Showing 93001 words to 96000 words out of 112768 words

Chapter 32 - Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel By ashwarmediahausa.doc

mai asarar cikinshi.

Parking yayi suka fito, a tare suka jera har cikin asibitin.

Doctor fareeda suka ci karo da ita ta gaisheshi cikin girmamawa, ya amsa. Kan Muhibbah ta gaisheta, ta amsa tana tambayarta ya tsoron allura, sukayi dariya. Dakin da Suhailat take ta fada musu suka karasa.

Bakinta dauke da sallama tashiga dakin banda Fu'ad da yayi tashi akan lips, tana zaune tana feeding baby suka sameta, Aunty Maiminatu na zaune gefenta.

Fuskarta dauke da fara'a ta karasa "Ina kwana Aunty Maiminatu" "lafiya kalau Muhibbah".

"Maman baby Ina kwana". "Lafiya kalau"
"Ya baby?" "Lafiyanshi kalau".

Cikin girmamawa suka shiga gaishar da Fu'ad, ya amsa cikin sakin fuska yana tambayar Suhailat karfin jiki, ta amsa da Alhamdulillah, tana mika mai babyn.

Karba yayi yamai addu'a, Muhibbah ta mika hannu ya daura mata yaron ta kalleshi tana murmushi, tareda manna mai kiss a kumata.

"Tubarkallah Masha Allah! Aunty Maiminatu kin Kalli yaron nan kam, kinganshi kyakkyawa".

"Na gani Muhibbah".
"Dan Allah Aunty Suhailat ki barmun yaron nan"

"Yanzu kuma kin fasa zarahn kenan? Haka zakiyima daughtern naki?".
Dariya tayi "jariri ne akwai sha'awa, bare wannan tubarkallah dan lukuti, dan Allah ki barmun shi sena hada duka harda zarahn".

Dariya sukayi har Aunty Maiminatu "Toh Muhibbah na bar miki, amma ki barmun zarah bana zauna ni kadai ba"
"Eh na yarda".

Hada idanu sukayi da Fu'ad ya harareta ta dauke kai tana turo baki.

Fita yayi ya dawo da wasu allurai yazo yama Suhailat, ya juya ya fice.

"Yunwa nakeji" tafada tana shafa cikinta.

"Bakiyi breakfast bane kika fito?" Cewar Maiminatu.

"Eh Aunty! Naga Yaya ze tawo yabarni ne shiyasa".

"Toh ga flask nan akwai ruwan zafi ki hada tea"
"Aunty! Bazan iya Shan tea ba".

Suhailat tace "Toh ga soyayiyar doya da miyan source da Aunty Maiminatu tazo dashi".

Yatsina fuska tayi "Kai bar doyan nan Aunty".

"Farfesun fa?" Ta fada tana bude kula, saurin toshe hanci tayi tana ja baya tareda girgiza kai.

Da mamaki suke kallonta, Aunty Maiminatu ta bude baki zatayi magana Aesha tashigo. Ta zauna tana gaishe su, suka amsa ta Karbi babyn itama se santinshi take.

Food flask din da Aesha tashigo dashi tashiga budewa, tayi murmushi ta dauki plate ta zuba ta koma ta zauna.

Tanajin Aesha na tsokanarta tayi banza da ita dan yunwa takeji jikinta har rawa rawa yake.

Sosai taci ta ajiye plate din, aka cigaba da fira.

Zare gyalen tayi ta jefar kasa ta kwasa bayi a guje ta shiga Kwara amai. Da sauri Maiminatu ta bita tana mata sannu, seda tagama ta taimaka mata ta kuskure baki ta rikota tazo ta kwantar da ita kan hadadden gadon asibitin da zaka dauka gida kake tsabar haduwar dakin da suke ciki komai akwai, fridge, tv dasauransu, Aesha ta karaso itama tanata jeramata sannu. "Gaskiya babyn nan yana wahalar mana dake". Ita dai bata kulata ba se numfashin azaba take saukewa

"Jeki ki kira Yaya" da sauri Aesha ta fice, ba jimawa se gashi sun dawo tare da Fu'ad.

"Heebbah! Jikin ne?" Kamar jira take yashigo tasa kuka.

"Wayyo Allah mummy na, nashiga uku na zan mutu, wllhi Yaya bazan iya ba na gaji....".

"Kinyimun shiru ko sena bige bakin ki". Bakin ta taja tayi shiru bata iya kara cewa komai ba se kuka kawai take

Kayan aiki ya dauko yazo yasamata drip yasa allurai a ciki ya hada dana bacci, ya zauna gefenta ya riko hannunta yana kallonta. Su Kuma su Aesha suka juya suka cigaba da firansu kasa kasa.

Seda yaji tayi shiru alamun bacci ya dauketa, kan ya zare hannunshi daga nata, ya gyaramata kwanciya ya fice.

"Wllhi natausayama Muhibbah laulayi me wahala takeyi, cikin zarah na sameshi a bonus amma wannan karon kam naci kwakwa, ko ruwa nasha seya dawo, seda ya girma nasamu sassauci amma duk da haka yau lafiya gobe ba kalau ba. Sedai banyi tsayin na kuda ba dan da tasowar na kuda da isowarmu asibiti befi 40 minutes ba, kuma Ina zuwa banjima ba na haihu".

"Kinsan cikin Khalil wahalar da naci, ni ko abincinma bana iya ci, ruwa wannan sena wuni ban kaishi bakina ba, ciki tun be kai sati 2 ba kowa seda yasani daga karshe gidan Ummi na dawo, har na haihu bazan ce miki gashi yau naji ni normal ba, Kuma ana cewa idan kayi laulayi me wahala kana samun nakuda me sauki, toh nikam har na kudan babu sauki seda na wuni cirr ina abu daya. Allah dai ya raba lafiya, amma haihuwa is not easy".

"Ameen" suka amsa dashi. Ita dai Aesha na jinsu tayi ta gumi tana tausayin yayarta, kawarta, kuma aminiyar ta.

Koda ta tashi taji karfin jikinta, sallah tayi taci abinci amma still seda tadawo dashi, ta gumi ta zabga tana hawayen tausayin kanta tana tinanin mafita, Aesha se faman lallashi take.

Se yamma ya daukesu gaba dayan su, duk ya dire ko waccen su gida. Suhailat tasamu uwar mijinta ta turo mata dattijuwar dazata dinga kula da ita da babyn ta.

Restaurant ya biya, ya siya musu abinda zasu ci, kana suka dauki hanyar gida, a masallacin unguwar su yatsaya yayi sallah kan suka karasa gida.

Wanka tayi, tayi sallah ta nufo parlourn

Har yasoma cin abincin ta karaso taja kujera ta zauna, tasa spoon suka cigaba daci tare, tana ci tana tsoron abinda ze biyo baya,
Tayi sa'a har ta kwanta bacci bataji aman ba.

Shiryawa yayi cikin kayan bacci wando iya guiwa ko riga besa ba ya nufa dakinta, gefenta ya kwanta ya daurata kan kirjinshi yanajin yadda feeling dinta ke taso mai

Mutsu mutsu ta fara, yayi saurin tashi zaune ta dirka da sauri tayi toilet.

Abinda taci ta fitar, ya taimakamata ta kuskure baki suka fito, kukanma nemanshi tayi ta rasa tsabar azaba, bakin gadon ya zauna yamata masauki kan kafafunshi.

Mannota yayi da jikinshi, yana shinshinan wuyanta tareda shafa gashin ta, ita Kuma ta sakalo wuyanshi tana kara lafewa a jikinshi.

"Sorry bloody! Babyn nan yana wahalar mun dake, duk randa yazo sena rankwashe shi"

Hawaye ta fara "Yaya kanajin azabar dana keji kuwa? komai naci seya dawo. Kona so naki ci bana iyawa yunwa bata barina, katausayamun mu zubar da cikin nan zuwa gaba, kaga nayi karama.....". Tayi maganan jiki a sanyaye

Bakinsu ya hade yashiga aikamata da hurt kisses, seda ya kashe mata jiki kan ya raba bakinsu.

"Bakya so ki haifamana irin yaron Suhailat ne?, kefa naji kina cewa tabaki yaron".

Kai ta gyada kan tace "Ina so mana, yaron kyakkyawa tubarkallah gashi dan lukuti nafi son irin yaran, wllhi dazata bani shi karba zanyi".

"Toh meyasa ke bazaki haifa mana ba?"

"Toh aini nayi karama"
"Injiwa? Waya fadamiki? 'yan 15 years ma suka haihu bare ke, ki daure please, gaba kadan aman ma ze tsaya ba kinga yanzu kindena zazzabin ba?" Kai ta jinjina.

"Kuma fa haihuwa babu wani wahala, kinga ni doctor ne nasha karbar haihuwan yaran da basu kaiki ba, sannan bamusan ko iya shikenan kwanmu a duniya ba, idan muka zubar Allah ze kamamu da laifin kisa, sannan ya jarabcemu a lokacin da muke nema ya hanamu saboda ya bamu a farko, munyi butulci bamu gode ba, zaki so mu kashe rai? Ran ma na danmu".

Saurin girgiza Kai tayi kana tace,
"Toh na yarda zan haifoma baby, amma kai zaka karbanmun haihuwan da kanka ba doctor fareeda ba, dan ita Kam barina zatayi nasha wahala" murmushi yayi tareda gyada mata kai
"Naji na yarda".

"Toh ai ni kunyan su Abba da daddy nake, idan suka sani fa"

Dariya sosai yayi "Toh menene dan sun sani? Ina su suka mana auren? ai murna ma zasuyi, barima na kira na sanar musu, su ma babyn mu addu'a tun kafin ya iso". Ya fada yana dauko wayanshi

Saurin rike mai hannu tayi tana kukan shagwaba, "Nidai kar ka kirasu, ai se suce bamuda kunya". Dariya maganan ta bashi ya ajiye wayan ya shiga yawo da hannunshi a jikinta, ganin zaman baze mai ba yayi baya baya suka kwanta. Se korafin batada lafiya take tana tureshi, ya birkitata tadawo kasa yamata runfa ya hade bakinsu.

Tun tana nokewa har ta biye mai suka sha bidirin su dan ba karamin missing dinta yayi ba itama tayi missing dinshi.

Aesha na shiga ko zama batayi ba ta hau sanarma ummi Muhibbah nada ciki, murna gurin ummi kamar me se washe baki take, Abba nadawowa tayi mai albishir, shima yayi murna ba kadan ba


Gidan ummi ya sauketa ya juya ya nufa asibiti, Ta karasa cikin parlourn kanta kasa.

"Ina kwana Ummi" "lafiya kalau Muhibbah! Ya karfin jiki" "da sauki" ta amsa a kunyace. Gaba daya kunyan ummin take ji har ummi seda ta ganota.

Har dare tana gidan, tausayinta ne ya kama ummi ganin yadda take amai, batada daman cin wani abu ta zauna lafiya.

Aunty Asma'u tazo saboda gobe sunan Suhailat, nan ta kira Mummy ta sanarmata autan ta nada ciki, nan tashiga murna kan kace me har su Anas duk sun sani.

Washe gari sukayi ma gidan Suhailat tsinke, Fu'ad yaso hanata zuwa tasa mai kuka dole yabarta. Wuni tayi daki dan bata so mutane suyita cewa tayi haske ta kara kyau, amma idanunta sun zurma.

Har Zeeee da Rumaisa ma sun zo, sunata tambayan ina Muhibbahn akace tana kwance batada lafiya. Anci ansha, yaro yaci sunan Fu'ad ana kiranshi da Aadil, murna gurin Muhibbah ba'a cewa komai akwati guda ta ciko da kaya, bini bini ta daukeshi ta manna mai kiss a kumata.

"No wonder! Shiyasa yaron nan yazo a kyakkyawa, Kuma tunda naganshi naji ina mutuwar kaunar shi ashe sunan habeebeee ze ci". Shima Fu'ad yayi bajinta ya kashe naira.


A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah, Cikin Muhibbah yashiga wata hudu har ya soma fitowa, tadena amai, sedai ba ko wane irin abinci take iya ciba, ta soma jin karfin jikinta sedai Kunsan yanayin jikin masu ciki yau lafiya gobe babu, Fu'ad kullum cikin karfafa mata guiwa yake da nunamata laulayi ne kawai keda wahala amma wajen haihuwa bazataji wani wahala ba.

Shirye shiryen komawa school ta shigayi, dan yau hutun su ya kare.....................






*>?p? AMINIYAR ANGO >?p?*


*>?p? Aminiyar ango >?p?*


[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*

*FATIMA A MUHAMMAD*
*AMINIYAR ANGO*


*Page 55*


Tana tsaye gaban wardrobe tana faman neman kayan da zata sa, ko wanne ta dauko idan tasa setaji ya matseta.

Hugging dinta yayi tabaya ya zira kanshi a wuyanta yana shin Shinar sihirtaccen kamshin ta.

Dago Kai tayi tana kallonshi ta sakarmai murmushi

"Maman baby ya akayi ne? Tun dazu inata jiran fitowarki najiki shiru"

Kukan shagwaba tasa mai "Uhumm uhummm! Baka gani narasa kayan dazan saba, duk wanda na dauko se inga yayimun kadan".

"Toh ai kece kinzama 'yar lukuta" yayi maganan yana dariya

"Toh ba babynka ne ya maidani haka ba" tayi maganan a shagwabe.

"Shiyasa nace idan babyn nan yazo se na rankwashe shi, saboda ya wahalarmun dake dayawa".

"Ai yana fitowa ni zan fara mintsinanshi, kafin kai Kuma seka rankwasheshi tunda baya jin magana". Ta karashe maganan tana dariya.

hannu ya kai ya shafa cikinta "Anya kina son babyn nan naki kuwa?"

Baki ta tura "Ni bana wani sonshi, ai shima ba sona yake ba tunda yana wahalar dani".

"Waya fadamiki baya sonki? Akwai dan da baya son mahaifiyar shi ne? Ko kuma akwai mahaifiyar da take kin danta? Duk da dai yau nafara ganin mahaifiyar data ce bata son babyn ta". Yafada yana dagemata gira

"Kaima fa Yaya sheda ne, kasan ba karamin wahalar dani yake ba, dan haka ni babu ruwana dashi kawai dan nariga nama alkawarine shiyasa ma zan haifoshi, amma daga nan na gama nawa aikin na fita, ko kaba mummy shi ko kaba Ummi ko Kuma Aunty Suhailat ta hada da Aadil ta shayar dasu".

Murmushin gefen baki yayi tareda girgiza kai, shirmen Muhibbah se ita. Wata doguwar riga me roba ya dubomata.

"Gwada wannan maybe ya miki"
Karba tayi ta zira, ta kalleshi, tayi dariya tana kai hannunta kan cikinta "Yaya kalla yadda rigar nan tasa cikina yayi Kato kamar wani kwallo".

Shima dariya yayi, yana dora hannunshi kan nata "babu ruwan riga bloody, dama cikin ki a haka yake"

"Amma harda rigan kaga tanada roba shiyasa ta kara fito dashi, salan naje school ai ta kallo na, su Umaina suyimun dariya".

"Nikam nafi son haka, kinga yanzu duk wanda ya ganki yasan ke matar aure ce, base an fadamishi ba"

Yayi maganan yana kwafa, tino sauban da yayi, dan bayajin haushin malam mukhtasir kamar sauban saboda ya daura laifin a kanshi, tun farko da yaje karba mata admission letter, be sanar mishi tanada aure ba da beyi yunkurin kulata ba.

Zatayi magana ya rikota "Let's go! Ki bar maganan su Umaina, suma ai mata ne idan layi naja ze zo kansu"

Yayi maganan yana mikamata hijjab.

Yatsina fuska tayi "Eyyyaaa Yaya bazan iyasa hijjab ba zafi nakeji, kuma kace mutum baze sha fanka ba bare naje da hand fan".

Beyi magana ba ya zaro wani gyale ya mikamata, ta yafa suka fito rike da hannun juna.

Basu fi 20 minutes ba suka kammala breakfast suka fice

Bakin gate din school yayi parking, ya ciro facemask ya Mika mata, ta bata fuska
"Dan Allah Yaya kayi hakuri, bazan iya sa facemask ba, a haka ma numfashin baya isata yadda nake so".

Kai ya Jinjina, yana kara jin tausayin ta na kamashi, kaunarta na ninkuwa a zuciyarshi. kudi ya mikamata tayi godiya, ta fito tana daga mai hannu ta shige cikin school.

Koda tashiga class tajima su Umaina basu iso ba, balance tayi a seat, ta ciro tsamiyar birinta tana sha.

Kamar hadin baki a jere su ukun suka shigo, da fara'arsu suka karaso ganganta. Itama da fara'arta ta mika musu hannu suka gaisa.

"Kai wllhi bamuda kirki, ace ayi hutu har a dawo ba'a ziyarci juna ba"

"Bari Fatima nima seda nayi maganan nan a zuciyata, gaskiya ya kamata mu gyara"

"Allah yabamu iko"
"Ameen" duk suka amsa dashi.

Tare suka fito daga hall din, gaba daya duk ta tsargu ji take kamar idanun kowa a kanta yake.

Waro idanu tayi, dasauri ta kai hannu ta tabo Umaina, a mamakance tace, "Umaina! Aesha!! Kunga abinda nake gani kuwa?"

Duk tsayawa sukayi suna kallonta, "A ina?me kika gani?" "Dama Fateema nada aure?"

Saurin kallon Muhibbah tayi, itama ta zaro ido tana murmushin farin ciki "Wllhi na dade ina zargin haka, tun lokacin da sauban ke binta tana mai wulakanci naji suna cewa kar Allah ya kamata tun a lokacin nasa ayar tambaya, kawai dai ban tabbatar ba ne shiyasa nabarshi cewar ko kuma ta kusa aure ne suke boye mana. Masha Allah, Allah ya fito mana da babyn mu lafiya, babu abinda yasani farin ciki a yau kamar wannan lamari. Mun kusa zama mothers". Takarashe maganan tana dage ma Muhibbah gira

Tsaki taja "Ku kam wllhi kuncika sa eyes, yaushe ma cikin yayi girman da har kuka hangoshi, nidai ba wannan ba, mu biya cafeteria nasamu abinda zanci, yunwa nake ji"

"Toh ya muka iya, ai yanzu kinzama a lallaba auren zamani" Aesha tafada tana dariya

Rumaisa tace, "Amma wllhi kun rufemu, bancin cikin nan ya tona da zamu dade bamu gano ba, nidai naga surname dinku ba daya ba nabada cousin sisters ne, ashe kam na cinka".

"Toh yanzu da lokacin sanin yayi ba gashi kun sani ba, Kudai ku fara shirye shiryen suna dan ranan akwai shagali" cewar Aesha

dariya suka yi suka karasa, ta siya meat pie da drink suka jira tagama ci kan suka karasa bakin gate.

Wanka tayi ta dauro alwala tazo tayi sallah, ta nufi dakin Fu'ad ta dauki jallabiyarshi ta zira ta shiga kitchen ta dafa indomie ta cika yaji, tadawo kan kujera ta zauna tana ci, yunwa takeji sosai kamar bataci snacks a school ba. Wayanta ne ya dauki kara tayi picking tareda mannata a kunne.

"Aesha ya akayi ne?"
"Albishirinki?"
"Goro, tasamu kenan? Bani nasha"

"Yanzu Abba ya kira Ummi yake fadamata, Sunje nema ma ya Suhail auren Aunty zeeee, a gurin aka biya sadaki aka gama komai. Har sunyi fixing time".

"Dan Allah fa?"
"Wllhi kuwa, nima yanzu ummi ke fadamun"

"Masha Allah! Kice akwai cin uwar sabada, fatana dai Allah yasa lokacin na haihu".

"Ameen, idan ba haka ba ayi bake" "kedai bari sister cikinan yana maidani baya a abubuwa, yanzu ko kwalliyar arziki baya bari nama hearty, sedai naita fama da jallabiya, ga jallabiyar hearty duk sun mun yawa har suna sharar kasa" dariyar mugunta tashigayi, seda tayi me isarta kan tace

"Sorry maman baby! Gobe ki tambaya Yaya idan muka tashi school se mu biya ki kaima tellor ya dinkamiki dogayen riguna, yadda zakiyi balance. Daga nan se mu biya gidan su Aunty zeeee tunda duk hanya ne".

"Ni wllhi banji haushi ba, kiyi dariyarki kwana nawa ne idan layi naja ze zo kanki. Amma inaji haka zanyi, sedai Idan mun hadu gobe school".

Daga haka sukayi sallama ta ajiye wayan

Ganin 5 tayi ta mike tashiga kitchen, abinci mara nauyi ta dafa mishi ta juye a food flask ta hada mishi zobo ta zuba kankara ciki ta jere a dining, ta nufi dakinta.

Wanka tafito, tayi sallahn magrib seda tayi isha'i ta nade pray mat din. Wardrobe ta nufa ta dauko vest tasa ta kawo wandon da iya karshi cinyanta ta zira, tashafa humra ta kawo turare ta feshe jikinta ta nufa parlour.

Shigowarshi kenan karar takalminta yaja hankalinshi gurin, idanunshi a kanta yaja ya tsaya yana kallon yadda take taka staircase din a yangance, ko ina na jikinta na motsawa.

Suna hada idanu ta saki murmushi ta karasa ganganshi ya wara hannu ta fada jikinshi. Hannunshi ya mayar bayanta ya rungumeta tsam a jikinshi

"Sannu da dawowa my heart" "Kina lafiya maman twins?".

Dariya mara sauti tayi "Nikam rufamun asiri, dayan dai ya ishemu Alhamdulillah" tafada tana raba hug din, ya rike hannunta suka karasa dining.

Yana zama yace, "ko triplet Allah yabamu wllhi ina so"

Hararan wasa ta watsamishi "Eh tunda ba tajikin ka zasu fito ba ai dole kafada haka".

Dariya me sauti yayi "Injiwa yace bata jikina suka fito ba?" murmushi kawai tayi saboda ta gane abinda yake nufi, ta dauki plate tayi serving dinshi ta turamai gabanshi, ta dale cinyarshi.

Abincin ya dibo ya kai bakinta tayi saurin dauke Kai, "no! ni kai na dafamawa, bazan ci ba"

"Shine kika kirani Kikace base na siyo abinci ba, yanzu ke me zakici?"

"Kar kadamu, nikam banajin yunwa, zobon ne dai dazaka taimaka mun kabarni nasha ko 1 cup ne dana kwana inasama albarka". Tafada tana marai raice fuska

"Aa, kigama wayanki, meyasa kafin kisa kan kara baki diba naki ba?"

"Ni ai me sanyin ne ya birgeni" "Hakanan ko zaki hakura, it will affect your baby".

Baki ta tura, a shagwabe tace, "komai baby! tun bezo duniya ba har kafi kaunarshi a kaina"

"Yau naga uwa me kishi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login