ya ajiye wayan.

Karasa shiryawa tayi ta fito, a parlour tasamu ummi "Ummi bari naje, Yaya ya kirani yace nabiya ta asibiti mu tafi da Muhibbah gidanta" "Asibiti kuma? Lafiya dai ko?".

"Nima Ummi bansaniba, abinda yace mun kena???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n ya kashe wayan".

"Toh A dawo lafiya".

Asibitin ta biya ta nufi office dinshi tayi knocking, ita ko duk an santa tunda ko ciwo suke asibitin suke zuwa. Izinin shigowa ya bata ta murda handle din ta kutsa kai.

Gaishe shi ta kumayi ya amsa. "Riketa da kyau ku karasa mota, ina driver ya kawoki?" "Eh Yaya tare muke dashi".

"Okay ki sama mata abunda zataci idan kunje, yau ma kijata kushiga kitchen tare idan kinga dama kiga yadda zamuyi dake".

Kai kawai ta gyada, gaba daya ta kosa su fice daga office din.

Taimakamata tayi ta tashi zaune "Hearty?" "bloody" yafada yana kallonta.

Hannunta biyu ta hada ta sumbata ta hura alamun kiss din iya isa gurinshi. Murmushi yayi shima yamata yadda tayi tasa dariya, ta rike hannun Aesha suka fice ta juyo tana mishi bye bye.

Suna isa ta zube kan kujera Jiri take ji yana diban ta ga yunwan dake kwakular ta.

"Maman un born baby! Me zakici ne?" Harararta tayi, "Kya gama abunki ki kyaleni malaria ce ba wani abu ba, in sha Allah bazan ga ciki yanzu ba kidena mun fata Idan ba haka ba ajimu dake".

"An dade ba'a jimu ba, dama yau aka fara jinmu ne? Nidai fadamun abinda zakici dan yanzu zakiji Kiran yaya, na shiga uku".

"Fate" waro ido tayi "Fate Kuma? Gaskiya ki canza wani abun".
"Toh shi nake so"

Zatayi magana taji ana danna door bell, mikewa tayi taje ta bude, ganin mairo yasa tayi murmushi "Allah ya taimake ki, ga Aunty mairo nan dan bazan iya wani fate ba".

"Wa ke son fate?" Ta fada tana shigowa parlourn.

"Muhibbah ce bata da lafiya shine tarasa abinda zataci se fate"

Murmushi tayi "Kibarta idan bashi ta samu ba bazata iya cin komai ba".

Hijjab ta zare ta nufa kitchen, Bata samu tsaki ba ta diba shinkafa tasa a blender ta nika. Batafi 30 minutes ba ta kammala faten ta zubo a kula ta kawo musu parlour ta ajiye.

Plate Aesha ta dauko ta zuba mata se taga ya birgeta itama ta dauki plate ta zuba ta fara Sha. Lumshe ido tayi "kai gaskiya faten nan yayi dadi". Har ta shanye amma Muhibbah na zaune ta tasa shi gaba tana kallo.

"Sister kisha mana kinga harma yayi sanyi"

Daker ta Kai chokali daya baki, ta yatsina fuska tana ture plate din gefe "Sister bazan iya Sha ba, idan nasha zan i amai zanyi. Ki dafamun indomie please kisa yaji sosai". Da mamaki take kallonta "kisa a dafa abu yanzu Kuma kice bazaki sha ba tsakani da Allah"

Mairo dake gyaran parlourn tace "Aesha kimata uzuri mana ko kinga dah tanayin haka ne?" Girgiza kai tayi, ta mike tashiga kitchen.

Hannunta rike da plate din indomie ta fito tazo ta ajiye gabanta, tako ci babu laifi dan kadan ta rage. Jingina bayanta jikin kujera tayi tana Jin yadda zuciyarta ke tashi cikin ta na ya mutsawa.

Da gudu ta nufa toilet, Aesha ta mara mata baya, mairo ma ta bisu. amai tashiga kwararawa seda ta fitar da indomie tass ta koma ta zauna tana sauke wahalallen numfashi hawayen wahala na bin kuncinta.

Aesha ce ta taimaka mata ta wanke baki ta rikota suka fito. Mairo nata jeramata sannu

Gefenta ta zauna "Sannu sister, meke miki ciwo?"
"Jiri nake gani"

"Ko zamuje daki ki kwanta?" Kai ta gyada, tarike hannunta suka haura dakinta. Kan bed ta kwantar da ita, itama ta zauna gefenta tana mata sannu.

Wayanta ce ta dau kara, Aesha tamata picking ganin sunan mummy na yawo kan screen din.

"Mummy na barka da safiya" "lafiya kike kuwa?" "Tun jiya da muka dawo bana Jin dadi malaria ke damuna"
"Eyyyaaa sorry, kinsha magani? Nasan ki da kin magani Muhibbah". "Munje asibiti, Yaya ze tawomun da magungunan" "Allah yabaki lafiya" "Ameen mummy na".

Sallama sukayi, mummy najin babu dadi ta bakin Muhibbahn nesa beda dadi amma yaza'ayi.

"Wllhi sister ko kiyarda ko karki yarda ciki gareki dan ban yarda dake ba, zaki lakama malaria saboda batada bakin karya taki, amma ai result ze nuna kuma zakice na gaya miki".

Gabanta ne ya fadi, kardai da gaske cikin ne da ita dan ko lokacin da likita yace malaria ke sata zazzabin dare, ai bata amai kuma bata Jin Jiri ko dai maganan Aisha nada kamshin gaskiya? Saurin girgiza kai tayi tana runtse ido idan ko ciki gareta ta shiga uku ya zatayi da karatun ta.

"Uhmmm idan tayi wari maji" cewar Aesha

Ita dai bata tanka taba har bacci ya dauketa.

Duk minti minti seya kira yaji jikinta Aesha tace mai bata farka ba.


Yana aiki a office yaji ana knocking, be tashi ba se izinin shigowa da ya bayar. Doctor fareeda ce ta turo kofan tashigo fuskarta dauke da murmushi

"Congratulations doctor! Madam na dauke da ciki har na tsawon sati 8 da kwana biyu" tafada tana ajiye mai result din.

Besan lokacin daya mike ba yana murmushi har hakoranshi na bayyana, duk da tun safe yasan da cikin sedai yana son tabbatarwa da kuma sanin adadin kwanakin cikin. Ba karamin Jin dadin albishir din nan yayi ba dan yama rasa abin fada se alhamdulillah kawai yake mai mai tawa a fili. Ita ko doctor kallonshi take da mamaki, dama ya iya murmushi har haka amma yake hade girar sama da kasa Koda yaushe.

Wayanshi ya zaro yamata transfern kudade masu yawa, yace tukuicin albishir, a take Kuma yamata Karin albashi.

Godiya tayi ta mai har tarasa abin fada ta fice tana fada ma wasu nurses boss ya kusa samun baby.

Tattare files din kawai yayi ya fice, nurses suna ta tayashi murna, suna mamakin yadda yake amasawa fuskarshi dauke da murmushi.

Gida ya nufa be gansu a parlour ba ya nufa dakinta, amai ya tarar tanayi Aisha na rike da ita. Dasauri ya karasa ya rike ta Aesha ta mike ta baro toilet din.

Tana gama aman ta fashe da kuka tana kiran mummyn ta.

Baki ya kuskure mata ya dakota suka fito

Aesha tayi musu sallama yasa driver ya maidata gida.

"Bloody! Me ke miki ciwo?" "Komai ma".

Tafada tana cigaba da kukanta, murmushi ya danyi Jin tace komai ma ciwo yake mata.

Zeyi magana wayanshi tafara ringing ganin sunan ummi yasa yace "Please bloody kidena kukan nan, kar kanki yamiki ciwo kinji?". Kai ta gyada, gaba daya tausayin ta ya kamashi da da yadda zeyi daya amsarmata ciwon.

Numbern ummi yayi dialing ringing biyu ta dauka, "Assalamualaikum, Ummi ina wuni" "lafiya kalau! Ya jikin Muhibbah?" "Dasauki". Yafada yana kallonta

"Allah yakara sauki"
"Ameen" "Suhailat ta sauka yanzu mijinta ya kira yake fadamun, A asibitin ku ne ma, kafita kenan su Kuma suka shiga".

"Alhamdulillah! Allah ya raya, me aka samu?".

"Ansamu dan saurayi" "Allah ya raya shi akan Sunna" "Ameeen! Kayi ma Muhibbahn sannu" kafin yayi magana ta yanke kiran.

Murmushi kawai yayi, idan da sabo yasaba da halin ummi yau ma yayi mamaki da sukayi magana har haka

Doctor fareeda ya kira yace a tabbatar an ba Suhailat kulawa na musamman kafin yaje asibitin dasafe.

"Aunty Suhailat ce ta haihu?" Kai ya gyada mata yana shafa fuskanta yanajin wani farin cikin dabe taba tsintar kanshi a ciki ba kamar na yau.

"Allah ya raya" "Ameen blood". Muma Allah yakawo mana namu babyn lafiya.

Murmushi kawai tayi tana rufe fuska.

"Albishirinki?" "Goro".

"Toh se kin bada tukuici kana zan fada miki" "Aa seka fara fada kana zan baka".

Lakace hancinta yayi "Aa banyarda ba, kiji wayau".

Dariya sosai tayi "Ai ni nayi alkawari zan baka kai dai ka fadamun".

Cikinta ya shafa yana murmushi "Congratulations mun kusa yin baby". Dan zaro ido tayi "baby Kuma?" Kai ya gyada mata kana yace, "Kinada ciki". Da mamaki take kallonshi "Ciki? Niiii?" Tayi maganan tana nuna kanta.

Gira ya dage mata "Uhmmm kinada ciki har na tsawon sati 8 da kwana biyu".

A zabure ta mike tana taba cikinta, tana girgiza kai.

"Aa badai ni ba" mikewa yayi ya riko hannunta ya zaro result din ya damka mata.
"To idan bake ba waa? Karanta kigani"Yafada har lokacin yana murmushi.

Karba tayi ta karanta tayo saurin wurgar da papern kasa, tana fashewa da kuka "ciki! Makarantan fa? Dame zanji rainon ciki ko karatu? Yaya kana ganin irin azabar danake ci tun daga jiya har zuwa yau ban isa inci abinci na zauna lafiya ba se na fitar dashi. wllhi bazan iya ba, inaa ban shirya ba, ba yanzu ba, sedai a zubar dashi, baze yuwu ba." tana maganan tana kuka kamar wacce ta zare.

Ranshi ne yayi kololuwan bacci ya fara matsawa inda take, ganin ya koma mata Fu'ad dinta na dah, yasa zuciyarta bugawa, tana ja baya har ta kai karshen bango.

Da yatsa yashiga nunata "Idan kika Kuma ambaton zubar mun da ciki wllhi sena tsinkamiki mari, kuma idan kika kara zancen akan makaranta bakya son cikina har kika bari naji toh wllhi wllhi keda makaranta har abada, zabi ya rage naki ciki dai yana nan daram a jikin ki kuma dole ki haifemun dana, makaranta Kuma idan kinga bazaki iya ba is fine, zaki iya hakura da ita banida matsala da wannan be da meni ba. sannan kince baze yuwu ba ko? Toh dan Allah kiyi abinda kika ga dama ai ga cikin nan a jikin ki, nace kiyi abinda kika ga dama kinji ko?" Masifa yake kamar ze kai mata duka beta ba tinanin yadda take fadan bata son cikin dagaske take har a zuciyarta ba. Beyi tinanin har yanzu bata san inda yake mata ciwo ba. Tsaki yaja ya juya ya fice dan yadda ranshi ya bacin nan ze iya Kai mata duka idan ya cigaba da tsayuwa.

Seda taga fitar shi ta sauke numfashi, dan ba karamin tsorata tayi ba, ko a baya bata taba ganin fushin shi kamar na yau ba. jira kawai take taji saukar mari.

Zamewa tayi ta zauna a kasa ta daura hannunta a kai tareda sakin kuka me sauti.............





*>?p? AMINIYAR ANGO >?p?*
[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*

*FATIMA A MUHAMMAD AMINIYAR ANGO*

*Page 54*


Dakinshi ya wuce yayi wanka yasa kaya ya fice masallaci.

Ta jima tana kuka, seda taji an soma kiraye kirayen sallahn magrib kan ta mike ta shiga toilet. Gaban shower ta tsaya ruwa nata sauka kanta, ta dade a haka kan ta fito daure da towel. Rigar bacci ta dauko tasa ta zira hijjab ta tada sallah, tana nan zaune tana azkar seda aka kira isha'i kan ta mike ta gabatar da sallahn, ta nade pray mat din tareda zare hijjab din jikinta ta haye gado.

Yunwa takeji amma tana tsoron sa wani abu a cikinta gudun ta shiga Kwara amai, Blanket taja ta rufe gaba daya jikinta tare da rufe idanunta babu jimawa ko bacci ya dauketa.


Seda yayi isha'i ya biya restaurant ya siyo musu abinda zasu ci kan ya shigo gidan.

Koda yashigo be sameta parlour ba, ya wuce kitchen ya dauko plate, ya dawo ya zauna a dining yayi serving kanshi.

Har ya gama bata fito ba be nemeta ba ya wuce parlour ya zauna tareda kunna tv, Rabin hankalinshi na kanta yana tinanin ko wane hali take ciki? kuma yasan ko abinci bata ciba. daurewa kawai yakeyi saboda yana so ta gane kuskuren ta.

Mutsu mutsu ta shiga yi, gaba daya ta kasa bacci cikinta se juyi yake, ji take kamar an mata yasa. Dole yasa ta ziro kafafunta kasa tasa takalmi ta nufo down stairs.

Jin taku alamun ana saukowa yasa ya Kalli gurin, zuciyarshi ce tayi tsalle lokacin da idanunshi suka kai kan 'yar rigan baccin dake jikinta dabata karasa guiwaba, hannunta na vest daga saman wajen kirjinta net ne ana hango komai na jikinta, wani abu ya hadiye yana jin zuciyarshi na fisganshi zuwa gareta, suna hada idanu ya dauke kai ya mayar kan tv.

Ita ma bata ce komai ba ta karasa dining ta zuba abincin tashiga ci, zuciyarta fal fargaban dawowan abincin.

Tako ci sosai ta dauki ruwa tasha tare da furta Alhamdulillah. Mikewarta keda wuya tafara yunkurin amai, ko dakinta bata nufa ba, ta fada wani daki a guje, ta shiga Kwara amai.

Da hanzari ya mara mata baya, seda ta fitar da abincin data ci tass kan ta zauna cikin toilet din tana sakin kuka me ban tausayi.

Mikar da ita yayi, ya kuskure mata baki yayi sama da ita suka fito daga toilet din

Dakinshi suka haura ya kwantar da ita saman bed, ya dauko magungunan daya tawo mata dasu daga asibiti ya balla yabata, tsabar Jin jiki batama San takarba ta watsa a baki ba ya mikamata ruwa ta kora, haurawa gadon yayi ya janyota jikinshi, har lokacin Kuka take sosai tana Kiran mummynta.

Hannunshi ta rike

"Yaya dan Allah katausayamun a cire cikin nan, zan mutu....." Kallon dayake watsamata yasata saurin yin shiru, tana kokarin zamewa daga
jikinshi.

Zamewa yayi ya kwanta, ya janyota ya dora kanta a kirjinshi yana shafa gashinta tareda dan bubbuga bayanta, a haka har bacci ya kwashesu.

Allah ya taimake ta yau zazzabin dare be rufeta ba saboda magungunan datasha.

Be tsaya breakfast ba yana shirin fita, tace "Hearty! Dan Allah nazo mu tafi naga babyn Aunty Suhailat?" Ta fada a dan tsorace, dan ganin har yanzu a Fu'ad dinshi yake.

"No! Zan turo Aesha ta tayaki zama". Langwabar da kai tayi, a shagwabe tace "Nidai dan Allah muje tare idan naga babyn semu tawo da Aesha nasan yanzu hakama maybe tana asibitin". Bece komai ba ya fice, tasan tunda yayi shiru ya amince ne miskilancin ne ya motsa, kuma koya za'ayi bazata haihu yanzu ba. Duk yadda zata kwatanta mai azaban data ke sha baze fahimta ba tunda ba'a jikinshi bane.

Mayafi tadauko ta yafa, da sauri tamara mai baya ta bude motan ta shiga yaja suka fice daga gidan.

Yana driving yana kallonta ta gefen ido, fuskanta yayi fayau idanunta sun zurma, gaba daya tausayinta ya kamashi, tayi yarinya dayawa 18 years ga cikin yazomata da laulayi me wahala, amma hakuri zatayi, dole ze zauna ya lallasheta gudun tayima kanta illa takuma yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login